Ciwon Ya Mace Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   23 / 25

66K to 69K   out of 73.1K words

an turo kofar, dan haka Nur tayi saurin waigawa
afirgice

CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

Page 49

Bashir suka gani tsaye dan haka Nur ta yamutse tare da neman abin yi, shikowa Bashir cike da
mamaki ya kara shigowa dakin yana kallon fuskar Aliyu ganin haka Aliyu ya mika mishi hannu,
Kamar Bashir bazai bashi hannu ba zuwa can sai ya mika suka gaisa sannan ya juya ya fice
tare da kallon Nur yace, "Nur zo" Bayan Bashir Nur tabi batare da ta baru sunyi sallama da Aliyu
dan haka shi ya dada mata hannu tare da biyo bayansu.
Bashir na gaba Nur na binshi abaya har suka shiga cikin gida, daga bakin falon Bashir ya
tsaya ganin hakan da yayi Nur ta tsaya ta kasa garasawa, kallo ya tsareta dashi sannan ya fara
takowa yana kokarin zuwa inda take. Ganin tahowan Bashir Nur ta fara kokarin komawa da
baya, dan haka yace, "Ina zaki?" Cike da tsiro Nur ta tsaya tana kallon shi, shima kallo ya kare
mata sannnsn ya juya tare da cewa "Ki shigo ciki"
Ganin ya shige ta waiwaya bayanta ganin babu kowa yasata fara tafiya a hankali zuwa cikin
falon, bataga kowa ba kamar yadda ta yi zato, Bashir ne kawai zaune afalon ya daura kafa daya
kan daya sai fama shafa gemon shi yake, jikin Nur a asanyaye ta tsaya a saitin kanshi. Bayan
tsayon wani lokaci ya juyo ya kalleta tare da cewa "Ki zagayo mana kin tsaya min akai"
Zagayawa ta yi ta tsaya tare da kallon yatsunta tana ya mutsawa, tsayon loaci ya dauka yana
kallon ta sannan yace, "Dama jiya wannan ne yazo wurin ki?" Batare da Nur ta dagoba ta daga
kai a lamar eh" Kallo Bashir ya kare mata tsawon lokaci sannan yace "Tun yaushe ya fara
zuwa?" Can kasa-kasa Nur tace jiya ne kawai" Kai ya jinjina zuwa can yace "Tun lokacin da
nace miki ki rabu dashi kuna tare kenan?" Wannan karon kasa amsawa Nur ta yi dan haka daya
gaji da tsammanin jiran amasanta yace, "Ba magana nake miki ba?"
Wasa kawai take da hannunta batare da tace komai ba, wani irin kallo Bashir ya mata sannan
ya mike ya fice a gidan, batare da ya sake waiwayen inda take ba, Nur ma cike da damuwa ta
wuce dakinta, washari da da safe cikin sanyin ciki tai sallama ta wuce makaranta, Bashir kuwa
Daker bacci ya iya daukanshi sabo da tunani, dan haka washegari yana tashi aiki ya wuce gida
domin ya dan kwanta, msalin karfe biyar ya shirya fitowa zuwa gidan Abba domin ya tabbatar
ma kanshi ta dawo makaranta yanzun, adakinta ya sameta, Nur na ganshi gabanta ya fadi,
daga tsaye ya tsaya Yana binta da kallo, cikin sanyin jiki ta gaidashi, jiran amsawarshi taitayi
saidai har aka dauki tsawon lokaci be amsa ba, dan haka ta dago ta kalleshi. "Kar na kara
ganinki da mutumin nan, idan Kuma har kika kara bari yazo gidan nan duk abin da ya biyo baya
ki kuka da kanki, juyawa yayi batare da ya jira amsa daga garetaba dan haka Nur ta matso
guntun hawayen da ya zubo mata ya sauka a kan kumatunta afili tace "Abin da nake ta gudu
kenan, ni yanzun ya zanyi? Bazan iya kiranshi in ce ance ya daina zuwa ba, nasan bazaiji
dadiba, kamar yadda nima bazanji dadiba, komawa tayi bakin gadon ta zauna, tunanin aunty
Bilikisu fal zuciyarta, kasa Kiran Aliyu ta yi ta gaya mishi har aka kira magariba, babu abin da
zuciyarta ke nuna mata sai Aliyu, ganinsa take yana Shirin zuwa wurinta, yayin da take tuna
murmushinsa, bata ankaraba aka kira isha'i, alwala ta yi sannan ta tada Sallah, tsintan kanta ta
yi ta idar da sallah batare da ta tuna maita karantaba dole ta mike ta sake kawo wata sallah tare
da tattaro nutsuwa tasawa zuciyarta, bayan ta idar hannunta ta daga tana addu'a Allah yasa
Aliyu yazama miji a gareta, karo na farko data fara addu'a akan aure, domin ada tafi yin addu'ar

Allah ya cika mata burinta akan karatu, yau sai gashi tana rokon Allah yasa Aliyu shine mijinta,
kiransa ne ya shigo wayarta, batare data tashi akan sallayar ba, yana sanar da ita gashi a kofar
gidansu, kirji Nur ta tafe tare da mikewa tsaye, tana ninke sallayar tare da cewa fili, "To ni Yaya
zanyi? Inje ne ko kar in je? Amman Yaya Bashir ba a gidan nan yake ba, kilama yau bazai zo
ba" Karfi guiwa taji, dan haka ta shirya ta fita tare da yiwa su Mamy sallama, Hira sukayi da
Aliyu sosai, saidai bata da walwala, kuma karfe tara da wani abu tayi sallama dashi ta shiga
gida, bayan ta shiga daki ajiyan zuciya ta yi, ganin Yaya Bashir bezo gidan ba, yau da wuri ta yi
bacci saboda bashin baccin jiya, dan haka washegari ma wuri ta tashi ta yi shirin makaranta,
bayan ta gama shiryawa tana kokarin fita wayarta ta yi kara, dauka ta yi ta duba, Abba ta gani,
dan haka tayi saurin fita ta nufa dakin Abbba, shikadai ta samu aciki bayan ta zauna ta gaidashi
tare da cewa "Abba na ga ka kiran ni." Dagowa yayi ya kalleta sannan yace, "Eh naso in shigo
tun safe nayi baki, kina jina? Gyara zama Nur tayi sannan tace "Eh Abba. Waishin wani yaro ne
ya ke zuwa wajen ki?
Faduwan gaba Nur taji nan danan yanayinta ya canza tare da kasa cewa uffam. "Ina jinki
Nur?"
Wannan karon ma batace komai ba bare ta dago Ido ta kalli Abba, kawar dakai Abba yayi
sannan yace "Dole ki kasa magana Nur, abun yabani mamaki, kuma ya daure min kai, a
unguwar nan idan akwai wadda yasan halin yaron nan a bayanki yake, acire maganar Addini
tun da ya musulunta, bana manta ranar da kika zauna anan wurin kina rokona in rike uwarshi,
sabo da ya gaza rike ta, Nur irin wannan mutumin zaki kawo min ya zama surukina? To ki shiga
hankalin ki, karki sake bawa wani dama ya shigo min gida, ban amince dashiba kuma bazan
amince ba." Zuwa wannan lokacin Nur ta fara kuka, idonta akasa, bayan Abba ya gama
magana yace tashi ki bani wuri" Kasa tashi Nur ta yi tsawon lokaci dan haka Abba yace ko kina
da mana ne?" Idonta na zubar da hawaye tace "Abba duk abin da yake da ya bari wallahi" Kallo
Abba ya kare mata sannan yace, "Wannan zaton kine ai baki zauna dashi ba"
Hannu Nur tasa ta share hawaye sannan ta sake cewa, "Abba kayi hakuri mun yi alkawarin
aure tun da dadewa dashi" Kallon mamaki Abba ya bi Nur dashi bayan tsayon wani lokaci yace,
"Maganar da aka gaya min gaskiya ne kenan, dama an gaya min ina ganin kamar ba hakaba,
tun kina secondary kike tare dashi, hakika kin yaudari kanki ni ma kuma kin yaudareni, sam
banzaci zaki aikata hakanba, wato makarantar da na baki dama kiyi yasa kike ganin kina da
'yancin bada kanki ga wani? Kin gama yankewa shi zaki aura sabo da kin riga?" Wannan karon
ma sunkuyar dakai Nur ta yi cikin matsanancin kuka, yayin da taji Abba ya ci gaba da cewa,
"Baki Isa ba Nur kije acikin manemanki ki kawo min wani, tun da ke yar boko ce kuma kin iya
munafunci" Kara roshewa Nur ta yi da kuka tare da cewa, "Abba wallahi shi kadaine, kuma
shima ta waya ne kawai muke magana"
"Ke kika san wannan Nur sai kuma Allah daya hallicemu, Ni dai abin da nake gaya miki ki
kawo min wani kafin sati biyun su cika"Jajayen Idonta ta dago ta kalli Abba tare da cewa "To ka
Kara min lokaci Abba"
"Babu wani lokaci dazan kara miki Nur, in dai ba kina son ki nuna min iyakata bane, ke zaki
kawo min wadda zaki aura, kinci sa'ar bani da ra'ayin yin auren hadi yau da kinsha mamakina
Nur, kin bata min rai tashi maza ki bani waje" Mikewa Nur ta yi cike da damuwa ta fito, ji tayi
kamar ta koma gida domin batajin kafafuwanta zasu ya fita da ita bakin get din gidansu, amman
sanin dole taje makarantar yasata daurewa ta fice, saidai har ta isa makarantar kuka take, kafin

ta dawo idonta duk ya kunbura.
****
Ban amince wani ya sake zuwa wajen Nur ta fita wajensa batare da iziniba ba" Abba ya fada
yana daga tsaye, yayin da Aunty da Mamy sukayi kasake suna kallonshi, ganin ya juya yana
shirin fita Mamy tace "Alhaji wani abu ne ya faru?"
"Ina da ikon da zan hana duk abin da bana so acikin gidan nan..." Baki Mamy ta saki, bayan ya
fice ta kalli Aunty Saratu tace "To kodai yayi mata miji ne, idan ba haka ba ai Nur ta isa abarta ta
fita zance kuwa, Kuma shi da kanshi ya bata dan kankanin lokaci" Tagumi Mamy ta yi batare da
tace komai ba, wuni Mamy ta yi da tunanin abin, har sai da Nur ta dawo suka kula tana cikin
damuwa, dan haka Mamy ta Kirata daki bayan ta tareta da ido tace mai ke damunki? Kasa Nur
ta yi da kai kamar Mai jira hawaye ya fara zubo mata, dan haka Mamy tace "Ina jinki" Nur na
wasa da yatsunta tace "Mamy Abba ne, kasa karasawa ta yi dalilin kukan daya kwace mata,
wannan karon Mamy batace komaiba, kallo ta bita dashi tsawon lokaci sannan tace, "Yayi miki
magana akan wadda ke zuwa wajenki ko?" Kai Nur ta daga, hannu Mamy ta mika ta riko na Nur
zuka koma bakin gado, sannan tasa hannunta ta fara share nata hawaye tare da cewa, "Daina
kuka, ki gaya min mene ne dalilin shi" Idonta akasa tace yace ne in dakatar dashi karya sake
zuwa." Jimmm Mamy ta yi sannan tace "Shi mai zuwa wajen naki wane ne shi Ina kuka hadu?"
Kara fashewa Nur ta yi da kuka batare da ta iya cewa komai ba, Tsawon lokaci Mamy ta dauka
tana tambayanta amma taki cewa komai, dan haka Mamy ta kira Bashir nan ya warware mata
komai, sosai Mamy ta shiga cikin tashin hankali tare dabin Nur da kallon Mamaki, zuwa can talli
Nur din tace, "Yanzun ke idan na fahimce ki son yaron nan kike kenan?" Nur Bata iya dagowa ta
kalli Mamy ba hawaye kawai take share dan haka Mamy tace, "Shikenan, ni banzan ce komai
ba, domin wani lokacin abin da muke so wata kila bashi bane alheri a garemu, dan haka zan
roki Allah idan alakarki dashi alherine Allah ya kawo mafita cikin sauki, idan kuma ba alheri
bane Allah ya canzashi da mafi alheri, kema kije kiyi iri wannan addu'ar, shi Kuma yaron ki
dakatar dashi kamar yadda Abbanku yace."Sanyi zancen Mamy yasa Nur taji a zuciya, amma
maganarta ta karshe ta Kara dawo mata da damuwa, domin Bata da bakin da zata iya dakatar
dashi, mikewa ta yi ta koma daki, kuka ta cigaba dayi tare da addu'ar Allah ya sausauto da
zuciyar Abba, domin shi kadaine zai bada matsala ko Baffah bazai bada matsala ba kamar
yadda Abba zaiyi. Bata iya kiranshi ba, har saida ya kirata, gashi a kofar gida, sannan ta sanar
mishi Abba yace ya dakata da zuwa, duk kokarin ta na kada ya fahimci akwai matsala Saida ya
gane, dan haka suka kusa kwana waya akan neman mafita. Haka sukaci gaba dayin waya
badare babu rana yayin da shakuwa ke kara shiga tsakaninsu, Yaya Bashir kuwa kwata kwata
ya daina mata magana, saidai ya kalleta ya wuce abinshi, yayin da aunty da Mamy ke Kara
karfafa mata guiwa akan tayi addu'a, dan haka Nur ta dan saki jikinta tare da yin alkawari babu
namijin da zata kula har Abba ya gaji ya aura mata Aliyu.
saidai halin ko in kolan da Bashir yake Nuna mata ya dameta sosai, yayin da take rasa dawa
zata tattauna matalarta.
Adaddafe sati biyu suka cika, Nur ce a farfajiyar makarantar su bayan kammala bikin yaye
daliban da suka kammala karatun lauyoyi, wurin da Abba da Yaya Bashir ke tsaye ta nufa,
Bashir ta gaida sannan suka jera yayin da Abba yake rike da hannunta yana mai nuna zallar
farin cikinshi tare da yi mata addu'a, acikin zuciyarta take mamaki yadda ya saki jikinsa da ita
yau, rabon da taka fara'a a fukarshi tun kafin ya san da zancen Aliyu, suna isa Motar taga Yaya

Abdallah zaune cikin motar, gani ta yi ya kara kiba yayi wani irin haske, kuma da alama kudi sun
zauna mai dan motar ma da alama mai tsada ce kuma sabuwa dal har tana sheki, a yanzun
gani ta yi kamar ba wanda ta sani bane abaya, dadewa da ta yi bata ganshiba da kuma mgnr
da basa yi yasa a yanzun take mishi kallon tamkar ba dan uwansu bene,, dauke kanta ta yi
daga kallonshi ta mayar da hankalin wurin Yaya Bashir domin yadda yake shareta yafi kona
mata rai, "Yaya Bashir zo kaji" Nur ta fada cikin sanyin jiki, zagayawa yayi ya shiga motar tare
da cewa "Sai mun hadu a gida" Abba ne ya shiga motar shima tare da murmushi sannan yace
"Akwai alamar Bashir yana fushi da kanwarshi" Bashir bece komaiba har motar ta tashi, tsaye
Nur tayi a wurin cikin sanyin jiki tabi motar da kallo, adaidai lokacin da Abdallah ya juya hancin
motar tare da yi mata wani irin kallo, kallonshi ta yi ta yamutsa fuska, a hankali yake juya motar
batare da ya cire idonshi akanta ba, mamakin kallon da ya ke mata yasata saurin Juyawa ta
fara manganu kasa-kasa "in kalleshi ya ce na Harare" Cikin kawayenta ta shige, Abba kuwa
bayan sun kama hanya hakuri ya bawa Bashir akan fushi da yake da Nur, shidai Abdallah besa
baki ba, dan besan akan abin da ake magana akai ba, adaren ranar Mamy ta sanar da Nur
dawowan Bilkisu, cike da mamaki take kallon Mamy tare da cewa "Mamy tun yaushe ta dawo"
"Ta dade da dawowa kuma ta samu lafiya, ta kira number Aunty ku yafi a kirga tana nemanki,
bamu gaya miki bane sabo da halinki, to jiya kuma ta kirani awaya na mata alkawarin gobe
zakije"
Cike da Farin ciki Nur tace to Mamy bani number insa a wayata, amsan ta yi tasa a wayarta,
washegari da wuri Nur ta shirya, Saida ta kira Bilkisu sannan ta fito ta yiwa su Mamy sallama,
bayan ta isa gidan cike da farin ciki suka rungumi juna sannan Bilkisu ta Nunawa Nur wurin
zama ta zauna, har yanzun dai wannan dakin ne wadda take ciki ada, saidai wannan karon
akwai dan walwala a tare da ita ta yi kiba sosai harta zarce da saidai ta yi baki sosai kuma fatar
jikinta ya nuna ba wani hoto take samu ba, hakama suturar jikinta, cikin rashin jin dadi Nur tace,
"Ina yata wadda bansan sunantaba har yanzu" Dan Murmushi Bilksu tayi sannan tace
"Sunanmu daya"
"Allah sarki" Nur ta fada cike da tausayi, murya Bilkisu ta daga ta ce "Ummi!" Karamar murya
Nur taji ta amsa, dan haka ta Nur ta mike tabi inda muryan yariyar yake, ganinta tayi tana
dahowa dan haka tai saurin rungomo yariyar ta dawo ta zauna tare da zuba mata Ido, sosai
yariyar take kama da Bilkisu, kamar harta bace, idon Nur cike da hawaye tace "Auntymu kiga
yadda ta girma, kai Masha Allah, yar dariya Bilkisu tayi, kallo Nur tabi yariyar dashi, da alama
itama bata da suturar kirki, dan kunnen dake kunnenta ma yayi baki dagowa Nur tayi ta kalli
Bilkisu tare da cewa, ta fara zuwa makaranta ko?
Yar dariya Bilkisu ta yi tare da cewa a'a bata fara ba Nur.
"Amma ya kamata ta fara zuwa makaranta"
Na sani Nur, amma babu yadda zanyi, ko kofar gida ba'a barina naje bare na nemi kudin dazan
kaita kuma acikin gidan na babu wadda zaikaita makaranta, Nur in takaice miki Kamar wata
bare haka nake acikin gidan nan, kinsan tunda wannan abin ya faru Momyn mu sun rabo da
Daddy, na kasa yafewa kaina wannan abu, sun hadu tun ba'asan damu ba, gashi nazo na yi
sanadin rabuwar su, wallahi Nur ni banzo duniya a sa'a ba, tun daga ranar da naga rikicin da
Daddy sukayi da Momy nazama kamar gawa gani a duniya ina kallo Ina ji amma inaji tamkar
acikin kabari nake, yanzun haka abu kadan zanyi kiji Daddy na zagina Kamar ba shibane
wadda na sani ada dan haka ni komai baya min dadi, itama Ummi dandai yariya ce bata san

ciwon kantaba da ko dakin nan ace mata ta fita baza ta fitaba amma sai kika ana mata mugunta
tana makalewa.
Cikin share hawaye Nur tace "Ki daina barinta tana fita, ku zauna tare"
"Idan na hanata fita Nur shima ba gata bane, zan iya mutuwa in barta, gara ta saba da walar
koda ace zai yi sanadin mutuwarta, kinga idan ta mutu ta huta.
Wanni irin kallo Nur tawa Bilkisu tare da cewa "Wacce irin magana ce wannan"
To Nur mai zata yi a Duniyar bayan babu ni, bata da uba bare danginshi, 'yan uwana kuma
sunki yadda da wannan kaddarar" Hawaye Nur ta share sannan tace, "Aunty dan da aka tsunto
ma ba'asan warshiba ba a san ubanshi yana samun iyayen da zasu rikeshi kamar dan da suka
haifa, kisa a zuciyarki wannan jarabawa ce kawai Aunty, sannan kuma

23 / 25