Ciwon Ya Mace Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   17 / 25

48K to 51K   out of 73.1K words

"Bacci nake ji" shiru ta sake yi
zuwa can ta sake fashewa da dariya tare da cewa "Ka bari karkasa cikina ciwo, gashi barin
bawa Nur ku gaisa" shiru taga ta yi tare da ya mutsa fuska, harta sauke wayar fuskarta bata
dawo daidai ba, ganin haka Nur ta juya mata baya domin tasan bazai wuce akan sunanta data
Kira bane, ita Bilkusu kallon Nur ta yi sosai sannan ta kwanta cike da tunani, washegari da safe
bayan Nur ta tafi makaranta Abdallah ya kira Bilkisu bayan sun gaisa ta ce, "Baby jiya daga
cewa ga Nur ku gaisa sai ka hau fada" Lumshe Ido Abdallah yayi sannan yace "Banson
maganar yariyar ne kawai, ko sunanta banson naji an kira" Cikin son taga ya sakko tace "To aini
ban saniba dasai ka gaya min, jiya daker na yi bacci"
"Ki yi hakuri bansan lokacin dana fara fadan ba amman ba'a dakinta aka barkiba ko?"
Jimmm Bilkisu ta yi zuwa can tace "Tare muke adakinta ne"
"Zanyi magana da Aunty a baki dakina ki zauna bana son alakanki da ita."
"Baby saboda me? Ni Inajin dadin zama da ita, tana da kirki"
"Eh, Nima ba cewa na yi bata da kirkiba, karkiga wai tana kusa da sa'arki ki saki jiki da ita, ba
kowanni abu Zaki dinga bari tanaji ba, kuma idan na kiraki a waya ki daina amsawa a gabanta"

Cikin rashin fahimta Bilikisu tace "Amman in tambaye ka?"
"Ina jinki?"
"Wai Nur ba kanwarka bace?" Ajiyan zuciya Abdallah yayi sannan yace "Wacce irin tambaya ce
Wannan kuma? so nawa zan gaya miki adadin 'yan gidanmu?" Cikin kwalwakl da Ido tace "Ai
ce min ka yi Nur ce autarku" Cikin son kawar da baccin ranshi yace "Eh itace auta"
"Mamy ce ta haifeta?"
Cikin sauri yace "Eh, Bakiga suna kama ba?"
"Na gani, to kaifa?" Wannan karon dariya Abdallah yayi sannan yace "Ai na gaya miki nine na
farko a wurin Mamy da Abba" Cike da gamsuwa tace "Na gane, to amma Nur ba Abba bane ya
haifeta?"
"Waye to?" Abdallah ya jefa mata tambayar, jin haka yasa Bilikisu cewa "Aini kai nake
tambaya"
"To Abba da Mamy sune iyayenmu gaba daya Baby, idan dan abin da kikaji na fada ne akanta
kike tunanin ba kanwata bace akwai abin da tamin ne."
"Toh ka yi hakuri kaji"
"Ai na hakura, amman dai bana wasa da ita, kema kuma bana son ki sakar mata fuska"
Dole Bilikisu tabar mgnr badan ankai inda take son akai ba domin har yanzun zancen be
shigeta ba. Hira suka ci gaba dayi kafin su kare har ta manta da zancen Nur.
****
"Mai yasa zaki firgice haka" Poul ke fadin Haka alokacin da ya tare Nur adaidai kofar gidansa
bayan sun rabo da Zainab. Kokarin gewayeshi take ta wuce saidai sai shan gabanta yake ya
hana mata wucewa, kwalkwal Nur ta yi da Ido tare da cewa "Ni ka rabu dani banso" lumshe
idon sa yayi tare da cewa magana zamu yi sai ki wuce. Dagowa ta yi ta kalleshi cikin sauri tai kasa da kanta dama can bata iya hada Ido dashi domin
sosai ya ke mata kwarjini, yau kuwa wani irin abu ne taji wadda ta rasa da wanni sunan zata
kirashi, gaba daya ji ta yi kamar zazzabi na son rufeta dan haka ta tsaya ta kasa cewa komai,
ita bata wuceba ita Kuma Bata dago ta kalleshi ba, zuwa can ya ce, "Nur yanxu bana iya bacci
sosai kodayaushe sai inji Ina son kallonki, gashi kin min nisa ban isa inzo gidanku ba, ke Kuma
ko kinzo nan bakya bani fuska." Sunkuyar da kai Nur ta yi bakinta zunbure batare da tace komai
ba, zuwa can ya sake cewa "Ina son ki dinga bani ko minti goma ne kowacce Rana nayin
magana dake" Can kasan makoshi ta ce "Sabo da me?" Lumshe Ido Poul yayi zuwa can ya
sauke akanta tare da cewa "Sabo da ina son ki."
"Mu ba haka muke yi ba" Cikin Ido ya kalleta sannan yace "Yaya kuke yi to?"
"Gidanmu zakaje sai ka gayawa Abbanmu " Da sauri ya dago ya kalleta tare da kiran sunanta
ahankali ta dago ta kalleshi, jawur taga idonshi cikin yanayin dake nuna yanajin tashin hankali,
cike da muwa taga ya bude bakin sa idonsa cike da ruwan hawaye yace, "Amman kina ganin
idan naje zai amince?" Tsintan kanta ta yi da cewa "A'a bazai aminta ba" Tsayon lokaci taji bece
komaiba dan haka ta dago ta kalleshi, gani tayi yana kawar da fuskarshi duk Yana yinshi ya
canza da ga ishashshe mai takama da naira ya koma kamar mai zama da damuwa, daker ya
iya cewa "Amman ke kin amince dani?"
Cikin Sauri Nur ta girgiza kanta duk da cewa tana tuna zancen Aunty Saratu amman ta kasa
yi kamar yadda tace. Bayan ya gama kare mata kallo yace "Mai yasa Nur?" Wannnan karon ma
tsintan kanta ta yi da cewa "Bakeje gidanmu ka gayawa Abbanmu ba." Jimmm, yayi zuwa can

yace "Na gane, to ai kince bazai yadda ba ko? Kina da wadda zaki aura ne?" Wannan karon kai
ta girgiza alamar a'a dan haka ya sake cewa to meye dalinlin? Sunkuyar dakai tayi tana mai
takaicin yadda take kulashi har yanzun ta kasa wacewa ta barshi, idon shi akanta ya sake cewa
"Ina jinki." Can kasan makoshi ta ce "Kai ba musulmi bane" Wannan karon shiru yayi tsayon
lokaci, zuwa can ya ce, "Amman ai addinin ku be hana ba." Can kasan ta sake cewa A'a
addinimu be yadda da mace ta auri na miji wadda ba musulmiba." Jimmm, yayi tare da
sunkuyar da kanshi kasa, gani yayi Nur tana kokarin wucewa Dan haka yai saurin cewa "Dan
tsaya" Tsayawa ta yi kamar yadda yace sannan ya ce, "Ni Kuma Gashi Ina son ki yaya kenan?"
Wasa Nur ta shiga yi da hannunta tsayon lokaci batare da ta ce komai ba, bayan Poul ya gama
kare mata kallo yace, "Ina jinki?" Dagowa Nur ta yi ta sata kallonshi sannan tace, "Hakan ba
daidai bane" Kallonta Poul yayi sosai sannan yace, Na gane, shikenan amman yanzun kinsan
mene ne?" Kai Nur ta girgiza tare da cewa A'a, Kara matsowa Poul yayi tare da cewa "Nasan
kin sanni barin sani, ina neman wani taimakone a wajenki, idan bazakiyi dan niba inci albarkacin
Helen."
Nur na wasa da hannunta tace "Mene ne shi?"
"Sai kin min alkawari tukuna in fada miki" Batare da Nur ta yi tunanin komai ba tace "Na yi"
"Na farkon shine kizo mu dan shiga daga cikin gida kin ga nan akwai idon mutane, na biyu
kuma sai mun shiga zan gaya miki...
CIWON 'YA MACE 20
By
Fadila Lamido

ADABI WRITER'S ASSOCIATION


Page 39- 40

Dagowa Nur ta yi ta kalleshi har yanzun ita ya ke kallo, cikin sauri ta sunkuyar da kanta kasa
tana wasa da hannunta ganin haka Poul ya ce, " Ba cikin gidan zamu shigaba daga bakin get
zamu tsaya in yi maganar da zanyi sauki wuce" Cikin Sauri Nur ta girgiza kai alamar a'a,
kallonta yayi ya sake cewa tsoron me kike ji? Bayan gidan ba bakonki bane, kuma da mutane a
cikin gidan nan bakin get ma akwai mai gadi, idan cutar da ke zanyi ai ba anan zance mu
shigaba ko? Wannan maganar da yayi yasa ta tuna waye shidin, hakika duk wadda yaganta
tsaye da Poul abin zai bashi mamaki matuka, dagowa ta yi ta kalli layin nasu babu kowa, tsoro
ne ya shigeta kar wani dan gidan su yazo ya ganta tare da Poul, yin wannan tunanin yasa ta
nufi shiga gidan, biyo bayanta Poul yayi yana Mai sauke ajiyan zuciya, mai gadin dake can
kofar dakinsa ne ya juyo ya kallesu sannan ya dauke kansa, in da Nur ke tsaye Poul ya tsaya
tare da kureta da Ido, sosai kallon da yake mata ya ke sata shiga cikin damuwa domin a duk
sanda yai mata irin kallon tana shiga cikin wani yanayi wadda take rasa gane kanshi, ganin
bashi da niyyar magana ta ce, "Ka yi maganar sauri nake yi a gida za'aga na dade" kanshi ya
shafa tare da matsowa daf da ita, can kasan makoshi ya ce" Duba yadda na zama Nur, gaba
daya banda nutsuwa, wata daya da ya wuce idan ance min zan zama haka bazan yaddaba, yau
da kika tsaya muka yi magana bakiji yadda naji dadiba, yanzun abu daya nake son kimin dan

Allah karkice a'a, ki taimaka min in samu nutsuwa yau in yi bacci mai dadi" Dagowa Nur ta yi ta
kalleshi, har yanzun a burkice ya ke, idon shi kawai ya isa ya tabbatar maka da hakan, cigaba
yayi da cewa, "Zaki taimaka min?" Ahankali Nur ta daga kanta alamar eh, matsowa ya sake yi
ganin haka Nur ta kara mannewa jikin get din kasa-kasa yace, "Dan Allah ki dan tsaya na
rungumeki kona minti biyu ne" Cikin sauri Nur ta dago ta kalli jajayen idonsa tare da girgiza
kanta, ganin haka ya kafeta da Ido tare da cewa mai yasa?" Kawar da kai Nur ta yi sannan tace
Haramunne" Lumshe Ido yayi zuwa can ya bude su akanta tare da cewa, "Haram? Wannan
karon ma kai ta daga mishi tare da cewa "Eh, babu kyau hakan ba daidai bane"
"Na gane, to hannun fa? Zaki bani hannunki mu gaisa?" Wannan karon ma kai ta girgiza alamar
a'a, yawu Poul ya hadiye sannan yace "To shikenan amman zan iya baki waya anjima mu
gaisa? Kai Nur ta sake girgizawa alamar a'a, cikin rashin jin Dadi yace "To shikenan, je ki na
gode" kamar jira Nur take ta wuce tana daf da fita gidan ya sake kiranta, tsayawa ta yi, wani kati
ya mika mata tare da cewa akwai number ta a jiki, anjima ki kirani" amsa kawai ta yi ta juya
domin sosai ta kosa tabar wajen. A sanyaye ta isa gida, sannu taiwa Mamy sannan tai saurin
wucewa dakinta domin gani take kamar mamy zata gane bata da gaskiya, a yadda ta shiga
dakin yasa Saida Bilkisu ta bita da kallo, domin yanayinta ya nuna kamar batasan mai take ba,
Daker ta iya cin abinci ta yi duk abin da zatayi sannan ta wuce islamiyya. Bayan sati daya Nur
ce tsaye bakin makarantar tana jiran mashin, tun daga ranar da Poul ya tareta ta daina jerawa
da Zainab, ana tashi take hawa mashin ta wuce gida abinta, yauma tsaye take tana jiran mashi
taga motarsa ta tsaya gabanta, wani irin faduwa gabanta yayi, bude motar yayi ya fito, gabanta
ya tsaya tare da cewa, "Sannu Hajiya" kawar dakai Nur ta yi kasa-kasa tace "Ina wuni"
" Lafiya" Ya fada idonshi a kanta, "Ya gida da karatu?" Wannan karon ma kasa-kasa Nur tace
Lafiya lau" Zo muje mana in sauke ki? A'a mashin zan hau" Jimmm yayi zuwa can ya ce,
"Shikenan, mai yasa baki kirani ba ranar dana baki kati na?" Na mance ne" Nur ta fada tana
wasa da hannunta, shiko Poul cike da damuwa ya maimaita zancenta sannan ya ce to yanzun
na tuna miki, dan Allah ki kirani. Da kai anur ta amsa Motar ya koma ya shiga tare da cewa
"Zaki kirani ko?" Wannan karon eh tace tare da tare mashin tahau, mashin din na shirin tashi ya
taho da motar wurin ya daga murya ya ce, "Katin na nan ko?"
"A'a ya bace" Wani katin ya sake cirowa ya mika mata, sannan ya figi motar kamar zai tashi
sama ya bar wajen, ko da Nur ta isa gida ciro katin ta yi ta kalla kamar yadda ta yi ranar da ya
bata wancen, bayan ta gama karewa katin kallo ta dauko Littafin da ta saka wancen tasa
wannan, sannan ta maida Littafin ta ajiye, tsayon wata daya suke shafe a haka, idan yaga
kwana biyu bata Kira ba sai ya sake aiko mata da wani katin, harsaidata tara koma sha tara
batare da ta kiraba, yasha aiko Zainab ta kawo katin tare da rokon ta kira din, amman ko sau
daya Bata taba kwatanta kiraba, sosai suka saba da Bilikisu a yanzun hira suke sosai ta saki
jikinta dasu Mamy ma, yau kawar Bilkisun ce tazo, wannan shine zuwanta na biyu gidan, tun a
zuwan farko suka saba da Nur, dan haka yauma har da ita ake hiran, labarin saurayinta take
bayarwa, sunata dariya, zuwa can kawar Bilkisu Madina ta kalli Nur tace "Ke baki bamu labarin
saurayin ki ba?" Tabe baki Nur ta yi tare da cewa "Ni bani da saurayi karatu nake son na yi
sosai."
"Wallahi karyane kice baki da saurayi, mu ma ai duk karatun zamu yi Amman ai da samarin mu"
Madina ta fada tana kallon Nur, "Niko bani dashi, ku gani kuke na girma ko?"
"Eh mana to dame muka fiki" Bilkisu ta fada tana dukan kanwason Nur, dariya Nur ta yi sannan

tace to awurin Abba da Mamy har yanzu karamar yariya ce ni, kofa waya basu yadda na rike
ba" Dariya Su Bilkisu suka kwashe dashi yayin da Madina tace "An barki a baya wallahi"
"Ba wani baya, ni haka yafi min, wayar ma mai zan da ita, duk wadda nake son nai waya dashi
zan iya amsan wayar kowa a gidan nan nayi wayata banda matsala da waya" Domin karatu
nake son na yi sosai." Bilikisu ce ta ce "Wai da gaske baki da saurayi? Maganarwa naji kuna yi
ke da Zainab ranar ce?" Juya baya Nur ta yi tare da cewa "Wannan yayanta ne fa, waishi a dole
sona yake, Kuma ba musulmi bane fa" Zaro Ido Bilkisu ta yi tare da cewa, "Kamar ya
bamusulmi ba? Ba kince yayan Zainab bane?" Dan Waigowa Nur ta yi kadan sannan tace, "Eh
yayantane amman ita da Mamman su ne masulmi shi arne ne, wai Kuma a hakan ya ke sona"
Madina ce tace "Kuma idan Yana sonki fa saikiga ya musulunta."
"Hmm umm lallai, wannan mutumin ne zai musulunta? Bashi da kirki sam, shi a tunanin shi a
hakane zan aureshi, kuma nasan Koda ace musulunta yayi Abba da Baffah bazasu yadda ba, ni
shiyasa ma ban kulashi, baranma ya Bashir, tab" Nur ta kareke maganar tare da juyawa baya,
Jimmm, Bilkisu ta yi yayin data shiga nazari jin Nur takira sunan mazan gidan bata kira na
babban yayanta ba, share tunanin ta yi ta hanyar cewa, "Gaskiya ki yi saurayi soyayya da dad"
Madina ce ta ce "Ke dallah rufe mana baki, keda kwana shidda da tarewa mijin ya bulaki ya tafi
ya barki" Aunty dake kokarin shigowa dakin ce taja ta tsaya alokacin da taji Bilkisu na cewa
"Wallahi yadda kike haka nima nake ba bulanin da aka yi" Madina ce tace "Wallahi karya ne,
kwanaki shidda fa tare dashi a dakin kice ba abin da yayi miki har ya wuce?"
"Eh mana, alkawari muka yi bazai tabani ba sai ya dawo."
Madina ce ta sake cewa "Eh, ji ya zama dole, amma yadda kuwa ba dole bace, daga ke sai
Abdallah adaki kice anyi kwana shidda be kusanceki ba?" Cikin da nishadi Bilkisu tace "a rantse
da qur'anin Ubangiji har mukai kwana shiddan abin da kike tunani be shiga tsakanina dashi ba,
kuma wuri daya muke kwana." "Tabb lallai, amman na sarawa Abdallah da kokari, Juyawa Aunty ta yi rike da kular abincin,
itako Nur bata saka musu bakiba saidai duk hiran tasu tana jinta cikin kunnenta.
*****
Gaban Mamy Aunty ta dire abincin tare da cewa, "Ikon Allah" Dagowa Mamy ta yi ta kalleta
sannan ta kalli kular abincin tace "Lafiya kuwa?"
"Dawowa nayi na kira Nur ta dauka"
"Lafiya ko?" Mamy ta tambaya, hiran da ta juyo ta kwashe ta gayawa Mamy cike da damuwa
Mamy tace "Ikon Allah, to Abdallah lafiya yake kuwa Saratu?"
"Nima dai abin ya daure min kai Mamy, sai dai fa kinsan yaso abar bikin har ya dawo watakila
shiyasa yayi hakan kinsan yaran nan idan Basu suka yi niyyar abu ba babu wadda ya Isa ya sa
su"
Jimmm Mamy ta yi tare dace "Niko da kinsani da baki Gaya min ba wallahi, yanzu zan shiga
damuwa da zulkumi, meye ribarshi ta yin hakan to? Idan haka ne manene amfanin auren?"
"Yaran zamanin kenan ai Mamy, faface kawai wata rana zakiga ya dawo ya daukita dan ban
tunanin zai iya hakuri har ya kammala batare da ya dawoba, suna waya da ita sosai, kuma
kullum mukayi waya saiyace ya take, ta saki jikinta ko a'a, hankalinnshi Yana kanta."
"Ajiyan zuciya Mamy ta yi sannan ta ce, "Shikenan, Allah ya kara karkato da hankalinshi
gareta,, Aunty ta amsa da Amin tare da kwalawa Nur kira. Bayan ta amsa tazo ta dauki abincin.
Sai yamma Madina ta tafi, har kofar gida suka raka ta ita da Nur sannan suka dawo cikin gidan,

kitchen suka wuce domin yau Aunty tace su zasu yi kirkin ginan, cikin kankanin lokaci suka yi
suka gama, suna yi suna kira, bayan sun gama ma jarashi sukayi kamar yadda aka saba,
sannan suka koma daki suka yi wanka. Misalin karfe 8:30pm gaba dayansu suka zauna akan
teburin cin abincin gidan Amman banda Bilkisu dan bata iya zama wurin har idan Abba na nan,
dan haka adaki take cin nata, suna cikin cin abinci Bashir ya shigo, da ledoji niki Niki a
hannunshi, afalon

17 / 25