Author : Binta Umar Abbale Category : Read Hausa Novels
sannan ka fitar da rikicin da ya faru a gidan nan har jama'a suna yamadidi da mu cewa mun had'e mata kai ni da Hauwa ba ma yin mu'amula da ita."
Ido ya tsira mini a rikice ya ce." Yanzu wanene ya kawo maganar Kamalu anan?"
Na ce." Ni ce na kawota domin na yi iyakacin bakin kokarina akan na ga na danne maganar a zuciyata na kasa abinda ya sanya ni sake gazgata cewa kai ka gaya mata a ina mutane za su samu labarin zaman da muke yi har su zage mu akan mun ware matarka tuntuni ka nuna hadin kan dake tsakanina da Hauwa baka so saboda ba mu sanya matarka a cikinmu ba har ka gaza ha'kuri ka fitar da maganar duniya."
Ya jima yana kallona cikin tashin hankali kafin ya ce." Ni ko Hajja ban ta'ba gayawa sirrin gidana ba mahaifiyata kenan. Baban Saude shine mutumin da nake ganin zan gayawa matsalar da ta shafe ni ya ba ni shawarwari saboda na yarda da nutsuwa da adalcinsa kuma ki ji tsoron Allah Amina
Idan har za ki yi mini adalci ki fadi gaskiya akaina kada neman fitina ya sanya ki haddasa mini ciwo, ki fadi gaskiyar abinda ki ka sani a kaina na daga da'bia na tabbatar da cewa tsayin zamana dake zaki gane abinda zan aikata da kuma wanda ba zan aikata ba mai zai sanya kawai na zaunar da Maryam na gaya mata abinda ya faru a baya me yasa zan yi haka? Uhm me yasa zan aibata Kamalu a wurin Maryam saboda soyayya ta yi mini dadi."
Ya kai karshen maganar cikin yanayi na damuwa da alhini."
Na ji hawaye sun zubo kumatuna ban goge ba na ce." To a ina ta samu labari idan ba kai ka gaya mata ba, ita kuma ta gayawa yaranta."
Ya yi d'an jim kafin ya furta." A lokacin da abin ya faru ke kan ki fa kin yi dogon rubutu a social media wato fecebook rubutun da ya zagaye kowace kafa ta sadarwa wanda bai san akan wane dalili ki ka yi rubutun akaina ba zai je ya bibiyi ba'asi kin manta da haka? kin manta cewa Salim zai iya cin karo da labarin ke ma fa kin bada gudummuwa wurin 'kara rura wutar lamarin domin dai kin san matsayina rubutunki kuma ya janyo cecekuce da yawa, me yasa za ki d'ora mini lefi?''
Shiru na yi ina kuka domin bakin cikin abinda ya faru ne gabad'aya ya taso mini.
Ya tashi tsaye yana fad'in." Ke duk yadda mutum ya so da ya zauna lafiya dake ba za ki ba shi damar hakan ba, ba ki iya rarrashi da tarairaya ba sai neman fitina."
Ya tafi ya je ya kwanta saman gadona tare da rufe k'afafunsa da bargo. Kuka na ci na koshi yana kallona bai ce mini komai ba. Na shiga bandaki na yi wanka na fito duk idonsa biyu na shirya jikina da kayan bacci.
Abinci na zauna na ci kad'an kafin na kwashe kayan na kai kicin na dawo d'akin yana dai kwance amma bai yi baccin ba.
Gefansa na zauna ina d'an kallonsa gabad'aya ya yi sanyi yanayin damuwa ya bayyana a fuskarsa.
Ban ce komai ba na ra'ba daga gefansa na kwanta ina jin bai fi sau uku ba ya ta'ba kwana a d'akina ba.
Ya mik'a hannu ya kashe fitilar gefan gado kafin ya janyo ni jikinsa sosai ya matse ni a kirjinsa muka sauka ajiyar zuciya kusan a tare jikinsa na dan rawa na ji maganarsa a hankali cikin taushi da rarrashi Yana fad'in." Da zan iya ha'kuri dake Amina da tuni na yi, Allah Ya jarrabe ni da sonki kada ki ga haka ki nemi halaka ni don girman Allah."
Shiru na yi ban ce masa uffan ba ina jin dai yadda hannunsa keta zarya a sassan jikina. yana mika bakinsa wuyana yana sumbata cikin sar'kewar murya yake fad'in." Mu yi soyayya irin wadda na Annabi s.a.w ya koyar Amina kada mu cutar da wani sashe na jikinmu ina buk'atar kulawa a yau ta mussaman kada ki yi mini 'kwange ki marabce ni da zuciya da gangar jikinki."
Na dai yi masa shiru ban tanka ba zuwa lokacin ma na fara bin layinsa. Ya dago fuskata yasa bakinsa yana ta sumbatar kumatuna kafin ya fara ko'karin had'a bakinmu wuri d'aya. Hannayena na sanya a tsakaninsa na janyo shi sosai muka had'e bakinmu cikin wata masifaffiyar runguma wadda take motsa duka ga'bban jiki.
Washe gari da safe kafin ya fita har da yi mini wa'kar soyayya ta Hamusu bireka tun ina daurewa har dai na gaza na dinga kyalkyala dariya ganin yadda yake ta rero wa'kar (Ashe da rai nake sonki jaruma ba da zuciyata ba, komai ruwa da iska akan ki ba za na daina kewa ba, idan na same ki.....) Na tambaye shi a ina ji ya wa'kar har ya haddace baitikan irin haka ya ce a gari ya ji shima. Kai na ci dariya sosai da ya fita na ce lallai na cinye wasan a daran jiya kenan irin wannan wa'ka haka......✍️
2k complete on telegram via 0542382124...binta Umar gtbank
*07084653262*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: Na jima kwance kafin na ji shigowar sa yana shafa bayana ban motsa ba "Ki yi hakuri My Lima, na je wurin Anna ta fada mini abin da ta fada miki. Kin san sha'anin manyan nan ki yi hakuri."
Na tashi zaune na fadi "Ya wuce."
Yawwa my lima zo ki hada mini garin."
Na mike na fita na hada mishi ya sha ya sha magani sannan muka kwanta.
Na dade barci bai dauke ni ba ina tuna maganganun Anna, duk da ina jin a matsayin ta na suruka bai kamata ta fada mini ba, gefe guda kuma sai na ji tamkar allura ta yi mini ta kuma farkar da ni. Ba zai zama abin damuwa wurin Mama ba in haihu ta ki yi mini abin da ya kamata, har wanda yan'uwa suka hada ta hada ta rike.
To ina mafita? Na tambayi kaina, "Allah ka ba ni mafita."
Na furta a hankali.
Da gari ya waye ranar zan fita girki, tun da na fito da safe Fauza ke ta kai da kawo tana kalkale falonta ga kamshi na musamman ta sanya, girki ma tun a sannan ta fara da na tabbatar shi ma na musamman za ta yi. Kirjina ya cushe ina lissafin da garin mu nake in tafi gidanmu ko gidan yan'uwa.
Hamid da ya shirya fita da wuri na tambaye shi zuwa gidan Innar su Aminu, ya ce A'a bai son yawan fita.
Komai ban ce ba ballantana ta kai ni ga magiyar ya bar ni, na gyara na kwanta.
A dakin na wuni ko abinci ban fita na nema ba. Na idar da sallar la'asar ina zaune kan sallayar wayata ta dauki kara na juya inda take sai na dauko ta, sunan Aminu ke yawo saman Screen din na daga bakina dauke da sallama ya ce "Aunty ina waje na zo gaishe ki."
Na dan yi murmushi "An shigo garin kenan? Ina zuwa."
Na yunkura sai na mayar da mayafin doguwar rigar da ke jikina na taka na fita dakin.
Kamshin girkin Fauza da kamshin turaren falon ya hadu ya ba da kamshi na musamman, ba kowa falon na koma dakina na ciro plastic chair da na saya guda biyu ko da zan yi bakon da dole sai na zaunar da shi a falon sai na sanya mishi.
Na fita har zuwa zauren gidan inda na tsinkaye shi, da fara'a nake yi masa sannu da zuwa tare da yi masa jagora muka shiga ciki, a saman daya daga cikin kujerun na yi masa tayin zama, na wuce kitchen na kawo masa ruwa, sannan na zauna a daya kujerar muna gaisawa na ce "Ina amarya? Ba ka kawo mani ita ba, sai wani za shi daga gidan Inna, in bi shi na gano ta."
Ya yi murmushi "Zan ma kawo miki ita Aunty."
Daidai nan Fauza ta fito daga dakinta ta dube mu, muka dube ta, ganin ta yi hanyar kitchen ya ce mata "Ina wuni?
Lafiya kawai ta ce ba tare da ta waiwayo ba.
Hira muka yi da ba ta wuce ta mintuna biyar ba ya mike bayan ya ajiye mini Envelope a kujerar da ya tashi.
Na bi shi ina mai godiya a gare shi, sai da na dan taka masa sai na juyo na koma dakina na bude envelope din rapper guda ce ta yan dari biyar"Dubu hamsin." Na fadi wani tunani na shiga kwanya ta.
Na janyo wayata na yi ma Hajara flashing don ba kudi a tawa wayar. Ba bata lokaci ta biyo tana mini tsiyar na shige Karfi na yi shiru.
Na tambaye ta yaranta da mai gidanta da can wurin Inna ta kuyanbana sai da muka tattauna har kan Haj Iya da ciwon kafarta ya motsa sannan na gangaro kan dalilin da ya sa ni kiran ta.
"Wasu kudi na samu Hajara, shi ne nake so na turo miki ki samu wani abu da ya danganci masu haihuwa ki saya mini."
Kamar ya ban fahimce ki ba."
"Ina nufin abin da ake kawo ma mace idan ta haihu daga gidansu."
"Lallai ma Halima mu duk yawan mu aikin me muke da ba za mu yi miki ba har sai kin kawo kudinki?
Na ce "Ba haka ba ne, ki dai yi hakuri zan dinga turo miki da na samu, kin san sha'anin gidan yawa, ga kishin sauri, ga uwar miji, ga kishiya a gefe."
Ta ce "Na fahimce ki. Allah ya raba ku lafiya."
Sai kuma ta fara mini iya shege "Iyee ta Hamid din ba, Karfi ta amshe ki har kin fara tara kudi? Na yi yar dariya na katse kiran ina tunanin wanda zan ba kudin ya kai mini wurin masu POS, shigowar sako daga wayata ya sa na dubi wayar Hajara ce ta sanya mini Credit na 500 na ji dadi na tura mata sakon godiya sai na kira Haj Iya na tambaye ta kafa na kashe na kira kanwata Bilkisu, muryar Naana na fara ji cikin kukan shagwaba tana fadin a kai ta wuri na.
Na lallashe ta na ce ta bari a yi hutu kasan zuciyata kuma zullumi ya rufe ni, Naana ta zo a wannan hali da ake ciki akwai kura, yaro bai san babu ba, ina kudin da za mu yi mata yadda ta saba?
Bilkisu ta karbi wayar tana fadin "Allah Aunty yar nan taki tana ba ni ciwon kai." Na ce "Me take miki Aunty Billy? Ta ce "Na kusa fara zane ta." Na ce "A'a ba a yi haka ba me take yi?
Ta ce "Sangarta mana. Yanzu haka ta sa na fara tunanin da zan samu aiki."
Na ce "Aiki kuma ko karatun ba a kammala ba?
Don Hamid ya nema mata gurbin karatu a ABU Zaria ya roki Baba ya bar ta ci gaba da karatu ita kanta ba kananan kudade ya kashe mata ba duk don tana kula masa da Naana.
Ta ce "Hmm ba za ki gane ba Aunty. Yau tun da ta dawo Sch ta sanya ni gaba sai na fita da ita ta sha Ice cream, Uncle dinta Abdullah ya ba mu 2000 na samu na aika aka kawo mana Ice cream din.
Ta kwanta tana kuka sai na kai ta Smart kick ina na ga kudin motar zuwa KD da abin da za mu kashe?
Na ja ajiyar zuciya "Zan turo 7k Aunty Bilkisu, ki rike ku lallaba kina saya mata abin da take so."
Shi kenan Aunty mun gode. Amma Naana ba ta san a lallaba ba. Teddy dinta yaron Aunty Sakina ya taba daga zuwa ta birkice ba ta so yanzu ita zan samu na saya mata kullum sai ta yi mini kukan banza
Na ce "A yi hakuri Aunty Billy. Ina jiyo muryar Mama tana sababin hidimar Naana da muka sakar musu.
Naana ta karbe wayar tana ba ni labari, duk wani abu da aka yi mata sai ta fada mini, da kyar na samu ta bar ni ba ta cinye kudaden wayar ba.
Na ajiye ta ina son fita in nemi abin da zan sanya ma cikina amma ba na son haduwa da Fauza, na daure har sai da na yi sallar magrib ina kan sallaya Hamid ya shigo wanda tun fitar shi da safe sai yanzu ya dawo na gaishe shi ya tambaye ni gobe zan koma Hospital na ce E ya ciro kudade ya ba ni na karba da godiya tare da ba shi labarin zuwan Aminu, ya fita ya ce mini zai je ya ci abinci.
Na tashi daga inda nake na hau katifa amma cikina ya ki ba ni hadin kai, da gasken gaske yunwa nake ji.
Na mike kamar mai tafiya kan kwai na fita dakin, ba kowa falon na shiga kitchen, ina da sauran Indomie ita na dafa cikin sauri na juye a flate na dauki ruwa na hada na fito, idona ya yi kyauyawan gani Hamid da Fauza suna cin abinci ta sheka ado cikin wani kankararren leshi wuya da hannu suna ta shekin sarka da yan kunne, na kawar da fuskata na wuce daki.
Na zauna ina cin indomie a hankali zuciyata na can ga tunanin kwalliyar da Fauza ta caba, ji na yi zuciyata na nadamar suturuna da na kyautar, yanzu sai dai na yi kallon Fauza na cancada kwalliya yayin da nake fama da suturu masu rangwamen kudi.
Na yi nisa cikin nadamar sai na ji kamar an mintsine ni, take na dawo cikin nutsuwa ta, istigfari na shiga kirgawa da yatsun hannuna.
Ba karshen nadama da ta wuce ka tashi gaban Ubangiji ka rayu da cin haram, suturar haram.
"Zan jure komai ya Ubangiji." Na fadi kamar mai magana da wani.
A daddafe na cinye Indomie na sha ruwa sai na yi shirin kwanciya.
Wayata na dauka ina dannawa sai na ji bugun kofa da na san Hamid ne na kasa motsawa don wani sake-saken daga zuciyata har ya gaji ya tafi na gyara kwanciyata ina jiran gari ya waye a yi wacce za a yi.
Da na tashi da asuba na yi sallah ban fita neman abin da zan karya ba kamar yadda na saba yi a cikin yan kwanakin nan, na dai bude kofa sai na koma na kwanta, kamar jira Hamid ya shigo sanye da jallabiya mai yankakken hannu.
Ta kasan ido na dube shi sai na lumshe ido, ya iso ya zauna "Lafiya ba ki tashi ba?
Na bude ido "Na tashi." "Lafiya kike? Na daga masa kai.
"Amma ba ki tashi kin fara shirin asibitin ba?
Na ce "Za ni, ina son yin magana da kai." "Ok ina jin ki."
Na ja ajiyar zuciya "Gaskiya ban aminta da kayan Fauza a falo ba."
Ya dube ni da alamar rashin fahimta "Ban gane ba to ina za ta kai su?
"Ko'ina. Amma ina son filin falon ni da ita kowa ya yi amfani da shi, ba ta gaje ita kadai ba, ni ina rabe."
Why Lima me zai sa ki yi haka? Tun kafin ta sanya kayan za ki yi magana ba sai yanzu ba.". Na ce "Ta kwashe ban amince ba."
"Hakuri za ki yi daga ba ki yi magana a farko ba."
"Ba zan yi ba." Na fadi ina tashi zaune "Wai me kike ji ne haka ina taro ki kina fada mini magana? Wuri dai nawa ne ba na wani ba da za a sanya mini doka."
Na mike tsaye. Tabbas naka ne. Amma ni ma ba za a tilasta mini zama da kayan ba, daga na ce ba ni da bukata."
"Me kike nufi?
"Komai ma." Daga haka na fara tube kayan jikina ya bi ni da kallo har na shiga wanka, ban tunanin zan fito na same shi ba sai na same shi zaune, na tsane jikina na fara shiri, kwalliyar doguwar rigar atamfa na yi na sanya farin hijab da farin takalmi na dauki jakata na kama hanyar kofa ya kira sunana ba tare da na waiwayo ba na taaya "Ina za ki? Ban amsa ba na kama hanya, ban san yana biye da ni ba sai da na fito Fauza na tsaye da alama cikin bacin rai mai yawa take "Aikina ka shiga dakinta tun asuba wallahi ba zan yarda ba."
Na wuce shi ma bai tanka ta ba ya bi ni "Ba ki rufe dakinki ba Halima."
Ya fadi daidai kunnena "Daki ai naka ne kamar yadda ka tabbatar mini."
"To ina za ki hospital?
Na yi mishi shiru ya juya cikin sauri na ci gaba da tafiya ta cikin sa'a na samu abin hawa ba bata lokaci ya haye titi.
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: A cikin kwanaki biyun da suka kasance na girkina mun yi abin arzi'ki sosai ni da shi ya dinga lalla'ba ni tare da ko'karin ganin wata matsala bata faru ba wadda zata janyo mana k'ananun maganganu . Washe garin ranar da girki ya bar hannuna kafin na sauko daga saman na sake tuntu'barsa maganar zuwa maiduguri ganin d'akin Fadila ya ce ai ya riga ya rantse na yi hakuri har su je su dawo daga asibitin da za su je shi da Momi tunda yanzu abinda ya sanya a gaba kenan idan ya dawo sai ya raka ni mu je maidugurin tare, shima sai ya gaishe da su Dada da sauran 'yan uwana,
Na ce amma maganar yara fa kai tsaye ya ce mini suna tare da Nabila a gidan domin ta d'an kwana biyu da zuwa wurin 'yar uwata, amma ba da ita za a yi tafiyar ba zata zauna ta kula da yaran gabad'aya har da su Salim da Adamu.
Rashin abin fad'a ya sanya ni kawai zuba masa ido, wace irin masifa ce ne wannan jama'a, shin yaushe yaranmu za su dawo hannunmu ne ni Aminatu?"
Ina zaune har ya gama kintsa jikinsa muka sauko tare babu kowa a falon Baba Tabawa ta gama aiki tun da wuri ta shige dakinta. Hauwa ba ta fito ba. Har zai fita sai ya tsaya yana kallona kafin ya ce." Ina Hauwa ne?"
Kai tsaye na ce." Ba kasan inda take ba?"
Ya zura mini ido na 'yan sakkoni kafin ya gyad'a kansa ya kama hanyar fita yana fad'in.'' idan ba ki yi tsiwa ba ai ba sunanki Amina ba."
Ya fice a gaggauce don da alama yana da wani babban uzurin da ya hana shi tsayuwa ma ya karya kummalo.
Ina juyawa