Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
bata fita sosai ta da ga kanta ta kalleshi, baki ne katon gaske, damtsen
hannunsa irin na masu da ga karfe, ga wani narkeken cross a wuyanshi, dauke kai ta yi da sauri
ta waiga bayanta da take jin motsi, dayan ta sake gani a bayan ta shima da cross dinne a
wuyansa, wannan ya tabbatar mata da su din ba musulmai bane, tafiya ta fara, ta na bin bayan
daya kamar yadda ta lura abinda da suke so kenan, acikin zuciyarta ta shiga Kiran sunayen
Allah.
Banda raba Ido babu abin da Nur ke yi, Cikin wani katun falo suka shiga, mutumin da ke zaune
ya daura kafa daya kan daya tabi da kallo, waya ya ke dannanwa har suka durkusar da ita a
gabanshi tare da cewa, "Gata" Da sauri ya dago kan shi ya kalleta tare da sauke kafar shi
kamar zai taketa. Ganin ya na kokarin sauke kafarshi tai saurin ja da baya, tare da dagowa ta kalleshi, "A fili ta
ce, Innalilahi wa Inna ilaihir raju'un" Ido hudu suka yi da Poul dake tsaye a gabanta ya na mata
kallo me cike da tsana, sunkuyar da kanta ta yi kasa tare da nemo dalilinsa na sawa a dauko
mishi ita, ko tantama ba ta yi akan su Mamma da Helen ne da suka musulunta, nan ta ke
hawaye ya fara zubo mata domin ta rasa abin yi, gaba daya jinta take a kidime.
Bata an kara ba ta ji an rike hijjabinta da karfe da alama shirin figeshi ya ke a jikinta, dan haka
ta mike da sauri tare da cikuikuye hijjabin a jikinta tana fadin, "Duk abin da zaka min kamin da
Hijjabina karka ciremin hijjabi."
Bece kala ba, ta bayanta ya miko hannun sa ya murde na ta duk biyun, cikin kankanin lokaci
ya cire Hijjabin yai jifa dashi, bayan ta tabbatar da ya rabata da Hijjabin ne ta fashe da kuka tare
da cewa, "Dan Allah ka bani hijjabina, ko kasheni zaka yi ka kasheni dashi a jikina." Tsaki ya ja
sannan ya koma gurin zaman sa ya zauna tare da cewa, "Idan na kashe ki ma ai ban huce ba,
aikin ku kenan hijjabi-hijjabi, can karshen naki zansa a yi fata fata dashi yanzunan, sai dai bakin
ciki yasa ki mutu da kanki, kamar yadda ni ma kika dasa min bakin cikin da zai yi saurin
hallakani."
"Babu ruwana, bani bace, su da kansu suka ka zabi hakan, ni ma daga sama na ji labarin."
Mikewa ya sake yi a karo na biyu ya fara zagaye Nur tare da fadin, Koma mene ne ke kika sani
wannan zai zama Jan kunne ne a gareki, dan da ga yau bazaki kara shiga gonata ba, ko ban
shata miki layi ba." "Wannan shine shata layin na ka ai, da ga yau bazan kara shiga gidan ka ba, dama Mamy ta
dade ta na gaya min irin wannan."
Ba irin wannan take gaya miki ba, dan na tabbatar ita kanta da ace ta taba yin tunani irin abin
da zai faru dake a yau zai iya faruwa ta dalin na da tuni ta rabaki da gidana, kamar yadda ni ma
da ace nasan irin abin da kika min zai faru da tuni na rabaki gidan Koda ace binneki zan yi da
ranki." "Karka lalatamini rayuwa ka kasheni kawai"
"Ko na kasheki ban huceba, gara ki rayu da kunar zuciya, kamar yadda ni ma zan rayu da
radadi acikin zuciyata."
"Allah bazai baka sa'a ba kan mugun nufinka akaina ba, Kuma Allah ya isa ciremin hijjabin da
ka yi..."
Tun kafin ta rufe baki ya wanketa da Marin me zafin gaske, cikin sauri Nur tasa hannunta ta
dafe gurin tare da runtse idonta, jin wann radadin Marin ya tuna mata zabar marin da Abdallah
yayi mata kwanaki, yau ga kwatankwacin shi. Bayan zafin ya lafa mata ta bude idonta tare da
kallon hannun da ta dafe kuncinta dashi, jini ta gani a hannun da haka ta Kara shafa kuncinta,
jini ne wadda ke fitowa daga hancinta, dan haka ta mike a lokacin da Poul ke cewa "Kuje da
ita."
Batare da wani bata lokaciba suka fara Jan Nur, ihu ta shiga kurmawa tare da cijewa, saidai
duk da haka Saida suka yi nasaran shiga da ita wani daki me dauke da gado, kara rudewa Nur
ta yi a lokacin da ta ga sun fara cire kayan dake jikin su, gaba daya su biyun suka cire, ya rage
da ga su sai gajeren wando, ganin su manya-manya ta kara firgicewa, kayan makarantar da ke
jikinta ta kalla riga da wando, kanta ta shafa dama hijjabi kawai ta sanya batare da ta daura
dankwali ba. Hankalinta da maida gurin tika tikan maza dake shirin dufarota hawaye na tsiyaya
a idonta take fadin, "Dan girma Allah ku yi hakuri, karku tabani, ko me kuke so mu je gurin
Abbamu ya baku, dan Allah karku tabani" ganin suna daf da ita ta tsuguna akasa ta kurma ihu
tare da sa hannunta ta kankame jikinta, sai dai duk da haka ji ta yi an dauktae cak, kamar an
dauki riga an yi jifa da ita zuwa gado, dan haka ta shiga fadin, "Allah karka basu dama, ka tai
makeni ya Rabbi, ya Allah ka kawo min agaji, dan darajan mazon Allah" cikin karaji take kiran
suna yin Allah da manzonsa, gani ta yi dayan ya rike kafafunta yayin da dayan ya kwanta
ajikinta yana kokarin fincike rigarta, duk da haka bakinta be mutuba, ihu kawai take tana Kiran
sunan Allah.
Duk ihun da Nur ta ke a kunnen Poul, har yanzun ya na zaune a falo kafa daya kan daya, a
wannan lokacin duk tabi ta dame zuciyarshi, ba ihun bane ke damun shi, Allah da Annabin da
take maimaitawa ne ke hanasa sukune, aduk lokacin da ta ambata sai gabanshi ya yi
mummunan faduwa, a hankali ya sauke kafarshi tare da mikewa da sauri, wannan lokacin yaran
nasa ne suke bashi haushi domin bega dalilin da zaisa su barta har tana magana ba, dakin ya
nufa da saurin sa, ganin shigowansa wadda ke rike da kafar Nur ya waiga ya kalleshi, cike da
tsawa Poul ya ce, "Mene ne haka? Wannan yar yariyar ce har zaku kasa make bakinta ku barta
taita mana surutu?"
"Oga duk ihun da za ta yi babu me jinta anan ai" Tsaki Poul ya ja tare da yi ma su alama da
hannu akan cewa su fita a dakin, cikin sauri wadda ya danne Nur ya sauka tare da daukan
kayanshi, shima dayan nasa ya dauka ya fici a dakin, tura kofar Poul ya yi sannan ya fara
takowa zuwa cikin dakin tare da balle butirin gaban rigarshi ya na fadin "Ki rufe min baki idan
kika sake magana saina zubar miki da hakora."
"Cikin muryanta data fara dashewa sabo da kuka ta ce, "Dan girma Allah ka taimakeni ka
barni in tafi agida za'aga na dade."
"Babu abin da ya dame ni" ya fada a lokacin da ya cire rigarshi ya fara kokarin cire agogon
shi.
"Addu'a Nur ta cigaba da yi afili, duk da cewa Muryanta ya fara dashewa Amman Yana jinta
dan haka alokacin da ya ke kokarin hawa gadon yake cewa, "Ki cigaba da kiran Allah har inzo
gurin in same ki, karki daina kiran Allah ki gani."
Gadon ya hau tare fincikar rigarta da alama yage rigar yake son yi bawai cireta ba, yana rike
da kafarta yake fincike rigar, tuni ta fara yagewa haka yayi ta farka rigar kaca kaca har har ya
ficiketa ajikinta; ya rage daga ita sai bra sai dogon waddon maka ranta, kallo ya bita dashi
sosai, har yanzun yana rike da kafarta har wannan lokacin bakinta be mutuba, duk wata addu'a
da tazo bakinta yi ta ke, tare da kokarin fincike kafarta, tana cikin wannan halin taji karan
barkewan dogon wandon dake jikinta, dan haka ta kara gigicewa tare da fita cikin hayyacinta,
alokacin da hankalinta ya dawo jikinta daker ta iya bude idonta, ganinta har yanzu acikin
wannan dakin ta furta "Innalilahi wa Inna ilaihir raju'un" jikinta ta kalla, ganinta tube tai saurin
jawo bargon ta rufe jikinta tare da waigawa tana kallon dakin kota wanni kusurwa, ganin babu
kowa a dakin ta yunkura da nufin tashCIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
PAGE 23-24
Ido hudu suka yi da Poul yana zaune ya kureta da Ido, cikin sauri ta sake kallon jikinta tare da
kara jawo barkon ta na rufe jikinta dashi.
Kallon shi ta kara yi har yanzun be cire idon shi a kanta ba, cikin sauri ta kalli kayan makarantar
ta dake barbarke akasa, a cikin zuciyarta ta shiga tunanin tare da sauraran yanayin jikinta, babu
wani canji baya ga makoronta da can cikin kirjinta dake mata zafi sosai, hankalinta ta mayar kan
Poul ta na mai mishi kallon tuhuma, saidai shi ta rasa gane kallon me ya ke mata. Mikewan shi
ya kara fadar mata da gaba, har yanzun dogon wando ne a cikinshi babu riga, rigar da ya cire
ajikinsa ya jeho mata sannan ya juya ya sake dauko wani dogon waddon sa ya sake jehowa
tare da fadin, "Kisa a mayar dake gida." Kallon kayan ta yi hawaye cike da idonta, sai dai bata
jin zata iya saka kayan sam, domin da gani nashi ne, zama ta yi a haka tsayon lokaci, bayan
kusan minti talatin ya turo kafar ya na sanye da manyan kaya na shadda kaikace cikakken
bahaushe ne, kallonta yayi sannan ya ce, "Me kike jira baki saka kayan ba?"
Tun kafin ya rufe baki tace, "Hijjabina zaka bani."
Kallonta yayi sama da kasa, har yanzun tana zaune a kan gado sannan ya juya ya fita batare
da ya ce komai ba. Be jimaba ya dawo tun daga bakin kofar ya jefeta da hijjabin sannan ya
zuba ha nunsa cikin aljihu yana binta da kallo.
Ta na daga zaune ta sanya hijjabin sannan ta ture bargon ta gyara hijjabin tare da juyawa ta
sauka agadon ta mike tsaye, har yanzu makoronta na mata zafi, shiko Poul ganin ta mike ya ce
"Kisa kayan ki fito falo ki same ni." Bin bayanshi ta yi da kallo, duk da cewa ta ji yace tazo ya
kaita gida bata wani ji farin ciki ba, domin bata gamsu cewa gidan zai kaitaba, duk da cewa bata
ji alamar yayi abin da yayii niyya da ita ba, koda ace gidan zai kaita bawani abin dadi bane
agaretadomin ya gana wulakantata bubu sutura ajikinta, kuma gashi yamma ta yi yanzu, dole
an nemeta har an gaji, wannan kawai take iya sakawa bayan haka bata hango mafita. Harta
taba kofar da zata fitar da ita daga cikin dakin ta ja ta tsaya, jimmm ta yi zuwa can ta juya babu
yadda ta iya dole ta saka rigar da ya bata, wandon ta dago tana kokarin sakawa wani irin
takaicine ya kamata wadda ya saka yin jifa da wandon, cikin kuka ta nufi bayin dake jikin dakin,
tawul din wanka ta dauko ta daura a kugunta sannan ta fito falon. Har wannan lokacin Poul ya
na tsaye a falon, gefensa gardawan mazan nan ne ke ta binta da kallo, sai dai tun kafin ta ksa
wurin ya sallame su suka fice, tsaye ta yi afalon ganin ya fita ta rofa masa baya, har suka fito
harabar gidan, bata wani tsaya kallon gidan ba, bayan motar ta nufa ta bude da hannunta ta
shige bayan motar ta zauna, wannan karon da kanshi ya ke Jan motar, tafe su ke hawaye na
cika idonta da tana matsewa suna tsiyayowa akan fuskarta, hannu tasa ta share hawayen
sannan ta dago a hankali ta kalleshi, toki ya ke hankalinsa kwance, can kasan makoshi ta ce
"Ina zaka kaini?" Nur ta yi tambayan tare da tsayar idonta waje guda hawaye na zubowa,
"Gida" Ya fada batare da ya waigo ba. Wannan karon cikin da ga murya ta ce, "Ka sauke ni a
nan ma ya Isa."
"Me yasa zan sauke ki anan bayan ba anan aka dauko ki ba?"
"Babu ruwanka da in da aka dauko ni, ni dai na ce ka saukeni anan."
Wannan karon be tanka mata ba cigaba yayi da tafiya batare da ya sake waigowa ba, zuwa
can Nur ta sake cewa, "Na ce ka saukeni a nan bana son komawa cikin unguwar nan har
abada"
Lumshe Ido yayi batare da ya waigoba, sannan ya ce, "Kofar gidan ku zan sauke ki."
"Banaso, Tun safe nabar gida, gashi yanzun har yamma ta yi ban koma ba, bansan me zance
ba idan na koma gida, sannan jikina babu kaya ta Yaya zan iya shiga gida a haka? ta yaya zan
bari su Mamy su ganni a haka, baza su fahimcini ba, ba ni da kalmar da zan gaya musu su
gane, ni rayuwata bata da amfani, dama kaaheni ka yi kawai"
"Ke! Ke! Dakata, me aka miki dahar kike cewa rayuwarki bata da amfani, kofar gidan ku zan
kaiki dan banga abin da aka miki ba, yariya dake sai ki dinga dagawa manya murya, waye dan
ki anan?"
"Ka cimin mutunci kai dinan Poul, kamin tsirara ta hanyar yage suturar dake jikina da karfin
tsiya, wallahi in sha Allahu Allah bazai barka ba sai Allah ya saka min bi izininlahi, tun aduniya
kafin mu je lahira ya gana maka azabar sa, idan kacika sunanka ka kasheni yau karka barni
darai, banza kawai wadda be san me ya ke ba. kuma idan har baka kasheni ba yau ka shiga
uku, kuskuren da zaka sake yi a rayuwarka shine barina a raye"
Wani irin kallo yayi mata sannan ya ce, "Ya isa ka, ina nan zan jira abin da zai biyo baya" Duk
da haka Nur tabar magana ba dan haka ya rabu da ita be sake kallon in da take ba.
Sosai ya ke jin zafin kalaman ta, saidai ya kasa tanka mata ko yi mata tsawa akan maganar
tata, tukin sa kawai ya ke ko sau daya be waigo ya kalletaba, ya na jinta tana ta manganganu
wani ya jiyota wani bayajin me take cewaba, dalilin muryanta da baya fita sosai, duk da cewa
wani baji yake ba sosai ya kosa ya sauketa domin gaba daya tun da ya kwanta jikinta yaki jinshi
cikin rashin nutsuwa me tsanani, kuma har yanzun nutsuwa taki zuwwar masa dan haka ya
kosa sosai ya sauketa, misalin karfe hudu da rabi suka shigo cikin layin su ta saman layin ya
biyo dalilin sauke Nur da zaiyi kofar gidan su, wannan karon ma sake daga ga murya ta yi ta ce,
"Ka sauke ni a anan toh.
Lumshe Ido yayi batare da ya tankaba Kuma babu alamar tsayawa a tattare da shi, dan haka
ta sake cewa, dan Allah na ce ka saukeni a nan karka kaini kofar gidanmu, kabarni anan in
nemi in da zani bazan iya shiga gida ba a haka."
Tamkar bayajinta haka yayi dan haka Nur ta tsananta Kukanta tare da fadin "Allah ka kawo
min mafita, Allah ka taimakeni, ta na addu'ar tana tunani cikin ranta ko meye dalilin sa da zai
kaini har gida ahaka ko tsoron iayeyena bayaji" tuna yadda ya hankadata waccen karon gaban
duk yan gidan su yasata ta nufi kofar motar iya karfinta take kokarin budewa saidai motar kulle
take. Ganin motar a kulle ta daga kai ta hangi kofar gidan su, da alama baki aka yi acikin gidan,
dan akwai motoci manya manya guda biyu a kofar, da Kuma maza da mata awurin yayin da
wasu ke shiga motar sai dai bata iya gane ko su wanene, nesa da gidan Poul ya tsaya, dalilin
ganin motocin da yayi a kofar gidan, waigowa yayi kadan ya ce "Sauka."
Nur kuwa idonta ta shiga rabawa domin son sanin su waye suke kokarin shiga gidan su
yanzu, sai dai har suka shiga bata gane kowa ba, motar farkon ce tayo kwana, yayin da ta
biyun ta miki layin, a daidai wannan lokacin Poul ya sako ya bude motar, saurin ficewa a motar
ta yi tare da tsayawa wurin, kokarin ta domin ganin motar nan ta wuce wadda ke ciki be
gantaba, saidai motar Sam taki wucewa har Poul ya zagaya ya shiga ya fiki motar sa a daidai
lokacin da motar ta gama yin kawana ta fara tahowa cak motar ta tsaya, Nur ko kokarin boye
fuskarta take ta hanyar durkusar da kanta, kafar mace ta gani fara sol ta fito daga motar, ko
tantama babu wannan kafar Momy ce, dan haka ta dago kanta da sauri alokacin da Jamal ya ke
saukowa da ga motar cikin fada ya ke fadin "Ina kikeje?" Jamil ne yayo kanta shima cikin fada
ya ke cewa "Waye wancen ya sauke ki a mota?" Itako Ummy cikin sauri ta rungume Nur ajikinta
ta na kokarin runtse idonta ta ji gabanta yayi mugun faduwa dalilin jin jikinta kamar babu kayan
kirki, hannu tasa ta bayanta ta shafa da kyau bra kawai take iya jiyowa dan haka ta dago ta kalli
Nur, ganin fuskarta a kunbure ta fara janta zuwa mota, Jamal da Jamil kuwa basu bar Maimaita
tambayan da su ke mata ba, Momy da Nur ne zaune a bayan motar, kallo take mata me cike da
tuhuma zuwa can tace Nur garin yaya babu kaya a jikinki? Jin wannan