Author : Binta Umar Abbale Category : Read Hausa Novels
zalika yarinyar mutane ma da ya auro bata ci ba ya tafi yana kaiwa matan banza shiyasa tunda ya yi auran nan kamar na sani ban sake ba shi kaina ba."
Na ce." Lallai akwai buk'atar ki sanya ido akan Idiris Sahura kada kishi ya sanya nan gaba ki yi nadama idan ya kasance Idiris ya fad'a harkar bariki kina da kamasho tunda ke kin San wanene shi gashi kina ba ni labarin irin durzar da yake wa yarinyar mutane yanzu da babu ita ai zai sake tsunduma tunda ke kin daina ba shi kanki. Haihuwar da ta ratsa tsakaninku ta wuce komai."
Ta ce." Haka kowa yake cewa Amina amma bari kiji wallahi yadda Idiris ya cire kawaici a kaina ya gwada mini rashin Imani babu wani dalili da zai sanya ni don ya shiga matsala a yanzu na damu. Na gaya miki fa yanzu ko ya sake ni ba ni da damuwa Allah ya yi mini rufin asiri ina da matsuguni da 'yan kudi a asusuna zawarci zan buga mai kasafiti Hajiya."
Dariya ta kama ni na ce." Sahura ki dai yi tunani akan maganata ki yi hakuri ku samu daidaito don Allah ko saboda yaranmu babu dad'i Idiris ya lalace dole za a danganshi dake ace tsohon mijinki ne kuma uban yaranki.
Ta furta." Ai ko zamu daidaita ba dai yanzu ba Amina wallahi yadda ya gumami ni ba'kinciki in sha Allahu masifar da zai tsinci kansa sai ta shige wadda ya jefa ni."
Da haka muka yi sallama tunda duk ta inda na biyo sai ta doje ta nuna yanzu ba lokacin da ya dace a ce ta tausaya masa ba ne.
A daran ranar da muka yi wannan tattaunwar da Sahura bayan isha'i muna falon gabad'aya masu aiki da yaran ban da Hauwa da yake girkinta ne tana ta kai wa da kawowa daga kasa zuwa sama. Na ce da Baba Tabawa ta kawo mini abinci. Towon shinkafa suka yi miyar taushe da tantakwashi. Sun jima ba su miyar taushe a gidan ba wannan dalilin ya sanya mini mugun mararin son cin towon. Ina ci muna hira da su jefi-jefi Hauwa ta sakko kai tsaye dakinta ta nufa sai ta d'an tsaya tana kallona kafin ta ce." Maigidan fa baya jin dad'i Amina."
Gabana ya buga da k'arfi a take a lokacin na ji abincin ya fitar mini daga rai Allah ma dai ya sa na ci da yawa. Na daidaita yanayina sosai kafin na ce." Mai yake damunsa?"
Ta d'an ta'be bakinta tana fad'in." Ciwon kai na ji yana gayawa likitansa yanzu tun rana da shi dai ya yini na yanzu ya yi tsanani ko 'daga kansa baya iya yi yana kwance."
Na yi 'kasa da kaina abin har ya kai ga kwanciya irin haka wace irin matsala ce take damunsa da har zai ajiyeta a ransa ta haddasa masa ciwo.
Ta shige dakinta ba ta sake yi wata magana ba.
Kafin na haura saman sai da na sanyo hijabi jin cewa likitansa yana kan hanya
Yana kwance shar'be a gado ya dafe kansa da hannunsa.
Na zauna gefansa jiki a mace ina fad'in." Baba baka da lafiya ashe?"
Ya dube ni da gefan ido ya furta." Ciwon kai ne Amina yanzu nan ya sake tsananta."
Na ce." Kana jin sa ashe a hankali a hankali ba ka yi magana ba sai yanzu da ya kwantar da kai an ta'ba wasa da lafiya ashe."
Ya yi shiru bai ce komai ba. Na gyad'a kaina ina fad'in." Ni ba yarinya ba ce duk yanayin da kake ciki ina hankalce ban buk'aci dole ka gaya mini sirrinka ba wata'kila baka son kowa ya sani shiyasa ka yi shiru abin yana cin ranka ya kamata a ce ka sassautawa kanka dalilin gudun faruwar mummunar abu akwai shekaran girma a tare dake kuma idan ban manta ba kana da hawan jini bai kamata a ce ka dinga ajiye wani abu a cikin ranka ba. Amma ina so na gaya maka cewa ko ka fad'a ko baka fad'a lallai kana cikin damuwa domin gabad'aya al'amuranka sun canza a tsukin lokacin nan."
Ya yun'kura ya tashi zaune yana kallona da wani irin yanayi ya ce." Lallai ina cikin damuwa Amina amma ban san yadda zan yi na fitar da kaina daga cikinta ba."
Na ce." Duk abinda ya yi tsanani ai maganinsa Allah kaine ka ke da hanyar fitar da kanka daga cikinta idan ka sanya hakan a ranka."
Ya gyad'a kansa yana kallona amma bai ce komai ba.
Jikina ya sake yin sanyi na d'an riko hannuna a hankali na ce." Idan babu takurawa ka gaya mini damuwar da take damunka ko Allah zai sanya ina da shawarar da zan baka."
na kudi ne wànnan littafin Yar uwa don Allah a duk inda za ki gan shi kada ki karanta sai kin biya ni hakkina.
Ya furta." Malam 'Daha ne ya ba ni 'yarsa amma ban san ko wacece daga ciki ba, kin san dai gidansa cike yake da yara ko?''
Kunnena ne ya yi dumm! kamar irin kumfar sabulu ta shiga ciki na ji ya sake rintse hannuna yana fad'in." Ban zan iya bijire masa ba Amina wallahil-azim ba zan 'ki 'karbar tayinsa ba."
Na zuba masa ido kawai ina kallo bakina ya yi nauyi na rasa ma abinda zan ce saboda zahiri na 'kadu da jin maganar nan gidan Malam D'aha babu wata cikakkiyar budurwa duk matasa ne kuma mafi akasari daga sassan gidan suke fitowa alamu sun nuna wasu daga ciki 'ya'yan yaransa ne irinsu malam Rabi'u. Jikokinsa kenan
Hajara ita ce kadai 'yar budurwar da ta fara tasawa tunda ta fara 'kirgar dangi sun yi cibir-cibir a cikin riga ba ma su kai a sanya musu rigar mama ba.
Na daure na ce." Ai duk babu wata budurwa cikakkiya a gidan Malam D'aha."
Ya ce." Akwai uku da bai aurar da su ba sauran jikokinsa ne a cikin ukun ya ba ni d'aya ban santa ba ni ma."
"Hajara ce abinda zuciyata take raya mini kenan. Muka yi shiru ni dashi muna duban juna Hauwa ta shigo sanye da hijabi a jikinta ta same mu a haka mun k'urawa juna ido ga hannuwanmu a ri'ke
ta kasa jurewa muryarta tana rawa ta ce." Ka ce baka da lafiya maganar duniya na yi maka baka tanka mini ba kana kwance kana jina yanzu gashi kuma yanzu na shigo na gan ku ma'kale da juna wallahi Amina ku ji tsoron Allah hakkina ba zai bar ku ba ba zan ta'ba sahale muku ba a ranar lahira."
Na juya da mataccen jiki ina kallonta. Wata gaud'iya da ita ana ga gabas tana ga yamma. Karamin tsaki kawai na ja ban ce komai ba na cire hannuna daga cikin nasa. Ya sake kamowa yana fad'in." Kin ce akwai shawarar da za ki ba ni ko Amina wallahi ba ni son auran da ake ko'karin ma'kala mini abinda yake zuciyata na gaya miki tunda kin matsanta ki ji kada ki d'auki maganata a matsayin dad'in baki a yanzu dai babu ajandar aure a tare budurwa ko bazawara kin san matsayin Malam D'aha a wajen mahaifina da ni kaina da irin gudumuwar da ya ba ni a rayuwa abu ne mai wahala na yi ja'in'ja akan wannan umarin nasa Amina
ba ni da mafita ne dole na gaya muku halin da ake ciki daga yau zuwa ko wane lokaci za ku iya jin labarin d'aurin aurena domin gidan Malam D'aha ba'a bida'a idan an d'aura aure yarinyar zan je kawai na d'auko."
Abin ya daki Hauwa k'warai da aniya ta zuba masa ido cikin k'aduwa tana fad'in." Aure da gaske za ka yi to kai yaro ne da za ka ce an ma'kala maka daman can kana so akwai wanda ya isa ya yi maka dole ne? ashe kana da lafiya ta mazantaka da kuzari irin na maza tunda har zaka iya 'karbar auran budurwa 'kan'kanuwar yarinya.
Ya 'kankance ido yana fad'in." Ba ni son hauka da rashin hankali Hauwa ki kiyaye ni wallahi kada ki sake ki fusata ni."
Ta ja tsaki ba ta sake cewa komai ba ta kad'a kanta ta kama hanyar fita.
Ya ja tsaki tare da sake juyowa gare ni yana fad'in." Ya za mu yi ne Amina ta ina kike ganin zan warware wannan mas'alar da na shiga.
Ajiyar zuciya na sauke a nutse na furta." To ai ni ban isa na hana umarinin Ubangiji ba. Na d'auka wata matsalar ce ta daban shiyasa ka ji na ce maka ka gaya mini zan baka shawara. Lamarin aure kuma ai yin Allah ne Amina bata da hurumi anan sai addu'a da fatan alheri."
Ya ri'ke hannuna sosai yana fad'in. " Kin amince a yi? kina ganin babu komai idan an yi din?"
Na gyara kaina gabana na dokawa na ce." Idan ma da matsala ai ban isa na sani ba tunda ni hallitar Allah ce a karan kaina ban san abinda zai same ni daga yanzu zuwa gobe ba kaga kuwa ba ni da abinda zan ce anan kamar yadda na fad'a da farko Allah Ya sanya alheri yasa abokiyar arzikinka ce. Wannan shine kawai addu'ar da zan yi."
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta.'' Ban za ci zan samu ha'din kanki cikin d'an'kankanin lokaci ba Amina. Lallai na yi sa'ar samun mace tagari mai ko'karin ganin ta samar mini da nutsuwa cikin kowane yanayi na gode sosai Allah Ya yi miki albarka."
A tak'aice na amsa da amin ina ta kallonsa ganin ya wartsake idan ma da ciwon kan to a kashi dari hamsin ya sauka sai abinda ba za a rasa ba.
A haka likitansa ya zo ya dudduba shi yana fad'in jininsa ya hau kad'an shine kuma ya haddasa masa tsananin ciwon kai da jirin da yake ji ya zama dole ya daina tsanantawa kansa damuwa.
Ya tashi ya fita minti talatin a tsakani ya dawo da magunguña a leda ya yi bayanin yadda ya kamata a ce an yi amfani da su daga yanzu. Ban sauka ba sai da na tabbatar da cewar ya ci abinci sosai sannan ya sha maganin a gabana tukkuna na yi masa sallama na sauka gwiwata kamar an rad'e da gora saboda mugun sanyin da jikina ya yi jin wannan batu......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124.....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*143*
Ni jin wannan batu gabad'aya ya kassara mini dukkanin karsashin jikina. Na yi shiru zuciyata na harbawa tare da tariyo maganganunsa akan auran da yake yi wa lak'abi dana cushe. Ba ni fargabar ya yi aure a gidan nan saboda na riga na san matsayina a zuciyarsa idan ma yana amfani da kalaman yaudare wajen nuna mini soyayya tabbas to akwaita a zuciyarsa ko da kuwa da akwai matsugunin wata. Matsalar dai anan 'kankanuwar yarinyar da zai auro ya kawota cikinmu shine tashin hankali tun lokacin da yake gaya mini zuciyata take hasaso mini Hajara ce domin kaf yaran da suke gidan Malam D'aha itace a samansu ba su kaita girma ba ita zamu kira da budurwa amma a rashinta domin yadda take a tsamure a tsuke sai uban tsayi bana tsammanin ta fara jinin al'ada.
Lallai wannan babban lamari ne da ya tunkaro mu gabad'aya domin idan har Allah Ya kaddara auran nan to sai da ya rainin yarinyar nan duk da matarsa ce ba zan yarda ya haye musu kan d'iya ta had'u da lalaruba. Malamai suna ta wa'azi kan cewa iyaye su daina irin wannan auran na cutarwa to da haka za mu kira shi ma a wannan zamanin domin dai muddin a fake da cewa sunnar manzon rahama ce yin haka to akan jefe yara cikin halin damuwa a gaba. Dalili zamanin Annabi Muhammadu S.a.w daban yake da wanda muke ciki a yanzu idan an fake da cewa za a yi koyi da shi akan abinda ya wanzar lokacin zamaninsa ana samun matsala dalili shi daban yake cikin duk wata hallita. Kai tsaye a yanzu ba zan zargi Malam D'aha da cewa shima kwad'ayin dukiya ne ya sanya shi daukar yarsa 'karama irin wannan ya bawa tsoho wanda idan da ya yi aure da wuri babu shakka ya kusa jika da ita domin dai Hajara ta wuce a ce 'yarsa idan auransa na fari ya d'ore duk da lokacin ma sai da ya zama tuzuru ya yi ya kuma fara da mace to ba ba shakka Hajara sai dai ta zo a jikanyarsa ta farko. Fisabillahi Malam D'aha bai dubawa yarinyar nan ba kuma ya tauye mata rayuwa ko da Alhaji Sulaiman ya yi aure eh tabbas budurwa ce amma wadda ta jima bata auru ba domin na ga calendar su shi da ita ta girmi Hajara sosai a k'alla ita za ta yi irin ashirin da biyar zuwa da bakwai. To idan ya zame masa dole auran budurwar sai ya nemi mai k'wari ba irin Hajara ba wadda yanzu ne take tasowa ba tasan ma menene auran ba. Na yi zaman sati daya a gidan na kuma fahimci cewa gidan na da tarbiya masu wadatar zucci da malunta ina ganin saboda kwad'ayin dukiya ba zai d'auki yarsa ya bayar ba sai don wani dalili nasa ko hango nagarta da tabbacin za a ri'ke masa 'yarsa a kula da ita. Wannan shine abinda na fi gazgatawa daga gare shi ba wai ya bashi ita ba ne domin ganin yana da kudi da rufin asiri.
Kwanan tunani da zullumi na yi kan wannan lamari gabad'aya kaina ya d'aure na rasa yadda zan yi na auna mas'alar a sikeli domin hango cancanta da dacewa.
Ina fitowa daga wanka kira ya shigo wayata dake ajiye a gefan gado na kàrasa da sauri na d'auka. Baban Saude ne gabana ya yanke ya fadi domin ban kawo komai ba sai mutuwa. Shikkenan Dada ta rasu ban je na dubata ba Allah ya raba ganawarmu.
Hannuna na rawa na sanya wayar a kunnena cikin mutuwar jiki da saranda na yi sallama. Ya amsa da dakakkiyar muryarsa wadda hakan bai zame mini abin mamaki ba tunda sanin da na yi masa mutum ne tsayayye ba komai ne yake gigitashi ba ko da kuwa mutuwar ce.
Murya na rawa na gaishe shi ya amsa a dakile kafin ya rufe ni da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita. Na yi kasa'ke da waya a kunnena ina sauraransa domin dai abinda ya tsana kenan yana magana a katse shi shiyasa na bari sai da ya tsahirta tukkuna gabana na dokawa na furta." Baban Saude Hauwa sharri ta yi mini wallahi tallahi ina ko'karin ganin na kiyaye shiga hakkinta wallahi Allah d'aya kenan ban san abinda yake tsakaninta da mijinta ba. Bana ta'ba yarda ranar girkinta na 'kebe dashi na tsayin lokaci ko jiya ma ita ta gaya mini bashi da lafiya na hau domin duba shi kuma babu abinda ta same mu muna yi a zaune kawai ta same mu."
Ya furta." Na dai gaya miki ki kula idan har don kina ganin kin fi ta fada a wajensa kuke had'e mata kai har ku dinga shiga hakkinta ki daina domin ba ni so a ce ranar lahira kun tsaya a gaban Ubangiji ana yi muku hisabi yadda ta kira ni tana kuka haikan shine abinda ya daga mini hankali Amina kada ki zalinci duk matan da zai kawo gidanki, ki yi iyakacin bakin kokarinki wajen ganin kin fita hakkin kowa ki kuma nuna masa kuskuran abinda yake aikatawa. Kada don kin samu dama a wajensa ki cutar da wata mu maza ba mu da tabbas watarana zai iya juyowa kan ki hakkin wad'anda ki ka zalinta ya fara bibiyarki. Ko kin ta'ba jin an ce gaskiyar mutum ta k'are. Idan kina da gaskiya da gudun hakkin wani sai ki ga kin zauna lafiya a duniya domin Allah ba ya shiri da mai zalinci.''
Ya kai k'arshen maganar da tausawa.
Na ce." In sha Allahu Baban Saude zan kula na gode sosai Allah Ya kara girma."
Ya amsa da "Amin Ya Allah."
Muka yi sallama. Na ajiye wayar ina dubawa. Lallai Hauwa bata da mutunci yau kuma abinda ta shiryo mini kenan.
Kayana kawai na zura zuciyata na tsalle na fita falon shiru ina d'an jiyo maganganun yara a d'akinsu suna shirin makaranta.
Na buga kofar dakinta da d'an karfi na ji tana fadin." Wanene?" Kai tsaye na ce." Ni ce"
Ta d'auki murya bata sake magana ba jim kad'an ta bude tana sanye da kayan bacci cotton riga da wando da hula.
Muka had'a ido ganin yadda fuskata take a murtuke ya sanya itama ta daidaita yanayinta. Na ce." Daga yau sai yau kada jahilar k'wakwalwarki ta yi miki tunanin kiran wayar wani daga cikin alhalina ki kai masa 'karata Hauwa wai shin me na yi miki ne? Ni ce matsalarki ko mijinki Hauwa? me yasa ki ka sanyo ni a gaba ki ke haka kan ki sukuni a kaina me na tsare miki na fad'a da babban sautin da kowa zai ji na ce.'' Yau sai kin gaya mini abinda na yi miki a gidan nan Hauwa ashe rashin mutuncin na ki har ya kai ki kira Baban Saude ki juya masa magana a kaina ni na yi mini ko mijinki da za ki nemi ki hada ni da iyayena."
Kada ki karanta wannan littafin ba tare da kin biya ba na kudi ne
Babu damuwa a tare da ita ta furta." Abinda ki ka yi mini a bayyane yake Amina tunda kin buk'aci ki sani ai zan gaya miki ko kin zata tsoronki nake ji ne? "
Ta fito falon sosai ta tsaya daf da ni ta cigaba da cewa." Na gaji da wannan kisan mummuk'en da ki ke yi mini a gidan nan, na gaji shiyasa na sanar da Baban Saude tunda na lura shi kad'ai ne yanzu zai gaya miki ki ji kuma ba mazalinci ba ne, kin had'a kai da miji kun ware ni kuna nuna mini cewa ni ba matar gida ba ce. Kin kanainaye shi da kissa kin hana shi yin mu'amula da ni, me yasa zan yi shiru a kan ki Amina ai ba ki isa ba wallahi dole ne na gayawa magabatanki."
Na ce." Banza shashasha sakarai kawai to