Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
dan haka ta hakura ta
mike ta nufi komawa cikin ajin su, sosai ta ji jikinta ya kara sanyi tare da jin komai baya mata
Dadi, ta na daf da shiga ajin wayar ta dauki kara, kallo daya tawa wayar sannan ta juya ta koma
gefe tare da ansa kiran.
Kuka ta saka cikin wayar, bayan tsayon wani lokaci ta sassauta kukan nata, zuwa can kuma
ta share hawayen tass, sannan tabar shashshekar kukan tare da fadin, "Eh ina ji" Shiru ta sake
yi tsayon lokaci, da ga can ta sake cewa, "Mamy kawai na fadamawa" Turo baki ta yi da alama
fada ake mata cikin wayar, zuwa can ta ce, "Ai be dace ba abin da ya ke, kuma kowa kallon
mtumin kirki ya mishi, ni ba sharri nake mishiba..." Shiru ta sake yi, bayan tsayon lokaci ta na
saurare tace, "Sabo da Mamy" Sosai ta kara bata ranta zuwa can tai jifa da wayar can nesa,
kallo tabi wayar dashi, kome ta tuna kuma saita mike da sauri ta dauki wayar, dake karamar
waya ce babu abin da ta yi, ganin wayar bata katse ba ta sake maida ita kunnen ta tare da
fadin, "Na bari" Shiru ta yi na wanni lokaci sanna n ta ce, ba yarwa na yi ba faduwa ta yi"
Wannan lokacin ma shiru ta sake yi, zuwa can ta sauke wayar sannan ta nufi ajinsu jikinta a
sanyaye.
Bayan an tashi makaranta ta koma gida, har yanzun Mamy fushi take da ita, dan haka ta
cigaba da yin duk wani abu da tasan zai faranta wa Mamy rai, shiko Yaya Abdallah ba ta sake
barin sun hado ba domin ya zun ta lura dashi ya riga da ya tsene ta.
Haka ta cikaba da lallabawa har saukanta ya rage saura kwana biyu, duk wani shiri ta gama
yin sa, Abba da Mamy sun mata komai da akewa yar gata daidai gwargwado, a na i gobe sauka
ta je lalle da kitsu, bayan ta dawo farin ciki ne ya kama Mamy kallon kurulla tai mata tare da
fadin "Ba karamin me sa'a bane mijin da zai aure ki, tubarkallah ma sha Allah, duk wadda ya
same ki a matsayin matar aurensa lallai ya tsinci dami akala
Murmushi ne ya subuce ma Nur cikin matsanancin jin kunya ta ce "Mamy ai fushi kike da ni
har yanzun"
"Eh, ai kece kika mata min rai, bedace ace kina boye min komai ba, ni uwarki ce, idan har
bazan san me kike ciki ba meye amfanina?"
"Toh ki yi hakuri kinji? Kuma ban boye miki komaiba wallahi Mamy, Yaya Abdallah yasan ba in
da naje wallahi"
"Na ji Nur, ni dai fatana ki nutsu, ke mace ce, dan haka ki daina karanbanin saka kafar a ko
ina"
Amsawa ta yi da to, sannan ta mike ta nufi dakinta, Mamy ko binta da kallo ta yi duk wani
alamar girma ya riga da ya bayyana ajikin Nurr, yariya ce kyakyawa fara sol me mayan idanu,
siriri ce sosai, saidai duk da cewa shekarunta bazai wuce sha shidda ba kirjinta cike yake taf ma
sha Allah, sauke kai Mamy ta yi, bayan Nur ta kule tare da cewa "Allah ya nuna min auren
yariyar nan lafiya sai naji tamkar inzoba ruwa a kasa in sha"
Washegari tun da sassafe ta shirya cikin fararen kaya safar hannu da ta kafa baki haka ma
fuskanta bakin nikafi ne, dakin Mamy ta shiga bayan ta gaisheta ta dauki turaren Mamy kan
madubi da fesa cike da murmushi Mamy tace "Allah ya kawo mu" Itama Nur murmushi ta yi
tare da fadin "Mamy zan wuce dan Allah kuzo da wuri" "In sha Allah Nur, dan ina ga ma ko Abban ku saidai ya saman acan" Da murmushi Nur ta nufi
dakin Abba, acen ta samu Aunty Saratu zaune bayan ta gaishesu Abba ya shiga mata addu'a,
in da ya kare da cewa, Allah ya sa in ga ranar auren ki kamar haka, duk yawan family nan
bamu taba aurar da diya mace ba" Cike da shagaba Nur ta fice tare da da cewa "Saura dai ka
ga na zama likita Abba" Abba daya juyota bayan ta fice yayi murmushi sannan ya kalli Aunty
Saratu ya ce, "In sha Allah tun da tana son karatu zan tsaya mata ta yi sosai" Gyara zama
Aunty Saratu ta yi sannan tace "Ai daman yaran gidan nan suna Karatu Alhaji."
"Eh haka ne, sai dai ita mace ce, amman bazai garara ba, in dai ta maida hankali zan cika
mata burinta" Nisawa Aunty Saratu ta yi sannan ta ce, "Amman Alhaji sai na ke ganin kamar
rashin sa'aninta mata da babu cikin dangi yana taba ta sosai" Murmushi Abba ya yi tare da
cewa, "A'a, babu wannan maganar anan gidan, sai dai da ya ke kinsan aski idan yazo gaban
goshi yafi zafi, Bashir da Abdallah su na janta ajiki, ga kuma Jamal da Jamil, nan gaba kadan
duk aure za su yi, matayensu suma 'ya'yayenmu ne"
Bude baki Aunty ta yi da nufin yin magana kome ta tuna kuma sai tai shiru tare da mikewa.
****
Misalin Karfe 10:am filin saukar ya cika ya tunbatsa, sai dai har wannan lokacin baza ido Nur
ta ke, domin bataga wani daga gidansu ba dan haka banda baza ido babu abun da ta ke,Tuni
aka fara karatu, gashi an hanasu tashi bare ta nemi waya ta kira Mamy, ta na cikin wannan
yanayin taji an kirayi sunan ta, Maryam Jibiril Mailafiya, mikewa ta yi tame jin kafarta na rawa,
har ta isa kan munbarin ta amsa abin maganar, cikin nutsuwa ta ke rairo karatun ta, yayin da
jama da dama suka maida hankali wajen sauraronta, bayan ta gama ta mika abin maganar ta
sauka akan munburin tare da isa gurin zamanta, tana zama ta fara share hawayeta cikin nikabi,
ganin har wannan lokacin babu kowa da ga gidan su, matar da ta dauki hoto ne a gurin tazo ta
mika wa Nur hoton da ta dauketa wurin karatun, karba ta yi ta kalla, ganin bata da kudin da zata
bayar yasa ta mika mata tare da fadin "Zan amsa anjima" Durkusuwa matar ta yi tace "Ina yan
uwanki suke in kai musu?"
Hawaye ne ya zubo wa Nur alokacin da take cewa "Basu karaso ba" kafadanta ta dan dafa
alamar rarrashi, daker Nur ta iya rokon matar aron waya, saidai har sau uku ta kira number
Mamy ba'a daga ba dan haka me hoton ta kara bata hakuri sannan ta wuce.
Acikin ranta ta ke tunanin ko menene ya hana su zuwa? sam bata tsammaci haka ba, nan taji
komai yabar yi mata dadi, kiran sunayin yan saukan da aka fara domin basu shahada ya dawo
da ita cikin hayyacin ta, agefe guda ta hangi mata nan nata mata wa su hoton dan haka ta nuna
mata alamar ta habari, matsowa matar ta yi kusa da ita tace "Wani ya amsa hotunan ki ya ce, a
kara miki wasu" Duk da cewa batasan wane ne ba dadi taji har tai ajiyan zuciya batare da ta
sani ba, zuwa can aka kira sunan ta, nan ta miki akaro na biyu ta isa gurin, acikin ranta take
cewa, "Allah yasa koma wanene yazo min yamin kara kar a gane Abba da Mamy basuzo gurin
nan ba, saidai ga mamakinta ta Abba tagani Yana tahowa filin cikin babban riga da hula,
bayansa Yaya Abdallah da Yaya Bashir ne sai dai Abba ya rigasu isa gurin dan haka shine ya
karban mata Shahada, bayan angama masu hototuna suka koma gurin zamansu, sosai Nur ta
cika da farin ciki acikin zuciyarta take cewa, "Abba ma yana farin ciki sosai, hakama Yaya
Bashir ya kasa boye farin cikinsa sai yake hakora ya ke, shi ko Yaya Abdallah fuskarshi babu
yabo babu fallasa, bayan an gama bawa kowa sannan aka sake kiran sunan Nur a matsayin
wadda tazo na daya, nan farin ciki ya sake rufe su Mamy, fitowa ta yi ta amsa kyautuntuka,
sosai taron ya kayatar, kowa na nuna sha'awarsa, bayan an tashi gurin zaman su Abba ta nufa
ta kwanta kafadan Mamy cikin shagwaba tace, "Mamy bakizo da wuri ba"
"Injiwa ya gaya miki, Yaya Bashir ne ya ce muna nan aka fara Karatu"
"Ni ban ganku ba har na fara kuka fa"
Dariya suka yi gaba daya da ga nan Yaya Bashir ya kira me hoton nan suka hadu suka yi gaba
daya har da Baffah da iyalanshi.
Kowa cikin fara'a ya ke, adaidai wannan lokacin ne Nur ta hangi kyawawan samari guda biyu,
tun da Nur ta gansu fara'ar fuskanta ya dauke, Mamy ce tace, "Nur ga su Jamal can ki maza
kije ku gaisa"
"Mamy su karaso nan mana' kasa Mamy ta yi da murya ta ce "Ki je dai domin kema kinsan ba
zuwa zasu yi ba"
Sakin hannun Mamy ta yi ta isa gaban su, tun tana cikin su Mamy su ke mata wani irin kallo
har ta iso gaban su, cikin girmamawa ta gaidasu yayin da suka amsa a wulakance tare da fadin,
"Da baza kizo bane?"
"A'a mu na yin hoto ne" Nur ta fada tana satan kallon fuskar Jamil wadda ko gaisuwar ma be
amsa ba, Muryan jamal ta ji yana cewa "Ke ma kinsan idan ba dole ba babu abun da zai
kawomu cikin wannan unguwar bare wannan yar tsukukuwar makarantar dako iska ba shigowa
ya ke ba"
Bakin shi kawai Nur ta kalla ta kara yin kasa da kai.
Jamil ne ya ce "Jamal mu je, ai dai ta gammu ko? Cike Da haushi Jamal din ya ce, "Ni
wallahi ko bata gammu ba babu abin da ya dame ni. Tsoronta akeji ne? Ko zumuncin dole ne?"
Lumshe Ido Nur ta yi ganin suna kokarin barin wajen ta ce "Baku gaisa da su Abban mu ba
gasu can"
Jamal dake baya ne ya ce "Ayya, haka ne fa, oya to mu je mugaida su" Yana maganar ne
yana cigaba da tafiya dan haka ta bisu da kallo har suka shiga motar su suka bar wajen.
Bayan ta ga wucewan su tsaki ta ja afili ta ce "Dadin abun dai mu ma ba matsiyata bane,
kuma da zuwan ku da karkuzo duk daya" A daidai wannan lokacin ta ji an gota ta bayan an
hankade kafadarta, dan haka ta bi mutumin da kallo, mamaki ne ya kamata dan haka ta kara
baza idonta domin gani ta yi kamar yayan Helen ne Poul ya wuce ta. Tsaye ta yi a gurin tana son tabbatarwa, motar da ya nufa tabi da kallo, har ya isa gabanta na
faduwa tare da tambayan kanta me ya kawoshi cikin musulmi? Yadda ya ke da shigarsa bazaka
taba gane cewa ba musulmi ba ne, haka Kuma ko magana yayi babu alamar da zata nuna
maka hakan, "Kenan ya yi amfani da hakan ya shigo makarantarmu?" Nur ta fada cikin
zuciyarta tare da saurin takawa domin tabbatarwa, motar ta ga ya bude ya shiga ya zauna,
sannan ya waigo ya suka yi ido hudu tamkar yasan tana kallon shi dama can. Sosai gaban Nur
ya fadi faduwa me tsanani, ganin irin kallon da ya ke mata, haka ta tsaya cak tamkar an dasa ta
agurin, fararen ya tsunsa ta ga yana karkadawa alamar tazo kusa...
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 13-14
Saidai ta na daf da isa gurin ta ga motar ta tashi dan haka ta tsaya cak a daidai lokacin da ta
jiyo Yaya Bashir yana kiranta. Juyowa ta yi cikin da sauri ta ke kokarin isa gurin tare da cewa
acikin zuciyarta "Kodai dama idona ne ya nuna mani kamar ya kira ni." Da irin wannan tunanin
ta ta koma cikin Mamy batare da tabar waiwayen bayantaba, har yanzun ta na mamakin zuwan
Poul wannan gurin.
Hotona suka kara yi bayan sun gama suka wuce gida, suna isa gidan ma samunsa su ka yi
cike da jama'a, Aunty Saratu ce ke kula da bakin, gaba daya dangin cike suke da farin ciki tare
da sha'awan Nur tare da ganin kazonta, ga uwa uba nutsuwa da hankalin dake gareta.
Shima Abba sosai ya yi farin ciki saidai a kasan zuciyarshi ya na da wani tunani akan Nur;
ganin inda kwana biyu yanayinta yake kokarin canzawa daga kyawawan dabi'u zuwa munana.
Ita ko Mamy a yau kallon tsananin kauna ta ke ma Nur; duk da cewa ta canza amman tasan
wane ne sular canzawan na ta.
Washegari Nur ta tashi da tsananin gajiya lokacin da ta isa dakin Aunty Saratu zama ta yi
cikin nuna gajiya. Kallonta aunty Saratu ta yi sannan ta yi murmushi tare da cewa "Ai zuwana
uku kina bacci"
"Da kin tashe ni Aunty, ina tashi naji kamar an kwashe min 'ya'yan hanjina." Mikewa Aunty ta yi
tare da fadin "Duk sabo da yunwar? Ai sai ki yi maza ki je ki karya ni na azama zaki makaranta
ne"
"A'a saida yamma zani" Nur ta fada tare da gyara zamanta. Adaidai wannan lokacin Abdallah
ya shigo dakin, sai dai ganin Nur yasa ya dan yi jimmm kadan, sannan ya shigo ya zauna tare
da fadin, "Aunty ina son na yi magana da ke" Kallon Abdallah Aunty ta yi sannan ta mike ta isa
kujeran da Abdallah ya zauna ta zauna gefen sa tare da cewa "Ina jin ka" Juyowa yayi ya kalli
Nur ya ce "Baza ki bamu wuri ba ?" Kallon shi Nur ta yi sannan ta mike ta na kokarin fita taji ya
ce, Kina kallona ne da wasu dakwa-dakwan idon ki kamar na mage, kallon aunty Saratu ya yi
sannan ya nuna Nur tare da fadin "Wai dan Allah aunty kuna ganin abin da nake gani kuwa?"
Jin haka yasa Nur ta tsaya cak, itama Aunty Saratu cike da mamaki ta ce me ye shi? "Jibeta fa
kamar sanda daka kalleta babu abin da kake gani sai dai katon hanci da wasu manyan
abubuwa da suke jan ta" Kirjinsa ya nuna da hannu dan haka Aunty ta yi murmushi kadan tare
da cewa, "Nur ki je abinki" Wucewa ta yi a hankali tanajin lokacin da Aunty ta ce "Abdallah
kenan, baka da dama"
"Wallahi Aunty da ka kalleta su kawai kake gani abun ko tsari babu, ko ta ina yariyar nan bata
da hali, a baya tausayinta nake ji, yanzun ko dana kalleta saina rasa da wacce dambar zan
kwatanta ta sabo da muninta da nake gani." Runtse ido Nur ta yi sannan ta wuce, sosai ta yi
dana sanin sauraron kalamansa, cike da damuwa ta koma dakinta, a cikin zuciyarta ta ce,
"Wato sabo da tsabar muni na ya rasa dambar da zai hadani da ita, hawaye ne suka zobo mata
tasa hannu ta share sannan ta mike ta isa gaban madubi, kallon kanta take acikin madubin tare
da rike hancinta sannan tace afili, "Mene ne wasu abubuwa da suke janna? Zan so nasan meye
shi wannan abin dake jana" Kiran da taji Aunty Saratu na mata ya sata share hawayen sannan
ta nufi dakin.
Wayar Abdallah ta miko mata tare da fadin, "Abdallah ne ya manta awayar shi, gashi ana ta
kiran shi, ki kai mashi ya na gidan su Auwal."
Amsa ta yi sannan ta fice a dakin, dakinta ta koma ta sanyo babban Hijjabi, sannan ta daura
nikabi ta rufe fuskarta, fitowa da ga cikin dakin ta yi tare da kallon wayar, wannan ne karo na
farko da ta fara ma wayarsa kallon kurulla, tsintan kanta ta yi da danna wayar yayin da wani
kyakyawan hoton budurwar yariya ya bayyana, sosai kyan yariyar ya dauke hankali Nur; har ma
ta fara tunanin inama ace takai ta kyau, wani abin da ya kara bata mamaki wayar a bude take,
cikin sauri ta shiga danna wayar, cika ta yi da mamaki lokacin da ta ga mutanen da yai waya da
su daren jiya, duk sunayen mata ne har su tara, Kuma ko wacce ya dauki tsayon lokacin yayin
da yai waya da ita, gurin adana hoton cikin wayar ta nufa, ta fara dubawa, nan ta fara cin karo
da hotonanshi dare da taurarin finafinen Hausa mata da maza, tun da ta bude bakinbta ta kasa
rufewa sabo da tsabar mamaki, tunani ta shiga yi shi kuma me ye ya hadashi da Yan fim din
Hausa ko shima ya na fitowa ne aciki ko kuma Fim din yake son ya fara, gefen videos ta gani ta
na kokarin shiga gurin taje motsin tafiya dan haka tai sauri ta maida wayar cikin hijjabinta tare
da fitowa daga cikin falon. Mamy ta gani ta na fitowa daga dakinta bayan sun gaisa Mamy ta ce,
"Ke zani in tado ashe kin tashi ma."
"Na tashi Mamy, zan kaiwa Yaya Abdallah wayarsa gidan su Yaya Auwal" Ajiyan zuciya Mamy
ta yi tare da cewa, "To yi maza ki dawo" Juyawa Nur ta yi ta fice da sauri take tafiya domin
yunwa ke kwakular cikinta.
Tafe take tana sake-sake cikin zuciyarta akan