Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
zai yi, bayan na yi magana dashi da kwana biyu yayi min bayani
akan iyayen yariyar da yake so, mun kuma je mun nema masa kuma sun bamu, a yanzun haka
su muke jira su tsayar mana da rana." Cike da fara'a Nur ta ce "Abba yaushe za'ayi bikin?" Kara fadada fara'a Abba yayi sannan ya
ce, mu a shirye muke su muke jira"
"Abba!"
"Na'am Nur, na lura akwai abin da kike so ko?"
"Eh Abba"
"Toh inajin ki"
"Abba kawata dinan Helen, itace Mamman su bata da lafiya wai zasu koma kauyensu da
zama"
Cikin rashin fahimta Abba ya ce "An nema maganin ne anan ba'a dace ba?"
"A'a Abba, kudin maganin ne babu ko abincin da zasuci basa samu agidan, kuma idan helen
ta tafi shikenan ba lallai azana jabawar karshe da ita ba"
Shiru Abba ya yi tsawon lokaci zuwa can ya ce "Mai kike so ne yazon?"
"Abba Helen na cikin gidan nan yanzun haka, dama ka barsu su zauna anan"
Shiru Abba yayi zuwa can ya ce, "Wannan ba mai yiyuwa bane Nur, idan d'anta ya kasa riketa
kamata ya yi ta koma gida kamar yadda zasu yi yanzun, shi taimako wani lokacin yana da wuya
musamman kinga su ba musulmai bane, duk da cewa sum dade acikinmu, yanzu Ina ga abin
da za'ayi zan bada kudi a kaita asibiti sannan zan musu sayayyar kayan abinci ta koma gida
suci gaba da hakuri."
"Amman Abba bata da lafiya yanzu, Kuma ta riga tayi fushi da gidan, dan Allah Abba kadan
barsu ko kwana biyu su yi a nan dan Allah, da mamaki Abba yabi Nur da kallo tare da ganin
tana dauko ma kanta damuwan da yafi karfinta, jimmm Abba yayi tsawon lokaci zuwa can ya
ce, "Shikenan" Cike da farin ciki Nur ta shigo da su cikin gidan, ganin yanayin jikin Mamma Abba ya bawa
Bashir izanin akaita asibiti, Mamy ce dauka zaninta na atamfa ta daurawa Mamma akan siket
dinta dabe karasa guiwa ba, sannan ta daura mata dankwalin atamfar a kanta, bayan motar ta
zauna saidai har yanzun rawan dari take dan haka Mamy ta kwalawa Nur kira bayan ta amsa ta
ce ta kawo mata hijjabi, cikin gudu gudu Nur ta kawo hijjabin kasancewa Mamy na gaban motar
bayan ta kawo Mamy ta ce tasawa Mamma, wannan karon cike da mamaki Nur ta nufa Mamma
Helen dake zaune kawai tana rawar dari, cikin sauri ta zura mata, yadda Mama ta cure acikin
hijjabin tamkar ba ita ba, sai da motar ta fice a gidan sannan Nur ta koma cikin gida, sai yamma
su Mamy suka dawo, wannan lokacin babu wani rawan sanyi da take abinci taci sannan Tasha
magani tai bacci.
Bayan kwana su uku sosai Mamma ta murje ta yi jawur da ita tamkar ba ita bace tazo da
masassara, har yanzun ta na sanye da hijjabi tare da zannuwan da Mamy ta bata, ga abinci me
kau har sai sunci sun barshi, komai da suka basu Mamy ta hada guri daya domin yaune Abba
yayi Umarni su koma gida, misalin karfe uku na rana Mamy ta raka Mama gurin Abba domin su
gaisa Kuma ta yi godiya, cikin Sakin fuska su ka gaisa da Abba, sosai ya nuna jin dadinshi
ganin ta samu lafiya, nan ya bata kauta kudi bayan kayan abinci daya haka hada mu su, kuka ta
fara tare da fadin, "Tun da nake a duniya ban taba tsintan kaina cikin nishadi da farin ciki kamar
na yau ba, na sha wahala tun ina da cikin poul, mijjna ya mutu tun suna kanana nakiyin aure,
duk domin ingina rayuwar Poul da kanwarshi, ba irin wahalan da basha ba wurin biya bishi
kudin makaranta, da hidimar rayuwar sa, har ya zama abin da ya zama yanzu, amma daidai da
rana daya betaba faranta min kamar haka ba, yata min alkarin zanji dadi amma Yana yin aure
komai ya canza, dakatawa ta yi da maganar ta share hawaye sannan ta ci gaba da cewa, "Da
Poul kadai nake takama, akanshi duk na aje burina, na dauki tallar ruwa akaina na biya mishi
kudin makaranta amman yaki kulawa dani alokacin da karfina ya ke shirin karewa, sai gashi ku
da bantaba tunanin zaku taimakeniba ku ne ku ka taimakeni, acikin kwana uku da na yi da ku
naji ina kaunar ku, ina jin kewan rabuwa da ku, Alhaji ni da Helen zamu musulunta" Cikin zare
ido Abba ya kalleta sannan ya juya ya kalli Mamy da fuskarta ya cika da mamaki, koda wasa
Bata tsammaci jin irin wannan kalamin ba, cikin daburcewa Abba ya ce, "Kina nufin zaki zama
musulma?
"Eh ta bawa Abba amsa cike da karfin guiwa, cike da sanyin jiki Abba ya ce, "Ikon Allah,
mikewa yayi ya dauke hularshi ya sanya sannan ya Kira Mamy su ka fita, bayan tsayon lokaci
Mamy ta dawo daf da Mama ta zauna tare da cewa Maman Helen kin yi shawara da yaranki
kuwa?, Musamman shi babban kar abin ya kawo mu ku matsala." "Karki da mu da shi Hajiya, bazai da mu ba, na yi magana da Helen mun yanke wanan
shawaran Poul ba ma gabanshi, zai yi rayuwarsa ne mu yi ta mu"
Jimmm Mamy ta yi tsayon lokaci zuwa can ta sake cewa ba kuma fushin abin da yaron ki ya
miki bane ya sa zaki musulunta? Ina nufin yanzu in da a ce zai bar abin da ya ke yi za yi
zamanki a addinin ki? Cikin sauri Mama ta girgiza kai tare da fadin, nutsuwa da kwanciyar
hankali da na gani a tattare da ku ya jawo hankalina, kana uku da na yi a gidan ku na fahimci
wasu abubuwa da dama a tare da ku da kuma yaran ku, sannan kuma bana iya tuna rabon da
na samu kwanciyar hankali da nutsuwa irin wadda na samu cikin kwana ukun da na yi a gidan
nan. Ajiyan zuciya Mamy ta yi sannan ta fita, zuwa can su ka sake shigowa tare da Abba, zama ya
yi sannan ya ce, "Yanzun abin da za a yi ki je gida ki kara nutsuwa tare da zurfafa tunani, ki yi
shawara da yaran ki, zuwa gobe ko jibi sai kizo...." Katse Abba Maman Helen da ta yi da fadin,
"Ni fa na riga na gama yanke shawara, yau nake son nabar addinin can" Murmushi Abba yayi
jin furucinta saidai ya na dan bargaba akan labarin nata, dalilin tuna waye danta, tun da ya
mallaki gida a unguwar ta su baya mu'amala da kowa, ko daga hannu baya yi, dan haka ba
kowa ne ya san fuskarsa ba, da wuya kasamu mutumin da zaice ya sanshi a fuska, saidai ana
iya shaida duk motocin da yake hawa, ajiyan zuciya Abba ya yi sannan ya ce, "Shikenan tashi
muje wajen Malam Zubairu. Mikewa suka yi fuka fito, yayin da Mamy ta kwalawa Helen Kira
bayan ta fito suka shiga motar suka tafi.
Ganin fitan su Nur tace Mamy naso na rakasu har gida, ba gida zasu ba, Mamy ta fada tana
gyara zamanta sosai nan ta kwashe komai ta bawa anuty da Nur labari, sosai Nur ta shiga farin
ciki hakama aunty Saratu, bayan kusan awa biyu su Abba suka dawo, wannan karon Helen
sanye take da hijjabi, ganin haka kwallar farinci ya cika idon Helen rungume juna suka yi ita da
Helen tsayon lokaci. Abba ne ya Umarci Nur da tazo ta raka su gida, fitowa suka yi har da
Abba, sabo da kayan abincin da ya hada musu ya sa ya kaisu har kofar gida sannan suka dawo
gida, sai dai har yanzun a cikin zuciyar Abba be gama gamsuwa da Helen da Mahaifiyarta ba,
dan haka ya ke dan rage fara'arsa, wani abu da yafi daga hankalinshi shi tunda suka fara
ganarwa komawa Musulunci gabanshi ya fara haduwa kuma har yanzun daya sauke su ya
dawo gida faduwam gaban nasa gaba yake ba baya ba, aduk lokacin da gabanshi ya fadi
fuskar Poul ce ke fado masa arai dan haka ya shiga karato addu'oi
*****
"Duk in da nake tunanin zasu je naje basa nan, na gaji sosai, Ina son in ganta tukuna in je
wurin aikina, komai nawa ya tsaya, babu Mamma babu Helen, anan babu Mamma a can gida
babu Mamma" Ajiyan zuciya matar dake tsaye a gabanshi ta yi sannan cikin hausarta da bata
fita sosai ta ce, "Wai dama ba kai ka sauke su ba, ai sun shigo dazon da kaya mai yawa" "Mamma? sun dawo?" Tabe baki Matar ta yi sannan ta ce sun dawo, amman fa akwai
matsala kamar dai almajirai haka suka dawo, kuma sun saka hijabi ajikinsu.
Hijjabi? Poul ya fada cikin daga murya sannan ya nufa hanyar da zata sadashi da dakin dasu
Helen suke yana tafe kamar mai shirin tashi sama.
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 17-18
Kallon kallo ne ya shiga tsakanin Poul da Mamma alokacin da ya tsaya a tsakiyar dakin, shigar
da ke jikin su ya bi da kallo, ganin kaya irin na Hausawa ajikinsu ya cika da mamaki, Mamma ko
tun da ta kalleshi sau daya ta dauke kanta tare da cigaba da tufke wa Helen kai, daf da su ya
karaso tare da fadin, "Ina kuka je kwana biyu?" Cikin daure fuska sosai Mamma ta ci gaba da abin da take batare da ta bashi amsa ba, dauke
kansa yayi ya maida wurin Helen domin wannan shine karo na farko da yaji nauyin sake jafawa
Mamma tambaya, "Helen ina kuka je?"
"Sunanta Zainab." Mamma ta fada fuskarta daure tamau. Cikin Sauri ya maida kallon shi ga
Mamma, "Bangane ba Mamma" Poul ya fada hankalin shi a tashi tare da ware idon shi waje
yana Kara bude kunnen shi.
Cike da karfin haki Mamma tace "Eh abin da ka ji haka ne, ni da ita mun karfi musulunci
yau...."
Me ya sa mamma? Poul ya fada cikin tsananin tashin hankali tare da kara matsawa daf da
Mamma ya na ware idon shi waje. "Idan bazaka iya za ma damu ba zamu tafi kauye mu zauna"
Mamma idan wasa kike yi mini ki bari, hakan bazai taba zama gaskiya ba, idan kuma kin yi ne
dan ki bata min rai wannan ba shi bane mafita, dan idan har kuna bin wannan addinin bazamu
zauna inuwa daya ba, kuma bazan fita in nemo kudi inci da ku ba"
"Poul babu wasa a idona, ni da Helen mun karbi musulunci, sabo da hankalina ya fi nutsuwa
dashi, yanzun hankalina ya kwanta, na samu lafiya"
Sosai ran Poul ya baci har kana ganin wasu irin jijiyoyim da ke cikin kanshi saboda tsananin
tashin hankali, idon sa kuwa wani irin ja yayi irin wadda be taba yi ba, cikin tsananin fushi ya ce,
"Bazan zauna da ku ba, na ji ke da helen kun canza addini dan ku bata min rai, idan ni ne na
mata miki rai ba wan ne mafita ba, da ga yanzun ko me kuke so ku fada min zan muku, amman
bana son musuluncin nan, ko a mafarki bantaba tunanin zaki yi haka ba Mamma...."
Poul ko me zaka ba ni bazan taba barin wannan addinin ba, rabon da na samu nutsuwar da na
samu yau na jima sosai, bazan ma iya tunawa ba, na gane babu wadda ya kamata na dogara
dashi sai Allah wadda ya halicceni ya halicci bayin da suka taimakeni; batare da mun hada
komai ba, na samu nutsuwar da na rasa ko rabinta a gareka" Wanni irin kallo poul yaiwa Mamma, bayan ya gama kare mata kallo ya ce, "Shikenan, ku
tattara duk wani abu da kuka san da gumina kuka siya ko na saya muku, ku aje min sannan ku
barmin gidana, bazan sake zama tare da ku ba, bana son in sake ganinku a rayuwata.
Bakin sa Mamma ta ke kallo a lokacin da ya ke furta wannan kalamin, sosai ya ke bata
mamaki nan ta tuna yadda mazan gidan su Nur ke mutunta iyayensu, sannan ta tabe baki tare
da daure fuska sosai ta ce, "Dare yayi amma idan mun wayi gari lafiya da safe zamu barmaka
gidan ka." Kallon Mama Poul yayi sannan ya juya ya fita adakin, afusace ya ke tafiya tare da sake sake,
wata zuciyar ce ta ce, "Ka korasu mana a daren nan" yin wannan tunanin ya sashi yaja ya
tsaya, sannan ya waiga ya kalli hanyar tare da tuna fuskar Mamma, besan me yasa ba haka
kawai ya ke ganin fuskarta a yau ta mashi kwarjinin, ita kanta da alama cike take da kwarin
guiwa, dan haka yaji Sam bazai iya kallon idonta ya ce sai sun fita a daren nan ba, saidai
zuciyarshi cike take da bacin rai har ya isa dakin sa, Yana shiga yasa makulli ya rufe dakin.
*****
Washegari da safe Poul ne zaune saman motar sa idonsa jawur, da ka kalli fuskarsa kasan ya
na cikin baccin rai, tun da ga nesa ya hango budurwar yariya cikin Hijjabi har kasa, jajayen
idonshi ya kara bazawa afili ya ce Nurr ce, ganin tana Jan akwati ya ji faduwan gaba afili ya
sake cewa, "Wato akwai sa hannun yariyar nan aka shirya min wannan abin, idan ba haka ba
me take a gidan nan? Yaushe ta shigo min gidan? Tun da sauran duhu nake zaune a wurin
nan" Sakkowa yayi sama motar a fusace ya ke takawa jikinshi har tsuma yake, waige ya shiga
yi domin neman madoki domin mudin yace zai dake Nur da hannu tana iya mutuwa, ganin babu
wani abu da zai iya dokan Nur din dashi ya maida hankalishi wajen da suke tahowa, sai yanzun
ya lura da dattijuwar da ke binta a baya, itama sanye cikin Hijjabi har kasa, bayan ya kare mata
kallo ya ce "Mamma?" Adaidai lokacin da Mamma ke amsawa ya juya ya kalli yariyar da ke
gefenta, Helen ce tsaye badan fuskarta ba kaikace Nur ce tsaye, sosai ya zuba mata ido tsayon
lokaci sannan yai saurin saka hannun sa ya rike hijjabinta tare da fadin, "Wannan abin na Nurr
ne ko?"
Da ga Helen har Mamma sun yi mamakin jin sunan Nur a bakin Poul, Mamma ce tai saurin
girgiza kai tare da fadin "Banata bane, masallacin da mukaje jiya acan aka bamu."
Lumshe Ido Poul ya yi sannan ya jawo Helen ya kai hijjabin hancinshi ya shinshina, dagowa
yayi ya kalli Helen sannan ya cewa, "Na Nurr wanna, kenan gidan su ta kaiku?" Wannan karon
ma cikin sauri Mamma ta girgiza kai alokacin da Poul ya ke cewa acikin zuciyarshi, "Amman
zan nunawa yariyar nan ta yi kuskure mara kyau a rayuwarta, barinta da na ke tana shigowa
gidan nan shine ya bata damar dauke min uwata da kanwata? Bazan taba bari hakan ya
tabbata ba muddin Ina numfashi, saina koya mata hankali, da ma na lura da yariyar nan, akwai
tsata me yawa a idonta, ko ma meye zan aikata domin in ga Mamma tabar wannan addinin da
take kokarin jefa kanta acikin" zuwa can ya dago ya kalli Mamma cike da kwarin guiwa ya ce,
"Ina zakuje?" Daure fuska Mamma ta yi sosai sannan tace, "Kauye, Ina ce kace in dai muna yin
addinin musulunci sai dai mu barmaka gidanka?" Da sauri Poul ya dukar da kanshi kasa
sannan ya ce, "Na sake tunani, zaku iya zama abin ku" Cike da mamaki Mamma ta kalli Poul,
sanyin da taga yayi abin yai matukar daure mata kai, dan haka ta ce, Na gaji da zaman
wulakanci da na ke yi a gidan nan idan har kasan zaka cigaba da mini abin da kake gara na
koma kauye."
Lebensa na kasa Poul ya cize sanna ya ce, "Zan kiyaye." Karake maganar ya yi tare da amsan
akwatin dake hannun Helen sannan ya juya cikin gidan, Mamma da Helen wadda ayanzun ta
koma Zainab kallon juna suka yi sannan suka bi bayansh,i sai dai har yanzun Mamma ta kasa
gamsuwa da sanyin da ta ga jikin Poul din yayi.
******
Nur ce durkushe ta na wanke kayan makantarta bayan ta gama ta dauraye, bayan gidan ta nufa
domin shanyawa, hannunta ta daga sama da nufin shanya hijjabin islamiyyarta, cikin sauri ta
saki hijjabin ya fadi kasa, tare da waigen falin da ita daya ce tsaye a gurin, diriricewa ta yi gaba
daya tana kokarin fita hayyacinta, daker ta iya lalubo jarumta ta nufi windows din dakunnan
dake bayan gidan na su, ahankali take bin sautin har ta isa bakin window da sautin ke tashi,
wani dutse ta dauko tasa a gurin, sannan tahau kan dutsen ta leka, saidai labulen rufe ya ke
dan haka ta kasa kunne, tabass da ga nan sautin ke tashi, dan haka ta sauka akan dutsen a
guje ta nufi cikin gidan tare da kwalawa Mamy kira.
Saukowa a gado Mamy ta yi da sauri tana dafe da kanta dake sara mata tun safe, jin kiran