Gudun Aure Book 3 Binta Umar Abbale

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Read Hausa Novels

Chapter   27 / 73

78K to 81K   out of 217.6K words

da Alhaji Amadu ya sanya da ya rasu ya aureta ni ma na bashi goyon bayan yin hakan tunda ya gaya mini a rubuce aminin nasa ya bar masa wasiyyar yin hakan. Me ya yi mata da zafi irin haka da za ta yi masa wannan mugun asirin."
Ya ce." Son shi take ainun kuma macace mai zafin kishi abinda na fahimta kenan."
Hajiya Saratu ta ce." Mun gode sosai Malam Ubangiji Allah saka da alheri, yanzu ya yanayin jikin nasa." Ta fad'a tana kallon wajen da yake.
Ya ce." A nan za ku bar mini shi daga nan zuwa sati guda zai warware in sha Allahu rabbi zai tashi ya cigaba da gudanar da al'amuransa."
Alhaji Sa'idu ya ce." Malam abin nan ya jefe ni a rud'ani ba kad'an ba. Ashe akwai irin wad'annan matan marasa Imani da tsoron Allah wallahi idan ana fad'a ba ni gazgatawa."
Ya ce." Akwai su da yawa muna ta fama da su. Ita wannan nata akwai razani k'warai domin tana iya bada jinin adam akan biyan buk'atarta tana aiki da ba'kar iska kuma suna iya neman jinin kowacce irin hallita. Kuma suna nan da yawa. Abinda dai na fahimta ga sha'aninta shine macace mai zafin kishi da mugunta. Kamar yadda na gaya muku da farko ni ba na bugun 'kasa akan neman sanin abinda Allah rufe bai bayyana ba. Istahara irin wadda Annabi ya koyar ita nake a duk dare kan wata mas'ala da aka kawo ta gabana idan na kwanta bacci Allah Ya akan nuna mini abinda yake faruwa. Iya fahimtata soyayyar da take masa ne ya sanya ta aikata masa haka saboda kishin ko bayan ranta kada wata mace ta more shi wannan shine
abinda ya halakar da ita har ta k'etare iyakar Ubangiji."
Hajja na girgiza kai tana fad'in." Kin yi kyawun dan maciji Maryam kin ci amanar mijinki, kin ci amanarmu da muka so ki muka kaunace ki, kuma duk inda muka zauna muke fad'in alherinki. Kin zalinci Tajo da iyalinsa kin mutu ba ki nemi gafara ba zahiri ba mu yafe miki ba maryam "
Tasa gefan mayafi ta goge hawayenta cikin damuwa.
Ya ce." Matarsa ta zauna nan har tashon kwanakin dana d'auka in sha Allahu komai zai wuce kamar ba a yi ba."
Hajiya Saratu ta ce." To shikkenan Malam yadda ka ce haka za a yi Allah Ya saka da alheri amma za mu dinga zagayowa muna duba shi ko?"
Ya ce." Hakan yana da kyau in sha Allahu."
Muka fito daga d'akin a tare da d'an sasaauci ba kamar lokacin da muka shiga ba cikin tsananin tashin hankali.
Hajja ta fara rigima wai itama sai ta zauna. Da kyar da jibin goshi Alh Sa'idu suka rarrasheta kan cewa ta yi hakuri su tafi idan ya so duk bayan kwanaki biyu sai su dinga zuwa.
Sai da suka yi sallar Azhar suka ci abincin suka yi shirin tafiya lokacin malamin ya yi b'aki ba su samu damar yin sallama da shi ba.
Tunda ba kasafai ake shiga wurinsa ba sai ya yi izini.
Da magriba yarinyar nan Hajara ta sake kawo mini dambu cikin langa tana fad'in.Matar yayansu ce ta ce a kawo mini tunda na jiya ya yi mini dadi.
Godiya na yi mata sosai na daure na ci ba don yana yi mini dadi irin na jiya ba sai don korar yunwa. Ba ni son na kwanta ban sake ganinsa ba.
Na fito tsakargidan suna zaune iyayen da yaran. Ban san ina su Sukairaju suke ba nasan dai tunda gidan karamci ne za a kula da su. Ina so ya je ya d'an yi mini sayayyar cikin kasuwa ko dogwayen riguna ne na yi na yi na kira Sahura a waya ta'ki shiga ina so na ce mata ta je can gidana ina da kaya ta debo mini sai ta kawo mini ba a samu network mai karfi a gidan sai an fita waje a tsakargidan kuma idan ya hau sai ya sauka haka yake yi.
Ina tsaye da waya a hannu Malam Rabi'u ya zo yana gaishe ni na amsa cikin dan jin nauyi domin yanayin yadda yake risina mini na sanya ni jin kuny. Ya tambaye ni ko ina da buk'atar eani na ce masa ina son na yi magana da Sukairaju.
Tare muka nufi wajan da aka sauke su. Ya fito ganina a tsaye ya risina na ce." Garin nan babu network mai karfi kasan gidan Sahura ko?''
Ya ce." E, na sani."
Na d'an yi shiru ina kallonsa gabad'aya shima baya nutsuwarsa botiran rigarsa duk sun zube idonsa ya yi ja da alamun bai samu bacci ba..
Na ce." Gidana na can kuntau can ta koma da zama."
Ya gyad'a kansa yana kallona na ce." Ku je tare da ita can gidana na sharad'a za ta debo mini kaya sai ka kawo mini akwai mukkuli a hannunta."
Ya ce." In sha Allahu zan yi wanka yanzu na tafi amma ya jikin oga, mun tambayi Malam Rabi'u ya ce mana da sau'ki ."
Na ce." Da sauki alhamdulillahi amma ku taya shi da addu'a domin ita ya fi buk'ata a yanzu."
Ya ce." In sha Allahu Hajiya amma a wane hali yake ciki yanzu ya tashi ne muna ta so mu shiga mu duba shi ba a ba mu dama ba ."
Na ce." Yana dai kwance har yanzu yadda kuka d'auke shi Sukairaju."
Sai ya yi shiru yana kallona cikin damuwa. Na juya ina fad'in.'' idan ka je ka dawo sai ka sanar da ni."
Na samu Rabi'u a soro a tsaye na ce." Ko za a yi mini iso wurin Malam zan shiga."
Da sauri ya ce. Eh amma yana d'an wani aiki yanzu zuwa an jima idan ya kammala zan sanar da shi sai ki shiga ko"
Na ce." To shikkenan na gode sosai. Ciki na shige gabad'aya jikina a sab'ule har in dai Hajiya Maryam ta samu nasarar nakasta mutumin nan ya tashi da wata tawaya ta cuci mutane da yawa wad'anda suka dogara da Allah suka kuma dogara da shi, halin da Sukairaju ya shiga yanzu abin jajantawa ne da tausayawa, to balle kuma yaransa da wad'anda suke makusantansa....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
🌲🌳🌿☘️

*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


*Gudun aure paid book complete 2k akan telegram normal What'sapp group kuma 1k via 0542382124.... Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*128*
Haka na yi ta zaman jiran ganin Malam Rabi'u ya yi mini izinin shiga d'akin malamin shiru har dare ya yi nisa ban ji daga gare shi ba hakan nan na ha'kura na kwanta a wannan daran ma bacci sai dai b'arawo domin da ya d'auke ni na 'yan mintina zan bud'e ido har dai asubahi ta yi motsin iyalin gidan ya sanya ni tashi na fito da buta cike da ruwa wadda Hajara jiya ta ajiye mini kafin ta je ta kwanta.
Na jima saman abin sallah ina jan carbi bacci ya fara shammatata tunda dama shi ba a cin bashinsa. Na ji maganarsa yarinyar tana fad'in." Ina kwana."
Na bude idona da sauri tare da shi zaune ashe har na kai ga kwanciya kan daddumar ta ajiye mini dogon kofi na kunu da silbar k'osai a gabana ta juya ta fita minti biyar a tsakani ta dawo da wata langa ta ajiye mini da ruwan pure water guda biyu.
Na bude langar dumamen towo ne na masara miyar kuka tana ta k'amshin daddawa da zafinsà nan da nan yawuna ya tsinke na mike na fita.
Yaran gidan da alama sun shiga makaranta domin shiru babu hayaniya kamar koyaushe. Inno na bakin tukunya da kwanuka a gabanta ta juyo tana kallona sai ta saki fuskarta tana fad'in." Hajiya kin fito.
Na daure sosai ganin yadda matar ke ko'karin ganin lallai sai ta faranta mini da kwantar mini da hankali na ce." Eh ina kwana ya hidima na gode sosai Allah Ya saka da alheri.".
Ta amsa cikin dadi tana fadin." Ai na ce Hajara ta kawo miki dumame nasan zai yi miki dadi."
Na ce." Sosai ma kuwa wallahi Allah Ya saka da alheri."
Ta amsa da Amin ya rabbi." Bakina na wanke na koma d'akin zuciyata cike da zullumi haka na ci towon nasha ruwa d'aya na fito tsakargidan shiru matan gidan na d'akunansu.
Can bakin 'kofar fita na nufa na lura wajen akwai network sosai na kira Sahura muka gaisa na ce." Sukairaju ya zo jiya ne?" Ta ce." A a sai yanzu dai ya zo kin ga ina shiryawa wai me yake faruwa ne ya ce mini Yallabai ne bashi da lafiya kuna kauyen Bunkure."
Na ce." Sahura abubuwa da yawa sun faru masu muni ba zan iya ba ki labari a waya ba amma ina cikin tashin hankali mai tsanani"
Ta ce." Idan babu damuwa zan iya biyo Sukairaju ko Amina wallahi hankalina ya tashi ban san a wane hali ki ke ciki ba." Cikin rauni take maganar. Na ji zuciyata ta yi nauyi lallai Sahura masoyiyace ta hakika duk lokacin da na shiga matsanancin hali takan rasa sukuni tun muna 'yan mata haka muke idan daya ya shiga wani yanayi duk sai mu rasa sukuni."
Na daure na ce." Me zai hana ki biyo shi amma bai zama lallai ki samu ganin Yallaban ba tunda ni ma sau daya na ganshi malamin baya bari."
A sanyaye ta furta." Zan dai biyo shi Amina domin ganin halin da ki ke ciki idan kuma ina da sa'a sai Allah yasa a bar ni na shiga na duba shi din."
Na ce." Shikkenan duk abinda ki ka san zan buk'ata ki kawo mini Sahura zama ya kama ni dole."
Ta ce." In sha Allahu."
Na kira layin Anti Yagana cikin sa'a ta shiga na sauke ajiyar zuciya ina jiran ta daga na ji maganarta tana kiran sunana na amsa a sanyaye.
Ta ce." Ya aka yi Amina ya kuke ya yaran fatan kowa lafiya, ki yi hakuri sosai domin ke nauyi ya hau a yanzu ki yi kokarin ganin kin ri'ke yaran nan na Maryam tsakani da Allah domin ki rabauta da lada."
Na ce." In sha Allahu anti Yagana amma akwai matsala fa."
Ta ce." Menene kuma?"
Shiru na yi domin ban ma san ta yadda za a yi na fara yi mata bayani ba.
Ta sake maimaita tambayarta murya na rawa na furta." Maigidan ne ba shi da lafiya anti Yagana ina nan kano wani gari Bunkure ana yi masa magani."
A dan tsorace ta furta." mai ya same shi Amina amma tun yaushe me yasa ba ki gaya mini ba?"
Na ce." Anti Yagana duk yadda za a yi na yi miki bayani ba za ki fahimta sosai ba tunda a waya ne, abinda zan iya ce miki anan shine matarsa ce da ta rasu ta yi masa asirin rai da rayuwa yanzu haka yana kwance sai dai a kwantar a tayar bai ma san a ina yake ba."
Sosai ta ki'dime tana fad'in." Maryam d'in Amina wane irin asiri ne wannan an ya kuwa babu sanya hannun magauta kin san fa ba zai rasa makiya na fili da boye ba don Allah ku daina amincewa da jita jita akan matar nan."
Murmushin takaici na yi tare da fad'in." Ba za ki gane ba ne ai anti Yagana kawai idan da hali ki zo sai ki ji komai ba sharri ake yi mata ba wallahi da gaske ne ga zahiri ya bayyana bayan rasuwarta."
A sanyaye ta ce." Zan zo in sha Allahu tunda jikin baba Sule babu dadi an ce yana kwance a asibiti sai na duba shi."
Na ce." Haka na ji a wajen Hajja ban sani ba wallahi yaushe za ki zo."
Ta ce." In sha Allahu cikin satin nan, zan dai kira ki."
Na ce." To shikkenan anti Yagana"
Sallama muka yi cike da yanayi na damuwa domin abin ya doke ta itama kwarai da gaske.
Wajajen daya da minti goma Sahura ta shigo ina d'aki a kwance na yi muryarta suna gaisawa da matan gida yara suna ta gaisheta sannan suka nuna mata d'akin da nake.
Ina kwance ban motsa ba ta shigo da k'aramar akwati a hannunta..
Na tashi zaune ina kallonta ta zo ta zauna kusa da ni hankalinta gabad'aya a kaina sai na ga ruwan hawaye ya ciko idonta ta ce." Amina ke ma jinyyar ki ka yi ne?"
A tak'aice na ce." Me ki ka gani ne?"
"Kin rame sosai wallahi kin yi wani iri?"
Ban ce komai ba na zuba mata ido ina kallonta ta goge hawayen da ya d'an zubo ta riko hannuna a sanyaye tana fad'in." Menene yake faruwa don Allah ina Yallabai din Amina na ji tsoron ganinki a hargitse cikin k'unci da damuwa."
Na yi ta ko'karin ganin na hana hawayen da yake dannowa zuba amma sai da ya fito ban goge ba na ce." Sahura ashe maganar nan da ki ka gaya mini farkon jin labarin auran Hajiya Maryam a wurin aikinku da gaske ne, ta asirce mini miji ta bi yaranmu daya bayan d'aya ta asirce ko na ce ta tsaface domin haka malamin ya fad'a tsafi take yi."


littafin nan na kudi ne Hajiya kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ta gyad'a kanta cikin al'ajabi tana kallona sannu a hankali na shiga warware mata tun daga farkon lamarin har zuwa yanzu da za a kira da fad'an k'arshe tunda komai ya bayyana.
Ta jima shiru cikin tsananin tashin hankali da mamaki kafin ta ce." Anya matar nan mutum ce Amina wane irin zalinci ne wannan. Mutum ta aure shi da iyalinsa da yaransa saboda tsabar mugunta da son zuciya. Wallahi tunda labari ya fasu a wurin aiki nake ta jin ana magana akanta har na gaza ha'kuri na gaya miki amma kin san abinda hana a gazgata gaskiya ne ayyukan da take yi na alheri da suke a bayyane shine dalili da ya sanya da yawa wasu ba su yarda da wancan zargin ba. Wai akan namiji Amina ki ga mace ta yarda ta mutu a matsayin 'yar wuta domin dai Hajiya Maryam babu abinda zai hana Ubangiji bai hukuntata ba idan an yi duba da irin ayyukan zalincin da ta gudanar a lokacin da take raye."
Na ce." K'warai kuwa Sahura a raina nake jin idan har mutumin nan bai tashi da lafiyarsa kamar da ba to har na koma ga mahallicina ba zan yafe mata ba zan ta yi mata addu'a har karshen numfashina.
Ta ce." Don kin yi hakan ba lefi ba ne Amina ta cuceku wallahi kuma ta cuce mu domin duka hanyar abincinmu tana ga Allah tana hannunsa babu abinda za mu yi masa sai dai addu'a Allah ya saka masa."
Hajara ta shigo da tire na silba jera da kwanukan abinci ta ajiye a gabanmu ta fita ta sake shigowa da ruwan pure water a leda ta dube ni tana fad'in." Hajiya ruwan da ki ka ce a dora miki ya yi har na kai miki bandaki."
Da kulawa sosai na ce to na gode kwarai Hajara Allah Ya yi miki albarka."
Ta juya ta fita da sauri. Na dubi Sahura ina fad'in." Akwai brush a kayan ko?" Da sauri ta ce." E a kwai na tsaya na sayo."
Ta fito mini dashi tare da matsa mini abin goge bakin da sabon soso da sabulu na kar'ba na fita
Sai da na fara wanke bakina tukkuna na shiga bandakin tsaf da shi cikin tsafta duk da na gargajiya ne ba zaka taba ce wa na had'aka ba ne suna da tsabta da kula sosai kuma sun horar da yaransu aiki da tarbiya."
Sai bayan la'asar tukkuna Sahura ta yi shirin tafiya ba tare da ta samun ganin Yallabai din ba Sukairajun dai shine ya mayar da ita bai dawo ba sai bayan ishai.
To a washe garin ranar da Sahura ta zo su Hajja suka sake zuwa tun safe haka muka yini tare da su a wannan karon ma ba su samu damar ganinsa ba haka suka hanya suka tafi cike da matsanaciyar damuwa.
Kwanaki hud'u yana kwance shi ba mai rai ba shi ba matacce ba numfashi ne kadai ke nuna tabbacin da rai a gangar jikinsa na shiga na gan shi da safe amma ban iya zaman minti biyar a d'akin ba na fito 'kafafuna suna rawa a ranar kuwa

27 / 73