Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
sake rikewa, ki gaya mishi wannan
haramunne a addininku, sannan in dai ba a gidan nan ba karki tsaya hira dashi a titi, duk da
nasan zai bukaci hakan, amman karki yadda, idan da gaske sonki yake yazo ya tunkare
Abbanku ya nema izini tukuna...
Cikin sauri Nur ta katse Aunty da cewa "Ba musulmi bane fa" Wannan karon cikin tsayawa
Aunty tacewa Nur "Ina ruwanki?" Sunkuyar da kai Nur ta yi yayin da Aunty taci gaba da cewa,
"Kamar yadda kika saba haka zakici gaba dayi, duk ranar da ya bude baki yace son ki yake sai
kice yaje ya gayawa Abbanku, ki sake jikinki ki daina tsoronshi ranar Monday idan zaki
makaranta ki biyawa Zainab kamar yadda kuka saba."
Wannan karron Nur batace komaiba saidai ta samu nutsuwa sosai duk da cewa har yanzun
tana tunani akan zancen Aunty, mikewa Aunty ta yi ta fita bayan ta Kara kwantar mata da
hankali, Aunty tana fita Nur ta shiga bayin dake makale jikin dakinta, auwala tayo sannan ta yi
sallah, bayan ta idar addu'oi ta yi wadda suka Kara samar mata da nutsuwa, bata tashi a wurin
ba har saidai aka yi isha'i sannan ta koma gado, wannan lokacin wani irin nishadi ta tsunta
kanta aciki musamman lokacin da ta jiyo gud'a tare da hayaniyar mutane afalo, durowa ta yi a
gadon cikin sauri ta nufi falon tana cike da fara'a, abokan Yaya Abdallah ta gani zazzaune a
kasa yayin data hangi Abdallah zaune saitin kamar Mamy, da alama neman Albarka yazo yi zai
shiga dakin Amarya, yin wannan tunanin ya kara fadada murmushi Nur, zagayawa tayi can
bayan kujeran da Mamy take ta zura hannunta ta dafa kadan Mamy tare da leken fuskar
Abdallah fuskarta cike da murmushi, tun zuwanta Abdallah ya kula da ita, saidai be nuna ma
yasan da zuwan nataba bare ya daga kai ya dubeta, 'yan uwan Mamy ne suka mishi nasiha
daka karshe Mamy tasa albarka sannan suka mike zasu tafi, wannan karon ma farin cikene ya
sake lullube Nur dan haka ta daga murya tace, "Yaya Abdallah!" Juyowa yayi ya kalleta tana
wasa da hannunta akan kafadan Mamy, hannunta daya ta daga mishi tare da yar dariya tace
"Allah ya sanya alheri" Azuciye Abdallah yayi kanta cikin tsawa yace "Ina wasa dake ne?" Baki
Mamy ta bude tare da cewa daga addu'a? Abokansa ne su ka jashi Dan haka ya fice a falon
yayin da mutanen dakin suke dariya haka itama Nur dariya tayi domin ko kadan batajin haushin
hargaginshi ba, afalon ta zauna akacigaba da hira da ita, washegari da wuri aka yi budankai
kowa ya watse, duk bakin da suka kwana a gidan sunje gidan Amarya sun ganu gidan yayin da
kowa idan ya dawo yake mamakin haduwan dakin Bilkisu, yayin da ake ta yabon amarya kowa
cewa yake yariya karama Mai hankali ga sanin darajar mutane, washegari ma Aunty da Umma
sukaje suma haka suka dawo suna yabawa, Washegari ya kama Monday dan haka Nur da wuri
ta shirya, bayan tawa su Mamy sallama ta nufi gidan su Poul gabanta na faduwa sosai.
Tura get din kawai ta yi ta shiga, Mai gadin gidan ne ya juyo ya kalleta sannan ya dauke
kanshi, tundaga nesa ta hanga Poul zaune a farfajiyar gidan, Saida gabanta ya fadi ganin shi
sannan Kuma batama taba ganinshi zaune a gurin ba. Wannan karon kasa kwalawa Zainab kira
ta yi kamar yadda suka saba, tsaye ta yi ita bata shigaba ita bata koma ba, tun da ta shigo Poul
din yake binta da kallo, zuwa can ya rufe jaridar hannun shi tare da mikewa tsaye ya fara
takowa, ganin haka Nur ta fara ja da baya batare data daina kallonshi ba ta ke nufar kofar
gidan. Ganin haka ya tsaya cak fuskarshi na dauke da murmushi yace "Yun da bazaki tsaya
inzo ba to ki kira Helen din ku wuce." Wannan karon ma bata tanka ba komawa yayi ya zauna
Yana cigaba da kallonta fara'ar fuskarshi Bata yanke ba har wannan lokacin, ganita jima tsaye
Kuma da alama Bata da niyar kiran Helen din yasashi yace "Helen!" Amsawa ta yi da karfi
yayin da ya sake daga murya yace "Ga kawarki, fitowa ta yi da Jakarta a hannunta tana kokarin
goyawa ganin haka Nur tai saurin ficwa agidan, cike da mamaki Zainab ke kallonta domin Bata
sa rai zata biyo mata ba. Misalin Uku ta dawo makaranta afalo ta samu Ummy zaune ita da
Mamy, rungumarta tayi itama Ummy cike da Murmushi tace ke na yi ta jira ki dawo ki rakani
gidan Abdallah" Batare da ta Nur ta Bari Ummy ta rufe bakiba tace "Ai bansan gidan ba
Ummy." Mamy ce tace "Ita ta sani tashi ki shirya tun dazon take jiranki."
Karyar da kai Nur ta yi tare da yin kwalwal da Ido tace "Mamy ni baxani ba gaskiya."
"Au bazakiba?" Ummy ta fada tare da cigaba da cewa "Toni barin wuce ai bansaniba dan ban
zauna na bata lokaciba ba."
Mikewa Nur tayi tare da amsar Jakar Ummy tace "Muje in rakaki mota ni sai in tare da Mamy
ne zani."
"Toh Allah ya taimaka" Ummy ta fada tare da yiwa su Mamy sallama, Bayan dawowan Nur fada
Mamy ta mata akan kin bin Ummy data yi kiri-kiri. Ranar da suka cika kwana na hudu da
tarewa Bashir yazo daukan Nur zuwa gidan Abdallah, wannan karon ma kememe taki zuwa,
dan haka Bashir ya tsareta da tambayan dalilinta nakin zuwa, ganin babu wasa a idonshi ta ce,
"Kawai nafi son in je ne tare da Mamy kasan yanzu haushina yake ji yana iya dukana"
"Kizo muje bazan bari ya dukekiba" tashi Nur ta yi da ga kusa da Bashir ta koma can bayan
Mamy tare da cewa "Ni gaskiya Yaya kaje abin ka ninafi son inje tare da Mamy, dan in da ita ko
kallon banza bazai min ba" Mamy ce tai saurin cewa Ashe kuwa bazaki ba Nur, ni me zai kaini
gidan su, ki tashi maza kina bata mishi lokaci dare na yi" Mikewa Nur ta yi tana me buga
kafarta tare da kunkunai take cewa "Ni Mamy nace bazaniba, ko an hana shi ya dakeni idan ya
yi ta hararata fa, saina dawo gida na ce ya harareni kuma kuce na yi hakuri ba gara banjeba"
Karake maganar ta yi tana hawaye dan haka bayan Mamy ta gama kare mata kallo ta juya ta
kalli Bashir da ke zubawa Nur harara tace "Jeka abinka" Kamar jira yake ya mike ya nufa kofa,
cikin murya kuka Nur tace "Yaya ka gaida Aunty Bilkisun" Wani irin kallo Mamy ta sakewa Nur
sannan ta kalli bayan Bashir da ya wuce ba tare da yace komai ba. Tun daga ranar babu wadda
ya sake mata maganar zuwa gidan Bashir har suka cika kwana shida da tarewa wadda ya
kama ranar ne Yaya Bashir zai wuce karatu, misalin karfe takwas na safe ta gama shirin
makaranta, fitowa ta yi domin yiwa su Mamy sallama, tun kafin ta isa falon ta jiyo muryan Yaya
Abdallah babu tsoron da taji domin dai tasan babu abin da zai mata, dan haka ta Isa falon tare
da Sallama, duk mutanen dake falon amsawa suka yi Abdallah ne kawai be ma waigo bare ya
amsa, karasawa ta yi kai tsaye ta nufa gurin amarya dake zaune daf da Yaya Abdallah cikin
katon hijjabi dan haka bakama iya hangen kayan dake jikinta, hannunta ta rike tare da cewa
"Auntymu Ina kwana" cikin sakin fuska tare da yanayin jin kunya ta amsa yayin da Nur ta kalli
Inda Yaya Abdallah yake tace "Yaya Ina kwana?" Tamkar besan da ita a wurin ba haka yayi,
dan haka ta sake cewa "Yaya Abdallah Ina kwana?" Batare da ya kalli In da Nur take ba yace
"Mamy in tafi zakiyi Mai bayani ko?" Cikin mamaki Mamy ta ce "Ban gane ka tafi ba?, Ko ba
komai ai dai ka bari ku yi sallama ko?" Nur sakin hannun Bilkisu ta yi sannan ta juya tai ma
Mamy da Aunty Saratu sallama ta fice abinta, gidan Poul ta nufa tana me ardu'ar Allah ya sa ya
riga ya fita acikin zuciyarta, bayan ta tura kofar ta saki ajiyan zuciya ganin babu kowa sai Mai
gadi, Amma da Alama Poul din yana nan danga motar shinan an sakko da ita, kira ta kwalawa
Zainab ta amsa sannan ta fito daga bayanta ta hangi Poul tafe, dan haka ta ji gabanta ya fadi,
kallo daya yawa gefenta sannan ya juya ya shiga motar, ita ko Zainab matsowa ta yi tace "Nur
zo ga Yaya yace zai kaimu" gabanta ne ya sake faduwa Dan haka tai saurin nufar get din gidan
tare da cewa "Ni bazan hau motar kowaba."
Muryanshi taji kamar daga sama yana bawa mai gadin umarnin ya rofe kofar gidan dan haka ta
kara sauri, saidai ki kafin takai wajen mai gadin ya rufe kofar, dan haka ta tsaya cak tana kallon
motar Poul din dake tahowa zuwa get din gidan. Daidai saitinta suka tsaya, Zainab na gefensa,
ganin haka ta yi kwalkwal da Ido, Poul din ne ya sakko ya bude bayan motar ta gefen da take
tsaye yace "Shiga muje"
Kallon shi ta yi sannan ta kalli motar daya bude yake rike da murfinta, Nan take zancen Aunty
ya shiga dawo mata...
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 37-38
Kallon shi ta sata fuskarta daure sosai sannan ta daga kafa ta shiga motar ta zauna, rufewa
Poul yayi sannan ya zagaya ya shiga alokacin da Zainab ke waiwayen Nur tana murmushi,
shima kallonta yayi kadan sannan yaja motar, gaba daya hankalin Nur a tashe ya ke, dan haka
ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da hannunta, daka ganta zaka fahimci tana cikin bacin rai. Tafiya su ke acikin motar shiru sai wata wakar inyamuranci dake tashi a radio motar, zuwa can
Nur ta dago kanta, gani ta yi Yana kallonta ta madubin dake gabanshi, dan haka ta karkace da
sauri ta juya mashi kafada, murmushi Poul yayi, duk da cewa ta juyar da fuskarta amma ya
kasa cire idonshi akanta, abakin makarantar ya tsaya, yana tsayawa Nur ta Bude motar ta fice,
idon shi akanta ya ciro kudi ya mikawa Nur yana fadin ke da ita, itama Zainab idonta akanshi ta
amsa kudin, mamakine ya kama Zainab ganin in da yake kallon Nur, bayan ta amsa ta kalli
kudin sannan tace "Mun gode." Muryanta ne ya dawo da shi cikin hankalinnshi, kokarin tada
motar yake batare da ya amsa ba, Saida ya ga shigansu makaranta tukuna ya wuce, sosai jikin
Zainab yayi sanyi ganin wannan labari dake faruwa, tunani da yawa azuciyar Nur akan wannan
abin, a yanzu ko tantama bata yi yayanta poul ya fada tarkon son, wurin Nur ta maida
hankalinta data shige ajinsu afusace.
Bayan sun zauna a ji ma zama Nur ta yi kamar kurma duk yadda Zainab ta so su yi magana
ki ta yi, haka Kuma ko da aka tashi kafin ta farga Nur ta wuce, hanya ta kamo ita daya acikin
ranta take sake sake, haka nan take jin tausayin Poul acikin zuciyarta.
Bayan Nur ta Isa gida sannu da gida tayiwa su Mamy sannan ta wuce dakinta, cak ta tsaya
bakin kofar dalilin gani mutum kwance a kan gadonta, sai yanzu ta tuna da dazon tabar
Abdallah da Amarya, kenan be wuce da ita ba, jakar makarantar ta ajiye sannan ta nufi falon,
tun kafin ta isa take fadin Mamy Yaya Abdallah be wuce bane? Na dauka yaune tafiyarshi ai"
Karake maganar ta yi tana kokarin zama kusa da aunty Saratu. Yayin da Mamy ke cewa, "Ya
wuce Nur tun safe"
"Toh Kuma naga Aunty Amarya anan" Nur ta fada tana kallon fuskar Mamy, "Eh nan zata
zauna"
"Har ya dawo?" Nur ta sake tambaya cike da mamaki, wannan karon Aunty Saratu ce tace, "Ya
ce idan ya gama saita komai zai dawo ya dauketa."
Tabe baki Nur ta yi yayin da Aunty Saratu ta sake cewa "Ta tashi baccin kuwa?"
"A'a Bacci take" Nur ta bata amsa, Mamy ce tace "Kije ki cire kayan makaranta idan kin ta tashi
kizo ki dauki abincinta. Mikewa Nur tayi bayan ta amsa sannan ta nufi dakin, kayan makaranta
ta cire sannan ta nufi bayi, zuwa can ta fito ta sake bin Bilkisu da kallo, gani ta yi kamar idonta
biyu dan haka tace Aunty Amarya! Bata amsa ba, ahankali Nur ta karasa bakin gadon ta zauna
tare da leken fuskarta tana sake cewa "Auntymu!"
Wannan karon hannu Bilkisu ta sa ta share fuskarta sannan ta juyar da kanta dayan gefen tare
da cewa "Kin dawo?"
"Eh na dawo" Nur ta fada na mai nazarin yanayin da Bilikisu ke ciki, kamar kuka take dan
haka Nur ta sake cewa, "Aunty ashe kina jina to ki tashi su Mamy nata jira ki tashi kici abinci."
"Banci Nur, bana jin yunwa." Lumshe Ido Nur ta yi Jim yanayin muryanta sannan tace "Kinci
wani abin ne to?"
"Eh kafin mu fito mun ci abinci." Wannan karon Murmushi Nur ta yi sannan tace "Ke dawa?"
"Cewa na yi kafin mu taho nan ni dashi mun karya" Dariya Nur ta yi afili tare da cewa "Ki fadi
Sunanshi mana"
"Haba Aunty tun safe ne fa, kina son kice har yanzun bakyajin yunwa?"
"Bana ji Nur" Dariya Nur ta sake yi sannan tace "Kenan bazaki sake cin abinciba har sai ranar
da Yaya Abdallah ya dawo?" Wannan karon yunkurawa Bilikisu ta yi ta tashi, bayi ta shiga ta
wanko fuskarta sannan ta fito, batasan meye dalili ba tun da Nur ta fara magana taji ta samu
nutsuwa tun bayan tafiyan Abdallah. Nur kuwa har yanzun fuskarta cike take da dariya domin ta gane Bilikisu kewan mijinta take.
Mikewa tayi ta fito falon, Aunty Saratu na ganinta tace yaya aka yi Nur da ganin ki akwai
magana a bakin ki, kamar jira Nur take ta fashe da dariya tare da waiwayen bayanta cikin dariya
tace "Ashe idonta biyu aunty kuka take Yaya Abdallah ya tafi ya barta, Karake magar tayi tana
kyalkyata dariya, ita ko Aunty daure fuska ta yi sannan tace "Haka ta gaya miki?"
Kafin Nur ta yi magana Mamy ta ce, "Ai dole bazataji dadiba Saratu, dashi ta saba kwana
shidda da rabota da yan uwanta wa ta saba dashi anan? Amman ya tsallaketa ya barta kuma
tafiya ba kwana biyu ba ba uku ba wata da watanni, abin da nake nuna muku kenan, ki dauki
abinci kije kuci kema aiki ya same ki" Mamy ta fada tana kallon Nur, tuni Nur ta tabar dariya
tunda taji ta bakin Mamy, dan haka koda ta shiga kicin tana deban abincin tana jinjina abin, har
ta gama zuba abincin ta koma daki tunanin da take kenan, zaune ta samu Bilkisu ta yi tagumi,
wannan lokacin tausayi tabawa Nur, dan haka ta zauna daf da ita tare da cewa, "Aunty kici
abincin barin yi sallah inzo" Mikewa Nur tayi saidai har ta idar da sallah Nur bata taba abincinba
dan haka Nur ta zuba masu tare sannan ta ce "Muci Aunty" Babu laifi Bilkisu ta danci kadan
sannan tace ta koshi, a daidai wannan lokacin aka kira ta a waya, da sauri ta dauka yayin da
Nur ta bita da kallo, wayar tasa a kunne tare da komawa bakin gado ta zauna, cikin shagwaba
Bilkisu tayi sallama cikin wayar hawaye taga Bilkisu na cirewa a gefen idonta tsayon lokaci
batace komaiba, da alama sauraron mgn take cikin wayar, zuwa can taji tace, "In je gida mana
to" Shiru ta sake yi zuwa can ta sake cewa, "A'a" Murmushi taga ta yi sannan ta sauke wayar.
Tunda ta fara wayar Nur Bata cire idonta akantaba dan haka da taga ta sauke wayar fuskarta
sake tare da saurin mikewa tana Murmushi, tun da ga lokacin Bilkisu ta sake jikinta Hira suka yi
da Nur tamkar Daman can sunsan juna, misalin takwas da rabi na dare Nur ce zaune adakin
Mamy yayin da ke kokarin gyara kaya tana sakawa cikin sif, Waigowa ta yi ta kalli Nur tare da
cewa "Taci abincin kuwa?"
"Eh taci Mamy harma sun yi waya da yaya."
"Yauwa ya kyauta yayan, yanzun wani abu kike so?"
"A'a" Nur tace tana kallon cikin idon Mamy. "To ki koma wurinta mana tafi jin dadin zama idan
kina wurin ko?" Amsawa Nur ta yi ta fice badan ranta yaso ba, lokacin da ta shiga dakin kan
gado ta samu Bilkisu tana danna wayarta tana murmushi da alama chart take, dan haka ta
nema wuri daf da Bilkusun ta kwanta saidai ta kasa cire idonta akanta, murmushi take sosai
zuwa can Nur taga ta saki wayar ta fashe da dariya cike da mamaki Nur ta kalleta tare da tashi
zaune tana sake binta da kallo, ganin irin kallon da Nur ke mata yasata cewa "Nur kina ganin
yayanki zai kasheni da dariya ko? Wallahi in dai zaka biye masa sai yasa cikin ka ciwo" Wayarta
ta jawo tana fadin "Barin kashe data na kawai Saida safe."
Nur kasa cewa komai ta yi sabo da mamaki, sai take ganin kamar mafarkine take yi, wannan
fuskar tashi har ta iya bada dariya, wani sashi na zuciyarta kuwa farin cikine ya kamata, tunda
dai har Yana son matarshi har yana wasa da dariya da ita ai AlhamduLillahi, wayar Bilkisu ne ta
sake daukan Kara, dauka ta yi tasa a kunnenta zuwa can tace