Author : Binta Umar Abbale Category : Read Hausa Novels
amsa mini da to shikkenan.
A gabana ya kira likitan ya yi masa bayani sosai yadda zai tsara malamin duk da aikinsa ne wayar da kan jama'a akan mas'aloli masu yawa a matsayinsa na likita amma dai ya kara tunasar dashi cewa wajan wanda za su je babban malami ne kuma mai tsauri wanda boko bata ratsa shi ba sai tsantsar tauhidi da kadaita Allah ."
Ya kira Hauwa ta ce sun taso tun wajen shida yanzu kuma k'arfe shida da rabi kenan sun yi minti talatin akan hanya.
Har mun yi sallama zai tafi ya dawo yana tambaya wai sai na gaya masa wanda zan nemawa auran idan dashi bai yi yuwa ba.
Na ce." Me kake ci na baka na zuba, za ka san shi in sha Allah."
Sai kawai ya girgiza kansa babu kuzari ya furta." Sai na dawo." Ya fice da sauri Minal tana fad'in." Baba sai ka dawo."
Ya daga mata hannu ba tare da ya amsa ba ya fita.......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*150*
Na sake sauke ajiyar zuciyar da ba zan iya lissafa adadinta ba.
Hannun yarinyar na ja muka nufi d'aki ina mamakin sha'anin Hauwa ni yanzu ma ta daina ba ni haushi da mamaki dariya take ba ni wallahi.
Gefan gado na zauna kafafuna na dan rawa haka kawai nake jin faduwar gaba da fargaba akan wannan sha'aninan wani sashe na zuciyata na gaya mini bai zama lallai malamin ya yarda da duk wani nau'in bayani da za a yi masa ba akan wannan lalura. Wanda na gama fahimtar cewa abinda shima ya assasawa maigidan gigita kenan da damuwa da kuma rashin nutsuwa. A nasa tunanin idan malamin ya kafe akan ra'ayinsa sai kawai ya bari a d'aura auran wanda hakan ba ita mafita ba tunda da wani kudiri a ransa da kuma abinda ya niyyata akan yarinyar wanda yake nuna tsantsar son zuciya da rashin tausayawa kuruciya. Malam D'aha Malami ne kuma mutumin da ne kuma mutumin karkara wanda ba shi da wayewa da ilimin zamani na boko abu ne mai wahala duk bayanin da za a yi masa akan illar ciwon ya amince da cewa ba kutse aka yi wa shariar Ubangiji ba gashi dai bincike domin samun mafita ya sanya har manyan likitoci da shugabanni suka kafa dokar yin gwajin jini kafin k'ulla rayuwar auratayya ta din-din don samun sahihan yara masu wadatacciyar lafiya.
Jikina a mace na dauki wayata dake saman dirowar gefan gadona
babu wanda na yi wa sha'awar auran yarinyar Hajara sai Usaini. Yaro ne nutsatstse mai kuma zuciya tun yana yaro ba shi da matsala har zuwa yanzu da ya kai munzalin girma. To sai dai kuma hanzari ba gudu ba anan shine duk da bai zama dole ba wata'kila Usaini yana iya zama As tunda ni ma itace mun had'a uba uwa kowa da tasa. Na ji daga bakin mutane da dama cewa yana iya canzawa a wasu lukutan amma zuciyata ba ta gazgata hakan ba a ganina idan har sakamako na farko ya nuna matsayin jini da wahala ya sake canzawa. Can kasan zuciya na ji tana gaya mini cewa babu lallai Usaini ya kasance As don kin kasance Amina. Wannan hasashen na zuciyata ya kara sanya mini kwarin gwiwa sosai
Har indai k'addara ta raba auran da za a daura shi a yau kuma za su ba mu yarinyar zan yi farinciki da hakan domin kuwa duk inda ake neman nutsuwa da tarbiya yarinyar ta kai daidai gwargwado kuma ta yi sa'a da auransa tunda shi ma bai wuce ashirin da takwas ba.
Bugun farko ya daga na ji shi cikin kasuwa da hayaniya a wajen da yake. Sama-sama nake jin maganarsa na ce." Har ka fita kasuwa Usaini k'arfe nawa yanzu.
Yana dariya ya furta." Takwas saura anti akwai ba'kin da muka yi daga nijar sun yi sayayya jiya mun had'a musu kayan ba su samu damar d'auka ba sai yau da sassafe suka yi mini waya yanzu na shiga kasuwar ma anti."
Na ce." Allah Ya taimaka idan ka sallame su kazo gidana na sharad'a na zo garin yau kusan sati daya kenan akwai maganar da za mu tattauna."
Ya furta." Ba na son rufe shago anti afuwaa zan iya jira Hamusu ya zo tunda sai tara da rabi yake zuwa kasuwar."
Na ce." Babu matsala ka jira shi idan ya zo sai ka taho ina sauraranka."
Sallama muka yi na kashe wayar na ajiye zuciyata na yi mini wani nazari. Kada fa Ummansu ta bijire akan wannan yun'kuri nasan ba ni da matsala da yaron haka zalika ba ni da matsala da Babanmu Ummansu Saminu itace birkitacciya dama tana jin haushi tana ganin duk sabgata idan ta tashi ba a gayyatarta gidana na abuja bata ta'ba zuwa ba Ummansu Hadiza ce ta je sau biyu ta jima tana yi wa anti Yagana wannan korafin tana gaya mata ita ba mu d'auketa a matsayin uwa ba duk hidimarmu idan ta tashi sai mu nemi Ummansu Hadiza kuma abin ba haka ba ne Ummansu Hadiza ta fita shishshigi ita kuma duk abinda zai faru sai ta ce lallai sai an gaya mata ba idan ba mu sanar da ita ba sai ta k'ullaci abin a cikin ranta. Itace damuwata kawai tunda d'anta ita take da iko da abinta idan ta ce bata yarda ba babu yadda zan yi dole na ha'kura amma zahiri na yi wa yaron sha'awar yarinyar.
Na nemi lambar anti Yagana ta katse ba ta daga ba ina sake kira kuwa ta daga muka gaisa ta ce." Ya ake ciki Amina Ina fatan babu matsala rashin sukuni ya hana ni kiran ki na ji ya ake ciki."
Na ce." Alhamdulillahi babu matsala ina ganin zan ci nasara akan abinda nake so in sha Allahu dama dalilin da ya sanya na kira ki wata shawara nake so mu yi shin ya ki ka ga ni?"
Duka na kwashe abinda yake faruwa na gaya mata. Ta ce." To ai wannan ba matsala ba ce Amina alheri fa ki ke niyyar k'ullawa ban ga dalilin da zai sanya mahaifiyarsa ta nuna rashin amincewarta akan hakan ba ke din Yar uwasa ce kuma ba za ki had'a shi aure da yarinyar da ba ki tabbatar da tarbiyarta ba. Bayan dangantaka ta jini ke uwar dakinsa ce a karkashinki yake idan tana da kunya ai ba zata kalubance ki ba."
Na ce." Hakane anti Yagana amma a cire maganar uwar d'akin nan na dai zauna a matsayina na 'yar uwarsa dalili anan shine ba ni so shi da mahaifiyarsa suga don yana karkashina zan juya masa rayuwa a yanzu ma idan ya zo zan fara tambayarsa shin yana da budurwa tsayayyiya idan ya ce bashi da ita sai na gaya masa shirina. Ina da tabbacin ba zai bijire mini ba."
Ta ce." Misali na yi miki ai idan ta yi tsalle ta nuna d'anta sai a nuna mata ke kuma uwar dakinsa ce a kasuwa sanadinki har yake saya mata atama super ta daura ta yafa mayafi mai tsada ."
Dariya ta kama ni ina fad'in." Anti Yagana kenan, to kin ji dama dalilin da ya sanya nace bari na gaya miki kafin na yanke hukunci Babanmu bashi da matsala hakan zai yi masa dad'i."
Ta ce." Ni ma na baki goyon baya amma kafin nan ki fara tambayarsa genotype dinsa da blood group idan ya sani shikkenan idan kuma bai san matsayin jininsa ba sai ya yi maza yaje a yi masa
Na ce." To shikkenan haka za a yi in sha Allahu anti Yagana a gaishe mini da masu jegon."
Ta ce." Gasu nan suna bacci gabad'aya tunda aka yi wankan safe suka kwanta." Na yi dariya ina fad'in." Fadila manya a shafa mini kan Shahida." Sunan anti Yagana aka sanyawa yarinyar sai uwar tace tana so a dinga kiranta da Shahida a lokacin da ta fad'i hakan na ce wata shekarar sai ki haifo Shahid. Kunya kuwa ta kamata na ce to idan ba rashin kunya ba duk muna zaune ita zata za'bawa 'yarta suna ai ta yi kara ta bari a samu sunan da za a dinga kiran yarinyar tunda ai dole a sakaye dalilin sunan uwarta ne.
Goma da sha biyu ya kira ni a waya ya shigo gate amma maigadi ya hana shi shigowa. Na sanya hijabina na fita harbar gidan suna daga can bakin gate har da Ayuba direba.
Ganin fitowata ya sanya ya kafe babur dinsa Yana kallon Ayuba yake cewa." Idan shi zai ce bai gane ni ba ai kai za ka sheda fuskata ko ba kai ba ne direban da ka dinga zurga-zurgar kai su asibiti a lokacin da Babanmu ya kwana rashin lafiya."
Ayuba ya dinga fad'in." Tabbas ni ne yanzu na sheda fuskarka ka yi hakuri wallahi d'ayan muka fi ganewa." Yana nufin Hamusu. Shi kuma Usaini haushi ya ji yadda suka tsayar dashi a bakin gate suna tuhumarsa domin ba mu yi kama ba ko daya gashi kuma ya ce musu shi kanina ne kuma zuwansa daya gidan shiyasa suke yi masa wanna titsiyar Hamusu suka fi shedawa."
Ayuba ya biyo shi a baya yana dan bashi ha'kuri na ce ya je kawai babu komai suma suna kan aikinsu ne babu lefi don sun ga bak'uwar fuska sun nemi dalili.
Da yake safiya ce ko ruwan da na ajiye masa bai sha ba muka gaisa sosai da bayan rabuwa zafin nemansa ya sanya shima ko gidana na Abuja bai taba zuwa ba kullum yana kasuwa a sanin da na yi masa tun Yana yaro manemi ne baya zama duk wasu lissafe-lissafe da za mu yi ta waya muke yin komai kamar dai yadda muke yi da Hamusu abinda ya gaya mini shima Usaini haka zai gaya mini sun yi bala'in cirar tuta a wajena dalili kuwa anan shine ni kaina sai dai na ce dukiyar itace tawa ta farko kenan da na zuba domin gudanar da kasuwancin abinda zai ru'banya daga baya kuwa duk kokarinsu ne kuma duk inda suka hango cigaba da sauri za su gaya mini a jarraba ko za a samu nasara. Shekara na yi kuwa za a yi lissafi a fitar da riba da uwar kudi a sallami kowa hakkinsa. Usaini yana tura kayanmu gari-gari ta hanyar yanar gizo an san shi sosai kamar dai yanzu da yake gaya mini ba'ki sun zo daga nijar domin sayan kaya ba ni tamtama a online suka had'u."
Ya dinga jan Minal da wasa tana janyewa na rashin sabo har sai da ya samu nutsuwa tukkuna na dube shi a tsanake na ce."kasan dalilin kiran ka da na yi?"
Ya girgiza kansa a hankali yana fad'in. A a anti amina Allah ya sa lafiya."
Na ce." Lafiya lau kuma alheri ne."
Sai ya saki fuskarsa sosai har da gyara zama yana fad'in." To Ina jinki anti ko za mu sake bude wani shagon ne?"
Na ce." A a matar aure na yi maka."
Saranda ya yi ya zare ido yana fad'in." Matar aure anti a ina take kuma? ban gama gini na ba dalilin da ya sanya kenan na janye idona daga kan 'yan mata domin ba ni so na fara soyayya da budurwa iyayenta su ce na fito. Ni kuma nafiso sai na kammala komai a tsanake sai na nemi mai hankali daidai da ni na aura."
Murmushi na yi Ina kallonsa yana ta jero mini bayani wanda na tabbatar da cewa gaskiya ce tsantsa kuma duk maganar da ya furta tana fitowa ne da can kasan zuciyarsa.
Na ce." Maganar gini mai sau'ki ne Usaini don ma dai ka d'auki irin na zamani da kyale-kyale ai da tuni ka gama ko ba shine wanda ka ta'ba turo mini ta waya ba kwanaki."
Ya ce." Eh shine gidan anti amma yanzu aiki ya kara nisa."
Na ce." To alhamdulillahi Usaini wata yarinya ce na yi maka sha'awarta nutsatstsiya kuma 'yar Malamai idan har Usaini ya samu nasarar mallakar yarinyar nan ina yi masa albishir da cewa ya gama dacewa da ma'aratussaliha."
Ya yi murmushi yana fad'in.'' Kai anti Amina wannan yarinyar a ina take yadda na ji kina kwarzantata wallahi har kin kwadaita mini ita a cikin raina."
Nasa dariya ina cewa." Ka ji d'an gari ko, sai ma ka ganta doguwa chocolate color ga ka farar fata yaranku za su zama wata kala masu kyau."
Ya sunkuyar da kansa yana murmushi."
Na ce." Ka amince kuma ka bar mini wuka da nama a hannuna?"
Ya gyada kansa yana fad'in." Na amince anti Amina wallahi ba ni da ja kuma ba ni da haufi a kan ki na yi farinciki da wannan zabin da ki ka yi mini tun banga yarinyar nan ba har ta zauna a zuciyata.
Fuskata ta kara yalwata da annashuwa na ce." Aikuwa na gode sosai na ji dadin wannan alfarma da ka yi mini amma yau din nan nake so ka sanar da Ummanku duk abinda yake faruwa kuma ina son sanin matsayin jininka."
Ya ce." Zan gaya mata a yau din in sha Allah. Matsayin jinina kuwa( O) ne genotype (AA)"
Wani irin sanyi ya sauka a zuciyata shikkenan an samu yadda ake buk'ata ta wannan bangaran akwai dacewa da cancanta wancan bangaran ne kuma ban san wainar da suke toya ba. Gabana ya fadi na daga kai na dubi agogo sha daya saura kuma yadda suka tsara jadawalin d'aurin auran bayan an yi sallar Juma'a ne.
Na saki ajiyar zuciya ina fad'in ." Ma sha Allah ta kowane bangare an samu daidaito idan har Allah Ya kaddara wannan auran Usaini ina yi maka murna sosai domin ka yi mata."
Ya ce." Na gode sosai anti Allah Ya saka da alheri ya kuma kara girma abinda ki ke yi mana na zumunci Ubangiji Allah sanya miki a mizani Allah Ya jikan iyaye da kakanni."
Na dinga amsawa da Amin Amin Allah Ya taimake mu gabad'aya."
Muka yi sallama kafin kafin ya tashi na gaya masa zuwa dare zan kira shi domin karin bayani.
Ya kama hanya ya tafi na zauna cike da nazari da zullumi hankalina kuma yanzu ya yi can garin bunkure ko a wane hali ake yanzu bai kira ni ba nasan kuma tuntuni ya isa garin tunda babu wata nisa.
Na d'auki wayata gabana na d'an fad'uwa na lalubi lambarwa wayar na shiga sai dai har ta katse bai daga ba. Na sake kira a karo na biyu nan ma bai daga ba jikina ya mutu na ajiye wayar da rashin kuzari."
BUNKURE.
Cike gidan yake zuri'ar Malam D'aha 'ya'ya da jikoki kadai sun isa gayya ba sai sun gayyatowa kowa ba. Amma da yake wannan sha'anin na mussaman ne a gare shi gidan cike yake da nau'in ba'ki daga gari gari nasa da na matayensa mussaman uwar bikin uwargidansa mahaifiyar amarya wato Inno.
An gama towon d'aurin aure suna ta malmale shi a leda ana zuba shi a manyan kuloli gefa guda kuma kirigar tukuwanan miya ne guda biyu kan murhu suke ta cin wuta suna zab'abbaka da tashin kamshi mai shanana a saman miyar.
Yaran mata surukan gidan suna can bakin turgijejiyar bishiyar darbejiya da ba a samu nasarar tun'buketa ba a lokacin da aka sabunta gidan suna ta d'aura zobo a leda suna zuba shi a wani mazubi mai girma. Kowa ka gani cike yake da annashuwa da farinciki daka kan iyayen 'ya'yansu da jikokinsu da surakansu.
Zaure malamin kuwa daga can bayan gidan akwai kofar da aka yi masa ta mussaman domin ba'kinsa wanda Malam Rabi'u ya buk'aci da a yi hakan dalilin gidan akwai matansu babu cancanta maza ma bambamta na shiga gidan kai tsaye duk da sashen malamin daban yake amma dai tilas ta tsakargidan za a bi kafin a isa zauran nasa kuma wasu lukutan iyalansu na fitowa.
Ta wannan kofar suka shiga zauran malamin shi da Dr Iliyas ba kowane ya san da zuwan na su ba.
Malam D'aha na sanye da manya kaya babbar riga da 'yar ciki shadda mai kyau daidai gwargwado da d'inki manya cike yake da Kamala da nutsuwa amma kana duban fuskarsa za ka gane cewa lallai yana cikin farinciki dalilin wanzuwar wani lamari da wata'kila ya jima da shi a zuciyarsa.
Tun bayan gaisuwar da suka yi da shi sai jikinsa ya kara mutuwa kwarai da gaske ya ji a ransa baya buk'atar wannan annashuwar da take fuskar malamin ta dusashe domin kuwa lamarin da suka zo dashi gare shi babba ne wanda zai iya rushe duk wata walwalarsa.
Lallai ne akwai buk'atar zama akan wannan mas'alar mai sark'akkiya kamar yadda mai d'akinsa ta gaya masa ya makara a yanzu ba lallai ne malamin ya yarda da uzurinsa ba tunda ai ya jima da bashi yarinyar mai yasa bai kawo tasgaro ba sai yanzu da aski ya zo gaban goshi
Jikinsa ya yi tubis bakinsa ya mutu d'akin ya d'auki shiru bayan gama gaishe-gaishe daga shi har Dr Iliyas din sai zare ido suke yi domin dai malamin bai fito ba sai da shirya Kuma yawanci irin wad'annan malaman masifar kwarjini ne da su da cika ido.
Dr Iliyas duk 'kumaji da karsashinsa na k'wararran likita sai da jikinsa ya mace ganin yadda wanda ya gayyato shima jikinsa ya yi la'asar sai rarraba Ido yake yi yana sinne kai wannan lamari yana da wahalar fahimtarwa a wajen irin wad'annan mutanan da tauhidi ya yi wa k'awanya da kuma rashin samun ilimin boko mai zurfi ga kuma rayuwar karkara abin dai goma da ashirin.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*152*
Suka juya gabad'aya suna kallonsa a lokacin da ya fara magana kamar haka. " Ya kamata a k'ara duba wannan uzurin da suka zo da shi Allah Ya gafarta Malam nasan da wahala Alhaji Tajo ya d'auki aniyyar tozartaka a irin wannan ranar da gabad'aya ta zame mana abar alfahari da farinciki mussaman da muka tabbatar da cewa wanzuwar lamarin shine abinda ka fi buk'ata a yanzu domin sake kulla zumunci mai karfi tsakaninka da abokinka Alhaji Ibrahimu Allah Ya yi masa rahama da gafara."
Suka amsa da "Amin gabad'ayansu kafin ya sake nutsuwa sosai ya cigaba da cewa zahiri wannan lalura da suke magana akanta akwaita kuma har