Ciwon Ya Mace Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   1 / 25

1 to 3K   out of 73.1K words

CIWON 'YA MACE

By
Fadila Lamido

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

GARGADI
Aguji daukan Labarin nan a daurashi a kowacce irin kafa batare da iziniba.

PAGE 1-2

BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM.


Dumin ruwan hawayen da ya sauka a kumatunta shi ya dawo da ita cikin hayyacinta, har ma ta
samu damar sa hanunta ta share hawaye. Kodayaushe cikin yaba tarbiyan gidansu ta ke, duk
irin tsaurara tsaron gidansu ba ta kallon shi a matsayin takura, asali ma sai hakan ya ke zamar
mata abin alfahari. Ajiyan zuciya ta yi mai karfi, sannan ta ci gaba tuna lokacin da ta yi ta ba wa Rahma damar
sanar da ita duk wani zance komai muninsa da dacinsa.
Hawaye ta sa ke sharewa a karo na biyu, ta na me tuna furucin ta ga Rahma, "Zaman tare be
ce haka ba Rahma. Domin ni duk abin da zan ji an fada a kan ki da 'yan gidan ku sai na fada mi
ki."
"Yanzu me ki ka ga an yi ban fada miki ba? Ni ma din ai haka ne, babu wani abun da zan boye
miki."
"Na gani a cikin kwayar idaniyarku wallahi. Na fa dago na ga irin kallon da ku ke mini, idan su
za su mini haka bai da ce ace hardake ba. Amma ba komai."
Yunkurawa ta yi da nufin mikewa Rahma ta yi saurin riko ta ta na cewa, "Shikenan na ji, da ga
yanzu komai na ji zan dinga fada miki. Amma karkiji haushina." Cikin sauri ta sa hannunta ta
dafe kumatunta tare da runtse idonta ta na me jin zafi har cikin tsakiyar kan ta, dalilin tuna marin
da ya zazzabga mata daren jiya. Ji take kamar ta na jin a zabar marin har yanzu, dan haka hawaye su ka zobo mata.
Hannu ta mika ta share, sannan ta yi saurin mikewa cikin yanayi irin na mai tunani, komawa ta
yi ta jingina bayanta da bango tare da kara yin zurfi cikin tunani, zuwa can ta shiga fadi afili,
"Bansan yadda zan yi ba ne, domin ya na sama da ni, sosai na ke jin bakin cikin marin nan da
yayi mini, a can baya ina amsan kowanni irin hukunci da ga gareshi, banajin zafi sam, saidai ma
abin ya zamar min abin alfahari. Me yasa wannan karon ya sauya? Jiya da safe da hannun sa
ya miko mini sakon Mamy, fuskar sa cike da walwala, zuwa dare komai ya sauya, saidai bana
bakin cikin sauyarwa ta shi, domin yadda ya ke ji na a ranshi inajin shi fiye da haka a kasan
zuciyata, domin da ina da dama ba marin biyu kawai zan mishi ba, saina mishi doka da ko lada
aka bashi bazai iya mikewa ba, amman Kash sai daman yazo a hannun shi." Nisawa ta yi a
daidai lokacin da ta ji kiran da Mamy ta ke kwala ma ta, cikin yar karamar muryanta da bata fita

sosai ta amsa, sannan ta fice ba tare da walwala ba.
"Nur! Lokacin fa yana kurewa, kizo karki makara."
"Mamy ni gaskiya a canza min makaranta." Wani irin kallo Mimy ta mata da mamaki akan
fuskarta, sannan ta ce "Lallai Nur kina da aiki, idan an canza miki makarantar kofar gida ma zaki
daina fita ne? Ko kuwa jama'ar unguwan ma zakibar haduwa da su ne?
Shirun da taga Nur ta yi yasa taci gaba da cewa "Bana son irin wannan, maza kizo ki wuce."
Cikin dakin ta juya batare da ta ce komai ba, a cikin kankanin lokaci ta fito fuskarta babu
walwala.
Kallon ta Mamy ta sake yi a karo na biyu sannan ta ce "To ki saki ran mana, me zaisa ki
takurawa zuciyarki bayan ke ce auta mowar 'ya'ya" Murmushi ne ya subuce mata, duk yadda
taso ta daure ta kasa, dariya ta yi kadan sannan ta hade fuska tare da cewa "Na tafi"
"Adawo lafiya Allah ya tsare. Kuma daga yanzu sai ki dinga kiyaye bakin ki, shi mai tarkon
tsuntsaye baya ɗaga kara. Kome zakiji karki tanka."
Jin furucin Mamy ya kara tada hankalinta, cike da bacin rai tabar gidan.
Bayan ta dauki hanyar ma tafe take tana waiwayen bayanta har ta kawo kofar wani
dandasheshen gida, duk unguwar gidan ne ya haska layin sabo da kyan sa da tsarin shi,
karamar kofar da ke jikin get din gidan ta nufa, kai tsaye ta tura kofar ta shiga, mai gadin gidan
ta gaida, sannan ta wuce ciki, a harabar gidan ta tsaya cikin daga murya tace, "Helen!" Batare
data rufe baki ba wata buduwar yariya ta fito yar kimanin shekara goma sha 16. Baka ce
amman ba can ba, kyakyawa ce sosai, uniform ne a jikinta riga da siket daidai guiwa, kanta
babu dankwali yasha kananan kitsu, hannu suka sha da Nur da ke tsaye itama cikin uniform din
ta ke, saidai akwai banbanci domin ita Nur siket dinta ya wuce guiwa, kuma bayan dankwalin
dake kanta akwai dan karamin hijjabi, bayan sun sha hannu da Helen su ka juya suka fice a
gidan.
Da alama gaba dayan su cikin damuwa su ke, domin gaba dayan su tafe suke suna tunani,
suna daf da barin layin wata zungureriyar mota da ta fito da ga bayan su ta faka a gaban su.
Tun kafin sukai ga inda motar ta faka Helen ta ce, "Poul ne"
Kallon motar Nur ta yi domin sai a yanzun ta dan ji nutsuwa tazo mata tun fitowanta gida, ita
ko Helen da saurin ta ta karasa gaban motar, lokacin da Nur ta iso gurin yayi daidai da lokacin
da yake mikawa Helen kudi. Kallonshi Nur ta yi ya na zaune a mazaunin driver, kyakyawa ne na
gaske, domin sabo da kyanshi baka iya yi masa kallo daya ka cire Ido, sai dai akwai tarin jin kai
tsiya a tattare dashi. Shigarshi akodayaushe kamar ta cikekken bahaushe, daker Nur ta iya
dauke idon ta a kanshi badan ta gaji da kallonshiba sai dan kar ya fahimci tana kallonshi. Kasa
ta yi da murya sannan ta ce ta ce "Ina kwana? " Kawar da kai ta yi tare da runtse ido, sai dai
harta bude idon be tankataba. Duk cewa Tasan yaji sarai amman be amsa ba. Bata ji mamakiba
dan tun da ta ke gaidashi be ta ba amsawa ba bare ya dago idon sa ya dobe ta, saidai hakan
be taba damun ta ba, kuma bata taba jin kyashin gaidashi ba aduk lokacin da zata ganshi.
Wajen ta bari bayan ta kara gaba ta tsaye jiran Helen.
Wucewan motar ya sa ta waigowa ta kalli Helen, ita kanta fuskanta babu walwala, dan haka ta
ce "Helen Duk da kyautan kudin da aka baki banga kinji dadi ba, kuma da alama ya bakine dan
ranki yayi fari tunda har ya biyoki hanya ya baki, ni ai dauka nake ko ke baya iya gane ki, dan
bantaba ganin ya kalleki ba bare yayi magana da ke, ni fa wallahi ada da farko na dauka kurma
ne, sai ranar da nazo na ji yana balbala balaki a cikin gida, kuma har yau bantaba jin sa yana

maganar arziki ba, idan har zakaji muryansa to fadane kawai."
Murmusawa Helen ta yi tare da cewa, "Ko maganar arzikin ma yake haka zakijita kamar yaki,
maganar sa babu yawa kuma babu dadi" Itama Nur dariya ta yi sannan su ka ci gaba da tafiya,
bayan sunyi tafiya me tsawo Nur ta sake kallon Helen, rashin kwanciyar hankali karara akan
fuskanta dan haka ta zungureta tare da cewa, "Helen wai me ke damun ki ne haka?" "Badan mun yi nisa da gida ba da na koma na bawa Mama wannan kudin"
Lumshe Ido Nur ta yi, domin dama tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, cigaba ta yi da tafiya tana
cewa, "Ki boye idan kin koma sai ki bata." wannan karon Helen ba ta ce komai ba, tun da ga
lokacin har suka isa makarantar babu me ma wani magana.
Haka har suka tashi daga ita har Helen din basu da wani walwala, wadda duk wadda ya san
su yana iya fahimtan hakan.
Helen ce ta fara shigewa gida sannan Nur ta isa na su gidan. Tana saka kafa a falon ta hangi
shi zaune ya daura kafa daya kan daya; tare da ware hannun shi duk biyun a saman kujira.
Tsoro ne ya so dirar mata, saidai wata zuciyar nacewa karki sake kiji tsoron sa, dan haka ta
dake ta shiga kwalawa Mamy kira. Har sau uku ta kira bata amsa ba dan haka ta tabbatarwa
kanta cewa Mamy bata cikin gida nan. Duk kokarin ta wajen ganin ta dake saida gabanta ya
shiga faduwa, daki ta nufa saidai tana daf da shiga dakin ta ji ya kirayi sunan ta cikin
kausarsiyar murya, "Ke Nur!"
Juyowa tayi ta na kallon shi, Ido cikin Ido suke kallon Juna tsawon lokaci, zuwa can ya fesar
da numfashi cikin sanyin murya ya ce "Idan Mamy ta dawo ki tabbatar kin gyara abin da kika
bata, idan ba haka ba kuwa zaman gidanan zai gagare ki.
Har ya gama zancen bata cire idonta akan nashi ba, ganin haka yasa shi kara kafeta da ido
"Au kin tsaya ne kin kafe ni da ido? Na lura baki san waye ni ba, ni mugu ne ki bar gani na
haka, Kuma karki yi abin da na gaya din ki gani. Me yasa zaki min haka? Nasan har yanzun
zaki iya tuna lokacin da nake goya ki a bayan nan nawa na kaiki kitso. Idan an gama haka zan
goyoki har mu dawo gida kina min kuka, rigana haka ya ke baci da hawaye da majinar ki, har
yanzun ina mamakin ta yadda akayi irin wannan maganar ya fito daga bakin ki, basan baki da
kunya ba sai jiya. Ashe ke din fitsarriya ce, ni sa'an kine ko nataba wasa dake ne?"
Tunda ya fara magana a wannan karon tai kasa da kanta, bata sake dagowa ba har yazun da
yake mata tambayan, tana jin yadda yake kallon ta tsayon lokaci,acikin ranta take jin kamar
bata kauta ba duk da cewa ba shirri ta mishiba sai dan girmanshi da mutuncin sa da take gani,
muryan shi ta ji ya ci gaba da cewa "Ina jin ki? Me na miki kika tsane ni?" Can kasa ta yi da murya sannan ta ce "Ni ban tsane ka ba kafin jiya"
Kafar sa da ya daura kan daya ya sauke, sannan ya mike tsaye ya fara takowa inda ta ke,
tsoro ne ke son mamaye Nur, saidai tana ta kokarin ta na jawo ma zuciyarta dakiya, a gabanta
ya tsaya sannan ya ce "Kafin jiya baki tsaneni ba? A cikin mu waye zai sha wuya da daya ya
tsana daya?" Kafada ya daga batare da ya jira amsantaba ya ci gaba da cewa Wannan
matsalar ki ce, amman ina son in san dalilin da ya sa kika min haka?"
Kasa ta kara yi da kanta yayin da jikinta ya fara rawa. Tuna azabar marin da ya yan-yan ka
mata a jiya, a kuma gaban Mamy, yau Kuma gashi babu Mamy daga shi sai ita. Ganin yana
matsowa ta fara ja da baya cikin muryan mai Shirin yin kuka ta ce "Yaya Abdallah karka mare
ni, hannun ka akwai zafi." "Haba? Ashe akwai zafi? To kinajina? Da zaran Mamy ta dawo ki gyara abin da kika bata

jiya."
Kallo ya bita shi tsayon lokaci bata ce komai ba illa bugun zuciyarta da ke tsananta bugu,
"Zaki yi abun da na ce ko baza ki yi ba?"
Mutsi ta fara da bakinta tsayon lokaci amman ta gaza furta komi, kula da hakan da yayi ya sa
shi cewa "ina jin ki?"
"Yaya Abdallah cewa na yi Kaine ya kamata ka gyara ai"
Lumshe Ido ya yi zuwa can ya bude sannan ya ce "Shikenan, kijira abin da zai biyu baya, da
kanki zaki gane maida ruwan rijiya ba barna ba ne, Kuma ke kin yi kadan ki ja dani, ki shirya
ganin azaba, ukuba, zalinci, daga gare ni"
Zalinci Kuma? Nur ta yi tambayan tana me bude idonta a kanshi. Sosai take mamakin
sauyarshi lokaci guda. Ayanzun gani take kamar wani ne aka sako ba waccen wadda ta sani a
baya ba. Katseta yayi da cewa "Tambaya ki ke yi?"
Yadda ya zaro ido ya sata lumshe ido sannan ta ce "Yunwa nake ji zanje inci abinci."
Hannunsa ya mika ya dungure mata goshi, kasancewar ta yi dafda bango hakan ya haddasa
mata kumewa da keya, koda ya ga kanta ya hade da bango ta baya be hanashi kara dannan
goshin nata ba, yana kara gurza mata kai da jikin bango, kokarin rike hannun shi ta ke amman
ya ki ba ta daman yin hakan. Yana kara dannan kannata yana fadin, "Kin yi kadan ki dagula min
lissafi, idan har kina son ki zauna lafiya a gidan nan kibini sauda kafa, ki kuma gaggauta yin
abun da na fada miki, idan ba haka saina bata miki jikin ki da tabban duka, kuma wallahi saina
saki kinyi nadamar zuwan ki duniya, sai kin fada da bakin ki ince ina ma ba'a haliccekiba."
"Wayyo Yaya Abdallah ka sa ke min wuya na zan mutu."
Kara danna kannata ya yi yana fadin, Da na yi farin ciki, me ake da irin ki, ki mutu mana, bana
son in karajin maganar ki anan gurin. Hannun sa ya sauke a goshinta sannan ya d'ana mata shi
a baki, ya bada sautin d'ass, cikin sauri ta runtse idonta, zafin da taji har cikin tsakiyar kwanyan
kanta, har yanzun bata iya dawo da kanta ba, saboda wuyanta da ya kage, dan haka tai saurin
sa hannunta ta dafe bakin tare da son taji ko hakorin wanni bangaren ne ya fita.
Hannun da ta dafe bakin yai saurin rikewa ya juyashi zuwa bayanta, sannan ya kamo dayan
ya juya shi ya bada sautin kas, a wannan karon ta gama barma zuciyarta ta karye kawai.
Hakorinta kuma ya fita, ga wuyanta da ya makale, zufane kawai ke yanko mata ko ta ina, bata
sake wani yunkuri ba domin zuwa wannan lokacin sama sama ta ke jiyo azabar da ya ke gana
mata. Yana murdeta yana aika mata tambayan zakiyi abinda nace ko bazakiyi ba, saidai ita ba
sosai take jiyoshi ba.
Zuwa can taji yayi saurin sakin ta, galabaita da rashin karfin jiki yasata zubewa a kasa, cak ta
ji ya dagata a tunaninta jifa zai da ita, amman ga mamakinta sai tajita kwance saman lallausan
katifa.

CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

PAGE 3-4

Muryarsa taji a saman kanta yana cewa, "Saura naga kafarki a falo"
Lumshe ido ta yi tana me jin kamar a wannan lokacin ne jinin jikinta ke sakowa, karan kofa ta
ji sannan ta shiga jin muryan Mamy tana kwada mata kira, har sau uku ta ji ta kirata da ganan
kuma ba ta sake jin kiran ba, bazata iya tantance iya adadin da ta dauka a wurin ba, bayan wani
tsayon lokaci ta fara jiyo muryar mutanan gidan a falo, kanta dake mata nauyi ta dafe, daker ta
iya daurewa ta tashi zaune, duk da cewa duk wuraren da ya yi mata mugunta radadi suke mata.
Runtse idonta ta yi sannan ta mike tsaye, tun da ta mike bata kara sanin me take ciki ba, sai-dai
jinta kawai ta yi rike gam a hannun mutum. Waigawa ta yi domin tasan waye ya ke rike da ita,
Mamy ta gani tsaye, saidai tun kafin ta kai ga karantar fuskar Mamy ta jiyo muryar Abban su
cikin fada sosai ya na cewa, "Mai ya yi zafi haka? Kina hauka ne? Ko tarbiyar da mu ka baki
kenan?"
Jin irin furucin Abba yasa ta waiga ta kalli falon, fasassun kwalabe ta ci karo dashi barbaje
afalon, yayin da Abba da Yaya Bashir suke binta da kallon mamaki, da ga can gefe ta hangi
Yaya Abdallah zaune babu riga ajikin shi, yana ta duba damtsen hannunshi yayin da fuskarshi
ke bayyanar da yana cikin tsananin bacin rai, muryan Abba ta sake ji yana cewa "Da ke na ke
magana, wanne irin rashin d'a a ne wannan?"
Nan danan Nur ta kara rikecewa, cikin yanayi mai cike da nadama ta ce "Abba ka yi hakuri,
bansan lokacin da nafito ba, a nan gurin kawai na ganni."
Kallon sosai Abban ya kare mata, sannan ya ce, "Ko da wasa kada irin wannan ya sake
faruwa." hawayen da ya zubo mata tasa hannun ta share sannan ta ce "Toh Abba"
Hannu Abba ya daga mata alamar dakatarwa tare da cewa "Zo ki tsuguna ki bashi hakuri"
"Basai ta bashi hakuri ba domin nasan da abun da yai mata"

1 / 25