Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
Mamy ta fada ta na wa Abdallah
kallon tuhuma.
Abba katse Mamy ya yi cike da fushi ya daga hannunshi yana cewa "Wannan be zama
hujjaba, gaskiyar daya ce, ko an kita sai an bita za'a zauna lafiya." Cikin gamsuwa da maganar
Abba Mamy ta saki hannun Nur, ahankali Nur ta fara takawa harta isa gaban Yaya Abdallah ta
tsuguna, hade hannunta ta yi wuri guda tare da fadin, "Dan Allah ka yi hakuri." Kamar jira ya ke ya mike tsaye batare da ya ce komai ba, rigarshi da ke gefen kujera ya
dauka ya maida ita jikinshi sannan ya nufi hanyar dakinshi. Har yanzun Nur na tsugune bata
motsa ba.
Ganin yana kokarin wucewa Abba ya ce, "Babana Nur ta na baka hakuri" Waigowa ya yi tare
da sunkuyar da kanshi ya ce, "Bakomai Abba ya wuce"
Ya na shigewa hanyar da zata sadashi da dakinshi Abba da Yaya bashir ma suka fita, Nur
kuwa zamewa ta yi tai zaman dirshen a wajen. Muryan Mamy ta ji ta ce "Tashi kije kicire kayan
makarantar ki yi sallah sai kici abinci" Mikewa ta yi da sauri ta nufi daki kamar yadda Mamy ta
ce haka ta yi, abincinne kawai ta ji sam bata sha'awarshi. Dan haka ta koma gado ta kwanta ruf
da ciki, sai a yanzu ta cigaba da jin rikewar wuyanta da duk wani guri da Yaya Abdallah yai
mata mugunta, da ga bisani ta shiga tuna irin fadan da Abba yai mata a yau, be taba mata
hakan ba, a cikin ranta ta ce, ban kyauta ba sam. Hakan ba daidai bane, be dace ace ina fada
dashi ba, kuma ba yau ya fara min hukunci ba. Mai ya sa zan mishi haka? Yana rike mutuncin
shi, ko kadan bebar wata kafar da wani zai rainashiba, Yamin duk wani abu da ya kamata dan
uwa yayiwa yar uwanshi, kafin jiya Ina alfari da Yaya Abdallah, da wuya ya taba lafiyar jikina
kafin jiya, mai yasa zan mishi haka? Duka na kai mishi ko jifanshi na yi ne ban sani ba. Tunawa
da ta yi da lokacin da ya mike ya na maida rigar shi ya maido da ita da ga tunanin da ta tafi, afili
ta ce, Dole Yaya Abdallah yayi fushi, dole ya kasa magana, abin akwai mamaki." Motsin da ta ji
ya sa ta rike bakinta tare da kallon kofar, "Au kwanciya ki ka yi ba zaki fito kici abincin ba?"
Mamy ta fada tana mika mata wayar hannun ta; tare da cewa Rahma ce"
Hannun Nur na rawa ta amsa kafin tasa wayar a kunnenta sai da ta ambaci Allah domin tun
da Mamy ta ambaci Rahma gabanta ya yanke ya fadi.
Tana amsan wayar Mamy tafita tana cewa, "Ki na gamawa ki fito"
Wayar Nur tasa a kunnenta sai dai tsawon lokaci ta kasa cewa komai, acikin zuciyarta take
ayyana sunan wadda za'a kira mata yau kuma, daker ta iya cewa,"Hello Rahma" Da ga can
cikin wayar aka ce ce, "Yauwa Nur kinajina?"
Ajiyan zuciya Nur ta yi sannan ta ce "inajin ki"
"A cikin yan gidan ku waye baya gida?"
Wanni irin mummunan faduwan gaba ne ya sameta dan haka tasa hannunta ta dafe kirjinta
tare da fadin, "Rahma mene ne kuma?"
"Ya na ga kamar a firgice ki ke?" Rahma ta fada ta na kallon cikin idon Nur.
"Bawai na firgita bane Yaya Bashir da Abba ne suka fita, su kadaine basa gida yanzu"
"Yauwa, zaki iya fitowa yanzun?"
"In fito in yi me? Rahma idan wani abu ki kajiyo a kan su kawai ki gayamini."
"A'a kizo dai kikagani da idonki shi zaifi"
"Kina ina yanzu?"
"Ina cikin gari yanzu haka, ke kadai nake jira"
Cikin rike cewa Nur ta ce, "Ai ya yi nisa bazan iya zuwa ba Rahma, Mamy bazata barniba,
tun da ga nan Kabala har cikin gari? Tafiyan akwai nisa ki gaya min kawai mene ne?"
"Nur toh zan taho ki yi kokari mu hadu a makabarta yanzun nan"
Sauke wayar ta yi batare da ta iya amsawa ba, saukowa ta yi a gadon ta na tunanin yadda
zata yi tabar gidan, hijjabin sallah ta dauka ta sanya sannan ta fito falon gidan, wata zuciyar ke
bata shawaran ta fice kawai wata kila har ta je ta dawo Mamy ba ta fito ba, saidai ta kasa yin
hakan sabo da rashin sabawa da fita ba'a sani ba, juyawa ta yi ta nufi dakin Mamy, ta na tura
kofar ta gansu ita da Aunty Saratu da alama wata mgn su ke mai mahimmancin domin su na jin
an turo kofar suka yi shiru tare da waigowa suka kalli kofar.
Cikin dakin ta karasa tare da kirkiro murmushi ta ce, "Mamy zanje gidan su Rahma in amso
littafina"
"Zaki gidansu Rahma ku je gidan su Helen zakice mini, Kinga Nur ku raba kan ku da gidan
yaron nan, domin wallahi miskili yafi mahaukaci banhaushi, na san ku gani ku ke besan me ku
ke ba, toh bari kiji, na gaya miki ko be kalle ku ba ya na kare mu ku kallo ta gafen idonshi, ranar
da ya gama raina wayonku, zakusha mamakinshi. Duk da cewa Nur ta na cikin damuwa sai da ta yi dariya sannan ta ce, "Ba abun da zai mana
Mamy, aishi jarabar shi akan Mama da Helen yake sauke ta, ko muna cikin gidan be ma kallon
inda muke."
Aunty Saratu ce ta ce "Waye dama ya ce miki zai kalleku, shi da be kalli babba bare yara, ai
Poul be da mutunci ko kadan, yaron da be wuce sa'an Bashir ba amman jira ya ke ka gaidashi."
Karaf Nur ta ce, "Aunty ko kin gaidashi ma baxai amsa ba, karake mgnr ta yi tana kallon
Mamy sannan taci gaba da cewa "Mamy na tafi yanzu zan dawo" Mamy nabin bayanta da kallo
ta ce "Ku dai bi ahankali wallahi.
"Cikin d'aga murya Nur ta ce "Mamy wallahi bacan zamu ba"
Aharabar gidan ta ga motar da Yaya Abdallah ya ke hawa, amma babu motar Abba kuma tare
da Yaya Bashir suka fita, cikin sauri take tafiya, acikin zuciyarta take cewa,"Yau Kuma me zan
gani da idona bayan jiya na ji mummunan labari da ga Rahma, a jiya na yi mugun ji yau Kuma
zan yi mugun gani kenan? Koma mene ne nasan ba abun Alheri ba ne, idan ina ganin laifin
Yaya Abdallah Yaya zan yi kuma idan idona ya gano min aibun wani bayan Yaya Abdallah,
tsayawa ta yi cak ta na kallon gidan na su tsayon lokaci sannan ta ce "Me za'ayi agidan nan
anjima bayan naje na dawo? In je ne ko kada na je? Rasa wadda zai amsa mata yasa ta kara
kallon gidan sannan ta fice da saurinta.
Tana isowa bakin layin su ta tare me mashin tahau, saidai har suka dauki hanya kirjinta bebar
dukan uku-uku ba, da ke mashi ne nan danan ta fara hango makabartan, dan haka ta shiga
raba ido, a wannan lokacin duk ta manta da wani ciwo da jikinta ke mata, da ga can gefen
makabartan ta hangi Rahma tsaye, tun da ga nesa take kare ma wajen kallo babu kowa tsaye a
wajen sai Rahma sai tarin motocin da mashinnan dake wucewa. Agogon da ke daure a
tsintsiyar hannunta ta duba, karfe 04:45pm ta gani, dago kanta yayi daidai da isowan su inda
Rahma ke tsaye dan haka ta tsayar da me mashin din.
Sauka ta yi akan mashin din, sannan ta biya kudin, in da Rahma ke tsaye ta nufa tana me
cewa, "Rahma men ene?"
"Ni yau sai na ga duk a firgice kike Nur, inason in kara nuna miki abu nagaba ne bayan wadda
na gaya miki jiya, in dai kin amince da hakan?"
"Hmm na amince mana Rahma, ai ni tun da kika gaya min jiya na yadda, saidai na yi tsananin
mamaki dan ba ma ni ba har Mamy ta yi mamaki sosai. Kuma ta yi mai fada sosai, ina sa rai
hakan bazai sake faruwa ba, dan ya ji kunya sosai, harma ya rasa bakin magana, Sannan
ciwon Mamy ya tashi adaren, hakan ya kara mishi damuwa sosai, abun na damun shi har yau,
nasan zai gyara in sha Allah."
Lumshe Ido Rahma ta yi sannan ta ce "Yanzun kina son ki gannin ma idon ki ko kuwa?
Me zan gani?, Kina son kice min bayan Yaya Abdallah akwai Kuma wani me yin abun dabe
dace ba agidanmu?
"Bance ba, ina magana ne akan shi Yaya Abdallah din."
"Me zaki nuna min to akan shi? Kin ga Rahma karki raina min hankali, abin ya isa haka, Yaya
Abdallah kamilin mutun ne duk jama'ar unguwarmu zasu iya bada shaida akan haka, waccen
ma ina kyautata zaton akasi aka samu, duk gidanmu bayan Abba babu me kamun kanshi, idan
an kamashi da wani laifi bashi zai baki daman da zaki dinga yi kowanni irin magana akanshi
ba."
Jikin Rahma a sanyaye ta ce "Ki yi hakuri Nur sabo da gudun irin wannan ya hana tun farko
na gaya miki, yanzu ma dan na ga kin nuna kina son ki sani ne, Kuma ke kika bani damar sanar
dake duk wani abu da zanji akan gidanku, Dan haka nasan wani abu kan Abdallah, amma tun
da kince haka shikenan mubar kaza cikin gashin ta." Baki Nur ta lashe sannan ta ce "A'a inajin ki?"
"Idan kin amince kizo muje naf club ki gani..."
"Ina ne haka?" Nur ta tambaya bayan ta tsurawa Rahma ido.
Daya ne da ga cikin wuraren shakatawa mafi kyawun otal a kaduna, naf club ya na da wurin
shakatawa. Dakunan suna da kyau saidai suna kusa da mashaya, waje ne wanda wani lokacin
ya ke zama da hayaniya musamman da daddare, abincin gurin na da kyau, akwai dakin motsa
jiki, da filin wasan. Akwai zauren taro. kuma wurin gabaɗaya yana raye komai dare..." "Ina ruwana da kyawun gurin ko rashin kyawunshi, ni kawai ki gaya min me zamuyo acan
din?"
"Yaya Abdallah zan nuna miki."
"Rahma Yaya Abdallah ya na gida be je ko ina ba wallahi, can na baroshi a gida, bashi ki ka
gani ba. Dan a gidama na same shi Kuma har na fito dinan ya na gida."
"Shine Nur, baya gida, kuma idan kinzo munje zaki tabbatar da hakan."
"Shikenan muje" Nur ta fada tare da tare me keke, shiga suka yi tare da gayawa mai keken
in da za su, Ko da suka kama hanya babu me ma wani magana.
Misalin karfe 05:10pm su ka sauka agaban shararren Otal din, Rahma ce agaba Nur na binta
a baya, tafe take tana waige-waige sabo da rashin sabo da shiga irin wannan wajen, Rahma ko
ajikinta ta kama hanya tiryen-tiryen ya yin da Nur ke daura kafarta a in da Rahma ta cire tata,
bayan sun shiga harabar wajen ne kuma suka rasa hanyar da zasu bi, da ga can babban kofar
da tazamo nanne mashigar gurin suka hango maza da mata suna fitowa, dan haka Rahma taja
Nur su ka boye a bayan wata mota, cigaba suka yi da kallon masu fitowa da ga ciki tsayon
lokaci domin gudun cin karo da idon sani, ganin kowa na harkokin shi wasu na shiga wasu na
fita ya sa suka fito daga bayan motar.
Nur ce tabi wajen da kallo sosai, tun da ta ke bata taba zuwa irin wannan wajen ba, tsoro ne
karara akan fuskarta yayin da yanayin ta gaba daya yake cike da daburcewa, musamman ganin
da ta yi ita kadaice aduk wurin take sanye da zunbulelen hijjabi har kasa, kallon Rahma ta yi
gyale ne ajikinta, haka duk mutanen da suke wajen ko kusa babu me shiga irin tata, dagowa
tayi ta kalli Rahma ta ce, "Rahma mubar wajen nan be dace damu ba"
"Ki Bari mu shiga ciki ki gani."
Gaskiya ni bazan iya shiga ciki ba, hannunta ta dago ta kalli agogon batare da ta ce komi ba
ta fara tafiya ta nufa hanyan ficewa daga Otal din, sauri take yayin da Rahma tabi bayanta tana
Kira "Nur! Ki tsaya mana."
Jin wata murya ta kira yi sunanta wadda ba na Rahma ba yasa ta ja ta tsaya cak, namiji ne
ya kirayi sunan nata sai dai ta rasa gane ko wanene dan haka ta waigo da sauri.
Ido hudu suka yi da Auwal, abokin Yaya Abdallah ne kut da kut, kallo take kare mishi kamar
yadda shima yake kare mata kallo, ganin yadda ya ke kallon ta ya sa tai saurin kallon jikinta.
"Me kike anan gurin Nur?"
Cike da kidemewa ta ce, "Babu komai" tafiya ta fara dan haka ya ce, "Zonan!"
Nur na jin haka ta cire takalmanta ta kwasa a guje, ganin haka Rahma ta rufa mata baya tana
me kiran sunanta, saidai ko da wasa Nur bata tsaya ba. Aguje ta nufa titin tana kokarin
tsallakawa, shiko Auwal kiran sunan Nur ya ke tare da bata Umarni tsayawa, amman ina Nur
gudu kawai take. Tsintan kanta ta yi dirshen zaune akasa, a wani layi me shiru sosai wadda bata iya banbance
ko inane, layin ta kalla babu kowa sai gidaje masu dan karan kyau, cikin sauri ta mike ta fara
tafiya, banda haushin karnuka babu abun da take jiyowa cikin unguwar, dan haka hakalinta ya
kara tashi, kokarinta kawai ta ga titi domin ta samu motar unguwar su, ganin ta yi tafiya me
tsayo bata samu babban titin da zataga motocin haya ba ta fara zubar da hawayen dana sani.
Da ga bayanta ta ji tahowan wata mota da mugun gudu, cikinta ne ya kara murdawa domin ko
tantama ba ta yi ita ake bi da motar, yin wannan tunanin ya kara sata diriricewa tare da ja da
baya tana kallon motar domin daf take da ta isowa gareta
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
https://www.wattpad.com/user/fadeelalamido?utm_source=android&utm_medium=link&utm_ca
mpaign=invitefriends
Page 5-6
Kwasa ta yi a guje, duk da gudun da take bata daina waiwayen bayantaba. Mamakine ya
kamata a lokacin da ta ga motar ta wuceta batare da ta tsaya ba, cak ta tsaya tare da sakin a
jiyan zuciya, acikin zuciyarta take cewa, "Ashe bani suke bi ba, Allah na gode maka, ina Rahma
ta tsayane? Ni ta ina zanbi in koma gida? Na shiga uku" Irin wannan sake-sake take har ta
samu ta fito bakin titi, duhu mangariban da ta gani ya kara daga hankalinta, tsoro da tashin
hankali ya hanata tunawa babu takalmi a kafarta, tun da ta fara tafiya a unguwa ko motar haya
daya bata cin karo da ita ba, illa zafafan motocin da suke wucewa jefi jefi wadda bata iya
hangen mutanen dake ciki.
Zuwa can ta fara hango titi, wanni irin nannauyan ajiyan zuciya ta sauke duk da cewa bata da
kudin mota, sauri ta kara har ta isa bakin titin ta tsaya, ga motocin hayanan burjik suna wucewa
saidai kowacce a cike take zuwa, wannan ya Kara daga hankalinta, kusan minti talatin ta dauka
awajen sannan ta kula da wata mota dake dawowa da baya, matsawa ta yi domin bawa motar
wurin fakawa, ahankali har motar ta iso daidai inda take, kallon motar ta yi sosai, tunani ta shi yi
domin tuna inda tasan motar, saidai duk iya tunaninta ta kasa tunawa, wannan yasa ta kasa cire
idonta akan motar.
Tsaye motar take tsayon lokaci ita bata wuce ba kuma kuma babu wadda ya fito daga cikin ta,
zuwa can aka bude motar ganin haka tasa ido sosai, wata kyakyawar kafa ta hango cikin
hadeden takalmi aka aje a kasa, kafin aka dauko dayar acikin zuciyarta tace "Wannan ba Yaya
Auwal bane Sam, duk da cewa shima dan gaye ne amman ko kusa wannan ba kafarshi bace,
waye wannan ta sake fada acikin zuciyarta, wani irin daddadan murya ta ji tana cewa "Me kike
yi anan?" Dan haka ta dago da sauri ta kalli fuskar mutumin da ke tsaye a gabanta, wanni irin
faduwa gabanta ya yi dan haka tasa hannunta ta danne kirjinta, tunda na ke be taba mata
magana ba, "Dama Ya sanni?" Nur ta fadin haka cikin zuciyarta, a afili kuwa yawu ta hadiye
tare da mikewa tsaye tana karkade jikinta tare da kokarin barin wajen, "Ina zaki? " Mutumin
dake tsaye agabanta ya fadi bayan ya tsareta da ido, ba ta iya amsa mishi ba illa kokarin
wucewa da take yi.
"Ke! Bakijin ina magana ne? Tsaya na ce!"
Tsintan kanta ta yi da tsayawa cak tana satan kallon fuskan shi.
"Daga Ina kike haka?"
"Gida zani"
"Cewa na yi da ga ina kike?"
Yadda ya ke maganar cike da karfin guiwa ya sata tuna zancen Mamy kafin ta fito daga gida,
acikin zuciyarta ta ce, "Dama mamy ta ce Poul yana sane damu gashi kuwa, ni bantaba tunanin
zai iya shaidani ba saigashi ya shaidani duk da cewa acikin duhu na ke, kenan idan