Ciwon Ya Mace Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   21 / 25

60K to 63K   out of 73.1K words

ga yau babu ruwanki
acikin wannan maganar, Abdallah ne ya kawo Bilkisu gidan nan, idan bata sanadinsa ba da
bamu santaba, kuma yanzun rabuwa ya shiga tsakaninsu, shakuyar da kukayi ita zata sa na
kaiki wajenta, dan haka ko kinje babu ruwanki da tattauna abin da ya shafi wannan matsalar,

bare kice zaki shiga tsakiya, ina son ki sani Abdallah shine dan uwan ki ba Bilkisu ba" Ciki
rashin fahimta Nur tace "To amman Yaya Bashir dan shine dan uwana kuma ai ba'aza hananin
tausayinta ba"
"Idan Kinga zakiji kije ki ta ji, kukan ne be ishekiba, idan kikace haka zakiyi bazan goyi
bayanki ba, ashe baki da adalci?"
Fashewa Nur ta sake yi da kuka tare da cewa "Me na yi to Yaya"
"In da kina da adalci ai Abdallah ya dace kiji tausayi ba matar ba, domin yanzu badan Allah ya
kiyayeba data kawo mana dan wani cikin gida."
Cikin turo baki tace "Aunty Bilkisu ba yar iska bace Yaya Bashir." Cike da fada Bashir yace
"Ok kina nufin Abdallah ne dan iskan kenan? Shiyasa daman yace kin harareshi."
Zaro Ido Nur ta yi tare da kallon Yaya Bashir tace "Ni? Yaushe?" Ni ban harareshi ba saidai
idan tsarguwa yayi"
"Zakiga tsarguwa idan ya fasa miki baki, dan ko yanzu nina hanashi shigowa, kiyi hankali da
kanki tun da yace shi ba ruwanshi dake kema ki kama kanki ko da wasa karki shiga tsakaninshi
da Bilkisu"
"Shike nan, kada Allah yasa yayi ruwa dani, ni bazan sake kallon inda yake bama, shima ya
daina kallon in da nake, shikenan kowa yayi harkar gabanshi" Wani irin irin kallo Bashir yawa
Nur mai cike zallar mamaki sannan yace, Nur ashe baki da kunya"
"To Yaya Bashir nifa ya isheni, ina gaidashi baya amsawa, darajarshi da nake gani bana iya
ganinshi batare dana gaidashi ba duk da cewa nasan bazai amsaba, sai an yi magana yace ba
ruwanshi dani, baruwanshi da ni kuma ya kalleni har yaga Ina hararanshi? tun da Babu
ruwanshi dani ai sai ya daina kallon Inda nake." "Ni kike gayawa magana?"
Kuka Nur ta sake sawa tare da cewa, "Ai dama ba dama mutum ya fada abin dake zuciyarshi
sai ace bashi da kunya, Duk abin da yake min hakuri nake yi yasha cemin nan ba gidan ubana
bane ko yace sai na koma gidan ubana, in da bani da kunya ai saina rama zagin da yake min,
amma ban taba tanka mishi ba sabo da ina ganin girmanshi" Sunkuyar dakai Nur tayi tare da
turo baki bayan ta gama rattafuwa, dan haka Bashir ya jinjina kai tare da cewa, "To kici gaba da
hakuri wata rana sai labari, sabo da ko ni bazanso ki dinga gaya min magana ba bare Kuma shi
Abdallah, duk da cewa yanzu nasan har da fushin wannan kila hada kuma shine abin da bana
so din kuma na tabbatar da cewa Kowa ma agidan nan bazaiso ace wannan abin ya kara
haddasa kiyayya a tsakanin ku ba, tun da Abdallah ya nuna beson kina shiga cikin lamarinshi to
ki bari." Ganin ta sunkuyar da kanta tana hawaye yace "Kina jina ko?" Kai ta daga alamar eh,
ajiyan zuciya Bashir yayi sannan yayi mata sallama ya wuce" Daren ranar Nur Bata iya
runtsawa ba, da safe tana kwance ta dinga jiyo hiransu Yaya Abdallah da Bashir afalo, bayan
wani lokacin taji shiru, hakan ya tabbatar mata da sun fita, sai wurin sha daya ta karya, shima
daker taci kadan, sanin damuwarta yasa ba wadda yayi mata maganar makaranta, har aka cika
sati da faruwan abin, yauma kwance take adakinta cikin tunanin Bilkisu tare da nemo mafita
domin burinta kawai taga Bilkisu ta dawo amatsayin matar Abdallah domin tuni take hango
hotonsu da yaransu acikin zuciyarta tare da auno irin zumunci mai dadi wadda zasuyi tare da
ita, zuwanta gidan ta fara mancewa da kewan 'yan uwa mata da bata dasu jinta take tamkar yar
uwanta ta jini, dan haka burinta kawai taga Nur ta dawo gidan, tana cikin wanna tunanin taji an
turo kofar, Abba ta gani cikin Babba riga da hula, yake ta yi tare da kokarin tashi zaune, Bakin

gadon Abba ya zauna tare da cewa "Haba Nur, mai yayi zafi haka? Sati daya kenan bansaki a
idona ba, hakama Bashir da Abdallah sunce suma tun wancen ranar basu sake ganinkiba,
Mamynki ma tace kin daina magana da kowa, abincima ba sosai kike ci ba" Wasa da hannu Nur
take, yayin da Abba yaci gaba da cewa "Makaranta ma bakya zuwa ko?" Wannan karon Kai ta daga alamar "Eh" Dan haka Abba yace "To kuncin ya isa haka, gobe
asabar ki shirya kije makaranta" ta kardun dake hannunsa ya mika mata, tare da ceawa " Ga
albishir na zo miki dashi, maganar makarantar ki ya kammala, i dan Allah ya kaimu ranar
Monday zakije." Fuskarta babu walwala ta amsa takardan hannun Abba tare da motsa bakinta, dan haka
Abba yace "Ko kina da magana ne?"
Kai Nur ta daga da sauri dan haka Abba ya kureta da idon tare da cewa, "To Ina jinki?"
Motsi tai tayi da baki ta gaza furta komai, dan haka Abba ya sake cewa "Ina jinki."
"Abba baza iya canza min ba?"
Cike da rashin fahimta Abba yace "Ban fahimceki ba?" Wannan karon ma magana ta kasa har
Saida Abba ya sake cewa "Ina jinki Nur?"
"Abba ina son na yi makarantar horas da lauyoyi domin na karanci shari'a yanzun nabar
sha'awan jinya."
Wannan karon cike da bacin rai Abba ya kalli Nur sannan yace, "Amma Nur kina da matsala"
shiru yayi tsayon lokaci yana bin yadda idonta ya cika da waye da kallo sannan yace "Me yasa
tunanin ki be tsayawa da wuri daya? Saida na gama shan wahala sannan kice min bakya so
Nur? Kinsan nawa na kashe akan neman makarantar nan, shike nan," Abba ya fada tare da
fizagar tagardan a hannun Nur ya fice, Gannin haka Nur ta mike tare da cewa Abba ka yi hakuri
to zamyi, ficewa yayi batare da ya saurareta. Da daddare Nur ce zaune adakinta tun da Abba
ya fita dazon take cikin damuwa, agogo ta kalla karfe Tara, hakan ya tabbatar mata da an gama
cin abinci a gidan, afili tace "Abba na fushi dani, tunda besa an kirani ba, Kuma har tara ba'ace
inzo in daiki abinci ba" Mikewa ta yi da nufin zuwa ta bashi ha kuri, falonshi ta shiga shinkadai ta
samu yana ta lissafi, yana ganinta ya dago cike da murmushi tare da cewa "Nur!"
Karasawa ta yi ta zauna tare da tace "Sannu Abba" Cikin sakin Fuska yace "Yauwa sannu
Nur ya gidan"
"Lafiya lau Abba nazo ne na baka hakuri, kayi hakuri ranar Monday zanje makarantar."
Murmushi Abba yayi tare da cewa "Bakomai Nur karki damu, na fara maganar akan sabon
zabin naki, matsalar dai ta kudi ce, amman na tambayi Abdallah be dai amsa ba amman yace
gashinan zuwa."
Idon Nur cike da Kwallah tace Abba abarshi kawai zanyi wadda aka samu di"
"Hmmm, Nur matsalar ki bakya tsayawa wuri daya, yau kice wancen gibe kice wannan,
amman duk da haka Ina da burin faranta miki, akwai akwai wani abu da iyaye suka dauramu
akai, shi ne duk wani zabi na yaro in dai ba ya sabawa addini ba to karka hanashi kace lallai
abin ka kake so shi za'ayi domin abin da yaro yake da sha'awa kai yafi maida hankali, fatana
kawai wannan yazama zabinki na karshe" Idon Nur cike da Kwallah tace, "Na gode Abba,
tunanin zancen Abba ta shiga yi Cikin zuciyarta tare da Jinjina irin kyaunar da Abba ke mata,
hawaye taji ya zobo mata adaidai lokacin da Abdallah yayi sallama ya shigo, yana zama ya
gaida Abba, sannan ya bude jakar dake hannunshi ya fito da bakar leda ya Isa gaban Abba ya
aje tare da cewa "Abba gashi dari biyar kace ko?" Cike da fara Abba yace "Eh an samu kenan?"

"Eh Abba, idan kana son kidi kawai kace min idan Ina da kudi in kawo, ka daina ce min bashi"
Dagowa Abbba yayi ya kalleshi tare da cewa "To ajiya na baka?" Gyara zama Abdallah yayi
sannan ya ce "Abba ni dai kyauta na baka ba bashi ba, godiya Abba yayi masa tare da saka
mishi albarka, Hira sukaci gaba dayi Nur na sauraron su zuwa can Abba ya bude kudin ya cire
wasu sannan ya turawa Abdallah ledar tare da cewa "Dauki wannan, idan Allah ya kaimu gobe
da duku-duku ka kaiwa Alhaji Ibrahim." Dauka Abdallah yayi tare da cewa "Gidansa ko office?"
"Gidan sa dai, shiyasa nace da safe ai, duba can, ga takardu can ka dauko" In da Abba ya
nuna masa ya nufa, daukowa yayi yayin da Abba yaci gaba da cewa, "Takardun Nur ne, ka
hada da kudin ka bashi duk abin da ya dace yayi."
Cikin rashin fahimta Abdallah yace "Abba ba ance an samu makarantar nata ba, wannan
Kuma na me ye to?"
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

Page 48

"Kasan Nur da tunane-tunane, shari'a take son ta karanta yanzun kuma" Cikin sauri Abdallah
ya juya ya kalli Nur sannan ya kalli takardun tare da kudin ya kada kai ya fice batare da yace
komaiba.
Bayan fitan Abdallah Nur tawa Abba sallama ta fito, dakinta da koma, tun bayan da Bilkisu ta
tafi gidan su sai yau Nur ta samu dan nutsuwa, sai dai har yanzu tausayin Bilikisu yana makale
da zuciyarta, a gefe guda kuma a kawai tarin Haushin Abdallah azuciyarta, musamman da taga
ko ajikinshi, be nuna damuwa ba, so da yawa takan kwatanta abin da kanta, domin har yanzun
tana kewan Bilkisu, tare da tuna halayenta nagari, mai yasa shi Abdallah be nuna jimami ko
kewanshi ba, wata zuciyar ce tace "Kila kuma yana yin kewan gabanmu ne baya nunawa"
Share tunanin tayi sannan ta mike taje dakin Aunty, gani ta yi ta fara bacci dan haka ta dauki
wayarta ta fito a dakin. Duk abin da ya zamar mata jiki kafin kwanciya ta yi, sannan ta rufe kofa
ta kwanta tare da saka number Poul acikin wayar Aunty, tana fara ringing ya dauka tamkar mai
jira, "Nur!" Poul ya fada a hankali, amsa ta yi kasa kasa "Lafiya kuwa kwana biyu? Nata jiran
Kiran ki har nagaji na kasa hakuri na kiran layin da kike kirana dashi" Cikin lumshe Ido Nur tace
"An dauka?"
"Eh, an dauka, amma ba ace komai ba, kira yafi sau goma, sannan wata ta dauka tace mai
wayar bata da lafiya."
Jimmm Nur ta yi sannan tace "Mai ke damunta?"
"Haka dai akace bakwa, tare ne?"
"Eh tana gidan su"
"Mijinta ya dawo kenan?" Cikin wani irin yanayi Nur tace "Eh ya dawo, amma basa tare sun
dan samu matsala." Sosai Poul ya nuna rashin jin dadinshi, sannan ya shiga fada mata halin da
ya shiga da baya samun kiranta. Nur kuwa nuna mai ta yi bata da lafiya ne, dan haka ya
tambayeta jiki, bayan ta amsa yayi ajiyan zuciya tare da cewa, "Ina son in yi wata magana

dake." Nur na daga kwance tace ina jinka" Kara jawo bargo yayi ya rufe jikinshi tare da cewa
"Ina son in nuna kaina a matsayin wadda ya ke son auren ki a gidanku." Jimm, Nur ta yi zuwa
can tace "Ai na ce maka gidan mu bazasu yadda ba" Cikin wani irin yanayi ya ce, "Kenan
bazamu yi aure ba? Idan baza mu yi aure ba meye amfanin wayan da muke yi? Kullum zuciyata
kara nisa take a son ki, na shirya in karbi musulunci a yanzun dan haka kawai dama nake jira
daga gareki in zo wurin Abban ku." Wannan lokacin cike da damuwa Nur tace "To idan har ka
shirya ka musulunta mai yasa zakaje wurin Abba tun yanzu, ai gara kaje kana musulmi."
Jmmm Poul yayi sannan yace "Haka ne, amman ina son insan ta bangarenki banda matsala
ko?" Can kasan mokoshi Nur tace "Eh"
Ajiyan zuciya Poul yayi sannan yace "Shikenan amma banson aja lokaci, cikin kankanin lokaci
nake son a yi komai a gama." Wannan lokacin cike da gamsu Nur tace "Haka ne" Domin burinta
kawai ya musulunta din, har sunyi sallama zai kashe wayar tai saurin cewa "Wurin Malam
Zubairu zakaje ko?" "Wurin shi kike son naje?" Poul ya jefa mata tambayar, can kasan makoshi tace "Eh"
"To Zanje" Tsintan muryarta yayi ta sake cewa "To yaushe zaka je?"
"Yaushe ki ke son naje?"
"Gobe" Nur ta fada a hankali, "Shikenan karki damu, amma ki bani shawara akan sabon sunan
da zan zaba?" Shiru Nur ta yi tsawon lokaci zuwa can tace " Kai baka da zabi ne?"
"Inadashi amman zanso inji naki ko yafi nawa dadi" Wannan karon ma shiru Nur ta sake yi
alamar nazari take yi, zuwa can tace "Kana son suna Abubakar?"
"Eh, sunan yana da dadi Nur, mai zai hanani so idan har kina so?" Dan murmushi Nur ta yi
sannan ta ce "To ka gaya min wadda ka ke so da?" Shima Poul Murmushi yayi sannan ya ce "Ni
ina son suna Aliyu ne amman tun da kina son Abubakar din shima yayi" Lumshe Ido Nur ta yi
tana maijin tsananin farinciki na lullabeta, zuciyarta fari kal tace "Zabinka suna ne mai daraja
shima, ni ma nafi son Aliyun to" Dan murmushi Poul yayi, cike da farin ciki sukawa juna sallama.
Washagari ta kama alhamis babu makaranta dan haka Mamy tace "Nur ta je ta gaida su Baffah,
badan ranta yasoba ta fice, domin tasan yanzun Baffah baya gida, Umma kadai ta samu a
gidan bayan ta gaisheta dakin Bashir ta shiga ta yi bincike-bincikenta tare da daukan duk wani
abin da take so tasa a lada, sannan ta fito ta yiwa Umma sallama, ledan Umma tabi da kallo
alokacin da Nur ke daf da barin gidan tace "Ji in da ta kwashe mishi kaya saikace ta bashi ajiya,
ko da yake laifinshi ne, dan ba yau ta fara ba, shike barin ta." Karfe daya ta dawo gida, tana
shiga falon Mamy tace, "Kin hadu da Bashir a waje? Girgiza kai Nur ta yi tare alamar a'a, "Kin
mishi wani abu ne?" Mamy ta sake fada bayan ta tsare Nur da ido. "A'a Mamy ni mun dade ma
bamu haduba." Zama tayi a hannun kujera yayin Aunty Saratu tace "Sai kikaji Poul ya
Musulunta, wani irin faduwan gaba taji, dan haka tasa hannunta ta dafe kirjinta, adaidai lokacin
da taji sallaman Bashir, waigawa ta yi ta kalleshi tare da saurin kawar da kant,a duk yadda yaso
su hada ido taki yadda har ya wuce ya zauna, shiko Bashir kokarin hada Ido yayi ta yi da ita taki
kallon shi, zuwa can ya mike ya nufa kofar fita tare da cewa "Nur zo"
Mikewa ta yi tabi bayanshi, motar shi suka shiga suka zauna, sannan ya dubi Nur yace, "Har
yanzun kuna tare da Poul ne?
Batare da ta kalleshiba a ta girgiza kai, idonshi akanta yace "Me kika kasani geme da
musuluntar sa?" Tana wasa da hannunta tace "Bansan komai ba."
"Karki min karya, gaskiya nake son ki gaya min, yana miki magana har yanzun ko?" Girgiza kai

ta yi tare da cewa "A'a"
"Amman kina da labarin ya musulunta?" Wannan karon ma kai ta girkiza tare da cewa aunty ce
ta gaya min yanzu" Shiru yayi tsayon lokaci yana binta da kallo, zuwa can yace, dazon ina wurin
aiki akamin waya wai ya musulunta nace badai sabo dake ba ko?" Kawar dakai ta yi tare da
cewa "Ni bana magana da shi." "Ya yi kyau kanwata" Duk nacin shi bazai aure ki ba, mu na haukane dan kawai ya musulunta
sai dauke ki abashi? Ai ba a garin gaba-gaba muke ba, idan shi ya musulunta mammanshi da
kanwarshi sun musulunta sauran dangin nashi fa? Irin shine sai kiga azo a haifi yara wasu
musulmi wasu ba musulmiba, dan haka karkiga wai ya musulunta ki ce zaki saurareshi, idan ma
musulmar ya ke son aure yaje can ya nemo a wata unguwa" Cikin sanyin jiki Nur tace, "Ni bana
ma magana da shi" Ajiyan zuciya Bashir yayi sannan yayi sallama da ita ya koma gida. Sai dai
ita Nur cike da damuwa take, dan haka ta shige daki, hawaye ta fara domin har ga Allah tana
son Poul, sai dai kamar yadda Yaya Bashir ya fada itama akwai irin tunanin aranta, saidai tana
ganin tunda ya musulunta ai tana iya aurenshi tunda da shi zata zauna bada yan uwanshi ba,
irin wannan tunanin taita yi har tsawon wani lokaci, sai dare ta samu tai waya da Poul, cikin farin
cikin yake bata labarin zuwansa wajen Malam Zubairu da yadda jama'ar unguwan sukayi
farinciki da komawarshi addinin Musulunci, a karshe ya sanar mata da cewa Abbanta ma yaxo
har gida da daddare nan yayi Murna, har ya kawo masa kyautar sallaya mai man sha'awa,,
sosai wannan labarin yasa Nur farinci mara misaltu, so ta yi ta tambayeshi labarin matarshi,
amman ta kasa, domin koda wasa be taba mata maganar matarshi ba, tuni Nur ta watsar da
zancen Bashir sukasha soyayyarsu da Poul, sai da safe ta mayarwa Aunty wayarta.

21 / 25