Ciwon Ya Mace Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   20 / 25

57K to 60K   out of 73.1K words

tabbatar eh lallai
karatun take so ganin bata taba kawo wani gida da sunan saurayiba, haka kuma bata da waya
hakan be taba damunta ba, a yanzun islmiya kawai take zuwa, ita ko Bilikisu cikin ta ya fito
sosai yayi girma, sai dai har yanzun bata da walwala ko waya suke da Abdallah hiran tasha
banban da ta da.
*****
"Na rasa dalilin ki na kin yiwa Abdallah magana ya turo kudi yariyar nan ta fara zuwa awo, abin
da fa baka son a maka karkawa dan wani, yanzun in da yarmu ce ai bazamu so ace ciki har
yana dhirin shiga wata na takwas ba batare da an san lafiyarsa ba" Cikin rashin walwala Aunty
Saratu tace, "Amman na ce miki kiyiwa Bashir magana ai yazo ya kaita, na mishi magana yace
wai mijinta bai sanar dashiba dan haka bazashiba, in da kece kikamai magana ai bazai baki
wannan amsan ba"
Wanni irin kallo Mamy taiwa Aunty sannan tace, "Ai ni bazance ya kaitaba haka kurumba, dole
sai an bashi kudi tun da ba hidimarsa bace, ai be dace kawai ace yayi hidimar da ba tashiba, ko
Abban su da nace ko zai bada cewa yayi yayi bashi da kudi sabo da yayi hidimar makarantar
Nur bashi" "To a yiwa Baffa magana mana" Aunty fada tana kallon Mamy, saida Mamy ta karewa Aunty
kallo sannan tace, "Ikon Allah, to waishi Abdallah cewa yayi bashi da kudinne? Nifa banson
iskanci, zan kirashi naci mishi mutunci wallahi"
"A'a Karki kirashi, ki bari zan kirashi" Aunty ta fada tare da mikewa ta nufi daki, Nur dake gafe
Mamy tabi da kallo, ganin inda take huci tace "Mamy kiyi hakuri" Batare da tace komaiba ta
mike ta shige daki, dan haka itama Nur ta mike ta koma daki inda ta samu Bilikisu na waya da

Abdallah, juyowa ta yi domin ta basu waje, wannan karon tana fitowa dakin autny ta nufa, saidai
tana shiga ta samu anuty tana kaiwa da kawowa adakin, ganin shigowan Nur tai saurin daukan
wayarta ta danna sannan tasa a kunnenta, zuwa can ya sauke tare da fadin "Busy" Nur ce tace
"Yaya Abdallah yana waya da Aunty Bilikisu" Waigowa Aunty Saratu ta yi domin sai a yanzun ta
gane ashe afili tai maganar ba azuciya ba, zama Aunty ta yi yayin da yanayinta ke nuna tana
cikin damuwa, zuwa can wayarta ta fara kara dan haka ta kalli Nur tare da cewa Nur bani waje
zanyi waya, mikewa Nur ta yi ta fita tare da jawo mata kofar, haka kawai taji tana son sanin mai
aunty zata ce da Abdallah, har tayi nisa da kofar ta dawo a hankali ta tsaya, yayin da ta jiyo
ayunty na cewa "Abdallah kwanaki da nai maka magana naga kamar kana nuna bakasan
Bilkisu nada ciki ba?" Kara kasa Kunne Nur ta yi zuwa can taji ta sake cewa "Eh mana, tun
lokacin datai rashin lafiya nan" A'a dakata mana Abdallah abin ba tashin hankali bane yarintane,
nima harda laifina danasani tun lokacin na gaya maka tunda Bashir suna dawowa ni ya bawa
sakamakon..." Shiru ta sake yi tsayon lokaci, da alama katseta yayi, zuwa can tace "Innalilahi
wa innalaihir raju'un, Abdallah ka rufa mana asiri, tsaya kaji, ai shine nace ka saurareni"
daganan Nur Bata sake jin komai ba dan haka da saurin tabar wajen, afalon ta zauna tai ajiyan
zuciya, nan danan taji wani irin tashin hankali ya dirar mata, bata gama dawowa cikin hankalinta
ba taga wucewar Aunty arikice zuwa dakin Mamy, wannan lokacin bata da kwarin bin bayanta
dan haka ta mike ta nufi dakinsu, Bilikisu ta gani rike da waya sai Kara take Amma taki dauka,
cike da damuwa Nur tace Aunty ana kiranki awaya"
Cikin wani irin yanayi tace "Bazan iya daukaba Nur, domin gabana faduwa yake haka kawai."
Leka wayar Nur ta yi tare da fadin, "Yaya Abdallah ne fa?" "Eh na gani gabana faduwa yake Nur
yanzu maka gama waya dashi" Bilkisu ta fada tare da kwantawa a gefen wayar idonta cike taf
da hawaye. Haka Abdallah yaita kiran wayar Bilikisu har sau Babu adadi taki dauka, kwanciya ta yi cike
da damuwa, hakama Nur take kiyasta abin da ke shirin faruwa cikin zuciyarta, saidai tana
korewa domin ko a mafarki batason hakan ya kasance, haka gidan ya wani Babu wani walwala,
adaren ranar Aunty Saratu ta shigo dakin Nur, bayan sun mata sannu ta ce da Nur ta jirasu a
waje zasuyi magana da Bilikisu, mikewa ta yi ta fita, sai bayan kusan awa guda sannan Aunty ta
fito, lokacin da Nur ta koma dakin samun Bilikisu ta yi Cikin kuka sosai, dan haka ta zauna a
takure, daren ranar cikinsu babu wadda ya runtsa, lokaci bayan lokaci Nur na jiyo ajiyan zuciyar
da Bilkisu take yi, yayin da hakan ke jefa Nur cikin damuwa, tare da kara yin nisa da tunaninta
dan haka bacci ya gagareta saidai ta juya ta kalli Bilkisu sannan ta hadiyi yawo saboda
makogoronta dake bushewa, abin da take tunanin yana shirin faruwa take ayyanawa akanta
dan haka damuwarta gaba yake karawa ba baya, washegari bayan Nur ta gama shirin islamiyya
ta fito domin yiwa su Mamy sallama, babu kowa acikin gidan dan haka ta nufi falon Abba,
tukafin ta ksa taji muryan Baffah na cewa, "To ai wata takwas kenan da auran, wannan kawai so
yake ya jawo mana kananan maganganu, sai ya bari ta haihu kafin yace wani abu, ai yanzun
dama cikin be isa haihuwaba ko?" Muryan Abba taji yace "To ai shi cewa yayi ma gaba daya be
kusanceta ba"
"Innalilahi wa innalaihir raju'un" Baffa ya fada yayin da taji Muryan Yaya Bashir yana cewa
"Ba yace sati biyu ya rage ya dawo ba, ni inaganin a bari ya dawo" Adaidai wannan lokacin Nur
taji kamar motsi a bayanta, dan haka ta karasa tare da sallama, amsan sallama suka yi cikin
sakin fuska har ta gaidasu ta yi musu sallama bataji an cigaba da maganar ba, bayan ta dawo

gidan ma shiru tajishi, Bilikisu kuwa cikin tsananin tashin hankali ta sameta, kuma tana kula har
yamma Yaya Abdallah be Kira Bilikisu cikin waya ba kamar yadda suka saba, a daren ranar Nur
na zaune adakinsu wayar Bilikisu ta dauka da Nufin Kiran Poul domin jiya Bata samu sunyi
waya ba, number ta saka tana kokarin kira taji muryan Kaka kamar daga sama, cikin daga
murya take cewa, "Ina take tazo ta tafi gidan iyayenta, bazamu dauki kazanta da ba namu ba,
yau na tabbatar da mutanen gidan nan basa kyaunar Abdallah, yariyar tashigo gidanshi da ciki
kuce Wai yayi shiru? To idan shi kun Isa dashi ni baku isa daniba" a firgice Aunty Bilkisu ta mike
tsaye cikin tsananin rudewa, ganin haka Nur ma ta mike tare da ajiye wayar hannunta, tuna irin
masifar da Kaka tai mata kwanaki akan Abdallah yasa tai saurin nunawa Bilkisu bayi tace
"Kisha Bilikisu" batai musuba ta shige ciki yayin da Nur ta kulle bayan ta cire key jikin kofar
sannan ta koma gadon ta kwanta, batajimaba taji an turo kofar, Kaka ce su Mamy na bayanta
suna Bata hakuri, Amman sai masifa take yi, neme nema ta fara adakin tare da cewa "Ina
tantiriyar take?"
Cikn nuna halin ko in kula Nur tace "Bata muku sallama ba? Yanzun Babanta yazon ya
dauketa, ajiyan zuciya Kaka tayi tare da cewa "Yafi masu su je ce su karata, ashe sunsan yarsu
lalatacciya ce suka lika mishi, Allah ya Isa tsakaninmu dasu, wato badan Allah ya dubi Abdallah
ba dan wani zamu ma bauta acikin gidan nan, yanzun sai ku kara tabbatar da cewa gemon nan
nashi bana banza bane, juyawa tayi kansu Mamy ta rufesu da fada ta inda take shiga batanan
take fitaba, sannan ta fice adakin tana cigaba da tsinewa Bilikisu da iyayenta,, bin bayanta
Many ta yi, Itako Nur suna fita ta bude Bilikisu cikin matsancin damuwa take zubar da hawaye,
wannan karon harda shashshekar kuka ahaka su Mamy suka dawo suka sameta, lallashin
Bilkisu suka kayi tare da kara kwantar mata da hankali, suna nuna mata rikicin tsofa ke damun
Kaka amman ta bari Abdallah ya dawo za'a samu mafita cikin sauki, saidai duk kokarinsu nason
su kwantar mata da hankali be gamsar da Bilkisu ba domin ko bayan fitansu kuka taita yi, Nur
ma tun fitan Kaka take share hawayen tausayin Bilikisu domin idan har Abdallah yace cikin ba
banshi bane to na waye? Juyawa ta yi ta kalli Bilkisu dake matsancin kuka, sam bata ta rawan
kai ko kadan, tunda Abdallah yabarta agidan kuwa za'a iya kirga fitan da ta taba yi Kuma duk
inda zasu tare suke zuwa, bata da rawankai ga kirkin dake gareta, kuka Nur take tsawon lokaci,
zuwa can ta saurara tare da kallon Bilikisu tace "Ki yi hakuri ki daina kuka"
Kara rushewa ta yi da kuka tare da cewa "Ta Yaya zan daina kuka Nur? Ina mai bakin cikin
iyayena suji wannan mummunan labarin, ina rokon Allah ya dauki raina kafin muyi ido biyu dasu
ina cikin wannan halin, Nur Babana, ina tausayin shi, bansan me zanyi ba, narasa in da
zansaka raina Nur, bani da bakin da zan wanke kaina, amman ni ba yar isa bace, sadai ba abin
da na sani da zan fada ya wankeni, Nur zo ki taba kirjina kiji yadda yake yi, Nur bayan bugawa
da yake inajin kamar zaiyi tsalle ya fito."
Kara fashe Nur tayi da kuka, haka suka raba dare suna abu daya, kafin safe gaba daya
idonsu yayi luhu luhu ita da Bilikisu gaba daya, ciwon Kai ya hana Nur zuwa makaranta, halin
da Namy da Aunty suga Nur aciki be basu Mamaki ba, domin suma cikin damuwa suke, tunda
ga ranar abincima saidai adancishi fan dole acikin gidan, Nur ko har tafi Bilkisu ramewa sabo da
ta saka damuwar a ranta duk da cewa Bilkisu Koda Yaushe cikin kuka take Nur kuwa tsabar
tunane tunen da nemo mafita tasa a azuciya dan haka duk ta fige, a daddafe aka cika sati biyun
da Abdallah yace zai dawo, be dawo a ranar ba sai Washegari da tsakar rana, Bashir ne ya
daukoshi kasancewar gidan babu yara masu oyayoto basusan da shigowanshi ba Saida

sukajiyo Muryanshi shida Bashir afalo, mikewa Nur ta yi ta fara kokarin fitowa domin gani take
Yana dawowa komai zai warware, tana fitowa suka yi Ido Biyu dashi Yana zaune yayi wani irin
fari tare da tara kasumba fiye da baya, kananan kaya ne ajikinshi dan haka sosai taga ya
canza, kallo daya ya mata ya kauda kai, gefen Yaya Bashir Nur ta Isa sannan tace "Sannu da
zuwa Yaya Abdallah" kanshi ya juyar wani gefen batare daya amsa ba, har sau biyu Nur ta Kara
mishi asannu da zuwa be amsa ba, dan haka ta juya ta koma daki, Mamy na lura dashi saidai
damuwan dake gabanta ya dame wannan, dan haka batabi takai ba, abincishi yaci sannan suka
fita tare da Bashir, Misalin 8 na dare yana kwance a dakinshi na gidan Mamy Abba ya kirashi
cikin waya, bayan dauka yace yazo falo suna jiranshi, mikewa yayi ya fito anan ya cika da
mamaki ganin falon cike da mutane ciki har da Baban Bilkisu da kanninsa, zama yayi akasa
wannan karon jikinshi yayi sanyi sosai, Baffa ne yace "To Abdallah mun hadu ne anan dominku
ku biyu kaida Matarka, ga iyayenka anan, ga nata, sabo da muna son mu tabbatar da adalci,
tun kana can kace Bilkisu ta tafi gida mukuma munga hakan ba daidai bane, dan mun
tambayeta tace ciki naka ne, to yanzun gata gaka ga Kuma iyayenta ga naka, kace ba naka
bane; tace naka ne"
Sunkuyar da kai Abdallah yayi tsayon lokaci, zuwa can yayi gyaran murya cike da nutsuwa
ya ce, "Baffa ina son zan mata tambaya daya zuwa biyu."
Gaba daya falon aka hada baki wajen fadin "Kana da damar yin hakan."
Juyawa yayi ya kallin Bilkisu yace, "Bilkisu har muka cika kwana shidda na kusance ki?"
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

Page 46-47

Shiru Bilkisu ta yi ttsayon lokaci, kowa ita yake kallo, ganin haka mahaifinta daya tsura mata Ido
acike da damuwa ya ce, "Ba magana ake miki ba?"
Wannan karon dago kai tayi ciki da hawaye tace "A'a" idonta a kasa ta yi maganar yayin da
hawaye ke gangaro mata masu tsananin zafi.
Cike da bacin rai Abdallah ya ce "To mai yasa zakice cikin nawa ne? Bayan kinsan babu wani
abu daya taba shiga tsakaninmu" Wannan karon Bilkisu bata iya cewa komaiba illa hawayen
dake zubo mata, tsayon lokaci ta dauka tana kuka zuwa can Babanta yace "Bilkisu mai na miki
kika min haka? Banji dadin ganin wannan ranarba sam, wannan ranar ita rana mafi kunar
zuciya a tarihin rayuwata, da ganin wannan ranar gara ace gawarki nagani agabana, tir dake
Bilkusu" Kareke maganar yayi tare da fahewa da kuka dan haka Bilkisu ta kara rushewa da
kuka, Abban ne ya shiga bawa mahaifin Bilikisu hakuri sai dai be saurari Abba ba mikewa yayi
ya fice cikin tsananin damuwa tare da nuna tsananin bacin rai, ganin haka kanin mahaifin
Bilkisu yace "Shikenan sai ki tashi muje muje gida, tun da haka kika zaba, Abdallah tun yana
can ya sake ki, kuma banga laifinshi ba" Mikewa yayi afusace dan haka itama Bilkisu ta yunkura
ta mike cikin matsanancin kuka, adaidai wannan lokacin Nur dake labe ta fashe da kuka,
waigawa kowa ke yi yayin da wasu ke cewa "Wa ke kuka?" Bashir ne ya mike tare da cewa

"Nur ce" hanyar dakin ya nufa inda ya sameta zaune dirshen akasa sai kuka take, hannunta ya
rike ya dagota tare da cewa "Mene ne haka Nur?" Kokarin rarrashinta yake tana gocewa dan
haka ya fara janta zuwa falon adaidai lokacin da su Bilkisu ke fita cikin falon itama tana
matsanancin kuka, kwacewa Nur ke yi tana kokarin bin su Bilkisu yayin da Bashir ke janta cikin
buga ganin haka Abba dake kokarin bin bayan Mahaifin Bilkisu yace ya saketa, sakinta yayi tabi
bayan Abba, har bakin motar suka Isa bayan Bilkisu ta shiga motar cikin matsancin kuka Nur ke
daga mata hannu, saidai ita Bilkisu da Ido kawai take kallon Nur bata iya daga mata hannu ba
barema tace mata wani abu, har motar ta wuce jajayen idon Bilkisu suna kan Nur, bayan motar
ta wuce Abba ya kalli Nur sosai sannan ya ruko hannunta suka dawo gida, daf shi ya zaunar da
ita tare da nuna alhininsa akan abun da ya faru sam beji dadiba, daga karshe ya juyo ya kalli
Nur yace "Ke kuma ki kwantar da hankalin ki, Baban ta mutumin kirkine, dan haka wannan
bazai zama yankewar alakarmu ba, kuma wannan ya ishe ki ishara, kin zabi karatun dan haka
kiyi taka tsankan karki yadda da ruden samarin zamani bare su kaiki su baro, yanzun Kinga
koma waye ya cuceta, Gashi tana son auren yafi karfinta, Nur batace komaiba hawaye take
sharewa har wannan lokacin, Mamy da aunty Saratu ne suka mike suka bar wurin cike da
jimami, itana Nur sallamanta Abba yayi dan haka ta mike da nufin wucewa, wanni irin kallo ta ga
Abdallah ya yi mata dan haka tamai kallon sama da kasa sannan ta wuce, Koda ta koma
dakinta Rufda ciki ta yi tare da cigaba da kuka, tare da tuna yadda zata yi rashin Bilkisu adaren
yau da sauran lokotan da batan iya adadin su ba, dan haka ta kara fashewa da kuka, bayan
kusan minti talatin Bashir ya shiga dakin tsaye yayi akan Nur yana kallonta tsayon lokaci zuwa
can yace, "Ke wai Nur Ina runkine acikin wannan mgnr da zaki zauna kina ta kuke koke? bata
motsaba bare ta tanka dan haka ya sake cewa "Kowa a gidan nan beji dadin abin da ya faruba
amman babu mai wannan koke koken saike kuma wama yaceiki kizo ki labe kiji abin da ke
cewa?"
Wannan karon ma bata tankaba, dan haka ya shafa kanshi tare da cewa "Shikenan, kiyi
hakuri ki tashi mu yi magana" Kareke maganar yayi tare da zama a gefenta Yana kokarin
dagata tare da cewa "Idan zaman gidan zai miki babu dadi kizo muje gidanmu" Hawaye ya
shiga share mata, kamar jira Nur ke yi ta shiga cewa, Yaya Bashir dan Allah ku bashi hakuri
Aunty Bilkisu ta dawo gidan nan, wallahi natsatstsiya ce, Idan ma cikin ba nashi bane to wallahi
ba iskanci ta yi ba" Dan ya tsanshi yasa akan lebenta tare da cewa karki kara shiga cikin
wannan maganar, ai ko ciki daya kuka fito bakya shaidaitaba bare wadda kika santa wata
takwas baya, kuma nasan kina da ilimi idon kine ya rufe kawai amman ko be saketa ba basu da
aure" Yana maganar yana share mata hawaye ganin wani na sake zubowa yace "Ya isa haka
mana Nur, ki daina kuka dan Allah"
"To Yaya dan Allah ka taimaka ta dawo nan ta zauna"
Girkizata yayi tare da cewa "Ke ki nutsu Nur kiji abin da zan gaya miki" Lafawa ta yi da kukan
tare da binshi da Ido ganin haka ya shiga cewa, "Zamanta anan bazai yuwuba, amman duk
ranar da kika son zuwa ki gaya min sai in kaiki, amman sai in kin kwantar da hankalinki idan
kina koke koke kamar wadda akawa mutuwa bazan kaikiba" Hannu tasa tana share hawayen
tare da cewa "Na Bari" Yauwa ko ke fa? Karki sake kuka kinji ko? da

20 / 25