Gudun Aure Book 3 Binta Umar Abbale

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Read Hausa Novels

Chapter   19 / 73

54K to 57K   out of 217.6K words

ka kammala aikin ko kuwa?"
Sai ya gyad'a kansa yana fad'in." Zan dakata gaskiya tunda Allah ya yi ikonsa akan wadda ta sanya ni sai dai da iska (jinnu) muke yi su kuma ba alkawari ne da su ba, idan na gaya musu mu tsaya da yin aikin bai zama lallai su tsaya kai tsaye sai sun gindaya abinda suke buk'ata amma ba zai wuce yanka ba."
Ya girgiza kansa cikin d'an karan mamaki da al'ajabi cikin zuciyarsa tana nanata istigifari. Ya dube shi kafin ya ce." Ka kyauta da ka d'auki aniyyar dakatawa zan kuma biya ka hakkinka. Amma ba yau ba ina so ka dawo bayan sadakar bakwai kud'i hannu da hannu."
Ya risinar da kansa yana ta godiya. Shi kuma ya yi ta nazarinsa cike da madaukakin mamaki gashi cikakken mutum cikin manyan kaya da kamala har da rawani ashe mushiriki ne ta'babbe ne, wato iskokan da suke yi musu aiki sune masu biyan buk'ata ba Allah ba.
Ya sanya hannu cikin aljihu dubu ashirin ya bashi kafin ya ce ." Ka yi kudin motar komawa gida amma kamar yadda na gaya maka bayan an yi addu'ar bakwai ka zo ka kar'bi kudinka."
Ya kar'ba da sauri yasa a aljihu yana ta godiya ya mika masa hannu wai su yi sallama bai kar'ba ba kawai sai ya daga masa hannu yana fad'in "A sauka lafiya." Daga haka ya koma cikin gidan cike da tunani da nazari..
Ya samu Bashir tare da su Salim da Yusi a zaune. Kallo guda ya yi wa yaron ya hangi kama sosai da Maryam domin duk irin fuskarsu daya sai dai shi fuskarsa ta yi duhu sosai da lebensa tabbacin wiwi ta ratsa shi.
Ya dinga sunkuyar da kansa kasa kamar munafiki ya fara gaishe shi cikin ladabi irin wanda suka saba.
Ya amsa yana dubansa tare da fad'in." Ko kaine Bashir din ne?''
Da sauri ya ce." Ni ne, eh ni ne?''
Ya fad'a yana wata dariya da sosa kansa.
Shigowar Alhaji Sulaiman gidan da iyalinsa ya d'auke masa hankali, da kansa ya tafi domin tar'barsa tun kafin ya karaso rumfar da suke zaune.

Tare muka yini da Hajiya azizi da abokiyar zamanta mai suna Hajiya Salamatu da Halisa 'kanwarta da ta ba ni labarinta kwanakin baya. Muka yini dasu a gidan sai wajan uku na rana bayan sun ci abinci sun yi salla muka yi sallama da su kan cewa za su shiga can gidan Maryam din domin yi wa danginta ta'aziyya na yi ta mamaki ashe ba su shiga ba sai yanzu da suka tashi tafiya.
Alhaji Sulaiman ya shigo har gida ya yi mana gaisuwa ni da Hajja ya d'an jima a tare da Hajja suna hira kafin ya yi mana sallama ya fita.
Daf da magriba mun d'an samu sau'ki shige da fice na mutane domin duk wanda ya je can gidanta ya yi gaisuwa sai ya shigo mini mussaman mak'otanmu dama wad'anda muke cikin estate din a tare.
Na shiga d'aki sallah na samu Anti Yagana har ta idar ta kashingida tana fad'in." Gobe ana yin addu'a da safe zan d'auki hanya da wuri Amina."
Na ce" Ba za ki ta ya ni zama ba anti Yagana kina ji su Hajja ma fa gobe suke cewa za su tafi."
Ta furta." Na so hakan Amina Amma hankalina ya yi gida saboda Fadila ban san a wane yanayi take ciki ba tunda an ce har da karin ruwa."
Na ce." Hakane kuma to shikkenan Allah ya kaimu zan gayawa maigidan idan ya shigo in sha Allahu."
Ba tace komai ba. Na shige band'akin domin d'aura alwalar sallar magriba.

Har bayan isha'i muna tare da anti Yagana a d'aki muna tattauna mas'aloli masu yawa. Hajja ta shigo d'akin da kanta tana fad'in." Yagana tun safe da ki ka fito mu ka gaisa ki ka auri zaman d'aki ko ba kya jin dadi ne."
Ta mike zaune tana yar dariya kafin tace." Wallahi lafiyata lau Hajja kawai gajiyar tafiya ce bata sake ni ba."
Itama da murmushi da kulawa ta ce." To ku fito mu ci abinci, ke Amina kema tun d'azu nake hankalce dake kowa ya ci abincin rana babu ke, maza ku fito mu had'u mu ci abinci yanzu nan Tabawa ta kammala har ta fito mana dashi."
Na ce." To shikkenan Hajja.''
Anti Yagana ta yi murmushi bayan fitarta daga d'akin tana fad'in."Baiwar Allah nan tana sona Amina, ko da yake k'aunar da take yi miki ne ta shafe ni."
Na ce." K'warai kuwa na sheda soyayyata da Hajja ta daban ce, amma shekarun baya anti Yagana an so a juyar mata da hankali wallahi na d'an fuskanci gizago daga wurinta da na ri'ke addu'a kuma sai abin ya shud'e kamar ba a yi ba."
Ta ce." Muddin baka nufi kowa da sharri ba Amina to ko shi ya nufe ka dashi ba zai yi tasiri ba, addu'ar nan dai da ki ka rike ki ajiye a ranki cewa itace makaminki."
Na ce." In sha Allahu anti Yagana."
Tare muka fito falon duk suna zaune wannan karon Sultan yana hannun gwaggo tana d'an jijjigashi.
Kafin na zauna na ce." Gwaggo yau kece ki ke auran kenan." Tana dariya take fad'in.'' E, ai yau yace da ni yake auran."
Ina Uwani ta yi murmushi tana cewa." An jima kadan zai ce da tsohuwar zuma ake magani ni ce uwargidansa. Hajja da tunda suke maganar ba ta sanya musu baki ba sai yanzu ta ce." Duk ku gama yin jigila dashi yace ni yake so ko Tabawa." Aka yi dariya gabad'aya cikin raha da barkwanci.
Cikin wannan yanayin ya shigo tare da Kamalu dama a tare nake ganinsu duk lokacin da suka tashi daga kar'bar ta'aziyyar.
Ya tsaya suka gaisa da su Hajja kafin ya haye sama. Shi kuma Kamalu ya zauna a cikinmu Hajja ta ce Baba Tabawa ta zuba masa abinci.
Saman na bi shi ina shiga d'akin na same shi ringine a gado. Na k'àrasa na zauna gefan kafafunsa. Ya tashi zaune yana sauke ajiyar zuciya." Na gaji tubis Amina ga'bobina ciwo suke yi mini wallahi na jima ban yi gajiya irin ta wannan lokacin ba."
Na sauke ajiyar zuciya Ina fad'in." Ya za a yi abu ne da aka asassa shi amma da yawa wasu ba sa yin wannan zaman."
Ya ce." K'warai kuwa gobe idan an yi addu'ar uku zan sanya a cire rumfunan da aka kafa kowa ya tafi kuma haka ya isa ranar bakwai zan sanya masallatai a yi mata addu'a."
Shiru na yi ban ce komai ba.
Gabad'aya tunanina na kan yaranmu. Amma har yanzu ban ji yace komai ba akansu. Ba ni son na yi magana ta zama fitina zan d'an jira shi daga nan zuwa ranar da za ta cika kwanaki bakwai duk wacce za mu yi sai mu yi.
Ya yun'kura zai tashi sai ya koma ya zauna. Na ri'ko hannunsa cikin mamaki ina kallonsa lallai da gaske ya gaji. Hannunsa da na ri'ke na ji d'umi ba kamar koyaushe ba. Sai kawai na ta'ba wuyansa zafi rad'au zazza'bi ne.
Na ce." Zazza'bi kake yi fa Baba?"
Ya ce." Zazza'bi ne ko?''
Wai tambaya yake yi. Na ce." K'warai kuwa zazza'bi ne ya kawo maka sagewar gabobi da ciwon jiki, ya kamata ka samu hutu fa."
Ya sake yun'kurawa a karo na biyu yana fad'in." Bari na yi wanka zan kira likitana yanzu ya duba ni tun wajan sha biyu na rana na ji yanayin jikina ya canza ina dan jin ciwon kai ma."
Na kama hannunsa muka nufi bandakin tare na hada masa ruwan wankan ina fad'in.'" Wankan ma da ka bar shi tunda ka yi da safe. " Ya ce." Ai ba zan iya bacci ba idan ban yi shi ba Amina, kada ki damu bari na yi na fito ki kawo mini abinci."
Na ce." To a sanyaye na fito na bar shi a toilet din na sau'ka kasa cikin 'yar damuwa ya jima kuwa bai kwanta ciwo ba tun bayan zazzafar murar da ya yi a gidana sakamakon ruwan saman da ya dake shi a shekarun baya.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
🌲🌳🌿☘️

*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


*Gudun aure paid book 2k complete on telegram what'sapp Gruop Kuma 1k via 0542382124.... Binta Umar gtbank.*
*07084653262*
*120*
Yusi Ya fito daga toilet ya same su a zaune shiru. Ganin Nusaiba a d'akin ya sanya shi d'an sakin fuska ya gaisheta cikin girmamawa ta amsa da yanayi na damuwar da take ciki ta tashi ta fita. Adam ya mike babu kuzari ya shiga toilet din domin yin wanka. Shi kuma Salim ya tashi ya fita daga d'akin. Daga lokacin ya fahimci cewa bayan damuwar da suke ciki ta rashin mahaifiyarsu akwai wadda ta k'aru duk da bai ji komai ba ya san abinda suke tattaunawa a kai ba mai dad'i ba ne.
Yana nan zaune cikin zullumi da nazarin yadda rayuwar 'ya'ya take sauyawa idan suka rasa wani jigo Adam din ya fito a gurguje ya shirya suka fito falon tare wanda ya yi daidai da lokacin da Mairo ta fito tare kaf da yaran kowanne cikin tsafta. Suka nufi masaukin Hajiya Ayya mahaifiyar Alhaji Amadu kenan wadda take tare da jama'arta. Bayan sun gaisa anan wajenta yaran suka zauna twins da Minal tunda Mairo tana can suna hidimar d'orawa da saukewa kamar yadda al'ada ta zama a gidan mutuwa.
Yusi ya ri'ke hannun Khalil suka fita tare domin duk zaman da ake yi na makoki da yaron suke zaune gabad'aya gaban babansu suna kar'bar gaisuwar tare.
Shi ma bai jima da zama a wurin ba suka fito can suka hange shi yana kar'bar gaisuwa daga jama'ar da suka yi dafifi domin jiran fitowarsa.
Muna zaune a falo gabad'aya har da su Hajja duk sun yi wanka sun fito ina ta kallon yadda inna Uwani take nan nan da Hajja har goya Sultan a bayanta tana ta jijjigashi duk da ba kuka yake yi ba. Sai ta ba ni tausayi sosai domin duk tana yin hakan ne domin dakushe lefin 'yarta amma ai ba haushe yace tun ran gini ran zane Hauwa ta bata goma daya bata gyaru ba, duk da gaskiyarta babu wanda zai gani saboda abinda tayi a yanzu ya dusashe lefin da take ji an yi mata.
Suka shigo a tare su uku har da Khali da ya d'an fara tasawa abinda yake burgeni da yaron nutsuwa sam bashi da hayaniya ba za ka ta'ba cewa Tajo da Hauwa ne suka haife shi ba.
Har suka 'karaso wurin da muke zaune ban d'auke idona daga kansu ba, wannan abota da soyayyar ta Yusi da Adamu sai Allah had'uwar jini babu dangantaka ko kad'an sai ta addinin islama.
Duka muka gaisa a tsanake don d'aya bayan daya suka bi suka gaisa da kowa. Na kasa janye idona daga kan Yusi ganin yadda ya kara zama saurayi wannan jikin da ake yi masa tsiya a kai duk ya rairaye da akwai dai amma ba kamar lokacin da yake tashar kuruciya ba.
Ganin kallon da nake yi masa ya yi yawa ya sanya ya sunkuyar da kansa yana d'an kalato murmushi ya sake fad'in ." Mama ya karin hakuri."
A tak'aice na ce." Ai ku zan yi wa ta'aziyya ko Adamu."
Ya d'an saki fuska kad'an amma bai ce komai ba sai tausayinsa ya sake kama ni.
Na ce." Allah Ya yi mata rahama Annabi ya san da zuwanta. " Gabad'aya muka amsa da Amin har ni da na yi. Addu'ar. Sun d'an jima a tare damu kafin su fita Adam yana tambayar Kamalu na ce ai shi tun sassafe ya fita don ya riga ma maigidan zama a wajen.
Gabansa suka je suka zauna gabad'aya har Salim ya dube shi yana fad'in." Ku kunna wayarta ku sanar da rasuwar duk da nasan da yawa wasu daga cikin abokan nan kasuwancinta sun san ta rasu tunda an yi jana'iza da wasu amma dai
a tambayi idan da wanda yake bin ta bashi ya fad'a a sauke mata nauyi daga nan zuwa ranar da za a yi addu'ar bakwai. Sannan ka nemi yaranta ina nufin wad'anda suke yi mata hidima ta kasuwanci idan da wanda yake da hakki a kanta ya fad'i a biya shi. Sanin da na yi ita mai bayarwa ce amma hakan ba zai hana a bibiyi abubuwan da ta wanzar a lokacin da take rayuwa ba, wannan shine gatan da ni daku zamu yi mata bayan addu'a."
Ya amsa cikin ladabi tare da tashi da sauri can rumfar da ya hangi yaranta sun zauna jiya ya nufa wasu sun zo daga ciki wasu kuma ba su zo ba kawai sai ya nufi cikin gidan domin kar'bo wayarta dake hannun Nusaiba tunda Allah Ya taimaka har da manyan wayoyinta masu tsada ta kwashe a lokacin da ta had'a da katin cire kudinta.

Yana nan zaune jama'a na 'barkowa ta ko'ina abokanansa wasu daga cikin abokanan tsohon mijinta da 'yan uwansa dama wasu sam da bai san daga ina suke ba sukan tsuguna gabansa da tafka tafka rawaninsu a kan su suna yi masa gaisuwa.
Wani daga cikin masu rawanin ya sake komawa wajansa ya gurfana Yana fad'in." Allah Ya taimake yanzu yaron mai rasuwar na ji yana magana a wajan da muke zaune cewa idan da wanda yake bin marigiyar bashi ya fad'a, to ina daya daga cikin wad'anda ta sanya a aiki."
Ya dube shi a tsanake kafin ya furta.'' Wane aiki ka yi mata, kuma nawa ne hakkin naka?"
Ya gyad'a kansa tare da dan juyawa yana waiwaye akwai jama'a sosai don dai hayaniya tayi yawa amma duk da hakan ko da suke maganar bai fasa kar'bar gaisuwa ba tunda har yanzu shigowa ake yi.
Cikin nazari ya ce." Ko akwai buk'atar sirri ne?"
Da sauri ya d'aga kansa yana fad'in."E, kwarai kuwa Yallabai."
Sai ya ce." To babu damuwa fita waje ka tsaya jikin gate zan fito yanzu na same ka."
Ya kuwa tashi da sauri yana sa'be babbar riga ya kama hanyar fita. Ya bi shi da kallon nazari kamar akwai rashin gaskiya a tare da shi. Yaran duk suna gefensa a zaune ya tashi ya bi bayansa.
Ya zuba hannuwansa duka biyun cikin aljihun tazarcen dake jikinsa tare da fad'in." To ina jin ka Allah Ya gafarta Malam."
Ya risinar da kansa yana fad'in." Hakika Maryam ta sanya ni aiki babba a wannan tsukin da Ubangiji Allah Ya d'auki rayuwata. Mun gama magana da ita akan kudin kayan aiki da duk abinda za a buk'ata wurin biyan buk'ata dubu dari bakwai da ashirin to sai ta kwanta ciwon nan da bata tashi ba daga shi kuma ba ta turo mini kudin ba ni kuma na juya dana hannuna na fara aiki domin nasan bata da wasa akan samun biyan bukatarta wallahi yanzu haka daf nake da kammala aikin kwatsam sai rasuwarta na ji kuma dama a satikan da suka wuce ba ni samun wayarta hankali ya tashi wallahi domin na riga na juya mata kuma kaf abinda yake hannuna kenan."
A tsanake ya ce." Wane aiki ne? kuma nawa ne kudinka."
Ya yi dan Jim kafin ya ce ." Duka dubu dari bakwai ne da ashirin kamar yadda na gaya maka da farko abinda ya ja kud'i shine rago mai tozali da muka nema akan aikin. Sai fatar karsana sannan mun nemo zuciyar jemage, akwai kuma kaji da muka saya jan zakara, wake-wake ba'kar kaza da kuma turarukan da muka saya wurin yin aikin."
Shiru ya ratsa wajan bayan gama maganarsa. Ya ce." To, na ji wane aiki aka yi akan hakan."
Ya yi shiru tare da yin kasa da kansa sai da ya kara maimaita tambayarsa tukkuna ya ce." Alhaji a zahirin gaskiya ni ina daya daga cikin manyan Malam Hajiya Maryam kuma duk lokacin da ta buk'aci wani aiki muna ko'karin ganin mun gudanar dashi duk rintsi domin samun biyan buk'ata. Wannan sirri ne tsakani na da ita amma yanzu ta ta 'kare sai dai mu ro'ka mata gafara wurin Ubangiji. Dole ta sanya ni neman ha'kkina domin dai aiki gaf nake da kammala shi rasuwarta ta katse na taho. Kuma kudin hannuna sun yanke Hajiya Maryam aiki ta sanya ni na yi akan wata baiwar Allah mai suna

19 / 73