Author : Binta Umar Abbale Category : Read Hausa Novels
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: 🌲🌳🌿☘️
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*2k complete a telegram. What'sapp group 1k*
*0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*101*
Muka cigaba da tafiya a gidan babu annashuwa da jin dad'in da ma'aurata kan jiyar da junansu. Ya sauko sosai ya yi tubis da shi domin salon horon da na d'auka ba karami ba ne.
Gashi har yanzu bai cewa Hauwa komai ba dangane da zamanta a gidan domin da ya mayar da auransu a k'alla zai samu jin sau'ki ta 'bangaranta. Ya mayar da ita bai mayar da ita ba Allah ne masani, suna dai zaune a haka ita tana wasan 'buya dashi shi kuma yana nuna mata isa da iko irin na d'a namiji tabbas ko bai fad'a ba nasan jiranta yake ta kai kanta ita kuma girman kai ya hanata ta lallaba ta bashi ha'kuri. Amma yadda yake ta kokarin ganin mun zauna lafiya ni da shi na tabbatar da cewar ya d'auki shawarwarin Baban Saude domin ya rage wasu abubuwan sosai da yake yi mussaman akan yaran. Ba su dai dawo gidan ba, amma a sati sukan shigo sau uku ko hud'u mussaman ranar juma'a muna yini tare da su uwar rik'on na su ta had'o su da kayayyaki masu yawa wai su kawo mana. Ban iya cewa su mayar mata ba domin ita Hauwa kallo ba su isheta ba, kusan ni nake diban turarukan ni ma kyautarsu nake yi sauran na ce Baba Tabawa ta yi amfani da su. Ban ta'ba tambayarsa yaushe zai dawo mana da yaran gabad'aya ba, kawai na zuba masa Ido domin ganin iya gudun ruwansa
Yadda na ri'ke wuta nake watangaririya da rayuwarsa abin har mamaki yake ba ni. A tsukin Allah Ya jarabce shi dani ainun, ni kuma na'ki bada dama yana ta dai lallaba ni domin idan ma ya yi fushin bai wuce na kwanaki biyu zuwa uku ba zai sauko ha'kuri kuwa ya ba ni ya fi a irga. Dad'i nake ji na ganshi yana karyar mini da kansa sai na yi ta tuna irin rashin mutuncin da ya dinga tsuga mini a can baya.
Matar da ya ratayawa fulawar so dama can ita ba wani kwanciyar aure yake yi da ita ka'in da na'in ba da bakinsa ya gaya mini hakan ba matsa shi na yi ba.Ashe ni da ya mayar towon tushe nice marufar asirinsa domin kuwa tuntuni ni nake iyawa da fitinarsa ko Hauwa ba za ta nuna mini komai ba.
Dama tuntuni na gama fahimta cewa ta wannan sigar ake gane rauninsa domin babban abinda yake daga masa hankali ya zo da buk'ata naki amincewa ko kuma idan muna yi na'ki taimakawa da wasu abubuwan da za su ba mu nishadi bakidaya hakan ma na kara rikita shi sosai
Gabad'aya ya nune koyaushe ya shigo gidanmu ba shi da wani kuzari tafiyarsa Legos ta dinga tangal-tangal domin ya turza-turza da ni na'ki amincewa da na bi shi, na gaya masa har abada kafata ta sake taka garin nan, idan lallai sai na yi zaman auran da shi to ina nan."
Saura kwana daya ya tafi Lagos din ya ritsa ni a d'aki. Da farko rarrashi ya fara yi da ban baki tare da alkawarin ba zai sake kai ni kara ba. Kamar koyaushe hakan bai sanya ni na sassauto ba domin kuwa a duk lokacin da zan daga kaina na kalleshi wallahi duhunsa nake gani, a ganina zamana a gidansa kamar takura kai ne tunda shi kam ai kansa ya sani, idan ma ya ce ya tuba da tafiya tayi nisa sai ya koma ruwa
Bai wani ba ni tausayi ba duk kuwa yadda yake rausayar da kansa da muryarsa hakan bai burge ni ba. Da ya lura duk abinda yake yi ban saduda ba sai fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Har da cewa ba zai ka'ra nema na ba har ya mutu na je za mu tsaya a gaban Allah ranar lahira idan har yana da hakki mala'iku za su yi mana sheda domin kuwa ba zai ta'be yafe mini hakkinsa ba.
Ban damu ba ina zaune ina kallonsa ya kama hanya ya fice cikin b'acin rai.
Sai bayan fitarsa kuma na ji wani iri a jikina a lokacin da yake had'a ni da Allah. To ban san yadda zan yi na huce takaicin da ya jima yana kunsa mini ba, kuma ni so nake ya gyara tunda ya zame mini takalmin kaza, ba zai yiwu ya saba take mini hakki ya kwana lafiya ba, Ubangiji zuciya yake dubawa domin ba ni da k'arfi ta kowane bangare sai ta wannan hanyar itace damata kuma hanyar da za ta sadudur masa da jikinsa gabad'aya.
Da zai tafi ko sallama bai yi mana ba, sai da ya kwana uku ma da tafiya tukkuna muka samu labari a bakin Masa'udu cewa ya tafi ban ji komai a jikina ba, dalili na riga nasan irin rabuwar da muka yi ta rashin arziki ba zata bari ya shigo ya yi mana sallama ba.
***
To kwanaki suka cigaba da tafiya har aka fara lissafin watanni da tafiyarsa bai kira waya ba haka zalika mu ma ba mu kira ba. Cikin zuciyata nake fad'in mai hali baya fasawa, aka ce idan ka kwana biyu baka ga mutum ba idan kun hadu to ka tambayeshi halinsa.
To sai na so tsokanar Hauwa tukkuna zan ce mata ta kira shi a waya ta ji yana lafiya. A lokacin zan ga b'acin ranta ta dinga fad'in mijinki dai Amina, ki daina danganta ni da wannan rikitaccen tsohon. Na yi ta dariya idan tana hayaniya a raina nakan ce jinin jikinku kuma yana yawo a junanku tunda duk rintsi a ba za a canzawa towo suna ba.
Babu wata ala'ka da ta sake had'a mu da Momi, tun bayan abubuwan da suka faru. Sai dai ko bayan tafiyarsa ba ta fasa turo mana yara ba, itama Hauwa ba ta sake maganar dawowarsu ba ban san abinda yake cikin zuciyarta ba kuma yanzu.
Wannan littafin na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina.
Har yanzu kadaran kadahan nake jin ta a zuciyata. Kuma ba na jin haushinta ainun sai dai irin kishin nan da ba za a rasa ba. A ko'ina zan fad'a alheri ta yi mini don yara sun shiga tsakaninmu hakan ba zai sanya ni na mance ba. Na dai nesanta yarana da ita shikkenan sai a zauna lafiya.
Sosai Nusaiba da Salim suka d'auki gaba matsananciya da mu. Adam ne kawai yake iya daurewa idan tsautsayi ya sanya mun had'u ya gaishe ni, amma tun ranar da su Yusi suka bar garin gabad'aya ya gaina shigowa gidanmu. Salim da 'yar uwarsa Nusaiba kam abin na su ya yi nisa idan za mu had'u sau goma cikinsu babu wanda zai dubi inda nake balle na sanya a raina cewa za a gaishe ni.
Yusi bai ta'ba gaya mini ce wa Adam ya ziyarce shi har sau biyu ba duk kuwa da cewa yakan kira ni a waya sa'i da lokaci mussaman a ranakun da ba su da makaranta tunda tuntuni sun cigaba da d'ora karatunsa a bayaro wasu lukutan ba su da isheshen lokaci mussaman Kamalu da ya ri'ke b'angare biyu. Karatu yake yi sosai irin na da'awa sosai yake bin Malam sunna domin samun ilimi kwanaki satinsa guda a Bauchi wurin Sheikh Guruntum. sai bayan da ya dawo tukkuna yake gaya mini da na tambaye shi dalili ya ce mini yana zuwa neman fatawa ne. Yanzu dai yana tare da Shaikh Abdullahi gadon-k'aya yana daya daga cikin yaransa da suke take masa baya.
To a bakin Hamusu nake samun labarin zuwan Adam din don har yake gaya mini irin kayan da Momi din ta aikawa da Gwaggo ta hanyar Adam din.
Na yi mamaki sosai kuma jikina ya kara yin sanyi da lamarinta a yi alheri da kyauta hannun hagu bai sani ba. Duk yadda na nuna mata rashin 'kara da kawaici akan yaran nan k'okarinta zumuncin nan da take ta nanata mini ya cigaba da tabbatuwa.
Ubangiji Allah Ya ba mu ikon yin abu dominsa.
Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya a hangunce ta fannin maigidan namu kam yadda ba mu neme shi ba shima bai neme mu ba. Tun abin baya damuna har ya fara damuna sai na fara fargabar kada ya sanar da Baban Saude cewa ga abinda na tsiro dashi dukda akan gaskiyata ne, to amma nasan ba ni da hujja Mai karfi idan baban Saude ya titsiye ni dalilin abinda ya sake nake haka Koda na gaya masa dalili zai ce mini Mai yasa ban fad'a masa ba ranar da ya zo ya sasantanmu tunda kafin ya tafi sai da ya dinga tambayarmu idan da wata matsalar mu fad'a bayan wadda muka gaya masa. Ga bikin Fadila babbar diyar anti Yagana ya tashi. An yi bikin Yusura sati shida da suka gabata lokacin muna tsaka da rikici dalilin da ya sanya ma kenan ban tambayeshi ba domin kuwa nasan zai huce fushinsa akan hakan ya samu damar gasa mini maganar da ransa yake so kuma ya hana ni zuwa, saboda kada dukan ya zama biyu ya sanya na k'yale shi.
Hajja da kanta ta kira ni a waya game da zuwa bikin Fadila da suke shirye-shiryen tafiya ita da Gwaggo tare da yaran wato su Kamalu ai anti Yagana mutuniyarta ce don haka ban yi mamakin nuna za'kuwarta akan sha'aninta ba. Rasa abinda zan ce mata na yi na kama inda-inda da kyar dai na ce mata ni ma ina nan ina shiri amma wata'kila za su riga ni yin gaba. Ba ta fahimci cewa da matsala ba muka yi sallama na ajiye waya cikin zullumi da tunanin yadda zan sanar da shi tafiya maiduguri ya bar ni kai tsaye. Da kunya kusan wata hud'u da tafiyarsa ban kira shi ba bayan kuma nasan da tsananin fushina ya tafi yanzu kuma na kira shi nace masa me?"
Haka kwana biyun nan na kasance cikin yanayi na tunani har sai da Hauwa ta fahimta ta tambayeni na gaya mata halin da ake ciki. A lokacin itama jikinta mutuwa ya yi ta dinga fad'in lallai a wannan ga'bar baki da bakin magana Amina. Bikin Fadila kuma ai ke ce kirjin biki, idan ba ki halarta ba akwai matsala gaskiya.
To katsam ina cikin wannan halin ya zo ba tare da tsammanin zuwan nasa ba, tunda ka'ida wata shida muke yi a can legos din mu dawo, wai ashe Momin ce babu lafiya hawan jini da sugar har sai da ta kwanta a asibiti tsayin kwanaki goma ba mu sani ba, na yi mamaki sosai domin yarana suna zuwa dukda a satin bai fi sau biyu suka zo ba amma babu wanda ya gaya mana. Kenan a hannun masu aikinta yaran suke har ta fito daga asibitin ko da yake dama sune suke dawainiya da su Mairo da Taburni yaran suna yawan kiran sunayensu
Masa'ud shi ya gaya mana wannan labarin domin kuwa shi din ma ya tabbatar mana da zuwansa kamar yadda ya tabbatar mana da tafiyarsa. Bai shigo mana a ranar ba sai washe gari da rana wajan daya da minti biyar lokacin ma daka gani daga massalaci ya fito.
Muna falo gabad'aya muka yi masa barka da zuwa ya amsa kadaran kadahan babu fushi haka zalika babu cikakkiyar walwala. Ya tsaya suna magana da Baba Tabawa kamar yadda suka saba har yana ba ta labarin rashin lafiyar Momi din da yadda ta ji jiki. Sosai ta dinga jajantawa tana k'ara tabbatar masa da cewa gabad'ayanmu ba mu sani ba. Wannan karon Hauwa ba ta tashi ba ban sani ba ko nauyin da jikinta ya yi mata ne oho, tunda cikinta a cikin wata na takwas yake ya fito sosai idan ta jibge a wuri d'aya da kyar take tashi. Ya kama hanyar samansa babu wadda ya sake kalla a cikinmu. Amma yanayinsa kadai ya tabbatar mini da cewa lalurar da matarsa take ciki ta dame shi saboda ga yanayin yadda yake bawa Baba Tabawa labarin ciwon tabbas ya ci jikinta da k'arfi.
Bayan shud'ewarsa daga wurin da kamar minti goma na tashi na bi bayansa zuciya cike da zullumi da fargaba.
A kwance na same shi kawai ya tsirawa rufin d'akin ido. Gabad'aya sai gwiwa ta yi sanyi (wai shin me cece ma duniyar nan ne) tausayinsa ya d'an kamani, amma bari tasirin hakan ya raunarta da ni ba. Har yanzu da sauran takaicinsa a cikin zuciyata.
A nutse na zauna gefan k'afafunsa. Ya dube ni bai ce komai ba sai ya janye idanuwansa. Na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." Wallahi ba mu san ta yi ciwo ba, ashe har kwanciya ta yi a asibiti babu labari ai da mun shiga mun dubata."
Ya yi shiru bai ce mini komai ba. Sai na janye idona daga kansa na yi kasa da kaina ina dan wasa da yatsun hannuna. Shiru d'akin ya yi na minti kusan goma kafin na sake dubansa yanzu idonsa a lumshe yake kamar mai shirin bacci ganin haka sai na tashi da niyyar fita. Ba tare da ya bud'e idon ba ya ce." Koma ki zauna ina son magana dake....
*Yau fa mutumin ko ni ma ya ba ni tausayi 😆😢🤭 Amina a sassautawa Babanmu mana.*
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: 🌲🌳🌿☘️
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*2K COMPLETE ON TALGRAM.*
*VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*102*
Na zauna din kamar yadda ya buk'ata. Ya tashi zaune tare da sauke k'afafunsa kasa. Ya dube ni a nutse kafin ya furta." Akwai matan da annabin rahama ya fad'a cewa ya gan su a can karkashin wutar jahanama, kuma suffofinsu sukan bayyana tun a duniya. Akwai kuma matan da tun a duniya za a dinga yi musu ishara da nuni da cewar aljannar Firdausi madawamiya ce a gare su.