Ciwon Ya Mace Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   15 / 25

42K to 45K   out of 73.1K words

karasa abin da yaso
fada, dan haka Bashir ma yayi ajiyan zuciya, daidai wannan lokacin suka Isa kofar gidan su
Auwal.
Ita ko Nur tana sauke wayar tace "Kaji Yaya Bashir, nikam karatuna zanyi bani son wani
zancen aure, idan lokacin yayi na yi amman yanzun nafi son naji ana maganar makaranta
kawai."
Shiryawa ta yi, cikkn les din da Mamy ta dinka mata, dikin ne na mutunci wadda be takura jiki
ba, dogowar riga, sannan ta yi daurin dankwalinta mara hayaniya, bayan ta saka dankunnenta
wadda suka dace da kayan ta dauki dan karamin gyale ta daura a kafada, turaroka ta fesa
sannnan ta zauna zaman jiran zuwan Bashir, agefe guda kuma ta na jiyo haniyar gidan sai dada
karuwa yake, ta jima sosai ta na jiran Bashir harta fara gajiya, sannan ta ga wayar tayi kara,

cikin sauri ta dauka tare da cewa "Yaya Bashir na gaji da jira."
"Fito mu tafi kanwata" Sauke wayar Nur ta yi tare da mikewa, ganin gidan ciki ta nufi dakin
Aunty, wayar ta mika mata sannan tai mata sallama ta fito kofar gida, motar Bashir ce kadai
tsaye dan haka ta bude ta shiga yayin da Bashir ya juyo ya kalleta tare da cewa "Kinga inda
wani haske ya lullube motar kuwa daga shigowanki, idonshi akanta yai maganar dan haka Nur
tai dariya tare da cewa, "Na yi kyau ko?" Kara karkacewa Bashir yayi Yana mata kallo mai cike
da tsokana ya ce, "Ba kadan ba Nur, Mamy ta ganki kuwa?" Cikin sauri Nur ta girgiza kai tare
da cewa, "Banjeba, dakinta cike ya ke da mutane" Dauke Ido Bashir yayi akanta tare da kokarin
tashin motar ya na cewa, "Ke kuma gaki mai tsoron mutane ko?" Girgiza Kai Nur ta yi tare da
cewa, "A'a kawai dai na kosa na fitone, kuma idan na shiga bakina sai yayi zafi wajen gaishe da
mutane, Mamy matsamin zata yi taita cewa mutane ga Nur nan, Nur ki gaishe su."
Dariya Bashir yayi bayan ya hau kantiti sosai tare da cewa "Wato abin da Mamy ke miki
kenan?, Su kuma mutane su yi ta cewa lallai Nur ta girma ko?"
"Wallahi kuwa kamar ka sani, haka suke cewa sai su yi ta mamaki" Waigowa Bashir yayi ya
kalleta tare da cewa "Ai dama na sani, dama dole za'ace kin zama budurwa, Yau dai Abdallah
ya girma zai tafi ya barmu ni kuma in sha Allah kafata kafarki" Wani irin kallo Nur tawa Bashir
tare da cewa zuwa Ina Yaya?" Zuwa gidan miji Nur, Ina son mu yi aure rana daya"
"Tab, wallahi badani ba Yaya, ni fa wallahi na tsana maganar aure ma, dan Allah ka daina yi
min"
Dariya Bashir yayi sosai Yana Satan kallon Nur sannan yace, "Lallai kince wani abu Nur,
amman fa kina bani dariya"
"To wai kai Yaya mai yasa ka cika yin mgnr aure?" "Sabo da ina son Auren ne Nur" Tabe baki
Nur ta yi sannan tace, "To dan Allah ka yi abinka karma kacewa Abba kana son mu yi rana daya
kajamin." Dariya Bashir ya sake yi dan haka Nur ta sake cewa "Allah Yaya Bashir da gaske
nake, ba cewa na yi Bazan yi kwata kwata ba, amman nan da shekara goma albarka." Wani irin
kallo Bashir yai mata zuwa can Kuma ya daure fuska tare da jan tsaki sannan ya ce, "Amman
baki da hankali ko? Tsaki ya sake ja sannan yace, Bari ma dai in daina wannan maganar dake"
Kallon shi kawai Nur ta yi ta dauke kanta bayan sun yi tafiya Mai tsayo tace, Yaya Bashi kaga
yadda Yaya Abdallah ya mayar min da sabulo daga yin wanka daya dashi, wallahi saura dan
mitsi ya bari, ai kace zaka saya min wani ko?" Kawar da kai Abdallah ya yi can gefe sannan ya
ce, "a'a" sosai Nur ta kalleshi tare da cewa "Sabo dame?"
"Bani da kudi" Bashir ya fada a gajarce, Kallon mamaki Nur tabishi dashi domin Bata tabajin irin
wannan maganar daga bakinshi ba, can kasa tace Allah ya kawo"
"Amin" ya fada a hankali bayan sun yi tafiya Mai tsayo Nur ta sake kallon shi tare da cewa "To
yanzun waye zai dauko Hajiya?" Wannan karon ma batare da Bashir ya kalleta ba yace "Ke" Da
sauri Nur ta kalli Bashir tare da yin yar dariya sannan tace ai ni ganin anan, sai dai Abba ko
Baffah wani ya daukota" Wannan karon Bashir baice komai ba, har suka isa wurin Satan kallon Bashir Nur ke yi, suna
sauka amotar Bashir yai ciki batare da yabi takan Nur ba, cikin gudu-gudu tabi bayanshi, cikin
katon dakin taron da ya cika makil suka shiga, wadda ya kawatu iya kayatuwa, da alama a
makare sukazo domin bikin ya riga da yayi nisa, a idon Abdallah Bashir ya wuce yayin da yaga
Nur nabishin abaya, hade fuska yaso yi sabo da ganin Nur, amman tunawa da yayi duk

mutanen wurin nan suna farin cikine sabo dashi sai ya cigaba da Murmushi, sai dai har yanzun
Idonshi a akansu, Yana kallo Nur ta tsaya a bayan Bashir, da alama neman inda zata sauna
take domin taburin da Bashir ya zauna shine cikon mutum hudun kuma duk maza ne a wurin,
gani yayi Bashir yayiwa Nur magana tai saurin kallon tebur din dake gefe sannan ta wuce ta
zauna, wadda ya zama itama itace cikon mutum hudu sai dai duk maza ne, acikin zuciyarshi
yake kwatanta abin da ke faruwa tsakanin Bashir da Nur da alama fada suka yi dan akwai bacin
rai a fuskar Bashir, yana cikin wannan tunanin yaga Bashir yayiwa Nur magana yayin da tai
saurin kallon can baya sannan ta make kafada, satan kallonsu Abdallah ya cigaba da yi zuwa
can yaga Abdallah ya mike ya isa wurin da Nur ke zaune ya riko hannunta sannan suka nufa
can baya suka zauna tare, Nur na zama ta kallo Inda Amarya da ango suke dan haka Abdallah
yai saurin kawar da kanshi, itako Nur tana kallo Amarya da angon tana cewa "Dan nace sai nan
da shekara goma kakejin haushina?, Nifa Yaya Bashir fada kawai na yi ba da gaske nake ba..."
"Toh ki daina irin wannan, fatan tsiya ne kikewa kanki" Idonta akan fuskarshi tace "Nabari to"
"Yafi kam" Idan kin gama Secondary kin fara makaranta ko a shekar farkon ne kika samu miji
kiyi auren ki yafi, ki kalli amarya Abdallah yar karama da ita, dan Allah bata burgekiba?" Kai
kawai Nur ta daga domin burinta kawai ya bar maganar, Ji ta yi ya sake cewa "Nasan dan baki
da saurayi kike fadan haka, Ina rokon Allah ya kawo miki miji na gari Mai hankali da nutsuwa
kafin lokacin da iyayen Aisha zasuce in fito, dan ni bazan tafi in barkiba kafata kafarki" Wannan
karon ma Amin Nur tace saidai bekar har zuciyartaba, hira ya cigaba da janta dashi
kadan-kadan, yayin da ta maida hankalinta a wajen kallon ango da marya, zuwa can Bashir ya
dauki Jakar Nur yasa kudi tare da cewa muje mu yi musu liki, gudun kartawa Yaya Bashir musu
ta mike ta bishi, duk kudin da ya samata ta lika sannan ta koma wurin zamanta ta zauna tana
kallon yadda Yaya Bashir yake ta watsar da kudinsa kamar besan darajarsu ba, Mai da
hankalinta ta yi Wurin jama'a wurin, gani ta yi da yawa sannune jaruman finafinan hausane
mata da maza ne wurin, kwalliya kuwa na waccen na wane wannan abin ba'a cewa komai,
tunani ta shiga yi acikin zuciyarta wai menene alakar Abdallah da 'yan fim din Hausa, tunawa ta
yi da hoton da ta taba gani a wayarshi da alama Yana cikin su dumo-dumo, tana cikin wannan
tunanin taji ance "Gashi kije ki karayin likin, tunkafin Nur ta dago ta shaida Mai Muryan, yayin da
kamshin turarensa ya kara tabbatar mata da hakan, dan haka tai saurin dago kanta ta kalleshi,
Poul ne tsaye cikin shadda Mai tsananin sheki babba riga da yar ciki yayin da ya daura hula
kalar aikin Dake gaban rigar shadda, sosai kayan ya haskashi, hasken fatarshi ya hade da
bakin sajenshi ya bada kalla, daker ta iya sunkuyar da kanta domin tabar kallonshi, kokarin
mikewa ta fara yayin da ya cigaba da Miko mata bandir din yan dubu-dubu dake hannun sa
yana fadin "Amsa."
Cikin daure fuska sosai tace "Banso" kokarin wucewa take ya sha gabanta tare da cewa
"Tsaya mana."
Cike da fada Nur tace "Ni ka wuce banso"
Tsaye yayi mata gaba yana kare mata kallo sama da kasa, itako Nur hankalinta ta raba
kashi-kashi ko a jamar wurin bata son hankalin kowa ya dawo kanta bare kuma Yaya Bashir ya
waigo ya gani, dan haka cike da karfin hali tacewa "Poul ka wuce ka rabu dani, idan ba hakaba
zan hadaka da yayana." Kara matsowa Poul yayi yayin da yai saurin rike hannunta tare da
cewa, "Na shirya tsayuwa a gabansu ai" Rawan jiki ta fara tare da kokarin kwacewa daga rokon
da yai mata, janta ya fara yayin da ta shiga turjewa dan haka hankalin wasu mutanen ya fara

dawowa kansu, sai dai Poul ko a jikinshi janta yake har yai nasaran fita da ita daga cikin dakin
taron, yayin da wajen ya kara kacamewa da kide-kide da hayaniyar mutane. Can bayan dakin
taron Poul ya tsaya tare da yiwa Nur rumfa da faffadan kirjinsa, jajayen idonsa ya sa mata, Yana
mata wani irin kallo, cike da tsana Nur take kallonshi saidai ta kasa cewa komai kallon shi kawai
take.Tsayon lokaci suka dauka haka zuwa can Nur ta fashe da kuka wadda ita kanta batasan
dalilin yinshi ba, ganin abin da take Poul ya hada goshinshi da nata tare da cewa "Kiyi hakuri na
dameki ko? Kamar jira Nur ke yi ta tsuguna ta dauki wani dutse dake kasa cikin sauri ya cire
hannunshi daya domin ya bata Tamar daga hannun nata kamar yadda yaga taso yi, daga dutsin
ta yi cikin matsanancin kuka tare da cewa "Wallahi zan fasa maka kai, ka fita daga harka ta, na
daina zuwa gidan ku, Helen dinma nabar kawance da ita, to me yasa zaka matsamin? Lumshe
Ido yayi cikin sanyi jiki sosai sannan ya maida hannunshi tare da cewa "Idan akwai abin da yafi
jifa kimin, duk abin da kike son kimin komenene shi bazan yi bakin ciki da faruwansa ba gani ki
min.
Wannan karon kallonshi ta yi tare da sauke dutsen sabo da hannunta daya sage sabo da
nauyin dutse, ki kwala min mana taji ya fada dan haka ta sake kallon shi cikin kuka tacigaba da
cewa, "Wulakancin da ka min be ishaka bane har yanzu? wai menene? Me kake so? Me yasa
kake bibiyata? Cikin sauri ya sake hada goshinshi da nata tare da cewa "Yauwa Nur, zan gaya miki, tun da ga
ranar da nasa aka daukoki kika tsaya min a zuciya, ko na yi kokarin share abin baya sharuwa,
kin tsaya min a zuciya sosai kodayaushe sai in ji ina son na ganki, tunaninki yana hanani bacci,
Koda ace na samu nayi Ina farkawa sai inji Ina tunanin ki, yana maganar ne yana goge
hawayenta da fuskarshi zuwa koshinshi yayin da hannuwanta yake kan kirjinshi tana kokarin
tureshi ta kasa, sosai yanayin da suke ciki ya rikita mata tunaninta tun daga lokacin ta kasa
gane me ya ke cewa, ganinta kawai ta yi tana kokarin barin wajen shi Kuma yasa hannun shi ya
riketa tare da tsugunawa yana kokarin dauko mayafinta dake kasa, bayan ya dauko daura
mata a kafada tare da cewa "Kibani amsa kafin ki wuce."
Sunkuyar da kanta ta yi kasa tare da kokarin kwace hannunta, zagayowa Poul yayi Yana
kokarin hada Ido da ita, ita Kuma taki barin hakan ya faru, "Nur ki amsa min saiki wace" Batare
data waigoba tace "Banji abin da kace ba" idon shi a kanta ya ce "Na ce Mene ne wannan nake
ji?" Sunkuyar dakai ta yi yayin da jikinta ke rawa dan haka ya sake cewa "So ne?" Cikin sauri
Nur ta girgiza kai dan haka ya kara matsowa batare da ya saki hannunta ba yace "To mene ne
shi?" Adaidai wannan lokacin taji muryan yaya Bashir yana kwala mata kira, dan haka ta zabura
tare da kokarin kwace hannunta, saidai ya hana mata yin hakan tare da kara marairaicewa,
kara rudewa ta yi domin har yanzun Yaya Bashir kwala mata kira yake har da muryan wasu
mutanen daban
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido

ADABI WRITER'S ASSOCIATION


Page 35-36

Awannan karon zabura Nur ta yi mai karfi dan haka ta kufce batare da ya fargaba, aguje tabar
wajen tana waiwayen shi, shikuwa Poul kansa ya dafa domin har yanzun beji hankalinshi ya
kwanta ba.

"Ina kika je?" Ya Bashir ya jafawa Nur wannan tambayan yayin da ya tsareta da ido.
Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da hannunta tare da motsa bakinta, sai dai ta gaza furta
komai, Idon Bashir a kanta ya sake cewa "Nur bakyaji ne Ina managa?" Dagowa ta yi ta kalleshi
can kasan makoshi ta ce, "Fitsarine ya matseni" Kallon sama da kasa yai mata sannan ya ce
"Fitsarin kikaje kenan?" Wannan karon daga kai ta yi, kallonta Bashir ya sake yi sannan ya bi
hanyar da ta fito dan haka gaban Nur ya fadi, kallo ta bishi dashi tana dafe ta kirji, zuwa can ya
dawo ya wuceta batare da ya kalli Inda take ba, bayan shi tabi da alama be gamsu da abin da
Nur din ta fadaba, yana shiga motar Nur ma ta shiga ta zauna, saidai ta kasa sakewa da ka
kalleta zaka gane bata da nutsuwa sam domin gaba daya jin ta take a yamutse, dan haka ta
fara hawaye duk da cewa tabawa Bashir baya Amman tanaji ajikinta kallonta yake saidai bece
mata komai, karatun Alqur'ani ya kunna yanabi acikin motar dan haka tuni Nur taci gaba sa
kuka.
Zuwa can taji ya tsaya tare da kashe karutun, waigawa tayi tare da zabura dalilin ganinsu a
kofar gidansu, hawaye ta fara sharewa tare da kokarin sauka acikin motar batare da ta bari sun
hada Ido ba, harta saka kafarta daya a waje taji yace, "Nur juyo mu gani" Ahankali ta juya ta
kalleshi bayan ya kare mata kallo ya ce, "Kuka me kike yi?" "Babu komai, ba kuka nake ba" Jinjina kai Bashir yayi sannan yace "Shikenan jeki" Sauka ta yi
Cikin Sauri ta shige gida, dare ya riga yayi domin tun suna hanya aka Kira mangariba, Kai tsaye
gefen Mamy ta shiga, wannan karon akwai saukin mutane, dafda Mamy ta zauna jikinta a
sanyaye, cike da mamaki Mamy ta kalleta tare da cewa "Nur Yaya dai, na ga kin dawo jiki a
sanyaye?" Kamar jira Nur take ta fashe da kuka dan haka Mamy ta saki baki, mamaki karara
akan fuskarta tace, "Me yayi zafi haka?" Mikewa Nur ta yi nata kokarin fita batare da tace komai
ba, dan haka Mamy ta mike ta biyo bayanta.
Bakin gadonta ta sameta zaune tana cigaba da kuka dan haka Mamy ta zauna a gefenta tare
da cewa "Ke da wa? Abdallah ko?" Kai Nur ta girgiza dan haka Mamy tace "To waye? Girgiza
kai Nur ta sake yi dan haka Mamy tace a'a bazai yiyuba Nur haka kawai mutum na kukane?
Bana son irin wannan gaskiya, yau kowa gidan nan farinciki yake mene ne naki na kuka? Ganin
Nur Bata da niyar magana Mamy ta mike ta fice, fitan Mamy ba jimawa Aunty Saratu ta shigo,
kallon Nur ta yi cike da mamaki ta zauna gefenta tare da cewa, Wai maye haka Nur? Hannu Nur
ta mika ta kara share hawaye, mene ne? Me aka miki? Aunty a fada bayan ta jawo Nur jikinta"
Nur ta dauki tsayon lokaci ba tare da datace komaiba, zuwa can ta shiga bawa Aunty labarin
abin da ya faru tsakaninta da Poul, bayan ta gama tace Aunty na gaji ya takura min. Fuskar
Aunty Saratu cike da murmushi tace, "Nur dan wannan ki ke kuka? Wannan ai ba wani abin
damuwa bane" Dagowa Nur ta yi ta kalli fuskar Aunty yayin da Aunty take cigaba da cewa, "Ni
dama tun da naga irin zaryar da yar uwanshi take a gidan nan na zargi haka, Allah ne ya nuna
mishi ikonshi, wannan shi zaisa ki sake agari batare da ya takura miki ba, ni dama bana wani
son aje a yi kararsa, sabo da yana da kudi Nur, abin mu zaifi tabawa ya lalata mana suna, yaron
yana takama da kudi Nur, yanzun abin da nake so dake ki kwantar da hankalinki ki daina sa

damuwa, yanzu bazai iya cutar dake ba, kuma ta sanadinki dabi'unshi suna iya canzawa ya
zama mutumin kirki." Wuri daya Nur ta tsurawa Ido tare da cewa, "Aunty tsoro nake ji, Kuma ni
na rikici, Inajin tsoro sosai kuma ni bansan yadda zanyi ba"
Kallon Nur Aunty ta yi sosai sannan tace, "Bari na fito miki a mutum, tun da naga kuruciya na
dibanki, duk da ada Ina miki kallon wadda wayaunta ya wuce na shekarunta, amman yau duk
kin daburce, idan baki fahimtaba ina son ki gane Poul son ki ya ke yi" Cike da mamaki Nur tace
to Aunty ana yin haka ne dama? baya sallah fa" Nur ta fada tare da kallon cikin idon Aunty,
"Cemin zakiyi ba fa musulmi bane, Ina sane Nur bakisan ta sanadinki konai na iya canzawa
ba?" Wannan karon shiru Nur ta yi tana sake-sake cikin ranta, zuwa can ta dago ta kalli Aunty
tace "Su Abba baza su yadda da wannan ba ai"
"In ji wa ya gaya miki? wuyarta ace be musuluntaba, iyayenku sunsan abin da suke yi, abu
daya zan gargadeki akai karki yadda ko hannunki ya

15 / 25