Author : Binta Umar Abbale Category : Read Hausa Novels
yadda Fati take gaya mini suna zargin ciki ne da ita ciwo take yi sosai har da su k'arin ruwa. Ikon Allah kenan
Wannan zugar da suka yi ta tabbatar mini da cewa dama sun shirya sun kuma tsara yadda tafiya za ta kasance amma rashin gaya mini shine abinda ya b'ata mini rai.
Sashenmu na ba'ki dake gidan na sanya aka gyara musu 'yan gidanmu kenan suka yada zango a can su Baba Tabawa na ta hidima da abinda za su ci. Sahura da Yusura kuma muna tare da su. Ita kadai ce na san da zuwanta a yau din saboda kayana da za ta kawo mini tunda mun yi waya da Hamusu ya ce mini ya kai mata tun kwana biyu da suka wuce amma shima bai gaya mini matarsa na tafe ba.
Sun yi mini bazata kuma na ji dad'i masu k'orafin ba su ta'ba zuwa ba dalili ya kawo su. Amma har yanzu ni dashi ba mu tsayar da ranar walimar ba. Kwana shida da haihuwa a yau din kenan gobe yara za su sake amsa sunansu amma ba ni tsammanin a ranar za mu yi taron walima kamar yadda ya saba duk haihuwar da za a yi masa alamu sun nuna akwai shirye shiryen da yake yi.
A daran da ya shigo na bi shi saman duk da ba girkina ba ne na Hauwa ne amma wasu lukutan yakan shigo ya yi sabgoginsa kafin ya fita kamar yadda idan ya je can yake yi, kuma ban ta'ba kalubantarsa ba ganin yadda shima yake takatsantsan da gujewa abinda zai kawo masa rikici yana wanka na zauna ya fito da ya gan ni a zaune sai ya d'auke kansa ya tafi ya tsaya gaban mudubi kad'an ya shafa basiline a jikinsa ya fesa turare ya sanya kayan shan iska fuskarsa ta nuna mini akwai abinda yake ji wa haushi.
Gaishe shi na yi ya amsa tare da zama gefena na d'an tsura masa ido ina kallonsa shima yana kallona kafin na ji ya furta." Zan ga ranar da zan yi miki abu ki yaba mini Amina har yanzu ban iya ba a wurinki na gode k'warai kin kyauta."
Na ce." Wani abu ne ya faru kuma?" Da wani irin yanayi ya ce." Saboda na baki wani abu da bai kai ya kawo ba shine ki ke bin 'yan uwanki kina gaya musu menene abin magana akan abinda na yi anan a gaya mini hujjar da ta rahamta mini yin kyauta da abinda nake so da dukiyata. Ke na ce na bawa wannan wuri ba 'ya'yan da muka haifa tare ba. Ko na ta'ba yi miki wata babbar kyauta duk tsayin zamana dake bayan wannan?"
A d'an sanyaye na ce." Wa na gayawa ka ba ni kyauta?"
Don har ga Allah ban yi tunanin su anti Yagana za su yi masa wata magana ba tunda ni su kadai na gayawa Babanmu bai sani ba haka zalika ban sanar da Baban Saude ba.
Ya gyad'a kansa yana fad'in." D'azu da safe kafin na fita 'yar uwarki ta same ni a haraba tana yi mini wasu maganganu shin me kuka d'auke ni ne? jahili wanda ba shi da ilimin addini ko me? kyauta ke na bawa ba yara ba. Ko kuwa idan na yi Hauwa ko a ahalinta alheri sai kowa ya sani. Za ku nuna mini yadda zan yi da abina ne Amina. Duk abinda nake yi ina sane babu wani yaro da zan haifa walau ke ki ka haifa ko ba ke ki ka haifa ba na fifita shi akan d'an uwansa. Ko an ce dole idan na kwanta dake a daren girkinki itama sai na kwanta da ita. An tilasta mini cewa idan na yi jima'i da Hauwa yau gobe sai na yi da Amina?."
Shiru kawai na yi ina kallonsa da mamaki. Lallai anti Yagana ashe shiyasa ta yi shiru bata tanka mana ba ashe da akwai abinda ta kud'irta a ranta yadda dai ransa ya 'baci hakan ya tabbatar mini da cewa ta fad'i maganar da ta tunzura shi kamar yadda yake nanata cewa dukiyarsa ce kuma duk abinda yake yi yana sane shi ba jahili ba ne.
Ya cigaba da cewa."
Babu d'ayanku da nake da ta'kidin takewa ha'kki ko na fifita yaranta duka ni na haifa kuma babu wanda bana so a cikinsu ina kuma addu'a Allah kada ya kama ni da hak'kinku, hakan kuma baya na nufin na sarayar da iko da mutuncinta ba duk wadda ta yi mini ba daidai ba a cikinku zan yi mata hukunci daidai gwargwadon abinda ta aikata mini. Idan har ba ki son abinda na baki shikkenan kada ki kuskura ki kara wata magana da wani zai tsaya gabana ya kalubalence ni. Na duba dacewa da cancanta a kanki ne Mutum nawa ne suke 'kasan ki? kuma mutum nawa suke ci da sha a karkashinki? mutum nawa ki ka tallafa suka tashi? ko kuma kin d'auka haka nake zaune dake kara zube ba ni bin abubuwan da ki ke gudanarwa
arziki na Allah ne amma menene makomar yaranki da koyaushe ki ke nanata mini cewa ba ni ne ubansu ba. Idan yau na fa'di na mutu a shari'a ba su da gadona. Idan na d'auki abu na baki sai ya zama lefi da tiri-tiri da magana kamfanin majizai na baki ne Amina?"
Na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Har yanzu bakina a mace yake na kasa cewa komai saboda mutuwar jiki da mamaki duk yadda yake ganin k'ima da mutuncin anti Yagana yau ta kai shi bango tunda gashi yana ba ni sa'ko zuwa wajenta. Na rasa abin cewa kawai sai na yi shiru da bakina domin ba ni so kuma lamarin ya girmama shi da ita anti Yaganar babu wanda zan za'ba tana da hujja shima yana da tasa hujjar kamfani kuma muddin ana so na kar'ba akashe shi ya daina aiki koma gabad'aya a sayar mini da shi a bani kudin na had'a da wanda suke hannuna alherin da abokansa suka yi mini na nemi plaza cikin kasuwa na saya ko Kuma na sanya k'wararru su gina mini na sake fad'ada harkokina wannan shine magana.
Adamu ne ya kira shi a waya ina ji suka gama magana yana gaya masa gasu nan shi da Yusi za su kawo sa'ko in ji anti Nabila ita ba ta kira shi ba saboda tasan yana gida sai ta sanya yaran.
ya ajiye wayarsa to a nan ne na magantu cikin had'e rai na ce." Ka ajiye wannan kaya domin kuwa yarana ba za su sanyasu ba Allah shine d'aya ko kuma kawai ku yi tanadi kai da ita idan kun yi aure kun haihu shikkenan kun huta. Ko sun kawo kayan nan a banza, idan lallai sai Nabila ce za ta sayowa yaran nan kayan sanyawa a bar shi kawai zan saya musu a matsayina na uwarsu."
Bai juyo ya dube ni ba ya ce." To shikkenan ai tunda kin ce haka ta riga ta sayo sai a ce mata me? ki a ajiye kada Allah Ya sa ki yi musu amfani da shi din."
Na ce." Ba kuwa zan yi ba, ai ga shawara nan na baka za su yi maka amfani idan kun haihu."
Ya dube ni yana fad'in." Kina da hankali kuwa
Giwa da wa zan haihu?"
Na tare shi da sauri ina ce wa." Da ita mana ko ka d'auka shashashai ne mu, ka ji kunya wallahi."
Ya 'bata ransa yana fad'in." Yanzu ke tsakani da Allah ba ki ji kunyar yi mini wannan maganar ba, duk kalolin matan da suke duniyar nan Amina na rasa wadda zan aura sai wannan matar me zan yi da ita?"
Na ce" Me yasa zan ji kunya tunda kai ba ka ji ba. Haba Malam babu wata magana da za ka fad'i wallahi tallahi na yarda da kai, ina ruwanka da ita da business dinta ka sayi kaya a wajanta saboda kana tausayata mata ko akwai shagunan sayar da kayan baby's cikin garin nan da yawa me yasa ba za ka je da kan ka ka sayo ba, ka bi dare da rana ka samar da cikinsu sayo musu kayan da za su sanya ne zai gagareka."
Ya girgiza kansa yana ce wa." Ba zan shiga shago sayan kaya ba. Ni ma wanda nake sanyawa telana ne yake kawo mini su a dinke ya san irin yaduka da shaddodin da na fi so ko tafiya na yi kin ta'ba ganin na sayo muku abu, idan kina ganin za ki iya zuwa ki sayo musu abar maganar don Allah don Annabi zan baki kudi wannan din kuma sai a ajiye idan Allah Ya sanya na samu wasu biyun daga wajan Hauwa shikkenan na huta.
Ta'be baki na yi tare da d'auke kaina ban ce komai ba.
D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci kafin na ji maganarsa yana fad'in." Kafin na shigo na ga alamar muna da ba'ki tun daga haraba hakene?"
" 'Yan gidanmu ne!" Na fad'a a takaice. Ya saki fuska yana fad'in." Sun zo taya mu murna kenan, na ji dad'i sosai kuma idan na ci abinci zan sakko 'kasa mu gaisa sai a yi musu magana."
"To." Kawai na ce na tashi tsaye. Ya rike hannuna na koma na zauna kusa da shi. B'akin lallen da ya zanu a saman fatar hannayena ya shiga dubawa. Ya bud'e tafikan hannayen yana kallo yatsun ya yi marron sosai zanan fulawar ya fito. Ya dinga sauke ajiyar zuciya yana fad'in." Ya yi kyau sosai mu ga na 'kafafun." Gim na yi kawai ta yaya zan iya nuna masa k'afafuna na cikin safa. Ya sunkuya kuwa ya cire safar yana ta dubawa na zubawa 'keyarsa ido takaici da haushinsa ya ishe ni. Maganar Nabila idan har ta yi nisa akwai wani gagarimin lamari da zai faru tunda shi bashi da tunanin yin nesa da mu'amula mai tsayi da ita bayan gaisuwa. Ai tsakanin mace da namiji idan sha'kuwa da tausayi suka shigo ciki akwai alamun kauna. Ya nuna son cigabanta da tausaya mata tunda idan an yi magana sai ya ce business d'inta ne a saya a wurinta kada a je waje a saya.
Ya d'ago da wani irin yanayi na yi saurin d'auke kaina ya tsira mini ido har yanzu hannunasa yana cikin nawa ya ce." Za ki ba ni abinci ko na tafi na kwanta a haka?"
Na furta." Duk yadda ka ga ni, amma ai ba ni ce mai baka abincin ba."
Ya ce." Kwana biyu itama tana ta ciwo kullum a kwance take ciki ne da ita ba kuma sosai take sarrafuwa ba ke kuma kin ga kina da masu aiki." Na katse shi da gaggawa ina fad'in.'' Na hana ka d'aukar mata aiki ne? tana da lafiya bata da lafiya ba abinda ya shafe ni ba ne. Cikin dai masu aikin gidan nan Wallahi babu wadda za a d'auka.''
Ya ce." Ba a ce dama za a d'auki ko daya ba, za a kawo mata nata masu aiki itama."
Na d'auke kaina ban ce komai ba. Ya ce."
A kawo mini abincin dai ko ba shi da yawa kada abin ya yi mini yawa kuma." Na tashi kawai na tsinci hannunsa saman tudun mazaunaina. Na juyo da sauri ina kallonsa. Ya cire hannun shima yana kallona. Wato da bai samu sararin d'ora hannunsa a kirjina ba kamar yadda ya saba sai Allah Ya bashi sa'a ya d'ora a na baya.
Ya furta." Menene fuskata za ki buge na tare."
Na janye idona daga kansa kawai na wuce cike da mamaki wai tambayata yake yi menene saboda na kalleshi wato shi bai d'auki abinda ya yi a matsayin wani abu ba."
Ina saukowa na tarar da ita ta zo ana ta hira da ita. Usaini ma yana hannunta. Hasan din na goye bayan Taburni yana bacci.
Ta miko mini shi tana fad'in." Tun d'azu yake neman nono."
Ban ce komai ba na kar'be shi na zauna gefan Hajja wadda suka ta hirar duniya da Ya Falmata tana ta basu labarin rikici da masifar tashin hankalin da aka shiga a maiduguri lokacin farkon boko haram.
Khalil na sanya ya d'auko mini wayata a d'aki na kira Fati na ce su zo gabad'aya za su gaisa da maigidan. Ta ce mini abinci suke ci da sun kammala za su zo.....✍️
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*162*
Ganinta a zaune ya sanya na share kawai ban kai masa abincin ba idan ya koma gidanta sai ta bashi abinda taci su kwanta duk rashin moruwarta da yake fad'i ai ba zata kwana da yunwa ba.
Na ji tana magana da Hajja kan zuwa inna Uwani gobe wai sun yi waya Hajjan ta bata amsa da cewar itama ta sanar da ita.
Ya sauko cikin mutunci da kulawa ya zauna a falon bayan shigowarsu Fati gabad'aya ya gaisa da su har yana jan su Hassanar gidanmu da tsokana haka dai suka dinga sinne kai irin na rashin sabo yadda ya zauna ya kula su shine abinda ya d'an sassauta mini zuciyata domin kuwa ko babu komai bai 'kyamace su ba ya nuna suma cikakkun mutane ne masu kima da karamci zuwansu ya sanya shi farinciki har yana mik'a godiyarsa wannan yana daya daga cikin kyawawan halayensa karrama mutum duk rauni da rashinsa baya ta'ba nunawa na 'kasa da shi cewa shi ba komai ba ne, fuskarsa a sake zai mu'amulanci mutanan da ya tabbatar da cewa ya fi suttura da rufin asiri.
Mun d'an jima tare da shi a falon da su ma gabad'aya kafin ya yi wa Hajja sallama ya fita. Jim kad'an itama ta tashi ta bi bayansa bayan ta yi mana sallama kamar dai gaske ta saki jikinta tana walwala tamkar babu komai a zuciyata Hauwa kenan .
Yusi kuwa kam ganina da shi biyu tunda suka zo yana can tare da Adamu sai da gari ya waye tukkuna suka shigo su biyu da akwatina hud'u jiyan ba su samu damar kawo kayan ba.
Muna d'aki gabad'aya anti Yagana Ya Falmata da Sahura. Yusra tana bacci saman kujera bata tashi ba.
Na bi su da ido har suka gama shigo da akwatinan kayan suka ajiyesu a gefe ban ce komai ba.
Muka gaisa da su suka zauna cikin nishadi da jin dad'in had'uwa da juna wannan so da k'aunar da suke yi wa junansu har mamaki yake ba ni.
Hassan na hannun Adam Usaini shi kuma yana hannun Yusi na ji shi Adam din yana fad'in." Mama Baba ne ya ce mu kawo miki kayan nan akwai wasu kayan ma da za mu d'auko da yamma anti Nabila ta ba ni lambar wayar direban idan suka iso zai kira ni."
A takaice na ce." To shikkenan."
Ya mi'kawa anti Yagana yaron da yake hannunsa ya riga Yusi fita shi yana zaune kamar akwai magana a bakinsa na dube shi ina fad'in." Kai ma ka zama munafiki ko?"
Ya dube ni da sauri yana fad'in." Munafiki Mama?" Na gyad'a kaina ban ce komai saboda takaici to bayan wad'annan kayan akwai wasu kenan.
Ya Falmata ta b'ata rai tana fad'in." Menene abin munafurci Amina."
Na ce." Haushi yake ba ni wallahi idan yana yin wani abin Ya Falmata yaron nan baya goya mini baya ya manta da ni ma gabad'aya."
Ta kama dariya tana fad'in." To yanzu me ya faru da kike barar goyan baya daga gare shi a da can fa shine shalele ko don yanzu kin samu wasu shine za ki cillar dashi."
Na ce." Shi ya fara cillar da ni ai Ya Falmata."
Murmushi ya yi kawai bai ce komai ba ya mika mata yaron yana fadin." Bari na je na same shi Mama zan dawo sai mu yi magana ko idan na yi lefi a yi hakuri.''
Hararsa na yi yasa dariya da sauri ya fice. Sahura ta fito daga toilet wanka ta yi ta ta zauna tana shafa mai. Na dube ta a hankali wata irin ki'ba ta yi zamanta a gefena da d'aurin kirji na sake gazgatawa na ce." Wai ke maganin ki'ba ki ka sha ne?"
Anti Yagana ta ce." Kin riga ni magana Amina na ce ko idona ne yake yi mini gizo ne."
Dariya kawai take yi tana fad'in." Kwanciyar hankali ne kawai. Ya Falmata na fad'in idan haihuwa ma ta tsaya ana samun canji irin haka."
D'akin ya d'auki shiru na wani lokacin na dubi anti Yagana ina fad'in." Wai ya kuka yi da maigidan nan ne?"
Ta yi shiru tana d'an kallona kafin ta ce." Na same shi ne domin na yi masa godiya bisa abinda ya yi miki na alheri da farko na yi tunanin ke kad'ai ya ware ya bawa tare da yaran nan sai daga baya kuma da yayi mini bayani na gane dalilinsa wallahi abin ne ya ba ni tsoro Amina shiyasa na gaza ha'kuri na ce bari na yi magana akai saboda ina jin tsoron k'aramar magana ta zama babba a zo ana ta maganganu marasa kyau a kan ki."
Ya Falmata ta b'ata rai tana fad'in." Akan wane dalili za ki tare shi da wannan maganar Yagana kin yi kuskure anan gaskiya tunda ta zo ta gaya mana na ce ta kar'ba tunda ba ita ta ro'ka ba shi ya bata. Amina mahad'in arzikinsa ce don ya dauki 'karamin kamfani ya bata bai nakasa kansa ba kuma yana da ninikin abinda ya bata din amma shine ki ka zame jiki ki ka tare shi ba ki ji nauyi ba don Allah Yagana."
Ta gyad'a kanta tana ce wa." Ni fa ba da wani abin na yi masa magana ba Ya Falmata kin san irin haka yana haddasa rigima tsakanin iyali ki ga gida ya rikice ana ta fad'a kuma da yawa wasu mazan sune suke asassawa wajan fifita wani bangare.
kuma ba ita kad'ai ce matarsa ba Hauwa yar uwarsa ce kuma matarsa itama tana da yara tana kuma da hakki."
Ta ce." Lokacin da zai yi mata kyauta kin sani ne Yagana? ke dai ba yar uwarki ki ka sani ba me yasa ba za ki goya mata baya ba bisa abin alherin da ta samu kin ga kenan anan gaba zaki sanya masa shakku idan ya yi