Ciwon Ya Mace Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   4 / 25

9K to 12K   out of 73.1K words

ce "Me ke faruwa ne?" "Ina son ne ka tambayeta me take so?"
"Ban fahimce ka ba Alhaji?" Baffah ya fada tare da gyara zamanshi, shima Abba gyara zama
ya yi sannan ya bude murya sosai yace "Gani na yi ta girma, wata kila akwai wani abun da take
so, kasan akwai wasu shekaru wadda yariya ke kawai ta dinga ji ajikinta daidai take da kowa,
Nur tana cikin irin wannan shekaron duba da yanayin dabi'ar data da data yanzu ba iri daya

bace" Sosai hankalin Nur ya tashi saidai har yanzun bata gane inda Abba ya sa gaba ba. Yaya
Bashir kuwa shuru ya yi tare da sunkuyar da kanshi kasa, shikuwa Yaya Abdallah har yanzun
wayarsa ya ke dannawa kamar besan me a ke yi ba.
Juyawa Baffah ya yi ya kalli Nur sosai cike da hade fuska,
Shiko Bashir satan kallon Baffah ya fara tare da mamakin furucin Abba. Cikin kausasiyar
murya Baffah ya ce Nur me ke faruwa kwana biyu?
Kasa Nur ta yi da kanta tare da yin kwalkwal da idon ta. Ganin haka Baffah ya sake cewa
"Inajin ki gaya min me kike so?"
Can kasa tai da murya sannan ta ce "Ba komai Abba"
"A'a ki bude baki ki yi magana, kina son aure ne?"
Cikin tsananin furgici Nur ta dago kai tare da fadi "Wallahi a'a."
"Eh mana idan ba hakaba me yasa baki da nutsuwa?"
"Baffah wallahi ban yi komai ba, yayan Helen kawata ne ya dauko ni jiya a hanya ya ganni,
lokacin na rasa in da zanbi inhau motar da zan dawo gida" Abba ne ya katse Nur cikin fada ya
ce "Yau ki ka fara zuwa gidan Salma dahar zaki mance hanya? Yarana maza basu bani wala
wajen tarbiyan su ba dan haka ke mace bazaki walar dani ba, duk da cewa na so ace kin yi
karatu sosai amman idan babu dama aurar da ke zanyi in huta, don ina son ki karatu bazan
barki ki lalaceba"
"Dama ya fi Abba, amata aure kawai, idan ma karatun ne ta yi shi a dakin mijinta" Abdallah ne
ke fadin haka cike da nutsuwa. Cikin Sauri Bashir ya ce, "Nur din za'a ma aure? Haba
Abdallah"
"Idan ba ta natsuba ba dole a mata aure, koko sabo da muna son tai karatu sai mu barta ta
lalace?"
"Ai Abba karatun ma be da wani amfani, a mata aure kawai, ko an barta ta yi karatu karshen
ta dai aure za ta yi, karatun ba wani amfani da zai yi mataba, dan mafi yawancin mazan basa
barin mace ta fita aiki bare wannan yariyar da bata jin magana"
Cikin bacin rai Bashir ya ce "Ko mace bata fita aiki ba Karatu dole zai mata rana ko wajen
tarbiyan yaranta ne."
Gyara zama Abdallah ya yi sannan ya ce "Wadda ta yi yanzun ya isa tabawa yaran na ta
tarbiya"
Ta gefen ido Nur ta saci kallonsa, cikekken mutum managarci me cikar zati da haifa, ga
kasumba cike da fuskarsa kai kace na Allah ne, acikin zuciyarta ta ce, "Yaushe ya tsane ni har
haka? kawai dan nafada gaskiya sai ya bada shawaran amini aure?" Muryan Baffa ne ya dawo
da ita cikin hakalinta, dalilin jin da ta yi yana cewa "Gaskiya ne Abdallah da ace ta lalace gara
amata aure shiyasa akoda yaushe nake yaba hankalinka, tunaninka irin na manyane"
Fashewa Nur ta yi da kuka ta na cewa "Wallahi ban son aure Abba, ni karatu zan yi, wallahi
bantaba yin irin wannan tunanin ba, karatu na ke so, yayan Helen ne ya kawoni gida, kuma aje
a tambaye shi"
"Ke dallah rufewa mutane baki! Baffa Karku saurareta, karatun da ta samu yanzun ya isa ta
kula da yaranta, aure shi yafi dacewa da ita, idan aka barta haka wlh za ku yi da kun sani"
"Ni badan in kula da yara na ke son in yi Karatu ba, ba na son aure sam, karatu zan yi abba
kum..."
"Ke! ina wasa dake ne? Dake nake Magana?

Shiru Nur ta yi tare da sa hannun ta tana share hawaye. Abba ne ya ce, "A baya nasan kudirin
Nur na son Karatu, dacan ta taba cemin likita take son ta zama, ina shiga farin ciki aduk sanda
ta gaya min kudirinta, kuma na yi mata alkawarin ko nawa ne zan kashe mata ta yi karatu,
amman kwana biyun sauyawan nan nata ya daga min hankali, daren jiya ban iya runtsawa ba." Bashir ne ya ce "Abba ai mata hakuri dan Allah, yariya ce, wata kila ta na da wani damuwa ne
kwana biyun zan yi mgn da ita inji"
Tunkafin Abba ya amsa Abdallah ya cigaba da danna wayarsa, sai dai har yanzun fuskan sa a
hade ta ke, Baffa ne ya yiwa Nur fada sosai sannan ya ce ta wuce.
Mikewa ta yi tai godiya sannan ta koma cikin gida tana share gutun hawaye, kai tsaye
shashin Mamy ta wuce. Akan sallaya ta samu Mamy jikinta ta rakube tare da shashshekar kuka
tare da fadin "Mamy kinga ya Abdallah ya na bawa Abba shawaran abin aure ko?"
Gyara zama Mamy ta yi ta kalli Nur sosai tare da cewa "Auren lafiya? babu me miki aure
yanzun, nasan abun da ya sa Abban ku zaice haka, tun da besan meke faruwa ba a gidan,
kema nace miki ki kwantar da hankalin ki..." Shigowan Yaya Bashir ya hana Mamy karasa
zancenta, zama ya yi gafen su ya na kallon yadda Nur ke kuka sannan ya ce, "Mamy wai me ke
damun Nur ne, a rikice ta ke fa, yanzun gashi har Abba ya kira Baffah wai gani ya ke aure take
so?"
Tsaki Mamy taja sannan ta ce, "Wanni irin aure, Nur fa duk wannan abun da kuke ganin tana
yi ita da Abdallah ne, Kuma na gaya mata ta rabu dashi baza ta iya ba, kowa ya gyara ya sani
haka kowa ya bata ya sani."
Cikin rashin fahimta ya ce "Me ya ke faruwa ne Mamy?"
"Bashir babu abun da be faru ba, ko wanne mutun da irin halin shi, na lura Yayan ku riga biyu
ya ke amfani da ita, azari mutum me mutunci acikin zuci kuma shi kadai yabarwa kanshi sani,
idan Yayan ku ya na yin abin da bedace ba Nur ba ta isa ta canza Shiba dan haka banga
amfanin damun kanta da take ba, ni kaina saidai in gaya mishi gaskiya in kuma nemar masa
shirya gurin Allah."
Shigowan Abdallah ya sa duk suka kalli kofar, cikin dakin ya shigo ya zauna, babu wadda ya
yi magana shikuwa Abdallah kallo ya bi Nur dashi cike da tsana, ayanxun ji ya ke babu abun da
ya tsana sama da Nur a duniya. Acikin zuciyar shi ya ke cewa, "Idan har ki na son zama lafiya
dole ki gyara abun da kika bata, idan kuwa ba haka ba dole acikin biyu za'ayi daya kodai ki bar
gidan nan ko kuma auren, dan bazan taba barinki ki zauna acikin gidan nan kina Karatu ba."
Dawowa yayi da ga duniyar tunanin ya kalleta saboda tsabar haushinta ji yake kamar yasa
kafar sa ya latseta, mikewa yayi ya fice batare da ya bari kowa ya fahimci halin da yake ciki ba.
Misalin Karfe 8 na dare Aunty Saratu ta gama hada abincin daren akan babban teburi da
kowa ke halarta kowanni dare, kira ta kwalawa Nur bayan ta fito ta zauna ta na jiran fitowan
sauran, saidai aunty Saratu na wucewa ta hango Yaya Abdallah na tahowa, bata ji komai ba
domin sun saba irin wannan zama, kujara ya jawo baya sannan ya zauna akai, tunda ya zauna
take jin kamar idon sa na kanta, tsayon lokaci su ka dauka amman taki kallon sa, dan ta na ji a
jikinta kallo ne irin na tsana yake mata, zuwa can Mamy ta fito saidai bata karaso ba can falon
ta zauna ta ce akawo mata nan, aunty Saratu ce ta deba na Mamy ta nufa kai mata, juyawanta
ya yi daidai da lokacin da Abdallah ya ce, "Idan har ina numfashi babu karatun da zaki yi,
wallahi summa tallahi bazan taba bari kisamu abin da ranki ke so ba, a haka ma kina neman ki
yi mana tsayayya ina ga kin yi karatu? Ki na kara girma agidan nan sai mun rasa inda zamu yi

da ke."
Kin dagowa Nur ta yi bare ta kalleshi, dan haka ya sake cewa, "Kina ji da wani dan baki dan
curr kamar na tsuntsu, abu daya ya rabaki da sadar fulani, shegiya magananna, sai kinbar
gidan nan tunda ba gidan ubanki bane!"
Cikin Sauri Nur ta dago ta kalli Abdallah sam bazakace daga bakinshi wannan zantukan suke
fitowa ba, ganin in da ta ke kallon shi yasa shi ya miko kafarshi ya mutsuke na ta, tare da fadin
"Zaki rama ne?"
Cikin Sauri ta girgiza kanta tare da cewa "A'a akwai zafi dai, ka daga min kafa"
"Idan har ki na son ki zauna lafiya kibar gidan nan, idan Kuma kin ki burinki bazai taba cika
ba, kin yi kadan ki zubar min da mutunci, in zauna ina kallon ki, saina saki hawayen da har ki
mutu bazaki daina kuka ba.
Zuwa wannan lokacin sosai Nur ta hada zufa sabo da radadin da take ji, daurewa take domin
kada su Mamy suji bare har tayi abun da Abba zai kara daukan zafi, amman sosai ta kara
kulewa da Abdallah jin muryan Abba ya sa Abdallah ya shafa kansa tare da cire idon shi akan
Nur saidai har yanzun yana take da kafarta. Zama Abba ya yi tare da aunty Saratu da Yaya Bashir kowa sannu yaiwa Abba Abban amman
banda Nur da take cikin jin azaban radadi. Dan haka Abba na zama ya kalleta cike da mamaki
ya ce ke lafiya kike hada zufa haka?"
Kasa bude baki ta yi ta bawa Abba amsa dan haka ta shiga cije lebe. Ganin haka Abdallah ya
sauke kafarshi a hankali batare da ya cire idon sa a kanta ba. Abba ne ke kallon Nur ba, ganin
ta bude ido ya ce mene ne ke damun ki?
Ba komai ta fada kwalla cike da idonta, gaba daya gurin hankali aka maida kanta harda
Abdallah da yake kallon inda kafarta ta ke Yana cewa wani abu ne a kafar taki?
Jin muryan Abdallah na mata tambaya ya sa ta kara ware idonta dake cike da hawaye tana
kallon shi. Gani ta yi fuskarsa warkan tamkar besan me ke faruwa, bata gama mamakin yanayin
na sa ba taji yana cewa "Nur wani abu ya samu kafar taki ne?"
Cikin Sauri ta cire idonta akan shi tare da girgiza kanta alamar a'a.
Cikin rashin gamsuwa Abba ya ce "Abdallah duba mata" Ahankali ya aje cukalin abincin
sannan ya durkusa kasa Yana leka kafar Nur tare da cewa "Ina ke damun ki?"
Ganin in da Abba ya tsareta da Ido ya sa ta saurin cewa Abba bigewa na yi a kafa dazon,
Aunty Saratu ce ta ce, "Me ya sa baki fada ba tun da wuri, ai irin wannan saiki fada da wuri
aduba miki kafin ya yi tsami" Karake mgnr ya yi tare da kallon Aunty Saratu yana cigaba da
cewa, "idan tagama cin abincin a duba mata."
Amsawa aunty ta yi, shiru wurin ya dauka tsayon lokaci kowa cin abincin yake, ita ko Nur daker
ta dan ci sannan ta mike ta ce ta koshi, ta na shirin barin wajen Abba ya ce, "Zo nan naga
kafar." Dawowa ta yi gaban Abba ta zauna akasa, shi ko Abba kujerarsa ya ja baya tare da
rankwafowa ya na kallon kafar Nur, gannin in da gurin yayi jawur ya sa shi shafa gurin tare da
fadin, "Wannan saidai idan wani abinne ya fado miki amman ba begewa ba, idan kin shiga daki
kishafa man zafi a wurin."
Amsawa ta yi sannan ta mike ta wuce dakinta, a bakin gado ta zauna yayin da hawaye ya taro
acikin idonta, zuciyarta cike fal da sake-sake, so ya ke ya tunxurani naita fada dashi Abba
kuma ya ce bani da kunya, idan ba haka ba Kuma me nai mishi yanzu? gashi Mamy bata da

lafiya, idan takuma jin irin wannan bazataji dadi ba, ta fada cikin zuciyarta a fili Kuma cewa ta yi,
"Bazan sake tanka mishi ba kuma ba ruwana da duk wani abinda zai yi da ga yanzu, hannun ta
tasa tana shafa saman kafarta inda yayi jawur, wata zuciyar kecewa kimai Allah ya isa ya yin da
wata zuciyar ke kwabanta tare tare da tuna baya kadan, tsitan kanta ta yi da cewa, "Bazan
mishi Allah ya isa ba, kila nan da wani lokacin ya huce ya dawo cikin hankalin shi"
Washegari misalin karfe 8 na safe Nur sanye cikin kayan islamiyya tun da ta fito gida take
murmushi domin yanayin garin sosai ya ke burgeta haka nan kuma taji yau tanajin farin ciki,
sosai ta kosa ta isa makarantar dan haka take ta sauri.
Ta na dafda isa kofar gidan su Helen ta fara jiyo muryan Mamma cikin kuka tare da hayani
take fada sosai. Wannan ba bakon abu bane agurin Nur domin idan da sabo ya kamata ta saba
da ganin kukan Mamma, saidai tana ji na yau ya banbanta, gashi har mama ta fusata ta na fada
har ana jiyota a titi, akwai alama Poul ya kai ta bangon da bazata iya hakuri ba, tsintan kanta ta
yi da tsayawa cak ta kasa wucewa, tunawa ta yi da wulakancin da yai mata daren daya rage
mata hanya, sam bashi da kirki, tsitan kanta ta yi ta na kokarin shiga gidan da har yanzun fadan
Mamma ke tashi...



Fadila Lamido
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido

ADABI WRITER'S ASSOCIATION


Page 9-10

Ahankali ta tura kofar ta shiga, matar dake zaune wajen shakatawan gidan ce ta dago ta kalli
Nur hannunta rike da jarida, yanayin da be nuna irin na wadda ake tashin hankali a gabanshi
ba, cikin kwanciyar hankali take, babu alamar damuwa a tattare da ita.
Cikin sauri Nur ta kalli daya gefen, Helen ta gani tsaye tana share hawaye, yayin da Mamma
ke rike da rigar Poul ta na maganganu cikkn fada sosai, tsaye ya ke cikin shadda me dan karan
kau hannun shi ya daura akan na Mamma da ta rike wuyanshi dashi yana magana cikin hargagi
yayin da Mamma ma take fada sosai. Matar da ke hakimce Nur ta sake kallo, wannan lokacin
idonta da hankalin ta ya na kan jaridar da ke rike hannu ta, dan haka Nur ta sake mayar da
hankalin ta kan Mamma.
Duk da cewa bata san me suke cewa ba, ta ga laifin Poul din sosai, domin Mamma ba
sa'arshi ba ce, a Kodadaushe bashi da aiki sai na saka Mamma kuka, sam baya darajata, gashi
kamar mutumin kirki, sosai take son ta ga karewar abin amma sai kara daukan zafi suke yi; da
shi har Mamma, abin da ya ke shirin yi yau yafi na kullum dan ba karamin balaki ya ke yi ba, da
alama so ya ke Mamma ta sakar mishi rigar shi amman sai kara rikeshi ta ke, hawaye Nur ta
fara sharewa kamar yadda taga Helen na yi, ganin hakan bazai mata ta nufa matar dake can

gefe zaune tana fadi, "Aunty dan Allah kizo ki mishi magana" Waini kallo da matar ta wurga
mata ya sata saurin barin gurin, tsintan kanta ta yi ta na rike da Mamma, cikin Sauri Poul din ya
sa hannun sa ya banbare na Mamma tare da hankadata takoma da baya da karfi tai zaman
dirshen a kasa. Rungume Mamma Nur ta yi hakama Helen da ta karaso yanzun nan, kuka sosai Nur ta rushe
dashi ganin Inda Poul ya ci gaba da balbala masifa ya na nuna Mamma da yatsan shi, ita ma
Helen rungume Mamma ta yi ta na kuka sosai, zuwa wannan lokacin kuka kawai Mamma ta ke
yi batare da ta furta komai ba, shikuwa Poul saida ya yi bala'inshi ma'ishi sannan ya juya kanshi
a fusace ya fice a gidan. Haka Helen da Nur su ka yi ta bawa Mamma hakuri, ganin in da suke
kuka ya sa ta miki tare basu umarnin mikewa, ko in da matar nan ta ke mamma bata kalla ba ta
wuce ciki abinta, Helen ce tabi bayanta yayin da Nur ta nufi kofar fita daga gidan zuciyarta cike
da tausayin su.
Akofar gidan ta tsaya tana kallon hanyar da zatabi ta isa makaranta, sosai ta yi latti, ko ta je
ma korota za'ayi, dan haka ne dokar makarantar su, ta jima a tsaye sannan ta kama hanyar
gida, har yanzun hawaye na zubowa a idon ta, tun da ta doshi gida gabanta ke faduwa, hakama
da ta tura get din gidan su har wani rawan jiki ta fara. Bashir ta hanga zaune saman motar da
mamaki ya juyo yana kallonta tare da fadin "Ba'a biya miki kudin makaranta bane?" Kai ta
girgiza alamar a'a, kallonta ya ci gaba da yi ta na kokarin wuce shi ya sake cewa "Dukan ki ayi
ne

4 / 25