Author : Binta Umar Abbale Category : Read Hausa Novels
Amin Ya Allah. Ta cigaba da cewa ita da mahaifiyarta suka buk'aci hakan ga ta a zaune hakane Uwani?"
Ta amsa "Hakane Hajja."
Sa ta cigaba da cewa." Hauwa a cewarta tana jin kunyarku ke da Tajo bisa abinda ta yi na rashin kyautawa a baya ta yi nadama ta kuma gane ba daidai ba ne. Ta ji labarin ibtila'in da ya samu mijinku shine ta ce tunda ke kina tare dashi kina jinyarsa ita sai ta koma ta kula da yaran. Jin hakan ya sanya na bada goyon baya domin yaran za su samu kulawa sosai kuma za su ji dad'i akan ace suna tare da masu aiki."
Falon ya yi shiru ina sauraran ta cigaba da magana domin nasan ba ta gama ba. Can kasan zuciyata kuma ina mamakin ta hanyar da suka b'ullo wato dama mafaka suke so su samu tunda ta fara gane kuranta tana bibiyarsa yana shareta da ya kwanta ciwo kuma ta tabbatar ina tare da shi ta san yara sun dawo hannuna sai ta lallaba ta koma ta fake da cewa za ta kula da yara da haka suka tsara Hajja har ta amince take kuma ganin sun kyauta sun yi tunani mai kyau.
Babu wata sha'kuwa tsakanin Hauwa da yara har na cikinta domin ba da ita suka rayu ba abinda yake tsakaninsu tsawa ce da hantara wataran har da duka. Khalil dai yana shan rank'washi ko ta kwashe fuskarsa da mari na gani kusan sau biyu. To balle Minal ma da bata son zuwa wajenta. A ganina babu wata mafificiyar kulawar da za su samu a wajenta baya ga ta Mairo da Taburni tunda da su suka saba kuma duk wata nau'in kulawa suna samu a tare da su.
Ta cigaba da cewa." A wani zuwa da Tajo ya yi nan farkon rikicinsu ya ce mini ya mayar da ita kusan wata hud'u kenan har yanzu tana a matsayin matarsa a yadda na sani dai ban san kuma shi abinda yake zuciyarsa ba sai ya shigo sai na tambaye shi."
Ta Nisa kafin ta cigaba da cewa." Shekaran jiya mun jima da ita a waya sosai na ja mata kunne kada na ji kada na gani ba ni son wata matsala ta sake faruwa idan ta shure maganata zan cire hannuna a kanta kuma zan bawa Tajo za'bi zama da ita ko rabuwa."
Inna Uwani ta yi k'asa da kanta cikin damuwa Amma ba tofa ba.
Na ce." In sha Allahu ma babu abinda zai sake faruwa Hajja, ni da ma tsakanina da Hauwa ai girmamawa ce wallahi kuma na ji dadin wannan sulhu wanda da tun farko ta yi aiki da shawarata hakan ba za ta faru ba, ina yi musu fatan alheri."
Ta ce." Ba wai ina goyon bayan Tajo ba Uwani ki zauna ki yi nazari da tsinkaye anan Hauwa ta yi daidai na yi shiru ne kawai ba wai don abin bai yi mini ciwo ba. Ban isa na bata umarni ta bi ba na sha gaya masu daga ita har abokiyar zamanta a duk lokacin da suka samu sa'bani da magidansu su sanar da ni, amma saboda ta raina kowa ta haihu da d'anyen jego ta tafi ke kuma ki ka bata wajan kwana har kina aiko mini da sa'ko iyayen Hauwa sun ce a ba su takarda domin su ga sheda."
Inna Uwani tasa kuka tana fad'in." Hajja ni kaina Hauwa taurin kanta ya ishe ni wallahi nasan bata kyauta ba kuma b'acin rai ne ya sanya na fadi haka abinda ya kara dagula mini lissafi yadda ta ce mini yana dukanta kuma ya mayar da ita koma baya a gidansa har hakkinta na aure baya bata shine hankalina ya tashi."
Hajja ta harareta tana fad'in." Baya bata hakkinta na aure a ina ta samu wannan cikin da ta haife wad'ancan yaran biyu Khalil da Minal a ina ta same su?"
Inna Uwani ta yi shiru tana jan hanci tare da goge ragowar hawayen idonta.
Ta gyad'a kanta tana fad'in. "Ai ban 'ki komawar ba domin ban san abinda Allah ya lullube ba, shiyasa tun da farkon faruwar lamarin na tura shi can bauchin domin a samu sasanci ba ni da niyyar raba uwa da yaranta tunda ni ma babu wanda ya yi mini haka. Nasan soyayyar da take tsakanin iyaye da yaransu me yasa na yi masa fad'a sosai a lokacin da ya kwashe musu yara ya kaiwa Hajiya Maryam. Ba daidai ba ne amma dole a wannan ga'bar mu yi masa uzuri tunda ba a hayyacinsa yake ba har yaran gabad'aya nasan yanzu ko giyar wake ya sha ba zai k'ara yarda ya d'auki d'ansa da'ya ya kai wani wajen ba sai dai idan ya zama dole."
Ta girgiza kanta tana fad'in." Hakane wannan hakane."
Ta ce." Ki ja mata kunne kwarai idan za ta ji tunda ta fi karfin ki ba tun yau ba na fahimci haka wannan ya zama na farko ya zama na k'arshe ta zauna ta kula da yaranta."
Ta ce." Ai tun a gida na yi mata fad'a sosai Hajja ai abinda ya fi alheri shine ta koma cikin yaranta domin duk wanda zai rike maka yara ba kamar uwa ba."
Hajja ba ta ce mata komai ba ta juyo gare ni tana fad'in." Ya gaya mini cewa gobe za ku tafi hakan ya yi ba zan dakatar da shi ba domin nasan yana da hurd'odi da yawa. Ki yi hakuri ki 'kara akan wanda ki ke yi Amina ni dai babu abinda zan yi domin na saka miki alherin da ki ka yi mini sai da na ce Allah Ya yi miki albarka ya albarkaci zuri'arki ya sa su zama abin koyi da kwatance a duniya."
Na ce." Wannan addu'ar ita kad'ai ta isa Hajja ai ban yi domin a gode mini ba ni ma kaina na yi wa kuma in sha Allahu ni dai daga bangarena zan yi iyakacin bakin kokarina wurin ganin mun samu zaman lafiya da juna."
Ta saki fuskarta sosai tana fad'in." Na gode sosai Amina Allah Ya yi miki albarka na gode."
To a daran ranar ta kira shi ya je ya same ta nasan dai ba zai wuce maganar da za ta yi masa ba kenan. Ko da ya dawo ya same ni tare da Yusi muna bankawana ban ga wani can ji a fuskarsa ba ya zauna cikinmu ana hirar da shi har yana tsokanar Yusi ya zama saurayi ko yana da budurwa ne shima. Abinda ya assasawa yaron tashi ya fita kenan yana sinne kai shi kuma sai dariya yake masa yana fad'in." Ta'b wa ya ga su wa'e da suruka humm tsufa ya zo garinsu wata mata."
Na gane da ni yake na share shi ban tanka masa ba ya cigaba da cewa ni kuwa kin ga ko yanzu zan iya auran budurwa ba ni da matsala.
Ban kula shi ba na tashi na shige band'aki ina murmushi wani sa'in idan yana barkwacin har mamaki yake ba ni.
A wannan daran kafin mu kwanta ya kar'bi details din Sunusi dubu dari da hamsin ya sanya masa ni kuma na sa hamsin a kai ya zama dubu dari biyu ta What'sapp na yi masa magana na ce ya duba sako an tura masa.
Ya kuwa kira ni a waya ya yi ta godiya kamar zai ari baki.
To duk yadda na kai ga nok'ewa a wannan daran kasawa na yi domin ha'din kai na bashi zuciyata na dokawa muka jima cikin wassanin soyayya ya yi kokari kwarai ta wannan hanyar ya samar mini da nutsuwa kafin ya nemi hanyar biyan tashi buk'atar cikin k'ankanin lokaci yana farawa ya kammala. Akwai sha'awar sosai da mazantakar amma karfin da za a jima ana yi ne babu wannan kuwa babbar matsala ce.
Da sassafe muka d'auki hanyar abuja bayan duka mun yi sallama da wad'anda suka dace....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *GUDUN AURE PAID BOOK 1K ON TALGRAM KO KU GARZAYA AREWA PEN.*
*0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*133*
Yadda yaran suka dinga tsalle da murnar ganin Babansu haka ni ma suka yi mini kamar dama can akwai tsananin sabo a tsakanina da su. Minal dama can 'yar gidana ce kai tsaye wajena ta taho da dan gudunta tana tsalle da dariya na kuwa sunkuya na sunkuceta duk nauyinta ni ma ina dariyar murnar ganinsu tsaf cikin annashuwa. twins kuwa dama wajan Babansu suka nufa ya rirri'ke hannayensu shima fuskarsa kamar gonar addu'a Allah ne kad'an yasan yadda yake ji a cikin ransa ganin ya dawo cikin ktoshin lafiya domin cigaba da rayuwa da su. uwa uba kuma samun iyayen rainon da suke tsananin kula da su tamkar suna rayuwa da iyayensu. Yarinyar ta dabaibayeni sosai ta sa'kalo wuyana da hannayenta tana ta dariya duk acikin farincikin ganin mun dawo. Ina nishi sosai gajiyar tafiya da yanayin jikina ga kuma nauyinta na fara ko'karin sauketa k'asa ina kallonsu Mairo da suke tsaye suna ta dàriya na ce." Minal ta kara girma da nauyi a 'yan kwanakin nan Mairo me kike bata?''
Cike da kulawa ta sinne kai ta furta. " Abiñci take ci ta k'oshi Hajiya bayan haka babu komai tunda ita dama can ba gwanar ciye ciye ba ce."
Shiru na yi ban ce komai ba na sauke yarinyar a k'asa tana riko gefan hijabina ina jin Mairo da Taburni suna yi masa sannu da zuwa. Baba Tabawa ta fito daga cikin fuskarta a washe take fad'in." Sannunku da zuwa Alhaji sannuku da dawowa."
Ya tsaya suka gaisa sosai kafin ya kama hanyar samansa yaran suka bi shi a baya Khalil da twins ita Minal tana tare da ni ta ri'ke mini hannu tamau.
Muna magana da Mairo Hauwa ta fito daga d'aki muka kalli juna babu yabo babu fallasa ta furta." Kun dawo kenan?"
A tak'aice na ce." E, mun same ku lafiya?'' Ta amsa da 'Kalau.' Ta nemi kujera ta zauna na d'an dubeta ta gefan ido ta k'ara ramewa abinka da mara jiki dama ai zaman gida sai dole ta so ta yi wa kanta ganganci. Ta yi kwalliya sosai wata'kila ta tar'bar angon nata ne naga har da lalle ja da ba'ki irin wanda yake so ya yi kyau sosai a farar fatar 'kafafu da hannayenta.
Na kama hanyar d'akina jikina a galabace Minal tana take mini bayana.
Ban yi wanka ba tukkuna sai da na yi sallar magriba na fito na sami yarinyar ta bingire a gado bacci ya d'auketa. Ba ta yi wani murnar ganin uban ba kamar sauran sau daya ta je wajensa ya d'an ri'ke ta kamar yadda ya yi wa sauran ta dawo wurina. Kamar yadda twins din suka yi mini.
Sai da na shirya tukkuna na tashe ta muka fita a tare babu kowa a falon. Kai tsaye d'akin ya yaran na nufa Mairo tana ta fama da su Khali na can gefe yana rubutu a littafi.
Ta burni kuma tana gyara musu wardrobe.
Na ce." Mairo a bawa Minal abinci." Da sauri ta ce." To ta janyo hannunta zuwa ciki. Usai ta biyo bayana muka zaune kujera a tare jim kad'an itama Hassanar ta fito na daga kai na dube su a nutse tare da fad'in." Kun yi sallah ko?"
Suka daga mini kai a tare na ce." Abiñci fa?''
Girgiza kansu suka yi. Na d'an 'bata fuska ina fad'in.'' Bebaye ne ku?''
Usai ta ce." Menene Bebaye Mama?"
Sai na fara gwada mata maganar kurame da hannuna da bakina." Aikuwa sai dariya gabad'ayansu suna kallon bakina yadda nake yi. Ni ma na kama dariyar ina fad'in." Bebaye ne masu magana da hannu da kuma gyada kai, ku kam ai kuna da baki ko?"
Da sauri Hassana ta ce." E, wanda muke magana da shi muna cin abinci."
Na ce." K'warai kuwa daga yau idan na yi muku magana ku daina yi mini ta kurame ku bude baki ku ba ni amsa."
Suka ce "to Mama."
Na ce." Aje a ci abinci idan da aikin gida na makaranta a d'auko a yi."
Suka ce "To" a tare da sauri suka ruke hannun juna. Na sauke ajiyar zuciya tare da fad'in." Hassana duba d'akina ki d'auko mini wayata saman gado."
A tare suka nufi d'akin jim kad'an suka fito na kar'bi wayar suke wuce dakinsu.
Ina dubawa na ga miss call Hamusu ya kira ni jim kad'an da fitowa daga d'akin.
Na kira shi bugun farko ya daga muka gaisa yana fad'in." Anti Amina Gwaggo tana ta fad'a wai ba ki sanar da ita cewa Yallabai bashi da lafiya ba. Yau a gidan Hajja ta yini ta sanya ni na kaita muka je muka tarar kun tafi."
Na ce." Wallahi Hamusu ku yi mini uzuri ka bawa Gwaggo hakuri ko kuma idan ka je gidan sai ka kira ni a waya abubuwan ne sai a hankali amma ka ce mata ya ji sau'ki sosai ya warware."
Ya furta." In sha Allahu rabbi."
Muna yin sallama na hangi Hauwa na saukowa daga benansa. Na yi gaggawar janye idona daga hanyar har ta sauko ta iso tsakiyar falon na daga kaina na kalleta duk yadda take ko'karin kalato annashuwa ta ya'ba a fuskarta sai da na gane karfin hali ne kawai ta kira sunana na amsa za ta shiga d'akinta na ce." Ni kuwa akawai maganin maigidan da ake yi masa kullum da daddare Hauwa bari na d'auko miki shi zai yi miki bayani yadda ake yi masa."
Ta ce." To tare da tsayawa na tashi na shiga d'akina na d'auko mata sauran maganin da ya yi ragowa da rubutun ina fad'in zai gaya miki yadda za a yi."
Ta sake cewa ." To." Kamar mai koyon magana ta kar'ba ta shige d'akinta.
Baba Tabawa ta fito da Sultan a hannunta ya yi wayo sosai yana ta furzar da yawu alamun hak'ori na kar'be shi Ina dariya tare da cewa" Yaro ya sake wayo duka bai fi sati biyu ba rabona da ku amma kowa ya canza mini a gidan na ji dadin ganinku cikin koshin lafiya."
Ta zaune tana fad'in." Alhamdulillahi kam sai godiyar Allah."
'Daga shi sama na yi na cafe ya dinga b'angala baki yana d'igo mini da yawu a fuska. Baba na murmushi ta ce." Ai ya yi wa uwarsa yankan k'auna a gidan nan Hajiya wallahi kamar al'amara ko wanda aka rad'awa a kunne koda ta dawo ya ga 'bakuwar fuska idan ya kalleta sai ya tsalla ihu duk ya sheda fuskokinmu amma ban da tata 'kiri-'kiri ya'ki yarda ta d'auke shi, da ta tsananta a washe garin ranar da ta dawo don kuka sai da ya kusan shid'iwa ya yini yana baccin wahala daga lokacin tace kada a kara fitowa falo da shi falo. Idan kuma ana canza uwa sai ya canza. Wai ta ji haushin abinda ya yi mata."
Murmushi kawai na yi ina d'an cire hannunsa da yake janyo mini d'ankunne a takaice na ce." A hankali zai saba da ita dama ai mussaman yaro mai 'kuiya yake." Ba na so maganar ta yi tsayi a tsakaninmu don ban san abinda za ta haifar ba.
Nan falon na zauna na ci abinci muka yi hira ta yaushe gamo da Baba Tabawa wajan yara da arba'in Hauwa tun da ta shiga d'aki bata fito ba shima maigidan tunda ya sauko wajejan Isha'i ya fita bai shigo ba har na yi sallama da Baba ba shige d'aki. Isha'i na yi kawai na sanya kayan bacci na kwanta amma raina gabad'aya babu dad'i ba na son wannan matsalar ta su ta shafi lafiyarsa Malam D'aha ya jadadda mini cewa kada a tsallake rana d'aya wajan aiki da abinda ya bayar. Ban hangi wani sasanci da d'okin juna a tsakaninsu ba. Hauwa ta kar'bi maganin ne kawai domin kada ta nuna mini akwai matsala tunda abinda na karanta kenan a fuskarta amma ai ni ba yarinya ba ce tun saukowarta na karanci tsananin damuwa da tashin hankali. Yadda na yi wa Hajja alkawarin kawo zaman lafiya a tsakaninmu hakan ne ya sanya ni bata damarta a matsayinta na wadda ta yi kome gidan mijinta dole ita zata shiga turaka idan magana ta gaskiya za a yi. Na d'auki wayata domin kiransa. Ko da ta shiga bai yi jinkirin d'agawa ba.
Na ce." Allah Ya taimake zan ce dama sai da safe domin na yi ta jiran ka shigo mu yi magana shiru ragowar maganinka na wajen Malam D'aha na bawa Hauwa na ce sai ka yi mata bayanin yadda ake yi maka ko?"
Ya ce." Akan wane dalili Amina?''
Shiru na d'an yi ina mamakin maganarsa. Dalili saboda matarsa ce ya yarda ta dawo su cigaba da rayuwa an yi musu sulhu iyaye sun shiga yanzu zaman aure za mu yi babu cin amanar juna da zalintar wani.
Ya sake maimaita maganarsa da b'acin uana fad'in." Sai ki je ki kar'bo mini maganina idan ba za ki zo ki yi yadda ki ke yi kullum ba ki kawo mini na yi abina."
A dan daburce na ce." Ai ba da gangan na'ki zuwa ba sanin da na yi cewa dole ne itama a bata damarta hakkinta ne kuma..... Ya katse ni
"Ni na ce ta dawo?"
Shiru na yi ina sauraransa. Ya cigaba da cewa." Ki je ki ce ta baki magani na ki kawo mini ina da lafiya Allah ya hore mini ba ni da nakasa a hannu zan gudanar da komai."
A tak'aice na ce." Gaskiya ba zan iya ba ai na riga na bata."
Ya datse wayar ba tare da ya sake magana ba.
Na kashe na nemi gado na kwanta ina fad'in" Ban da rigima ai da tun a can sai ka gayawa mahaifiyar taka baka amince ba, haba a yi ta abu daya sai kace 'kananun yara."
Jin yawu ya d'an ciko bakina ya sanya ni tashi na bud'e dirowa nan na sanya ledar da Hajara ta aiko mini da ita na ji dad'i sosai kuwa tun a gidan Hajja dana bud'e na gani magarya da kurna taura da aduwa har da tsamiyar biri irin kayan motsa baki na gargajiya.
Aduwa na d'iba na zauna gefan gado ina tsotsa a tsanake ina duba wayata What'sapp na shiga na ga sa'kon Nusaiba ya shigo voice note ko da na bude sai na ji muryarta har tana rawa tana gaishe tana fad'in ta zo gidan ba na nan har sau biyu zuwanta na k'arshe Hauwa ta ce kada