Author : Binta Umar Abbale Category : Read Hausa Novels
ni zan tabbatar da cewa karfinsa na d'a namiji ya ninka na baya kafin a yi masa d'aurin goro.
Muna gamawa ya dinga godiya ga Allah har sai da ya ba ni tausayi a d'akina ya tsarkake jikinsa yana fad'in." Amina zan iya mallakawa Malam D'aha rabin dukiyata domin wallahi ya taka muhimmiyar rawa ga rayuwata na riga na sare fa ban ta'ba tsammanin mazantaka zata dawo ba sai gani rass da ni ki gaya mini ya ki ka ji don Allah."
Ya fad'a yana kanne idonsa daya.
Ni ma cikin tsokana na ce." A wallahi ras da kai Baba gaskiya ka yi bajinta Allah Ya sakawa da Malam 'Daha da alheri ya cancanci komai daga wajenka
Ya riko ni yana fad'in." A hankali duk zan biya ki bashin da na ci miki ko?"
Cikin nuna ya yi kokari na ce." Haba ai tun jiya ka biya ni Allah Ya taimake ka, a ai sai da na ce alhamdulillahi."
Ya kuwa fashe da dariya yana sake rungume ni a jikinsa.
Na kudi ne littafin nan kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
To a haka na yi kwana biyu na muna morar juna da nishadi ranar da Hauwa ta kar'bi girki kuwa ya rasa gane inda ba dosa tunda na hau na gaishe da safe ban yadda mun sake had'uwa ba marigaba na yi na shige d'akina na kuma kulle kofata duk da nasan aikin banza na yi yana da mukkulin d'akin amma dai hakan zai fi mini kwanciyar hankali ya kwana shi kadai idan ma ba zai kwanta da ita ba.
Babu kalar rarrashin da bai yi mini ba ta waya na ce ba da ni ba wallahi duk yadda nake jin zafinta a raina ba zan yadda ya had'a kai da ni a zalinceta ba to ballantana ma yanzu da da ta sauko take neman shiri ba na jin haushinta amma fa na ki sakin jikina da ita.
A haka muka cigaba da rayuwar a gidan har ya ha'kura ma duk ranar girkinta baya nema na ban san dai ya suke 'karkewa ba tunda nakan dan ganta jefi jefi ta hau saman a ranakun da take da girkin ta kara ramewa kwarai da gaske ta zama silent ma kamar ba Hauwan da na sani ba mai neman fitina da son kin zaman lafiya. Kuma har yanzu jiya I yau tsakaninta da 'ya'yanta sai dai ido idan ma ta kira su wajenta Minal dai ba ta zuwa Khalil ne koda zai je a cikin fargaba da shakku yake zuwa saboda ta saba dukansa."
"Hauwa Legos za mu tafi ni da matata ban hana ki zama ba tunda kina ganin za ki iya amma wallahi tallahi kada na ji kada na gani akan yarana da wanda ki ka haifa da wanda ma ba ki haifa ba lafiya lau za mu tafi mu bar basu da masu yi musu hidima duk abinda ya faru a gidan nan zan yi kuka dake kuma zan yi miki hukunci mai tsananin gaske."
Ta ce." Hukunci ya wuce wanda kake yi mini a yanzu. Ni ina ruwana da yara kuma abinda ya dame ni daban me zan yi musu ai ni ba azzalima ba ce."
"Na dai gaya miki domin na san halinka ba ki da mutunci babu ruwanki da kowa."
Ta fashe da kuka tana fad'in." To na ji, yanzu sai ka gaya mini menene makomata ai ba maigadi ba ce ni. Wane irin zalinci ne wannan kake yi mini 'kiri-'kiri an raba da ni da yarana suna k'yamatata ai duk tsiya ba za su canza ni ba."
Shiru ya yi mata. Ta cigaba da cewa." Ka gaya mini menene matsayina gaskiya na gaji wallahi, Allah kuma yana ji yana gani."
Ya dube ta sosai tare da cewa." Na yi na yi na ga na ha'kura na yafe miki na kuma sanyawa zuciyata sonki da kaunarki amma kin san Allah babu waje a cikin zuciyata da farfajiyarta Amina ta shimfida mashinfidinta ta zauna daram da can Samira tana da waje amma yanzu Amina ta mayaye ko'ina ita kadai ce a ciki ba kuma na tsammanin har abada wata maccan za ta samu irin wannan sararin."
Ta dinga wani irin kuka mai tsuma zuciya da sosai rai wanda duk wanda ya ji sautinsa sai ya tausaya mata amma a wajensa ma damunsa take yi so yake ta tashi ta fita ta bar masa d'akinsa.
"Ni ba zan ta'ba yi maka irin wannan 'kiyayyar ba domin ko banza mun had'a jini kuma na haihu da kai yara uku duk irin cin fuskar da za ka yi mini da tozarcin da za ka yi mini ba zai dame ni ba, hakkina dai da yake rataye a wuyanka wallahi ba zan yafe maka ba, ka zalince ni kana k'untata mini kuma ba zaka sawwa'ke mini ba idan an yi duniya don manzon rahama ba zan sake nemanka ba."
Ya ce." Hakan ya fi miki Hajiya ai ban hana ki ba idan kina da kwanjin da za ki kwaci hakkin na ki bismillah ai ga ni a zaune."
Ta tashi jiki a sab'ule ta kama hanyar fita kamar zata mutu saboda b'akinciki.
Har ga Allah ba na jin dad'in fuskar gizagon da yake yi wa Hauwa gabad'aya duka kowa ya gane Hauwa bora ce a gidan zaman ha'kuri take yi masu aiki duk sun gane irin zaman da suke yi da ita da maigidan. Abin ya dinga damuna a ganina ai shi ne namiji kuma jagora ce ya ci ace ya tsahirta da wannan tsatstsauran hukuncin da yake yi mata ta dahu lugub ta yi mugun laushi ta kuma tsunduma a cikin nadamar abinda da ta aikata. Shine bai sani ba ko kuma na ce ya sani yana takewa amma mugun zunubi yake nannagawa kansa domin wannan fad'in Annabi Muhammadu S.a.w ne.
Wannan dalilin ya sanya ni ranar da za mu tafi Legos din da daddare na shiga d'akinta na sameta a zaune ita kadai kan gado ta kunna tivi amma gabad'aya hankalinta ma baya kanta kuka take yi tana waya ganin shigowata ta katse wayar tana share hawaye na yi kamar ban lura ba.
Na zauna gefenta muka gaisa na ce." Ya gaya miki Legos za mu tafi gobe ko?''
Ta ce." E, ai jiya mun d'an jima muna magana da shi akan tafiyar taku.".
Na d'an yi shiru Ina nazarin maganarta wadda na tabbatar da cewa 'karya ce kawai wai ita dole sai ta nuna mini suna shiri bayan komai a bayyane yake.
Na ce." Ai da so na yi ku tafi tare idan kun dawo zai sake komawa sai mu je kamar hakan zai fi."
Ta yi ya'ke tana cewa." Duk daya ne Amina ku je tare ni zan kula da yara kamar yadda jiya ya gaya mini cewa ya ba ni amanarsu za ku dawo ku same su lafiya in sha Allahu."
Kamar zararriya haka take magana a tsorace tunda tasan duk abinda zata fad'a ba gaskiya ba ne shiyasa ta kasa had'a ido da ni.''
Na ce." Hakan ya yi Hauwa dama na ce bari na shigo mu yi sallama tunda da wuri za mu tafi wata'kila kina bacci a lokacin."
Kanta a 'kasa ta ce." Hakan ya yi na gode sosai Amina sai kun dawo din.''
Na mike tsaye ina fad'in." To saduwar alheri Hauwa sai mun yi waya." Daga haka ban sake cewa komai ba na kama hanyar fita zuciyata da damuwar halin da take ciki kada fa mutumin nan ya zautata da bak'incikinsa domin duk ta shiririce wallahi........✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK.*
*V-VIP AREWA PEN*
*07084653262*
*139*
Ba na tsammanin ya yi sallama da Hauwa da za mu tafi haka na bi shi ba don zuciyata ta so abinda yake aikatawa ba sai don sanin rashin yadda zan yi da shi. Tunda tsakani da Allah daidai gwargwado yana da ilimin addini ya kuma san abinda yake yi din ba daidai ba ne. Na zura masa Ido kawai domin nasan muddin bai gyara ba Hauwa za ta sake tafiya gidansu mahaifiyarsa kuma ta samu labari anan sai ta gane cewa shima ya fi kyarfinta ba Hauwa ba ce kad'ai mara ji shima lamba d'aya ne.
Zuwanmu legos ya sake haifar mana da nutsuwa da kula da juna da kuma bud'e babin soyayya kamar sabbin aure duk da 'karamin cikin da nake d'auke da shi bai hana mun mori juna ba
a duk lokacin da ya zo wajena da buk'ata irin ta d'abia. Daga lokacin na gama gazgata k'aunar da yake mini cewa babu algus ko almundahana domin duk wani nau'in kulawa ina samu da tarairaya har da kyautar kud'i miliyan biyar ya yi mini yana gaya mini na kara akan kasuwancin da nake yi domin yana hankalce da irin nauyi da d'awainiyar da nake yi a b'angarena.
Na yi godiya sosai da addu'ar k'ara samun budi da fatahi ya ce babu godiya a tsakaninmu a duk lokacin da nake da buk'atar kudi domin yin wani abu da zai kawo mini cigaba zai tallafa mini saboda yana girmama duk wani wanda yake tsaye don dogaro da kansa karin abin kuma ina ko'karin ganin na yi alheri da taimakawa wad'anda na fi su wadata.
Na ji dad'i sosai da sosai dama kuma mun yi magana da anti Yagana akan jari da zan bata ta yi sana'a ta ce mini tana so ta bude shagon jikin gidanta ta fara harkar provision da awo na ce mata harka ce mai kyau sosai kuma za ta samu alheri domin yanzu masu sayar da abinci kayan masarufi sune suke da kudi a hannu. Abinda na yanke a raina cewa ita zan turawa kudin gabad'aya ta fara idan Allah ya sanyawa kasuwancin albarka sai ta zama babbar dila ta bud'e manyan shaguna. Sai dai abinda yake dan damuna shine shin kudin da ya ba ni zai bawa Hauwa ko kuwa. Ina sonsa ba kuma zan yi farinciki da cewa ranar lahira ya tashi a cikin sahun mazan da za a yi musu azaba dalilin fifita bangare daya na daga cikin matansu.
Kuma daidai gwargwado Hauwa ta kar'bi kuskuranta yau satin mu uku a Legos idan ba ta kira ni a waya yau ba to gobe za ta kira ni mu gaisa a sati sai mu yi waya biyar ko hud'u mun yi vidiyo call sau d'aya da ita kuma ban hangi nutsuwa da kwanciyar hankali a tare da ita ba. Abinda na fahimta shine kamar tana kamun kafa da ni akan mijin nata wanda ni kuma nasan ban isa na sanya shi ko na hana shi ba tunda ga abinda ya yi wa mahaifiyarsa na yaudara ya nuna mata kamar ya ha'kura ashe akwai abinda ya ajiye a ransa na ramuwar gayya.
Na dinga nanata masa kan cewa yadda ya ba ni kudin nan Hauwa ya bata hakkinta ne. Na farko da na gaya masa shiru ya yi mini bai ce komai ba ya cigaba da sabogoginsa tunda ya ce mini yana shirye-shiryen bud'e sabon kamfanin na suminti ne wanda suka yi tarayya da yaran Alhaji Amadu abokinsa Salim da Adam da Nusaiba. Yana so ya fara sanya Salim din cikin harkokin da yake gudanarwa domin ya tsaya da kafarsa a matsayinsa na namiji babba da ake sanya rai a nan gaba zai zama wani abu. Mahaifinsa Alhaji Amadu harkarsa kenan sayar da siminti da sauran abinda ya danganci gini gidaje to shine yake so ya d'ora yaronsa a kai.
A k'alla dai sai da na yi masa maganar Hauwa ya kai sau shida tukkuna ya tanka mini da tashin hankali ya rintse idonsa yana gaya mini babu ruwa da duk abinda yake yi na dawo masa da kudinsa idan ba na so tunda bai isa ya yi mini kyauta na ce na gode ba sai na yi masa gyara saboda na mayar dashi jahili Wanda ba shi da addini.
Na kuwa bud'e wuta ni ma na ce ai gaskiya ce kuma d'aci ne da ita ban iya munafurci ba kuma zan yi masa shiru ya danne mini baki da kudi mu zalinci wata ba domin ba ni so na mutu da hakkin kowa.
Ya ce idan akan Hauwa nake yi masa rashin kunya sai ya saketa kowa ya huta.
Na ce masa dama hakan ya yi shi zai kara tabbatar mini da cewa babu wanda ya isa.
Magana ce mai harshen damo ya tsargu sosai daga ranar da muka yi haka ya daina kula ni tsayin kwana uku muka yi ba ma magana gashi Muna kwana a d'aki daya a gado daya sai da ya juya baya ni ma na juya nawa.
A ranar na hud'u ne muna bidiyo call da Hauwa na ce mata ta had'a ni da yaran mu gaisa na yi hakane domin na daidaita alakar da take tsakaninsu..
Aikuwa da azama ta tashi ta fita falo alhamis ce babu islamiyya ta yamma ina zaune ina kallonta ta shiga dakinsu tana Kiran sunan Khalil.
Ya zo ya zauna a gefena ban ce masa komai ba shi ma bai ce mini komai ba amma dai tun shekaran jiya na fahimci jikinsa ya d'an yi sanyi ya rasa yadda zai yi ya rarrashe ni ya kuma nuna zai gyara kuskuransa.
Daya bayan d'aya muka dinga gaisawa suna ta tsalle da dariya mussaman Minal sai washe baki take yi. Ya yi gyaran murya yana fad'in." Ni ba bu wanda yake nema ko?"
Jin muryarsa ya sanya suka dinga kiran sunansa." Baba" Baba.'' Ya kar'bi wayar ya haska musu fuskarsa sai dariya suna kiran sunansa yana amsawa cikin nishadi yana cewa ni babu wanda yake nema na ko?"
Usai ta ce." Baba yaushe za ku dawo?"
Ya ce." Mun kusa in sha Allahu ana zuwa makaranta ko?"
Suka ce "Eh.'' Ya gyad'a kansa yana fad'in." Muna nan dawowa in Allah Ya yarda."
Hauwa ta kar'bi wayar daga hannun Khalil tana hasko fuskarta ta ce masa "Ina yini?'' Ya amsa da sakin fuska har yana tambayarta yara."
Cike da jin dadi ta ce." Gasu nan ai suna ta kewa" a Takaice ya ce." Mun kusa dawowa amma ke ba ki yi kewar ba."
'Yar dariya ta yi kamar an yi mata dole ta ce.'' Sosai na yi kewar ku gabad'aya."
Ya yi murmushi a hankali ya ce." Duk ranar da na yanke mana dawowar zan sanar dake."
Da jin dadi ta furta." To shikkenan." Ya mik'o mini wayata na kar'ba muka d'an yi magana da ita akan yaran sannan muka yi sallama tare da bata sakon gaisuwa wajan masu aikin gidan.
Na kashe wayata na ajiye ban dube shi ba na sake hade raina sosai domin har yanzu ina jin haushin bala'in da ya yi mini sai kace 'yar cikinsa daga kawai an ce gaya kayanka.''
Ya riko hannayena duka biyun na dube shi amma ban saki fuskata ba. Sai ya sanya hannunsa d'aya a kumatuna yana ta'be mini fuska da hanci yana d'an murza mini fatar le'be. Tankwa'be hannunsa na yi ya sake mayarwa ya cigaba da ta'bule mini kumatuna da hanci na sake cire hannunsa a karo na biyu.
Ya sauke ajiyar zuciya a 'dan sanyaye ya ce." To ki yi dariya mana tunda na yi magana da ita?''
Juyar da kaina na yi gefe ban ce masa komai ba. Ya matso sosai yana fad'in. Ki yi dariya my love menene haka umm!
Na ce." Wallahi ka ba ni haushi sosai wai me kake ji idan kana gaba da mutum ne babu kyau fa kuma ba abin burgewa ba ne saboda kawai na baka shawara ka gyara sai ki dinga fad'a mini magana zagi na ne fa kawai ba ka yi ba."
Ya d'an yi shiru na wani lokaci kafin ya furta." Na gyara daga yau idan hakan zai kasance farincikinki shikkenan ko?"
Shiru na yi tare da ta'be bakina ya juyo da fuskata yana fad'in." Mu yi soyayya ko?''
Ban ce masa uffan ba ya d'ora kansa a saman kirjina tare da zagaye k'unguna da hannayensa yana sakin ajiyar zuciya.
Tun daga ranar Hauwa take yi mini vidiyo call a ranakun da yaran suke gida ta had'a ni da su mu jima muna hira. Wannan dabarar ta kara mata kusanci da su kwarai da gaske na ji dad'i sosai kuma ina sa ran nan gaba duka za su manta da abinda ya faru su d'auketa a matsayin uwarsu kamar ni.
Ranar litinin da daddare muka yi waya da ita take gaya mini ai maigidan ya sanar da ita cewa za mu dawo alhamis nan da kwana uku kenan. Na ce mata eh haka ya gaya mini ni ma. Mun jima muna magana akan yara tana labari yanzu Sultan na yarda ta d'auke shi yaran kuwa gabad'aya sun daina gudunta. Cike da jin dad'in hakan na ce dama ai sakarci ne irin na yara cikin ko'karin nuna mata kuskuranta na baya na ce ai shi yaro baya son hantara da kyara duk inda ake dukansa ko aka nuna masa tsana zai guji wajen kuma kwakwalwarsa bata saurin mance abu.
To a daran ranar da za mu tafi sai ga wayar Idiris mijin Sahura muka gaisa da shi sosai ya fara gaya mini dalilin da ya sanya ya kira ni cewa Sahura ta tare a sabon gidanta kuma ya sanya kwa'do ya kulle tsohon wanda na mallaka mata ya yi-ya yi da ita ta bashi aron gidan ya sanya amaryarsa ta ce 'yan haya zata zuba. Da farko ya kama hayar d'aki daya da rumfa mutum biyu ne a gidan da ya kama hayar to dakunan k'ananu ne gashi iyayen amaryatasa sun yi mata kayan d'aki a matse suke a gidan. Shine yake neman alfarma a wajena na yi mata magana ta d'an ba shi aron gidan su zauna shi da amaryar tasa na d'an wani lokaci.
Na yi dariya sosai har sai da jikinsa ya yi sanyi ya dinga fad'in.'' Amina dariya ki ke yi mini tsakani da Allah daidai ne abinda Sahura ta yi mini ai mun zama daya ni da ita kuma ban auri yarinyar nan domin na wulakantata ba Allah Ya kaddara ne kawai."
Na ce." To Idiris gida dai na mallakawa Sahura shi tuntuni ka ga ba ni da hurumin da zan ce mata ga yadda za ta yi da shi tunda yanzu mallakinta ne ai daidai ne idan ta zuba 'yan haya ba wata matsala ba ce."
Ya furta." Ai