Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
a makarantar?" Wannan karon ma kaita girgiza ahankali ya furta, "Allah ya kyauta to, aiki ne
ya same ki haka kenan"
Cikin gidan ta shiga batare da ta tanka mishi ba, ta na shiga falon gidan Mamy ta ce "A'a
lafiya?" Gefen Mamy ta zauna tare da rufe fuskanta da tafin hannunta ta fashe da kuka.
Aunty Saratu ce ta ce "Mene ne haka Nurr" shiko Abdallah da ke can gefen aunty kallo daya
yai mata ya dauke idon shi. Mamy ce ta kwantar da ita akan kirjinta sannan tai kasa da murya
tace"Gaya min yaya a ka yi?" Ta na shashshekar kuka ta sanarwa Mamy komai, ta na mgnr
Abdallah na satan kallonta Ya na kuma mamakin halinta, bayan takai aya Aunty Saratu ta ce,
"To ke me ye na ki na shiga gidan su?" Dagowa Saratu ta yi tana kallon Mamy tare da cewa,
"Idan ba an yi da gaske an hana Nur shiga gidan can ba akwai matsala" Mamy Kuma bayan ta
gama karema Nur kallo ta ce "Be kyautaba Nur, amman to yanzun me ye abin yi?" Idon Nur a
kasa ta ce, "Mamy ki je kimai fada ya daina hakan babu kyau"
"Ni nahaifeshi kenan?" Mamy ta yi tambayan ta na kallon fuskan Nur. Wannan lokacin idon
Abdallah ya na kan Nur. Cikin sanyin jiki Nur ta girgiza kanta, ganin haka Mamy taci gaba da
cewa "To ko d'an da ka haifa yanzun saika bishi ahankali bare wani baligi da na ke hangensa da
ga titi, haba Nur yanzun sabo da wannan kika fasa zuwa makaratar? Ki fita sabgar gidan nan,
babu ta inda mu ka hadu dasu, dan haka dabi'ar mu ma bazata zama daya ba. Fada Mamy
taita ma Nur har ta dawo cikin hankalin ta da ga karshe ta ce, "Tashi kije ki cire kayan
makarantar" Mamay ta fada ta na bin Nur da kallo, ta na kokarin mikewa Abdallah ya mike ya
juya yana kokarin fita yana fadin "Ta zo muje in rakata makarantar" Mamy ce ta ce "A'a yanzun
yan mintina ya rage a tashi da yamma ta je"
Batare da ya juyo ba ya ce, " Mamy tazo mu je babu abin da za'a mata"
Ficewa ya yi, tu na yar tsama dake tsakaninta dashi ya sa Mamy ta ce, "Ku je Nur"
"Mamy ai yanzun an kusa tashi" Nur ta fada cikin Yana yin da ke nuna tsoro.
Mamy ce ta ce, "Nur bishi neman abin magana ya ke, ya na iya hadaki da Abbanku" Dole tabi
bayan Abdallah badan ranta ya so ba, acikin mota ta same shi zaune tana shiga ya figi motar
sa, be tsaya ko Ina ba sai a cikin makarantar tasu, batare da ya kalleta ba ya fice acikin motar
dan haka itama ta fito jikinta a sanyaye, tuni ya shige Ofishin din da malamai ke zama, ganin
haka ta tsaya a bakin Office din, bayan wani lokaci ta ga ya fito, wannan karon ma be kalli inda
take ba ya wuce abinshi. Daga cikin Office din aka kira sunan ta dan haka ta nufa shiga ciki
tana waiwayen Abdallah data hango ya shige motar sa ya tafi abin shi.
Cikin Office din ta shiga da Sallama a bakinta, gaba daya ta ga malaman sun dago suna
kallonta, Dan haka ta sunkuyar da kanta kasa, Daga can taji muryan Malam Zubairu ya na cewa
"Tsuguna anan" Tsunawa ta yi kamar yadda ya ce, saidai yadda suke binta da kallon ya sa ta
kasa da go idonta ta kalle su. Muryan Malam Zubairu ta sake ji yana ce wa, "Ina kika tsaya tun
dazun da aka turoki makarantar?" Shiru Nur ta yi idonta a kasa har Malam Zubairu ya sake
cewa, "Da ke na ke magana?" Cikin samyin murya Nur tace Malam na fada fa a gida, ai daga
gida muke yanzun."
"Da aka ganki ba!" Malam Zubairu ya fada cike da tsawa sannan ya mike yana cewa Malam
Sale miko min dorinar can" Dorinar aka mika mishi sannan ya taho yana cewa, " Me kikaje yi a
Nafclup kuma?" Wani irin mummunan faduwan gaba ne ya samu Nur tare da zaro duk idonta
waje saidai ta rasa kalmar da zata yi amfani dashi dan haka hawaye suka shiga zubo mata,
tarowa sukayi duk Malaman akan ta gaya musu me ya kaita can, ganin ta kasa cewa komai
Malam Zubairu ya fara zuba mata bulalar tare da tambayanta in abun da ya kaita, ganin taki
mgn duk suka dauki bulala gaba dayan su suke kaimata dukan tare da neman amsa amman ta
gagara gaya musu komai dan haka saida suka yi mata lilis sannan suka barta.
Bayan Malam Zubairu ya koma ya zauna ya na huci ya ke cewa, "Ba mahaifinki ba, koni
malamin ki kin bata min rai, duk acikin daliban da zamu yaye wannan shekaran ke ce abun
alfaharinmu, abin bakin ciki ne ace mana kina zuwa irin wannan gurin, baki tashi sama
rayuwarki shiriritaba saida kikakai wannan matakin? Ki yi maza ki gyara dabi'ar ki, har aka tashi
makarantar ba su barta ba, fada suke ta mata, yayin da jikinta ke mata azabar radadi sabo da
dukan da suka mata, duk jikinta ya fashe. Daliban sun watse amman ita sunki ba ta damar
wucewa. Bayan tsayon wani lokaci Malaman suka mike sannan suka bata damar mikewa tana
gaban su suna binta abaya, abakin makarantar kowa ya kama hanyar gidan shi da ga ita sai
Malam Zubairu agurin, fuskar shi a daure ya ce, "Muje" Gaba ta shiga kawai suka fara tafiya
tare da Malam Zubairu saidai ba hanyar gidan su aka bi ba Dan haka abin ya shiga bata
mamaki.
Hanyar gidan sa ta ga yabi, a cikin ranta ta ce "Ina kuma zai kai ni?" Afili kuwa ta gefen ido
take satan kallon Malam Zubairu, Hango motar Yaya Abdallah da ta yi can nesa ya sa ta sakin
ajiyan zuciya domin ta manta ma Malam Zubairu anguwarsu daya da Kaka, "Kenan Yaya
Abdallah ne ya ce idan an gama jibgata akawo masani gidan kaka." Nur ta fada azuciyarta,
sosai gabanta ya fadi, ahankali ta saci kallon Malam Zubairu, sannan ta dauke kanta, su na isa
kofar gidan ya tsallaka kwatar kofar gidan ya na kwada sallama, kamar dama jira Yaya Abdallah
ya ke saigashi ya fito, hannu su ka bawa juna alokacin da Malam Zubairu yace "Ke shiga ciki"
Cikin gidan Nur ta shiga, ta na tafe ta na waiwaye, Allah-Allah ta ke ta shige bayan Kaka kafin
Yaya Abdallah ya dawo. Koda ta yi sallama babu wadda ya amsa kasancewar dama gidan babu
yara Kaka kadai ce a gidan dan haka ta karasa da gudu; dan kada Yaya Abdallah ya cin mata.
Bata tsaya ko ina ba sai bayan Kaka tana mai da numshi, tun da Kaka ta ji shigowanta ta fara
fadin wacce almurance wannan?, Banbarakwai ta ji zancen a bakin Kaka domin bata saba jin
irin shi da ga bakinta ba, Saida ta mayar da numfashi a bayan Kaka sannan ta kalli kofar da
Abdallah ke shigowa yanzun nan tace "Ni ce Kaka"
'Toh, ke ce Nur ko? Kin iso?, Nur da ke bayan Kaka ta ce "Eh" Batare da Kaka ta juyo ba ta ce
fito nan ki zauna.
Fitowa ta yi ta zauna domin dama Kaka bame wasa da jikoki bace, kodayaushe ta na cikin
tsare gida tare da tsage gaskiya da adalci. Kallo Kaka tabi Nur dashi har Nur ta tsargu da
kallonta da Kaka ke yi ta sunkuyar da kai. Kamar da ga sama ta ji Kaka na cewa "Idon ki kenan
Nur ? Ashe baki da ta Ido? Ko kadan, ki rasa wadda zaki jefa da irin wannan sharrin sai
Abdullahi, yaron da duk jikokina babu me nutsuwar sa, Ina ce ko mutum zai kashe ya binne a
gaban ki zaki rufa mishi asiri, ashe abin ba haka yake ba, yar kankanuwar ki dake kina cin
mutuncin gemo, ke Nur dago idon ki ki kalle ni nan" Kaka ta fada cikin daga murya.
Dagowa Nur ta yi ta kalli Kaka, yayin da kaka ta ci gaba da cewa "Juya ki kalli Abdullahi
Kuma" Wannan karon ma kamar yadda kaka tace haka ta yi, sai dai kallo daya ta mai ta maida
kanta kasa, muryan Kaka ta ji tana cewa "Kowa ya kalli tarin kasunbarsa yasan mutumin kirki
ne shi, dan me zaki dinga aibatashi, dan wata shasha ta fada miki karya da gaskiya kike kokarin
bata mishi suna? Ni wallahi kin yaudareni domin sai yanzun na ke hango tsayayya a idon ki, ke
yanzu dan Allah ko kunyan gemun nan nasa bakya ji, yar kankanuwar da ke ki dinga lalibu
sharri ki likawa mutum kirki, yaron da ko hannu aka saka masa a baka baya cizawa, to ki shiga
hankalin ki tun muna shaida juna, idan ba haka ba zaman gidan nan saiya gagare ki, dan ko ni
nan Ina iya karya ki akan Abdullahi, idan Bashir ne ko wani can babu abin da ya shafeni, amma
wannan yaron me nutsuwa da hankali kin yi kadan ki matsa mishi, ai duk unguwar nan babu ne
nutsuwarsa dan iyayen na ku daga maza har mata idan suna neman muhimmin shawara shine
suke nema domin shine ke iya warware musu matsalolinsu cikin sauki sabo da basirarshi, dan
haka ki fita da ga idona in rufe, idan ba haka ko zakisha mamakin rashin mutuncin dazan miki.
Yadda iyayen na ku ke daukanshi mai mutunci da daraja kema dole ki kalleshi a haka ko kinki
ko kin so, duk ma beson karar mishi da mutunci ya yi ya gama, yar kankanuwa da ke sai iya
tsaro zance da iya cin mutunci gemo. Ashekarar da uwarki ta kasa zaman aure ta wurgar da ke
a tsakar gida shekaranki biyu da rabi, nan Halima ta matsawa kan ta saida ta daukoki
hankalinta ya kwanta, kan nan naki cike da kwarkwata, babu in da be yamushe ba a jikinki sabo
da rashin kulawa, to idan baki yi hankaliba ungulu zata koma gidanta na tsamiya, ita Halimar
wani dadin gidan mijin take ji?, ta yi hakurine sabo da yaranta, ke ko uwarki ta garara zama
kuma bata damu da duk irin rayuwar da zaki taso ba dan haka bazaki takurawa Abdullahi
Tunda ta fara magana Idon Nur na a kasa yake, duk da cewa ba kuka ta ke ba amman idonta
ya kara yin ja sosai, sannan hankalinta ya kara tashi fiye da abaya. Domin ba ta taba tunanin
Kaka zata mata haka ba, ba abin da yafi makanta mata rai kamar maganar mahaifiyarta data
sako, muryan Kaka ta tsinkaya da ga saman kanta tana cewa, "Kizo ki tsuguna ki nemi
gafararshi sannan ki wuce kiban gurin" Kaka Nur ta kalla, sannan ta mike ta dawo tsakiyar su
Kaka tasa guiwarta akasa kamar yadda Kaka ta ce, can kasa ta yi da murya sannan tace, "Dan
Allah kai Hakuri na bari" Hannun sa ya sa ya shafa gemun sa tsayon lokaci be Bari ba, zuwa
can ya ce, "Idan kin koma gidan ki wanke ni agurin Mamy" Sosai gaban Nur ya fadi, domin sam
ba ta son wannan maganar, shi kanshi ai ya rasa kalmar dazai kare kanshi a lokacin. Muyar
Kaka ta ji tana cewa "Ba magana ya ke miki ba?" Cikin sauri Nur ta ce, "To zanyi hakan"
Kaka ce ta ce "Ai ya zamar miki dole ki yi, ni tashi ki bamu guri" Mikewa Nur ta yi tare da kallon
agogo gani ta yi har biyu ta gota, dan haka ta dan waiga ta kalli Abdallah tare da cewa "Yaya
lokacin makaranta yayi ko in wuce da ga nan sai ka gawa Mamy a waya?" Tun kafin takai aya
yai saurin daga kansa. Juyawa ta yi tana kokarin fita Kaka tace "Munafuka ta na tafe
zakal-zakal kamar sandar fuluni" Dariyar Yaya Abdallah tajiyo dan haka ta kara sauri tabar
gidan, tafe take ahanya tana jin duniyar tai mata zafi, sai wannan lokacin ta samu hawaye suka
zobo mata; tasa hannu ta ahare, ta na isa makarantar ta wuce masallaci, alwala ta yi tai sallar
azahar sannan ta wuce aji, da ka kalleta zaka kamar ba ta da lafiya sabo da tsabar damuwan
da take ciki, mahaifiryarta ke ta fado mata a yau, tare da jin haushin Kaka mai tsanani ya na
shirgarta, duk da cewa wannan ne karo na farko data fara samun matsala da ita, alkawari taita
ma zuciyarta cewa bazata sake zuwa gidan Kaka ba, misalin karfe uku su na tsakiyar Karatu ta
hango Mamy ta wuce ajin su cikin yanayin tashin hankali, da sauri Nur ta bita da kallo da alama
Ofishin Malam Zubairu zata je, wannan tunanin ya sa gabanta kara faduwa acikin ranta ta ce
"Kodai Yaya Abdallah be sanar da ita na wuce makaranta bane? To yanzun idan ta je me
zatacewa Malam Zubairu?" Yin wannan tunanin yasata mikewa zubur batare da wani tunani ba
ta fice a ajin.
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/G07V53Lfxp4KyFPbYSLjyS
Page 11- 12
Can ta hangeta bakin Ofishin su na tsaye da Malam Zubairu, hadawa ta yi da gudu domin ta isa
wurin tun kafin Mamy na fadawa Malam Zubairu abin da ya kawota. Ta na daf da ta isa gurin tai
saurin cewa, "Mamy!" Cikin Sauri Mamy ta kalleta adaidai lokacin da Mamy take cewa, "A'a ta
dawo fita ce ta kama mu, ina tunanin kar a tashi makarantar ta dawo ta iske bama nan, shi yasa
na ce barin biyo"
Cike da gamsuwa Malam Zubairu ya jinjina kansa, kallon Nur yayi kadan sannan ya wuce
Ofishinsa.
Kallon Nur Mamy ta yi cikin daure fuska sannan ta ce, "Ina kika tsaya Nur baki dawo gida ba?
Sawuna uku makarantar nan babu kowa aciki?"
Kwalkwal Nur ta yi da ido sannan ta ce, "Mamy Yaya Abdallah be miki bayani ba? Mu na tare
da shi a gidan Kaka, Kuma na ce mishi ya gaya miki." Jimm, Mamy ta yi zuwa can ta ce,
"Wanne Yayan?" Hawayen da ya zubo mata tasa hannu ta share sannan ta ce "Yaya Abdallah"
Shiru Mamy ta yi a lamar nazari ta ke, zuwa can ta ce, "Shi na fara kira da na ga yaci ace kin
dawo gida ya ce min shi tun da ya sauke ki ya wuce abin shi" Da Sauri Nur ta dago ta kalli
Mamy "Mamy wallahi ba haka ba ne, Kuma a tambayi Malam Zubairu sannan mu je gidan Kaka
kiji, a gaban ta na ce mishi dan Allah ya gaya miki..." Hannu Mamy ta daga wa Nur alamar
dakatarwa sannan ta ce, "Bazan tambayi Malam Zubairu ba, kuma bazanje gidan kaka ba, ke
da bakin ki zaki gaya min in da kika tsaya, daure fuska sosai Mamy ta yi, sannan ta ce, "Wuce
muje gida" Nur batai musu ba ta shiga gaba, Itako Mamy juyawa ta yi gurin Malam Zubairu,
lokacin da Mamy ta fito makarantar Nur na tsaye tana kuka, hannunta Mamy ta rike tare da
fadin, share hawayen ki karki sake min kuka atiti, shasha kawai, so ki ke sai kowa ya fahimta
me kike ciki?" Daker Nur ta iya dakatar da Kukanta har suka isa gida, a harabar gidan su ka
samu Aunty Saratu, tasowa ta yi itama cike da damuwa ta na cewa, "Ina kika tsaya Nur?, Kallo
Mamy tabi Nur da shi tare da cewa "Ta ce, gidan Kaka ta tsaya, ta kuma cema Yayan su ya
fada min" Mamy ta karake maganar tana kallon fuskar Yaya Abdallah da ya fito da ga cikin
gidan yanxun.
Kallo daya Abdallah yayi ma Nur, sannan ya ce "Ke! Me kike cewa?"
Dagowa Nur ta yi da jajayen idonta ta ce, "Ai kai kace Malam Zubairu ya taho dani gidan Kaka,
kuma da na ga lokacin makaranta ya yi nace maka zan wuce makaranta ka gayawa Mamy..."
Afusa ce Abdallah ya tako gaban Nur cikin yanayin da ke nuna cewa yana cikin mamaki ya ce,
"Maimaita in ji! Ke dan baki da kunya har ki iya kallon idona kimin Karya?" Ganin yana Shirin
daga hannun sa tai saurin matsawa tare da fadin, "Karka da ke ni hannun ka akwai zafi" Kara
yowa kanta yayi Mamy ce ta ce "Karka taba ta wuce abin ka" Wayar sa ya dauko a aljihunsa
yana cewa, "Ba dai gidan Kaka ta ce ba barin kirata"
"A'a karka kirata." Mamy ta fada cikin bada Umarni. Juyawa ta yi ta kalli Nur, sannan ta ce muje
ciki" Cikin gidan suka nufa, yayin da Abdallah yai ficewan shi waje. Bayan sun shiga ciki ma
Mamy da Aunty Saratu matsawa Nur suka yi, akan ta fada musu in da ta tsaya, amsan nan dai
da ta bada tun farko ita take sake badawa, dan haka suka barta kawai badan sun gamsu da
zancen ta ba.
Washegari ta kama lahadi Mamy bata barta taje makaranta ba, hakama ranar litinin daker
Mamy ta barta, saida ta hada mata da magiya, daka kalli fuskar Nur kake gane tana cikin
damuwa, idon ta duk sun kunbura ga yawan tunani da take yi.
Misalin karfe 8 na safe ta isa makaranta, ita da Helen kamar yadda suka saba, acan suka
samu Rahma dake dama can tana riga su zuwa, wayar Rahma Nur ta amsa ta fita waje ta
zauna, number data riga ta haddace cikin kanta tasa wayar sannan ta kara a kunnen ta tsayon
lokaci tana jiran taji an dauka amman harta katse ba'a dauka ba, batare da wani bata lokaci ba
ta sake danna kira, sai dai wannan karon ma harta katse ba'a dauka ba,