Gudun Aure Book 3 Binta Umar Abbale

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Read Hausa Novels

Chapter   26 / 73

75K to 78K   out of 217.6K words

can gidana na sharad'a mu kwana idan ya so idan mun gaisa da Hajja zuwa jibi sai mu tafi.
Mun samu tar'ba ta mussaman a gidan Malam D'aha. Na ga kara da karamaci irin na mutanan kauye domin kuwa ina idan da sallar magriba aka cika gabana da kwanukan abinci har daga ma'kota. Mafiakasari towo ne na masara dana dawa sai wata langa da aka kawo mini ita daga baya cike da dambu na tsaki wanda ya ji zogale da gyad'a yana ta k'amshin mangyad'a zuryan da yajin barkono a gefe.
Ya ba ni sha'awa sosai na kuma yi masa cin yaushe gamo na toshe cikina da shi duk tarin yunwar dana nad'a a tsukin nan sai da na rasa yadda zan yi da cikina. A daddafe na yi sallar Isha'i. Ina idarwa wata matashiyar budurwa ta shigo doguwa mai duhun fara ba ta da jiki sosai akwai yarinta a tare da ita ta sake gaishe ni na amsa ina fad'in ta kwashe kwanukan abincin da ta dinga kawo mini gasu nan shida a jere.
Ta tsuguna tana bubbud'awa ta dube ni tana fad'in." Ai d'aya kawai ki ka ci Hajiya."
Na ce.'' Ina zan kai wannan abincin yar uwa wannan ma na gode sosai kuma wallahi ya yi mini dadi 'kwarai da gaske."
Ta yi murmushi ba tace komai ba ta fara had'a kan kwanukan tana fita da su.
Na d'auki wayata dake gefena na duba na ga network dina ya d'auke gabad'aya wata'kila yana da ala'ka da yanayin d'akin da nake ciki tunda na 'kasa ne kuma a k'asa yake sosai.
Gabad'aya hankalina yana can b'angaran malamin tun zuwanmu da muka shiga tare na gaishe shi na fito ban sake jin wani motsi ba sai ta hayaniyar iyalin gidan da shige da fice da ake ta yi na d'aukar abinci daga almajiran malamin.
Gajiya na yi da zaman d'akin na fito tsakar gidan na samu jama'a a cike da yake mai yalwa ne kwarai matan gidan su hud'u suna can daga gefe suna cin abinci a tare wasu daga cikin yaran kuma sun ci sun gama wasu na cin na su. Kwanuka gasunan birjik a bakin manyan tukwanansu.
'Yar budurwar nan da har yanzu ban san sunanta ba na ji tana fad'in." Bandaki za ki shiga.''
Kafin na ce komai daya daga cikin matan gidan ta ce." Hajara zuba mata ruwa maza a buta Hajiya alwala za ki yi ne?"
Na ce." A ai na yi sallah na fito na sha iska ne." Yarinyar da aka kira sunanta da Hajara ta d'auko tabarma da sauri ta shimfida mini can gefe na je na zauna ina yi mata godiya cikin ikon Allah zamana ke da wuya network din duka layukana ya dawo.
Na fara neman number Sahura muka gaisa sosai ta sake yi mini gaisuwa nan nake sanar da ita cewar na shigo garin zan kira ta zo gida ta same ni zuwa gobe.
Muna sallama na nemi number Hajja da ta shiga sai ta katse na kira ya kai sau biyar nan na gane network din yake hawa da sauka wai ina so na gaya mata cewar za mu shigo gobe.
Na dauki kimanin minti talatin da zama a tsakargidan wanda ya yi daidai da lokacin tara na dare da minti biyar.
Daga can b'angaran malamin na ji maganarsa alamun zai fito na sauke ajiyar zuciya a hankali idona a kan hanyar suka fito tare da wannan Rabi'u da yake yawan kiransa a waya wanda shine ya kan gaba wurin tararmu lokacin da muka sauka a garin.


littafin gudun aure na kudi kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.


Suka fito tare da kuzarinsa ya tsaya cikin kulawa yana yi wa matan gidan sallama na tashi ina gyara mayafina na d'auki jakata can inda suke zaune na nufa ina fad'in." Za mu tafi, na gode sosai da karamaci Allah Ya saka da alheri, na dubi Hajara dake zaune cikin 'yan uwanta na ce." 'Yar uwa sai Wani lokacin ko na gode da kulawa."
Ta washe bakinta tana fad'in." Ku gaida gida Allah Ya tsare hanya."
Na ce." Amin Ya Allah tare da yin gaba ganin ya riga ni fita ina jin matan da yaransu suna ta yi mini fatan alheri.
Ina fita daga can wajen motar da mu ka zo Sukairaju nake hange da D'ahuru sai Rabi'un suna taga-taga kafin na hangi Baban ya yi wata irin fad'uwa irin ta ruf da ciki da kirji.
Ade ya fito daga mota a ki'dime! yayin da gabad'aya suka rufu a kansa duk da yake dare ne amma ai irin na karkara ne da suke da wadatar kwanciyar hankali ba irin cikin gari ba hakan ya sanya mutane fara tsayuwa a wajen.
Ban san inda nake jefa k'afafuna ba kawai dai na tsinci kaina a tsakiyarsu lokacin da suke ko'karin ciccib'arsa. Rabi'u yana fad'in da k'afafunsa ya fito kuna dai kallo magana ma muke yi da shi ya yanke jiki ya fadi."
Jikina ya dinga kyarma na tsuguna ina d'ago kansa yana karyewa ganin haka ya sanya ni ihu! ina Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Baba Baba, na dubi Sukairaju a gigice ina fad'in." Ku d'auke shi mu tafi asibiti."
Rabi'u ya ce." Cikin gidan za mu mayar da shi Hajiya ."
Daga haka suka fara kici-kicin ciccib'arsa Sukairaju ya cire gilashin idonsa da wayoyinsa tare da wallet dinsa ya sanya cikin aljihunsa su biyu shi da D'ahuru suka kama saman shi ta wajen kansa. Rabi'u da Ade suka rirrike k'afafunsa a haka ina kallo suka taitayeshi suka koma dashi cikin gidan suna ta Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un.
Na bi bayansu k'afata na karkarwa shikkenan kuma tunda har kansa ya karye ya mutu.
Kai tsaye d'akin malamin suka nufa da shi gidan ya rud'e sosai da hayaniya duk kowa a tsaye na bi su ina kuka na fitar hankali. Babar yarinyar nan Hajara ta zo ta ri'ke ni ta baya ina cire hannunta tana sake ri'ke ni fadi take yi "Yi hakuri ki yi masa addu'a kin ji, Allah ya ba shi lafiya."
Na dube ta ina cewa." Ya mutu ko?"
Sai ta girgiza kanta cikin ko'karin kwantar mini da hankali ta ce." Bai mutu ba ke waye ya gaya miki."
Hawaye ya sake tsinke mini na ce." Kansa na ga ya karye ko'ina na jikinsa ya shika. Kin ga ai lafiya lau ya fito har muka yi muku sallama ko?''
Ta daga kanta cikin alhini ta ce." E, kwarai kuwa amma hakan ba shi yake nuna cewar bashi da rai ba zai tashi in sha Allahu."
Na ri'ke hannunta tamau ina fad'in.'' Ta cutar da ni, ta cutar da yaranmu ta zalince shi, ya yi mata alheri ta saka masa da sharri. Ta gigita mini rayuwata."
Kawai sai itama ta fara kuka ta rungume ni a jikinta tana cewa." Ki yi hakuri ki samu nutsuwa mu je can wajenmu ki zauna ki nutsu kin ji ko, ki yi wa mijinki addu'a."
Hajja ta fad'o mini a rai. Na sake fashewa da kuka mai gunji!
Ta kama ni sosai muka nufi d'an wajenmu a hankali take ta fad'in." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un. Na kama ni ma idan ta ajiye na d'auka.
Ta zaunar da ni saman tabarma tana cewa Hajara ta d'auko mata mafici.
Ta kar'ba ta fara fifita mini har yanzu ba ta cika ni ba domin ni kaina nasan ba a hayyacina nake ba gabana duf-duf kawai yake yi mini daga zarar na yun'kura zan tashi sai ta riko ni.
Gabad'aya yaransu da manya sun yi cirko cirko a gaba.
Da wani irin sauti na ce." Wayyo Allah anti Yagana kina ina?" Na silale saman tabarmar na kwanta hawaye suka dinga biyo gefan idona. Na riga fa nasan mutumin nan ya mutu kawai a fito a gaya mini ne ba za a yi ba.
Na riko hannunta ina sake tambayarta a karo na biyu ta girkiza kanta tana cewa." Na gaya miki fa bai mutu ba Hajiya yana da rai in sha Allahu."
Na zuba mata Idona kafin na ce." Wuyansa ya karye ana gane alamun rashin rai a jikin dan adam tana nan fa kada ku yaudare ni."
Ta ri'ke ni da kyau a hannunta sai ta dubi yaran tana fad'in." Ku tafi ku yi alwala kowa ya d'auko al'kur'aninsa a yi karatu.
Jin haka ya sanya ni k'ara gazgata abinda zuciyata take gaya mini me yasa ba su yi karatun tun d'azu ba sai yanzu k'wa:kwalwata ta dinga gaya mini cewa a gidan mutuwa ne kad'ai ake yin karatun al'kurani.
Jakata na d'auka da take ajiye a gefena na d'auko wayata a karo na shida number Hajja na kira ta yi ringing sau biyu a na ukun ta d'aga. Tana magana na yi shiru hannuna yana ta rawa kiran sunana take yi Amina, Amina, bakina ya yi nauyin gaske hawaye ya ziraro daga idona cikin 'karamin sauti na ce." Ya mutu Hajja ta kashe mana Babanmu Hajiya Maryam ta cuce ni......✍️
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *Gudun aure paid book complete 1k akan telegram via 0542382124.... Binta Umar Opey bank*
*127*
Da tsananin damuwa nake jin ta tana kiran sunana na ajiye wayar ba tare da na kashe ba jikina na rawa sosai na 'kunshe bakina da hannu jin yadda wani mahaukacin kuka ke ko'karin kufce mini.
Mahaifiyar Hajara da na ji suna kiranta da Inno ta d'auki wayar tana fad'in. Hajiya halima ce. Daga daya bangaran ita hajjan tana ta fad'in." Ko Baba Sulen ya rasu Amina domin shekaran jiya Kamalu ya ce mini ya je ya duba shi a can asibitin Murtala an kwantar da shi. Amina, Amina kina ji na."
Ta ce." Ni ce Inno uwargidan Malam D'aha nan Bunkure."
Hajja ta ce." Inno me yake faruwa ne, wanene ya rasu ina Amina take?"
Duka ta jero mata wad'an nan tambayoyin.
Cikin sigar kwantar da hankali ta ce." Babu wanda ya rasu Hajiya Halima gigitace dai kawai ta sanya har ta gaya miki haka."
Ta ce." Inno ki gaya mini gaskiya kin san dai ni ba yarinya ba ce?"
Sai ta dabarbarce ta kasa gaya mata komai. Zuciyata ta sake karyewa tabbas bata da abinda za ta fad'a kuma da bakinta take cewa bai mutu ba gashi yanzu an tambayeta ta yi shiru.
Ina jin Hajjan tana ta magana Inno ki gaya mini menene, ki bawa Amina wayar mu yi magana na ji ta a kusa dake tana kuka."
Ta miko mini wayar jikinta a sanyaye. Na kar'ba nasa a kunnena na ji tana fad'in." Yi shiru ki kwantar da hankalinki Amina ki gaya mini abinda yake faruwa kin ji ko, ki gaya mini ko menene ina sauraranki."
Da kyar na daidaita kaina na ce." Muna nan Bunkure ni da Baba amma ban san halin da yake ciki ba yanzu Hajja ki zo don Allah."
Ta ce." Yi shiru zamu zo in sha Allahu, yanzu dare ya yi amma da asuba zamu d'auko hanya dukkan tsanani yana tare da sauki."
Ban iya cewa komai ba sai jan hanci na ji ta kashe wayar sai ni ma na ajiye tawa na matsa jikin bango na takure can 'kasan zuciyata ina ta ambaton Allah akan ya kawo mana d'auki.
Dare ya tsala sosai muna zaune a tsakargidan ni da Inno mu biyu kacal ta yi ta yi da ni na shiga na kwanta na ce mata ta barni ko na kwanta din ba bacci zan yi ba gabad'aya hankalina na sashen malamin shiru ya hana kowa shiga Sukairaju da yan uwansu su Dahuru tunda suka shiga dashi ban sake ganin gilmawarsu a hanyar ba Rabi'u ne ya shiga sau d'aya kafin ya fito ya nufi bangaransa dake cikin gidan bai sake fitowa ba. Muna zaune har aka kira sallar asubahi. Kowa ya fito ya yi alwala yara da manya na yi na shiga d'akin da suka sauke ni a tun farkon zuwanmu gidan na yi sallah ina kuka sosai ina yi wa rayuwarmu addu'a.
Karatun al'kurani tun daga almajiransa na waje da cikin gidan iyaye da yaransu. Na kar'bi al'kur'ani wurin Hajara na bude nima ina karantawa a hankali a hankali na ji zuciyata tana sanyi. Gari ya fara haske Hajja suka shigo gidan ita da Hajiya Saratu da kanin mahaifinsa alh Sa'idu.
jin maganarsu ya sanya na rufe al'kur'anin da sauri na fito tsakargidan.
Inno ta sauke su tare da shimfida musu tabarma suka zauna yanayinsu ya nuna tsantsar tashin hankali a haka suka dinga gaisawa da jama'a.
Ba su wani jima da zama ba. Rabi'u ya fito daga wurinsa suka gaisa a gurguje ya nufi sashen malamin minti biyar a tsakani ya fito tare da fad'in." Hajja Malam yana magana."
Kusan a tare muka tashi gabad'aya ya shige mana gaba kowanne mu zuciyarsa na dokawa.
Yana zaune saman buzu da al'kur'ani warshu mai falle-falle a hannunsa d'akin tsaf Y
yana ta k'amshin turaran wuta. Can muka hange shi kan wata katifa madaidaiciya da shimfidar bargo a samanta. Yana kwance sambal sun cire masa rigar jikinsa daga shi sai singileti da dogon wandon rigar da suka cire hannayensa nade a k'irji ido a rufe.
Kafafuna suka fara kyarma Hajja kuwa kuka ta sanya tana fad'in." Me ya faru Malam ma'kiyane suka jefe shi ko, Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Ta nufe shi tana kuka sosai ta tsaya a kansa tana fad'in." Ni kuwa me ka yi wa jama'a ne Tajo daidai gwargwado kana alheri da kyauta da yawa wasu na ta ganin wautarka akan dukiyar da Allah Ya baka. Ka yi kyautar hajji ka yi ta umara, ka yi kyautar kud'i ka yi ta gida da mota da jari, duk hakan bai yi musu ba sai sun kwantar mini da kai."
Shiru d'akin ya yi tana kuka da sambatu Hajiya Saratu na kusa da ni tana goge hawaye ta ma kasa zuwa inda yake kwance. Gabad'aya ta gigice sai kuka take yi na kasan zucciya.
Ni kam idona bushewa ya yi k'amas ban yi mamakin hakan ba wata'kila hawayen idona ne ya 'kare sai dai wani kutittiran abu da nake jin sa ya tokare mini a wuya. Da na d'aga kaina na dubi wurin da yake kwance sai gabana ya yanke ya fadi.
Alhaji Sa'idu ya tashi a hankali ya je ya kamo hannun Hajja ya zaunar da ita a gaban malamin wanda tunda take koke-koken bai ce komai ba.
A nutse ya had'a al'kur'anin da yake hannunsa ya mayar da shi ma'adanarsa ya kalli Hajja da har yanzu ta kasa nutsuwa ya ce." Hajiya Halima kukan ya isa haka, mu godewa Allah da ya takaita lamarin kuma aka samu hanyar warware shi cikin sau'ki.

Littafin nan na kudi ne yar uwa kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba


Kamar yadda ki ka sani dai ni malamin zaure ne mai almajiran mai kuma hidima da al'kur'ani. Na ji dad'i sosai da Allah ya tsawaita mini nisan kwana wannan al'amarin ya kasance ya kuma ba ni iko da damar warware shi. Ba ni cutarwa ta hanyar sanin da Ubangiji ya ba ni kamar yadda wasu malaman suka d'auki wannan hanyar ta zalinci domin neman abinci da cutar da hallitar Allah.
Hakika a wani zuwa da Alhaji Tajo ya yi gare ni wattanin baya na karanci akwai rikici da makaru a tattare da shi. Wannan dalilin ne ya sanya ni gaya masa cewar ya dage da addu'a akan shi da kuma yaransa idan ban manta ba na tambaye shi iyali da adadin yaransa ya sanar da ni. Na bashi adduoi sosai na kuma yi masa da kaina domin samun mafita da warware wa.
jiya suka zo nan da matarsa ya yi mini bayanin dukkanin abinda ya faru bayan rasuwar matarsa Maryam wadda itace musabbabin kwantar da shi tunda aikin da ta sanya aka yi akansa ni kaina ya tsorata ni ba don komai ba sai don ganin irin d'aurin da aka yi masa bayan lokacin da Ubangiji ya d'iba masa bai cika ba.
Na jima ina aikin warware asiri iri iri wannan ya ba ni mamaki ya kuma tsoratar da ni k'warai da gaske, kuma an cire tsoron Allah wajen aikata shi.
Ya yi shiru yana duban inda yake kwance tare da girgiza kansa tabbacin da gaske abin ya bashi tsoro da mamaki kamar yadda ya fad'a..
Hajja ta ce.'' Ni ai a zatona abokan kasuwanci ne ko wasu da ba sa kaunarsa suka jefe shi tunda kasan yadda duniyar take."
Ya girgiza kansa yana cewa iyalinsa ce Hajiya halima kin san ku mata wani lokacin da son kai kuke da kuma mugunta. Ba dai a tara sani da Allah wata'kila ta ji a jikinta za ta riga shi mutuwa ne sai ta yanke shawarar yi masa d'aurin rai da ajali idan ta rasu a cikin biyu ko ya bi bayanta ko kuma ya kwanta kamar dai yadda yake a haka yana numfashi amma bai san a duniya yake ko a lahira ba."
Shiru ya ratsa kafin ya cigaba da cewa jiya na kwanta bacci bayan na yi sallar istahara akan lamarin domin kara tabbatarwa Ubangiji Allah Ya nuna mini ita ko ba ita ce 'yar fara mai karamin jiki ba da doguwar fuska?"
Hajiya Saratu da sauri ta ce." K'warai itace malam suffarta kenan."
Ya gyad'a kansa cikin jajantawa yana fad'in." Rahama sai ta Allah a wajen da take domin irin shirkar da take yi Allah Ya la'ancesu. Ba za mu yanke hukunci kai tsaye a kanta ba amma tunda har son zuciya da mugunta ya sanya ta kafurta kanta ta iya yadda da juya zancen Allah wurin neman biyan buk'atarta tabbas alkawarin Allah baya ta shi."
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa." Na warware duk d'aurin da ta yi a kansa da yaransa zai tashi da izinin mai buwaya. A yadda ta so shine ko ya tashin ya zama mutumin-mutumin kamar gunki tunda da ayar nan ta (Summunbukkum!) aka yi aiki akansa bayan ita suka had'a (Makisinafiyiabada) ayoyi ne masu zafi wurin dakusar da duk wani karsashin dan adam idan aka juya su ta gefan zalinci.
Ita kuma wannan kwalbar ya fad'a yana nuna musu ita ya cigaba da cewa." Kowacce laya akwai sunan mutum guda a ciki. Amina Hauwa Kamalu Yusuf Khalil Hassana Usaina da kuma Minal. Mallaka ce aka yi akan wad'annan sunayen da na zayyano da kuma jefa soyayya a zuk'atansu.
Hajja na kuka tace fad'in." To me ya yi mata ni Halimatu na ga da iyalinsa ta same shi. Tsananin abotar da take tsakaninsa

26 / 73