Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
nai wasa
ma yana iya samin dukan kamar yadda Mamy ta ce." Yin wannan tunanin ya sa ta dago ta kalle
shi, ido su ka hada dan haka tai saurin sunkuyar da kai. Murya kasa-kasa ya sake cewa ina
takalminki?
"Kallon kafarta ta yi sannan ta ce, Na baro su acan."
" Can Ina?"
Wannan karon kanta ta sunkuyar dan haka ya wuce ya bude motar tare da fadin "Shiga mu
je" A wannan lokacin kasa musu ta yi domin wannan shine kadai mafitar ta, don ko tabarshi ya
tafi batasan hanyar da zatabi ta koma gida ba; asali ma bata da kosisi.
Motar ta shiga ta zauna sannan ya rufe ya zagaya ya shiga motar, kallo daya yama Nur ya
tada motar, tun da ga lokacin be sake kallon inda take ba, i ta ko Nur mamakinsa ne ya sa ta
kallonshi domin bata iya tuna rana daya daya dago ya kalli idonta dahar zai ganta a hanya ya
shaidata, satan kallon shi take sosai abin ke bata mamaki a zuciyarta ganin abun take kamar
mafarki, tafiya suka yi mai tsawo sannan ta fara gane hanya, kasa-kasa ta yi da murya ahankali
ta ce "Anan zan sauka."
Ko motsi beba bare ya nuna ya ji ta, gudu kawai yake yi akan titin.
Ganin ya yi banza da ita ta juyo ta na kallon window motar sannan tai saurin juyawa ta sake
cewa, "Anan zan sauka, ina son inje gidan Ummy ne ta rakani gida, idan na koma ni daya za'a
min fada."
Wannan karon ma ko motsawa be yi ba illa kara tamke fuskarsa da ya yi.
Gani ta yi ya koma Poul dinshi sosai, yanayinsa da da zubinsa yafi kama da na yaran
manyan malamai hakama shigarsa da kasunbarsa, yafi Yaya Abdallah da duk mazan da ta sani
yin shiga ta mutunci irin na cikkkun Hausawa haka kuma ya na da Hausa radam a bakinshi,
amman kash bashi da mutunci ko kadan, duk da cewa ya mallaki makudan dukiya tare da
manyan motoci amman rashin kirkishi yasa besan ta yadda zai kashi kudin su amfane shi ba,
tsaki taja afili batare da tasan lokacin da ta sakeshi ba, sabo da tsabar takaicin halin shi, duk da
cewa ita bata yii tunanin ma ya santaba bare har ya iya shaidata amman ita tasanshi farin sani,
bawani bane Poul ne yayan Helen mai share jama'a tare da sha musu kunu. Ta gafen idonta ta
saci kallon shi, wannan kallon ya kara mata nutsuwa sosai domin fuskarsa kawai ta tabbatar
mata da babu wasa kuma bazai taba sauraranta ba, dan haka itama ta gyara tata fuskar tare da
tunanin yadda zata tunkari Mamy ita daya a wannan daren. Babu abin da motar ke yi sai zuba
kamshi duk da cewa gudu sosai ya ke amman tankar suna tafiya sama babu gargada sam,
sosai Nur ta kosa ta sauka a motar sabo da tsabar kyamarsa da ta ke ji.
Daidai kofar gidan su Nur Poul ya faka motar shi bayan sun iso, kokarin bude motar Nur ke yi
ta hango su Abba na tahowa. Yaya Abdallah da Yaya Bashir suna biye dashi abaya da alama
da ga masallaci su ke, dan haka tai saurin komawa cikin motar ta zauna tana satan kallon su,
hannun ta daya na rike da murfin motar.
Muyarsa taji cikin bada Umarni ya ce, "Fita!"
Da sauri ta kallishi tare da fadin, "Ina zuwa dan Allah bari su Abba su shiga gida"
"Fita nace na ce!"
"Ka yi hakuri su Abba su shiga gida"
"Fitan min amota!" Ya sake fada tare da zare mata Ido. Wanni irin kallo tamai sannan ta ce
"Baza ka bari su shiga gidan ba?"
"Eh bazan Bari ba ki fita, sauri nake"
Wanni irin ajiyan zuciya ta yi tana rike da murfin motar saidai ta kasa budewa, gani ta yi ya
rankwafo ya hankada murfin motar ta bude gaba daya dan haka ta zare ido tare da binshi da
kallon mamaki, su Abba kuya yadda aka hankado murfin motar shi ya jawo hankalinsu suka
dawo da hankilinsu wurin, Poul kuwa hannu ya daga da alama hankadata ya ke shirin yi dan
haka tai saurin ficewa cikin motar batare da yin wani tunani ba, hannun sa ya rufe motar da
karfi sannan ya figita ya wuce abun shi.
Gaban su Abba Kawai ta ganta batare da tasan lokacin da taje ba, suma din cike da mamaki
suke kallon ta, mamaki karara a fuskan kowannen su, sunkuyar dakai ta yi yayin da zufa ke
yanko mata ko ta ina, domin tasan Abba baya wasa kuma ba a masa karya ko kauce-kauce,
duk wayon ka duk dibaran ka kanayin magana yake gane inda ka dosa. Jin shirun yayi yawa ta dago ta ta saci kallon su, gani ta yi su Yaya Abdallah na kallon Abba
yayin da shi Kuma Abba ya kafe ta da ido, sosai yake kallonta dan haka ta ji kafafuwanta sun
gaza daukanta, durkushe ta yi ta zauna akasa.
Zuwa can Abba ya gyada kai juya yayi ya shige gida tare da fadin "Bashir dauko min yariyar
nan."
Amsawa yayi da toh, sannan yai tsaye har Abba da Yaya Abdallah suka shiga gida, ahankali
Yaya Bashir ya ce "Mike"
Babu misu Nur ta mike yayin da Yaya bashir ya bi bayanta yana cewa, "muje"
Tafiya take tana waiwaye har suka shiga cikin falon.
Mamy naganin shigowanta ta ce, "Ke Kuma da na ce miki kiyi maza ki dawo shine kikai dare,
ita Kuma hajiya Salma ta barki har wannan lokacin?
Lumshe Ido Nur ta yi tare da kallon cikin idon Mamy ta ce "Na fito da wuri wasu ne suka biyo
ni har na bace nara inda zanbi indawo gida"
Abba ne ya ce "Ku saurara min, kenan ke ce kika turata gidan Salma?
"Ita ta ce zata Alhaji"
"Ke Kuma kika bata dama?"
Shiru Mamy ta yi dan haka Abba ya ce "Dake na ke magana."
"Eh" Mamy ta fada tana kauda kai.
Shiru Abba yayi tsayon lokaci, zuwa can ya kalli Nur ya ce, "Waye ya sauke ki a mota?"
"Yayan Helen ne" Nur ta fada tana wasa da yatsunta. "Aina kuka hadu?"
Wannan karon Saida hawaye ya zubo mata sannan ta ce "Abba bansan sunan gurin ba"
Lumshe ido Abba ya yi sannan ya bude su a kanta tare da sake jefa mata tambaya "Ina
takalmin ki?"
Kasa magana ta yi tsayon lokaci dan haka Abba ya mike Yana fadin "Bashir kabawa yariyar
nan kashi"
Mikewa Nur ta yi tana cewa "Abba dan Allah ka yi hakuri saidai be ko juyo ya kalletaba ya
fice abinshi.
Yaya Bashir ne ya zagoyo ya zauna falon yana cewa, "Nur me yasa bakyajin magana, dazon
nan fa kika yi laifi fushin be saki Abba ba amman kin sake yin wani, duk kinbi kin canza kamar
ba ke ba"
"Yaya Bashir ka yi hakuri kaba Abba hakuri dan Allah" Nur ta fada tare da share hawaye.o
"Zaneta a kace ka yi ka wani tsaya kana lallashin ta" Ya Abdallah ya fada Yana zafgawa Nur
harara.
"Yaya mu rufa mata asiri dai sai in ta kuma tunda Abba ya fita"
Tsaki Abdallah yaja tare da mikewa yana kokarin kwance bel din dake daure ajikinshi, Mamy
ce ta kalle abin da ya ke kokarin yi dan haka ta ce "A'a karka taba ta, mikewa ta yi tana cewa ke
Nur muje daki"
Akofar dakin Nur Mamy ta tsaya itako Nur ta na sauke ajiya azuciya ta shiga cikin dakin, cak
ta tsaya dalilin hango takalmanta saman gadonta juyawa tayi ta kalli kofa da alama watso su
aka yi, cikin sauri ta kwashe ta boye gudun kar Mamy ta gani,sosai taji damuwanta ya karo,
hijjabi ta cire sannan ta shiga bayi tai wanka tare da daura alwala tana fitowa tai sallah, bayan
ta idar kwanciya ta yi domi bazata iya cin komai ba, tunani kawai tai ta yi da sake sake har bacci
ya sace ta, washegari ma bata fitaba saida ta gama shirin ta tsaf, sallama taima Mamy ta wuce
makaranta sai dai ko tantama bata yi Mamy ma ta yi fushi da ita dan haka take jinta tamkar
mara lafiya.
Gaba daya duniyar jinta take ta canza mata komai ya cakude mata, yau ce rana ta farko da
taki biyama Helen domin haushin yayanta da take ji sosai ya shafi Helen din.
Har aka tashi makarantar bata wani saki jikintaba, ita da Helen din suka jero kamar yadda
suka saba, saidai akwai alamar itama Helen din cikin damuwa take.
Bayan Helen ta shiga gida Nur ta harari gidan tare da Jan tsaki, tsintan kanta ta yi da cewa a
fili, "Da wannan dauko ni din da ka yi har gara ace ka barni inda ka ganni" tsaki ta Kuma ja tare
da kara sauri domin idan tana ganin gida ji take kamar yanzun ne ya ke mata abun da yayi jiya.
*****
Nur ce zaune ta na cin abinci, shigowan Mamy tagani dan haka tai saurin tsame hannunta cikin
abinci; jikinta a matukar sanyaye.
Gefenta Mamy ta zaune, sannan ta zuba mata idon tana kallon ta tsayon lokaci, Nur kuwa tuni
cikinta ya duri ruwa saboda tsabar firgicin da damuwan domin taji ajikinta Many fada zata mata
akan lefinta na jiya. "Nur!"
Can kasan makoshi Nur ta amsa. "Nazo in yi magana dake ne kuma gaskiya nake son ji karki
kuskura kice zaki gaya min karya" Ahankali Nur ta ce "Toh Mamy"
"Jiya ina kukaje ke da Rahma? Dan na tura gidan akace Rahma batanan ke kuma bakizoba"
Idon Nur akasa tana wasa da hannunta ta kasa cewa komai.
"Dake nake magana fa?" Mamy ta sake fada bayanta tsare Nur da Ido.
Ahankali Nur ta ce "Mamy Rahama ce ta kirani awaya"
"Eh, ai na sani, bani na kawo miki wayar ba? Yanzun cewa na yi ina kukaje?"
"Can wajen makabarta muka hadu Mamy" Kara sunkuyar da kanta ta yi tana tunani ta ina zata
fara ne mawai
Mamy ce ta sake cewa "Ina jikin ki, ki bude baki ki mini magana mana"
"Mamy Rahma ce ta ce mini in zo inga Yaya Abdallah"
Lumshe Ido Mamy ta yi sannan ta ce "A ina?" "Wani Otal ne wai sunan shi Nafclup"
Wani irin faduwan gaba ne ya samu Mamy daker ta dago ta kalli Nur ta ce "Can ku ka je?"
Wannan karon da kai Nur ta amsawa Mamy.
Kara sunkuyar da kai Nur ta yi, tsayon lokaci ta dauka tana jiran jin muryan Mamy amman
shiru dan haka ta dago ta ta saci kallonta, sosai ta ji gabanta ya fadi ganin inda hawaye ke gudu
akan fuskar Mamy dan haka ta dago sosai tana kallonta.
Ganin Nur ta dago tana kallonta ya sa ta fara share hawayen tare da cewa "Kina jina ko Nur,
karki kara zuwa wani waje da nufin bin Abdallah, zuwan ki babu abun da zai amfanar illah zubar
mana da mutunci, asalima kin yi kankanta a dinga ganin ki a irin wannan wajen, shi din ba
danki bane, ya na sama dake ne, ko mu da muke iyayenshi sai dai mu gaya mushi gaskiya
amman bazamu bibiyeshi ba bare har mu kai mishi duka, Jiya kinban mamaki gaban kowa kika
fito kina jifanshi da kofuna duk irin tsawan da ake miki baki saurari kowa ba, jifanki nasamun shi
ya fadi kasa kofin ya bashi kikacigaba da daukan kina jifanshi har saida aka rike ki Nur, har yau
da safen nan saida Bashir ya cire kwalba ajikinshi, sama kike dashi da zaki mai hukunci?"
Cikin sauri Nur ta girgiza kai sannan tai kasa da murya ta ce "Mamy wallahi bansan lokacin da
nafara ba ni dai kawai ganina na yi rike hannunki, Amman Mamy kafin ku dawo shine ya min
duka afalon nan ya murdemin hannu yaita gana min azaba"
Jimmm, Mamy ta yi idonta akan Nur zuwa can ta ce "Kin mishi wani abu ne?"
"Ba abin da na mishi ina dawo makaranta ya tareni yaita hadamin kai da bango"
Ajiyan zuciya Mamy ta yi sannan ta ce "Idan ya sake miki irin haka karkice komai kawai ki gaya
mini, amman duk abin da zakiji akanshi karki sake binshi wani waje. Koda wasa banson in
karaji, Abdallah ba karamin yaro bane, ki barshi kawai kowa ya gyara ya sani haka kuma kowa
ya bata ya sani, ki daina tunanin zaki iya canza komai, kuma banda abinki Nur lokacin da kika
fita ai Abdallah yana gida shina tura gidan su Rahma nemanki danaga kin jima baki dawoba."
Cike da mamaki Nur ta ce, "My to waye ya dawo min da takalmana gida, acan fa na bar
takalmina amman ina shiga daki na gansu a kan gadona"
Jimmm Mamy ta yi zuwa can ta ce, "Ai banki ta takun ba Nur, amman ai ansan da wuyan biri
ake daure shi a kafa, dan haka karki sake binshi, Rahma ma karki sake sauraronta" Amsawa
Nur ta yi da to sannan Mamy ta mike tana share hawayen ta fice adakin.
Nur ma mikewa ta yi jikinta a matukar sanyaye, hannunta ta wanke sannan ta zauna a bakin
gado cikin zulkumi da tunani, sosai take son ta ga komai ya gyaru, Sam bata son irin wannan
matsalar a gidan su. afili ta ce, yanzun kenan babu yadda za a yi da shi ya bari? haka za a
zauna ana kallon shi? wani irin zafi ta ke ji a zuciyarta mara misaltuwa sosai take jin zuciyarta
na mata kuna afili ta sake cewa, "Mataki ya kamata su Mamy su dauka, idan kuwa ba haka ba
bansan ranar da zuciyata zata daina min zafi ba, ina ma ace nice Babba agidan nan, wallahi da
daga yau Yaya Abdallah bazai sake fita ko kofar gida ba. Sallah ma ya daina bin ta a jam'i,
Tsaki taja tare da mikewa tana tunanin ta yadda zatabi ta share lamarin Abdallah kamar yadda
Mamy ta fada.
Misalin Biyar na yamma Nur ta fito ta zauna afalo tana yanke farce, ganin babu motsin kowa a
gidan ya sa ta shiga kwalawa Mamy kira, da ga can cikin kitchen taji muryan Aunty Saratu ta na
cewa "Ka da ki tadata tasha nagani ta kwanta batajin dadi"
Jimm Nur ta yi ta na tuna hawayen da Mamy ta yi dazon, sosai ta ji damuwanta ya karo domin
tasan mgnr dazon ita ta tada ciwon Mamy, tun daga lokacin ta shiga tunane-tunane ba ita ta
dawo cikin hankalinta ba sai da taji dawowan su Abba. Sallah magarin da ake kira ya sata
mikewa, dakinta ta nufa tai alwala tai sallah sannan ta ci gaba da aikin tunani. Tana cikin
wannan yanayin tajiyo muryan Aunty Saratu ta na kwala mata kira. Amsawa ta yi tare da
mikewa ta fito falon tana fadin "Aunty gani" "Abban ku na kira"
Cikin sauri Nur tasa hannunta ta dafe kirjinta domin in dai Abba yai kira to wani abu ne me
mahimmancin, kofa ta nufa batare da ta sauke hannun da ta dafe kirjin dashi ba, sashin Abba ta
nufa gabanta na tsanta faduwa. A kofar falon ta tsaya ta sauke hannunta a kirjinta ta na me
karanto addu'oi, yadda take juyo muryan su Yaya Abdallah da Yaya Bashir acikin falon ya kara
daga hankalinta.
Da Sallama a bakinta ta shiga falon duk dagowa su ka yi suka amasa sallaman nata cikin
sakin fuska, amman banda Abdallah da Abba da su ka hade fuskokin su. Baffa ta hanga daga
gefe dan haka taji gabanta ya sake faduwa
Fadila Lamido
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
https://www.wattpad.com/user/fadeelalamido?utm_source=android&utm_medium=link&utm_ca
mpaign=invitefriends
Page 7-8
Zama ta yi a kasa ta na gaida su, sai dai yadda ta ga sun amsa cikin sakin fuska ya sa ta ji
nutsuwa kadan. Shiru falon ya yi tsayon lokaci, zuwa can Baffah ya ce "Nur ya karatu?"
"Lafiya lau Baffah"
"Karatun ne lafiya lau? Alhamdulillah za ki ce" Bashir ya fada ya na kallon fuskar Nur yana
dariya. Baffah ma murmushi ya yi yana kallon Nur din ya ce "Ina labarin saukan ki"
"An kusa Abba saura kwana arba'in da hudu yau"
"Allah ya nuna mana lokacin" Baffah ya fada cike da farin ciki. Abba ne ya yi gyaran murya
wadda ya sa duk wani dake cikin dakin maida hankalinsa kanshi, sosai Baffah yabi Abba da
kallo bayan tsayon wani lokaci sannan Abba ya ce, "Dama na yi kiran ka ne akan Nur" Cikin
Sauri Baffah ya kalli Nur sannan ya juya ya kalli Abba ya