Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
da
Nur ke kwala mata hankalinta ya kara tashi domin tasan babu lafiya.
Aunty Saratu dake kicin ko fitowa ta yi tana cewa, "Nur mene ne haka, kin dai san bata jin dafi
ko?" Zaman dirshen Nur ta yi a dakin tana maida numfashi, da ga Mamy har anuty Saratu
afirgice suke tambayanta me ya ke faruwa?
Cikin tsananin haki take cewa, "Mamy, Aunty Saratu ku je dakin Yaya Abdallah ku gani..."
Anuty Saratu ce tace, "Meye a dakinsa? Me zamu gani acan din?"
"Mamy ku je ku gani wallahi ku yi sauri."
Mamy ce ta kalli Aunty Saratu sannan ta ce, "Saratu jeki gani"
"A'a, yanzun fa ya min sallama baya gidan nan, ina ga fa firgita take yi" juyawa ta yi ta kalli Nur
ta ce, "Ke! ki nutsu dallah ki yi magana, mene ne kika gani a dakin?" Cikin numfarfashi Nur ta ce
"Mace ce Yaya Abdallah ya shigo da ita cikin dakinshi...."
Hannu Mamy ta sa ta dafe kirjinta tare da runtse ido, cikin daga murya ta ce, "Mace! Acikin
gidan nan?" Ganin in da ta runtse ido tana dafe da kirji Aunty Saratu tabita da kallo cike da
fargaban kar ciwonta ya tashi, ganin Mamy na kokarin ficewa a dakin afusace Aunty Saratu tai
saurin riketa tare da cewa, "Karki je, ki bari ya fito dan Allah." Bige hannun Aunty Saratu Mamy ta yi tare da cewa, Bazan iya tsayawaba Saratu, wannan
iskancin har ina, tun munajin waiwai ace har takai acikin gidan nan yake damar da zai mana
haka."
"Koma mene ne karkiji dan Allah, kindai san baki da lafiya, ki bari ya fito, ko Kuma a kirashi a
waya."
"Sakeni ina zuwa." Mamy ta fada tana kokarin zamewa daga rokon da Saratu tai mata. "Bazan
sake kiba, ki yi hakuri bari na kirashi a waya"
"A dai dinga jin tsoron Allah, abin da baka son a maka kar bari amawa wani, ta yaya muna cikin
gidan nan zamu bari haka na faruwa? Ina yar mu haka ta faru a kanta zamuji dadi? Saratu
muna cikin gidan nan kuma kice wai in bari ya fito? Cikin sauri Saratu ta saki Mamy jikinta da
sanyi sosai, afusace Mamy ta fice yayin da Aunty Saratu tabi bayanta. CIWON'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 19-20
Afusace Mamy ta tura kofar dakin Abdallah tare da runtse idonta tsayon lokaci, Aunty dake
bayantane tabi dakin da kallo, ganin babu kowa adakin yasa tabi Mamy da kallo tare da fadin, "
Kinga Babu kowa a dakin fa?" Cikin sauri Mamy ta bude ido ta, ganin babu kowa ta shiga
waige-waige, ko ina gyare ya ke tsaf, ban da tashin kamshi babu abin dake tashi a dakin, da
sauri ta kalli kofar bayinsa da ke cikin dakin, ahankali ta fara takawa har ta isa wurin ta tura
kofar, ko ina bushe ya ke, alama ce dake nuna anjima ba'a shigaba, juyowa Mamy ta yi cike da
mamaki, da ga gefen gadonsa Mamy ta hangi tarin littafansa na addini daya karanta wadda har
yanzun baya rabo da karantasu, domin ta na yawan ganinshi yana bude dasu, ji ta yi
kafafuwanta sun gaza daukanta dan haka ta tsinta kanta da zama bakin gadonshi tare da fadin,
"Saratu abubuwan da suke faruwa kwana biyu cikin gidan nan suna daure min kai. Kindai ga
yadda Nur take a rikice, ta ce dakin nan akwai mace Kuma gashi babu kowa adakin, ni Kuma
basan Nur da karya ba." Nisawa Aunty Saratu ta yi sannan ta ce, "Tashi mu je Mamy, ni dama
can bana zargin Abdallah, dan dai kuna cewa ba'a shaidan yaro yasa nai miki shiru kawai,
amman ni aciki raina ina tantama, Abdallah fa ko daga kai ya kalli mace baya yi, kuma tuntuni
ku ke cewa yayi aure amman sai ya ce shi ba aure bane a gabanshi, sanin kankine Abdallah ya
tsana mace mara kamun kai, ko ita Nur kullum cikin mata nasiha yake karta yi wani abu dazai
taba mutuncin gidan nan." Lumshe ido Mamy ta yi alamar nazari take, zuwa can ta ce, "Amman
Nur bazata mishi sharri ba fa" Wani irin kallo Aunty Saratu tayiwa Mamy "Ni dai na fara zargin
Nur tanason ta batawa Abdallah suna ne, tunda duk abin da take fada babu daya daya
tabbata."
Ajiyan zuciya Mamy ta yi sannan suka fito a dakin, adaidai lokacin da suka fito falon, lokacin
Abdallah ke shigowa falon, gani fitowan su da ga gefen sa ya ce, "Lafiya?"
Sauke ajiyan zuciya A unty ta yi sannan tace, "Lafiya lau" Kujera Mamy ta nema ta zauna
dan haka itama Aunty Saratu zama ta yi jikinta a sanyaye. Ganin Mamy na share hawaye ya isa
gabanta ya zauna tsakiyan kafarta tare da saurin rike hannunta ya ce, "Mamy wai mene ne?"
Yana yin tambayan Mamy ta fashe da kuka, dan haka hankali Abdallah ya kara tashi. Cike da
damuwa ya ce, "Aunty meye ya ke faruwa ne? Mamy me ya faru?"
Cikin kukan Mamy ta ce, " Duk abin da na ce ka yi ka na yi, abu daya ta taba umartanka da
ka yi kaki yi, kuma shi ne babban abin dake sani damuwa a yazun, kullum bani da kwanciyar
hankali na kasa sukuni...
"Me ye shi Mamy? Mamy tun kafin in ji meye na miki alkawarin duk abin da kike so shi za'ayi,
ki fada min Mamy."
"Aure na ke son ka yi" Mamy ta fada cike da damuwa, dagowa ya yi da sauri ya kalli Mamy
sannan ya ce, "Aure kuma Mamy?, yanzun akan auren kike irin wannan kukan?"
Dole ne in shiga damuwa, baka yi rashin ji tun farko ba dan haka banajin dadin ganinka a haka,
idan ba aure na ga ka yi ba hankalina bazai kwanta ba." Hannu Abdallah ya mika ya na share
hawayen Mamy tare da fadin, "Yanzun to ba maganar auren ake ba?, ai mun riga mun gama
mganar da Abba komai ya kusa zuwa karshe in sha Allah ki kwantar da hankalin ki, ko ance
miki na yi wani abinne Kuma?"
"Hankalina ne kawai ya kasa nutsuwa, aure nake son kayi kawai" Hannu Abdallah ya mika yana
share mata hawaye tare da cewa, "Shikenan zanyi Mamy ki kwantaar da hankalin ki" Daker
Abdallah ya samu kan Mamy sannan ya wuce dakinsa cike da damuwa, Mamy ko bayan ta
koma daki samun Nur ta yi tana Bacci, dan haka itama ta kwanta gefen ta zuciyarta cike fal da
tunani.
****
"Mairo! Mairo!" Wata tsuhuwa ce ke kwala kira tare da kotsuwa cikin falon tana sake cewa wai
ina Mairon!? Can cikin baccinta ta jiyo muryan tsuwar dan haka ta diro a gadon ba tare da ta
shirya ba take cewa, "Oyoyo Hajiya!"
Itama Mamy da saurinta ta sauko a gadon ta biyo bayan Nur tana fadin, "To fa ko me ya kawo
hajiya da tsakar ranar nan?" Ajikin Hajiya Mamy ta hangi Nur kwance cikkn tsananin murna,
tsaye ta yi tana kallon su, muryan Aunty Saratu Mamy ta jiyo da ga bayanta tana cewa, "Hajiya
lafiya?" Sakin Nur Hajiya ta yi tare da rike hannunta ta karasa shigowa falon ta zauna tare da
cewa, "Me kuke nufi ne? Jikata nazo gani, ko laifine dan na taho?" Da ga Aunty Saratu har
Mamy murmushi suka yi sannan suka karaso su ka zauna tare da hada baki wajen cewa, "Babu
laifi, sannu da zuwa"
"Yauwa ku bani ruwa nasha kishi nake ji da kafa na taho na gaji sosai." Mikewa Aunty Saratu ta
yi tana kokarin shiga kicin ta kula da Abdallah dake tsaye ya hade fuska babu abin da ya ke sai
kallon Hajiya, murmushi Aunty ta yi sannan ta dan waiga ta kalli Hajiya, ganin bata San da
Abdallah a gurin ba yasa ta yi murmushi tare da cewa, "Abdallah wannan kallon fa?" Kicin din ta
shiga batare da tajira amsanshi ba, ita ko Hajiya tun da aka ambaci Abdallah ta bishi da kallo,
ganin ya ki motsawa ta ce, "Kai kuma me aka maka ka tsaya anan? baki gaba kamar na biri
yayin da ya so tsegumi" Kallon Hajiya yayi yana kokarin kawar da kai ya hangi Nur tana dariya
kasa-kasa tare da boye fuskarta jikin hajiya, dan haka yai saurin tahowa gurin tare da nuna Nur
da hannun sa ya na cewa, "Ke dan ubanki wa kike ma dariya? Ina wasa da ke?" Tun da ya fara
maganar ta hade fuskarta, Hajiya ce ta kalli Abdallah sannan ta kalli Nur ta ce, "Ikon Allah, idan
kai ba kayin dariyar ai baka hana wani yayi ba, haka kawai, yau na ga jaraba"
"Yanzu dai me ki ka zo yi? Ba su Abba sun hanaki yawon nan ba?"
"Ai duk fadin duniyar nan babu uwata babu ubana dan haka babu me saka min ta kunkume
hana zirga-zirga, ko akwai me aurena fadin duniyar nan?" Karamin tsaki Abdallah ya ja, sannan
ya nemi guri ya zauna tare da cewa, "Dan kiyaye lafiyan ki akace ki zauna wuri daya; ba wani
abu ba, amman idan kinga za kiyi ta yi sai ki yi" Ruwan da Aunty ta mika mata ta karba tasha bayan ta sauke ruwan ta ce, "Ni dan jikata na zo
badan wani kato ba, karka dame ni da fada, ko iyayen ka basu isa ba bare kai, ledan dake
gefenta ta dauko ta mikawa Nur, yayin da Nur ta shiga budewa cike da murna, kayan kwalliya
ne cike da ledan, dubawa take tare da yiwa Hajiya godiya, Mamy ma godiya ta yiwa Hajiya,
hakama Aunty Saratu, shiko Abdallah cewa yayi "Wato Hajiya kudin da su Abba ke bakine ki ke
mata siyayya dashi ko?"
"Eh, idan banyi mata siyayayya ba me zan da su?" Tsaki Abdallah ya ja, sannan ya ce " Amma
ai ana bakine dan ki dan dinga siyan wani abin kici badan mutum daya ba" Tabe baki Hajiya ta
yi tare da cewa, "Oho nifa duk abin da zaka fadi ka dade baka fadaba ita kenan guda daya
tamkar tsuka daya amiya, idan ma bakin ciki kake Kai ka sani, lokacin danai wahala da ku ita
batazo ma duniyar ba"
"Wanni wahala kika yi damu?" Abdallah ya fada yana kallo Hajiya, "Ka tambayi ubanka tun da
ya ke ya taba siya maka hula?" Yar dariya Abdallah yayi sannan ya ce "Wannan danki kika
sayawawa ni bani ba, kuma saina ce musu su daina baki kudi"
"Eh ka hanasu, ai ba kirki gareka ba, bansan in da ka samu wannan dabi'ar ba ta shirin son
abin arzikiba" Mamy ce ta ce "Hajiya da gangan yake miki ai be isa ba ma."
Toh banda iskanci ni mahaukaciya da da zai dinga min da gangan, idan basu bani kudin ba
waye zai bani?
"Ai shine Hajiya" Wasa ya ke miki. Aunty Saratu ta fada tana hararan Abdallah.
Hajiya ko cewa ta yi, "Ni bana wasa da jikoki, sabo da banson raini da rashin kunya, hawaye
Hajiya ta share sannan taci gaba da cewa, ruwane ya daki babban zakara amman ba komai, ka
hanasu subani ko bara naje na yi na karasa tara kudin dankunnen gwal din da na ke kokarin
tarawa na sayawa Nur." Ganin in da take share hawaye Abdallah ya ce, "Nifa wasa nake miki Hajiya, amman idan sun
baki kibawa Tani ta din ga sawo miki abun dadi kici"
"Kayan kwalliyar da gwal da nake son sayawa Nur fa?" Murmushi Abdallah yayi sannan ya ce,
"Ni zan din ga baki kina tarawa wannan" Murmushi Hajiya ta yi tare da cewa, To ai shikenan
tashi muje ka kaini gida, nagaji sosai, haka kawai ina zaune kamar an mintsineni nace ni
sainagano Mairo" Gudun karya ballo wata rigima ya mike tare da cewa, "Mu je to" Mikewa ta yi cike da fara'a ta ce "Ko kaifa, dan albarka, na ji ance min ka kusa aure, ina ka
samu yariyar?" Ficewa yayi afalon, su Mamy ma sallama su ka ma hajiya, itako ta na rike da
hannun Nur har suka zo kusa da Abdallah dan haka Hajiya ta sake cewa "Ina ka samu mata?"
Hannun Hajiya ya rike yana duba yadda fatarta duk ta yamushe alamar tsufa ya ce, Hajiya yar
unguwar rimi ce, sati daya da ya wuce Allah ya hadani da ita, kallo daya nai mata na ji son ta ya
kamani, bata da rawan kai, kuma bata surutu bare ta yi gulmace-gulmace, yar karamar yariya
ce shekaranta goma sha bakawai danya ce sharaf, tana so na sosai, ko mutum zan datsa in
binni a gabanta bazata fadawa kowa ba" Ciki da fara'a Hajiya tace, "Yo dama ai bata fada ba
tun da tana kaunar ka, ai in kaji ana binciko aibu babu babu so" Lasan lebe Abdallah yayi
sannan ya ce, "Yauwa Hajiya kin gane kenan, babu tarkon da zai kamani, duk in da aka dana
min tarko ina tsallakewa, shiyasa ma Allah ya hadani da kyakyawar yariya" Lumshe Ido Nur ta
yi domin ya na lissafin tana jin son yariyar na shiga ranta, kosawa ta yi sosai ya ambaci
sunanta, ji tayi ya cigaba da cewa, "Hajiya mun hadu da itane a hanya lokacin da ta taso
islamiyya, ta gama secondary bata tsaya yawon biyawa gidan kawaye ba, shi Abbanta daman
tsarinsa da yariya ta gama secondary ya aurar da ita ya huta, sabo da bata da bakin kudiri
acikin ranta Allah ya hadata dani, ni kuma sabo da Allah na sona ya hadani da ita, a lokacin da
ake kokarin hadamin tuggu acikin gidan ubana, idan na yi aure sai munafuki ya cire idonshi a
kaina aiko?"
Cike da murna Hajiya ta ce ai kuwa ai dama duk wadda yace tukunyar wani bazata tafasaba
to tashi ko dumi baza ta yi ba, Allah ya tabbatar mana da alheri yasa zamu ga ranar, ya sunan
yariyar?"
Adaidai lokacin da ya shiga motar ya zauna ya ce "Sunanta Bilkisu.
Da taimako Nur Hajiya ta zauna motar sannan Nur ta rofe motar, tana daga mata hannu
fuskarta cike da murmushi, itama Hajiya cike da murmushi take dagawa Nur hannu, bayan sun
wuce ta juya cikin gidan ta na me farin cikin da jin Yaya Abdallah ya na yabawa da yariyar da
zai aura, kwanciyar hankali ta ji yana shiganta lokaci daya.
*****
Bayan kwana biyu, Nur ce tafe akan hanyarta ta zuwa islamiya, kasancewar yau asabar, ga
wani irin sanyi da aka tashi da shi, tafe take akan hanyar cike da nishadi, da zaran ta tuna an
tsaida ranar auren Yaya Abdallah take jin wani irin nishadi tun tasowanta ba'a taba yin biki aure
a cikin dangin su ba, dan haka tafe take tana kirga sati biyu da aka tsaida, saidai ganinsu take
kamar shakara, sabo da tsananin kosawa, bata ankaraba taga wata mota sha gabanta, nan ta
tsaya tana kallonta, duk gilashinta rufe ya ke, bata iya hango komai da ke ciki, bata wani ji tsoro
ba, domin uguwar ta su lafiyar yiyiyar unguwa ce, dan haka ta fara kokarin kewaye motar ta
wuce. Cak taji an dagata, kafin ta yi wani yunkuri ta ji an wurgata bayan motar tare da jin karan
rofe motar, tashi ta yi zaune a rikice, wasu gamza gafzan maza biyu ta gani a gaban motar
wadda bata taba ganin su cikin unguwar ba, figar motar suka yi sukabar unguwan aguje, tsoro
da firgici ya sa Nur sakin kuka, tare da kokarin bude motar, duk da cewa gudu motar ke yi saidai
duk kokarinta ta gaza budewa, dan haka ta shiga magiya, cikin kuka tare da firgici me tsanani
akan fuskarta take fadin, "Na shiga uku, ina zaku kaini! Dan Allah ku yi hakuri ku rabo dani
makaranta zani" Ko juyowa su kalleta ba su yi ba, zuwa wannan lokacin har sun fita daga
unguwar su Nur sun haura sanmn titi, dan haka ta cigaba da kuka tare da magiya, "Ina zaku
kaini? Me na yi muku.
07014197556
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 21-22
Aguje su ke tafiya, duk irin magiyan da ta ke mu su basu juyo sun kalleta ba, dan haka ta daina
bige bigen da ta ke ta zauna kawai tana kuka tare da magiyar su yi hakuri su sauketa.
Babu wadda ya juyo ya kalleta, tun ta na gane hanya har aka shiga in da bata ganewa,
wannan ya sake daga hankalin Nur, tafiyan kusan awa daya sannan ta ga sun doshi wani katon
get, wannan lokacin so tayi ta dauke numfashinta domin ta fara cire rai da duniya, gidane
dandasheshen gaske, gani kawai ta yi get din ya bude batare da tasan waye ya bude ba,
wannan lokacin raba ido kawai take da busheahen hawaye a idonta. Bayan motar ta faka a
cikin harabar gidan matukin motar ne ya sauko da saurin sa, sannan ya bude bayan motar ya
ce, "fito"
Jin hausarshi