Ciwon Ya Mace Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   11 / 25

30K to 33K   out of 73.1K words

yasa Jamal da Jimil
juyowa kusan a tare suna kallon Nur a lokacin da hawaye ke zubo mata.
Jamal ne ya ce "Baza ki bude baki kiyi mgn ba?
Jamil ko fadi ya ke wai Ummy kina nufin da ga ita sai hijjabin?
Kasa amsa masa Momy take dalilin hawaye da ya fara zobo mata idonta akan Nur.
Jamal ne ya cije le lebensa sannan yace "idan baki bude baki kinyi mgn ba har nazo gurin nan
jikinki zai gaya miki."
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido

ADABI WRITER'S ASSOCIATION


PAGE 25-26

Ummy ce tai saurin takatar dashi da hannunta sannan ta juya ta kalli Nur ta ce, "Fyade aka miki
ko? Cikin sauri ta girgiza kai tare da fashewa da kuka, itako Ummy ajiyan zuciya ta yi sannan ta
ce, "Gaya min mene ne ya faru? Garin Yaya Nur? Jikin ki babu sutura kirki, haka kika fita
dama? Cikin ma tsanancin kuka ta ce, "Ummy Poul ne, na fito zani makaranta ya turo aka
daukeni, kuka ne ya kwace mata dan haka Ummy ta sake jawota jikinta ta rungome a lokacin da
Jamal ya ke cewa, "Karyan banza kawai, yanzu nan aka sauke ki a mota sabo da kin rainawa
mutane wayau kice wani an daukeki a mota, wadda bashi da gaskiyan ne ya dawo dake? Ko
yasa aka dawo dake?, kinje yawon banzaki zakizo kinawa mutane karya." Wannan karon ma
dakatar dashi Ummy ta yi ta hanyar cewa "Waye Poul din?"
Jamil ne ya ce, "Ummy ni abin da ya ke bani mamak,i me ya faru ta dawo gida daga ita sai
hijjabi? Garin yaya hakan ta faru? Babu ruwanmu da wani can, ita tasanshi mu bamu sanshi ba,
hankalin sa ya mayar kan Nur ya ce "Wallahi yau saina zaneki, saina farfasa miki jiki, da alama
wannan ba sabon abu bane a wajen ki, tun da har kika iya dawa gida a haka, yar karama dake
kin lalata rayuwarki" In da suke shiga shi da Jamal batan suke fita ba, dan haka Ummy ta daga
waya ta kitmra Aunty Saratu, bayan ta daga ta mata bayanin a yadda suga Nur sannan ta
sauke tana me dakarat da su Jamal daga fadan da suka rufe Nur din dashi.
Cikin kankanin lokaci Aunty Saratu ta fito da ga cikin gida, bude motar ta yi sannan ta kama
hannun Nur tana fadin "Sai munyi waya." Binsu da kallo Ummy ta yi har suka shige gida sannan
ta dauke idonta tare da share gutun hawayen ta.
*****
"Nur karki yadda Mamy ta ji wannan maganar bare kuma Abbanku, ki yi shiro da bakin ki
zansan duk yadda zan yi wajen ganin ba a zargeki ba."
"Amman Aunty ki gayawa Abba yasa a kama Poul, ya cutar dani aunty, bansan yadda akai ya
barni ba da kayan makaranta ajikina ya yayagasu ya ganni tsirara Aunty."

"Duk ki daina tuna wannan Nur, idan Abba ki ya kai mishi yan sanda kowa saiyaji wannan
wulakancin da aka miki, ko kina sone kowa sai ya ji? Wani ma cewa zaiyi karya ne an miki
fyade, sanin haka sai kiga mijin aure ma kin rasashi, Nur ke yariya ce shiyasa kike ganin fada
dashi zain yi amfani, kowa cikin unguwar nan yasan Poul yana da kudi, idan ya ga dama ma
zaice sharri kikai mishi, ko ya kashe kudi maganar ta mutu batare da an hukuntashi ba, mu
Kuma mun riga muntowa kanmu asiri shiko na mijine, asalima ba musulmi bane, ina abin da ya
dameshi, da wannan ya ke gadara, shiyasa har zai kawoki har kofar gida, dan haka kada ki
yadda kowa yaji wanna maganar, domin idan har Abdallah ko Bashir wani yaji kinsan zaman
lafiya a unguwar nan ya kare."
Hawaye Nur ta share sannan ta ce "To yanzun Aunty shikenan barinshi za'ayi? Ni ko duk
duniya ce zata taro nafison a kamashi Aunty, Koda ace yau zai kashe kudi maganar ta kare
nafison haka Aunty"
"Nur ke yariya ce bazaki gane abin da nake nufi ba, ni zan nemo mafitar cikin hikima, amman
kama Poul babu abinda zai haifar illa zubar da mutuncin gidan nan a karshe ki kasa aurowa"
"Dama Ni bani da burin aure Aunty, Ni ban damu ba, kawai a dauki mataki, in dai dan aure ne
bazan yi auren ba" Daure fuska sosai Aunty ta yi domin tuni ranta ya kara baci cikin fada ta ce
"Wallahi kiji na rantse idan har kika bari maganar nan ta fita cikin gidan nan sai ranki ya yi
mugun baci" Shishshekar kuka Nur ta cigaba da yi, yayin da Aunty ta ci gaba da cewa "Lokacin da aka
dinga cewa ki bar zuwa gidan baki kikayi ba, sai yanzun da komai ya dame zaki damu mutane"
"Aunty kayana fa ya yagesu a jikina ya min tsirara"
"Ki godema Allah da be lalata miki rayuwa ba sauran kibarwa Allah, shine kadai zai saka miki"
Kuka Nur ta cigaba dayi, sosai kukan ke damun Aunty, ga bakin cikin abin dake cin zuciyarta
dan haka ta mike ta fita tare da neman mafita. Dakin Mamy Aunty Saratu ta shiga jiki a
sanyaye, ganin shigowanta Mamy ta cire tagumi tare da cewa "Ta gaya miki da ga inda ta ke
kuwa?" Ajiyan zuciya Aunty ta yi sannan ta ce "Poul ne yasa a dauko masa ita, domin yana ganin
itace taja ra'ayin yan gidan su suka musulunta."
"Inna ilaihir wa Inna ilaihir raju'un, be mata komai ba dai ko?" Mamy ta yi tambayan ta na gyara
zamanta.
"Babu abin da yai mata, tana can ta na kuka wai ita aje a kamashi"
"Gaskiya gara aje ko kotu ne a yi mana iyaka dashi, wuni daya? sabo da ya raina mutane?"
Jimmm, Aunty ta yi sannan ta ce, "Ni kuma sai nake ganin gara a bishi a hankali, Kinga na
farko yaron nan ya na da kudi, ga rashin mutunci, uwa uba kuma ba musulmi bane, kinga shi a
gurinshi wannan ba abin kunya bane, mu kuwa ya na iya kawo mata matsala."
Jimmm Mamy ta yi Cikin yanayi irin na me nazari, zuwa can ta ce, "To yanzun me ye abin yi?"
"Ni dai abin da nake gani Mamy mu hana Nur fita ko makaranta, kafin mu ga yanayin abin, dan
ni yanzun kaina a kulle ya ke, na tsorata ainun, saidai naki bari Nur din ta gane haka."
Ajiyan zuciya Mamy ta yi sannan ta ce "Ai abin tsoro ne Saratu, amma baki ganin kar nan
gaba Alhaji yaji Kuma bayan yanzun mun boye masa?"
"In sha Allah komai zai wuce cikin sauki, tunda har ya dauketa ya kuma barta batare da yai
mata wani abu ba, ni ina ganin kila ya fahimci babu sanintane."
Cike da damuwa Mamy ta ce "Allah yasa" Mikewa Aunty ta yi ta koma gurin Nur saidai ta

boyewa Mamy a yadda Nur ta dawo gida.

Tun da ga wannan ranar yanayin Nur ya canza, Bata da walwala kodayaushe. Abin da Poul yai
mata ya kasa bace mata, kullum cikin kuka take, duk hali da take ciki aunty na sane da ita,
saidai ta yi buris da ita, sannan duk wata hanya da zata kadaita da Abban su Aunty ta
tausheshi, sabo da gudun karta gayawa Abba. Aunty da Mamy ne zaune suna Hira, yayin da Mamy take korafi akan rashin sakin jikin Nur,
Duk ta rame bata da walwala kamar da, Mamy ce tace, "Ina ganin ya kamata ta saki jikinta
zuwa yanzun."
"Kin Santa da son makaranta, wata kila da ace tana zuwa makaranta ta ji saukin abin, na lura
da Nur ma dai matsoraciyace."
"Dole ta ji tsoro Saratu, Kuma har yanzun babu matakin da aka dauka fa, Ni kaina banason ta
fita a yanzun, ina ganin Dole mu gayawa Alhaji fa, domin a yi mana iyaka dashi, duk ranar da
bamu ganta ba shine, ina nufin idan anje kai karar sa kawai muna zargin zai sacetane. Idan ba
aka sake nemanta aka rasa ahine." Cikin gamsuwa da maganar Mamy aunty tace "Kuma fa hakane, me yasa ma ba ai haka
bane tuntuni, ni lokacin kaina kullewa yayi."
"Abin da yafi dacewa kenan idan har Nur zata ci gaba da karatu."
Shiru aunty ta yi tsawon lokaci, zuwa can ta ce, "Gashi yanzu bikin Abdallah sati daya ya rage,
sai a bari bayan bikin sai a gaya mishi ko?"
"Amman sai dai mu toshe kunne, don zai yi fada da ace mun yi magana tun farko da yanzu
an gama maganar"
Shigowan Abdallah ya sa duk suka maida hankalin su kanshi, Bashir ne a bayan shi, har suka
zauna kallon su Aunty take tana kokarin ganu damuwarsu, ita ko Mamy su na zama ta ta ce,
"Lafiyar ku?"
Bashir ne ya shafa kai sannan ya ce, "Munje wurin Abba ne akan maganar auren
Abdallah...."
"Me ya faruwa akwai matsala ne?" Mamy da Aunty suka fada da saurin su"
Kawar da kai Abdallah yayi, yayin da Bashir ya ce "A'a ba matsala bace, kawai dai mun neme
da adan Kara bikin ne zuwa gaba."
Wannan karon ma Katseshi Mamy ta yi da cewa, "Sabo da me?"
Cikin sauri Bashir ya kalli Abdallah ya ce "Ka mata bayani mana."
"Kawar da kai Abdallah ya sake yi dan haka Bashir ya ce "Mamy kinsan be wuce saura sati
biyu ya wuce makarantar ba, Kuma karatun nan ya na da matukar mahimmancin, shine yake
ganin gara a daga har ya dawo."
"Ya dawo Ina? Mamy ta tambaya tana kallon su daya bayan daya."
"Karatun mana Mamy, kinsan fa zai iya daukan shekara daya batare da ya dawo ba." Cikin
sauri Mamy ta daga mishi hannu cikin fada ta ce, "Baza'a daga ba Baahir, ai yasan da maganar
karatun ya fara neman auren, sai yanzun da aka gama magana biki ya rage sati biyu ka bijiro
da wani salo?" Kasa Abdallah ya yi da murya ya ce, "Mamy ba haka bane, acikin dangin yariyar ma akwai
waddanda basa son a yi auren yanzu, Kuma ni tunani na yi, nauyin zai min yawa agarin da
bansan kowa ba, ni ba wani karfene dani ba, ga yariya karama, nauyin zai min yawa Mamy

kilama in kasa karatun da ya Kaine, kamar fa mutum ne zai yi tafiyan kasa mai nisan gaske, sai
kuma ya dauki buhun shinkafa ya goya, ya kamata ku duba wannan al'amarin.
Tun da ya fara maganar Mamy ke Kallon shi, zuwa can ta ce, "Me Abban ku ya ce?" Wannan
karon Bashir ne ya ce ai yaki amincewa Mamy bema bari mun gama mai bayani ba."
"Nan din ma haka ne, baza'a daga ba, idan an daura auren kaga babu Inda zaka ajeta acan
kana iya barinta anan, ka tafi abinka Kuma da kake cewa karama ce dacan bakasan da
kankantar tata ba sai yanzu kasan dashi?, To gudun karka yarda karamin buhun shinkafa a
hanya sai ka barshi agida, auren dai sai an daura" Wannan karon ma kasa ya sake yi da murya ya ce, "Nifa Mamy abin da yasa na ce haka, ina
ganin zata iya jirana ne har indawo sai a yi"
"Toh bazata jirakaba, ai mace bata jiran na miji sai dai namijj ya jira ta, tun da iyayenta sun
baka banga dalilin wannan maganar ba."
"Shikenan Mamy sai ta zauna anan din har na dawo."
Aunty ce tace "In sha Allah za'asan inda za'ayi ma ka tafi da ita."
Mikewa Abdallah yayi yana kokarin fita Yana cewa ta dai zauna anan din.
Bayan sunga ficewan shi Aunty tace "Wai meke damun Abdallah ne?"
Bashir Mamy ta kalla sannan ta ce "Me kuke shiryawa ne?"
"Ni fa Mamy babu ruwana, yanzu yaje har gida ya daukoni, ya ce mini ya tura Auwal wurin
Abba da maganar amma sai Abba yace yazo da kanshi, shine fa ya ce nazo na rakashi."
"Sam ya Bata wayon shi, gaba daya ya siremin, a da nafi dayya dashi akan kowa a gidan nan,
yanzu duk ya zama wani iri, bashi da gaskiya, shiyasa baya rawan jikin auren, idan aka barshi
haka zai zauna tun da azuciyarshi babu Allah, afili ya ke mutum. Sabon Allah ya sa a gaba"
"Kashhh, Mamy dan Allah ki daina mishi irin wannan tunanin." Bashir ya fada tamkar zai fashe
da kuka, itama Mamy cikin bacin rai taci gaba da cewa, "Ai gaskiya ne Bashir, ni ma ba farin
cikin fadan nake ji ba, kafin kayi da na wani gara ka farayi da naka, neman mata ya ke yi, dake
munafukine a haka bazakace ba, shiyasa baya daukin auren sam." Tsaki aunty Saratu ta yi sannan ta ce "Wlh bana son kina irin wannan maganar, ba kowa bane
ya hada wannan sai Nur, Kuma bata kyautaba sam, yanzu gashi da ga ya dan fadi ra'ayinshi
kince neman mata ya ke, ni dan Allah ku goge wannan zargin akanshi, aure zai yi, kar matar
tazo ta ji ana cewa neman mata ya ke, ta fara zarginshi kamar yadda Kuma kuke zarginshi, kai
Kuma Bashir ka jawa Nur kunne dan aure zaiyi"
Mikewa Mamy ta yi tana kokarin barin falon take cewa "Baza dai a dagaba, tun da shi ya
kawota da kanshi ba wanine ya nemo masa itaba bare ya ce dole aka mishi, kuma iyayen
yariya basu kawo wata matsala ba dan haka duk gidan nan babu mai sauraron shi."
"Ai shima ba cewa ya yi baya sonta ba, shawara ya kawo tun da kuma baku fahimcishi ba ya
bar maganar" Mamy tabata tsaya ta gama sauraron Aunty ba ta shige dakinta.
***

Nur ce kwnace tsakiyar gadon aunty tun daga ranar da abin ya faru Bata sake fita waje ba; bare
ma taje makaranta, rashin karfin jikinta yasa akace ma Abba bata da lafiya dan haka ya sanar a
islamiyya da boko, tun a ranar Abba ya bada kudi akaita asibiti, har yanzun a tunanin sa tana
shan magani, ayanzun Nur ko son tunawa da Helen bata yi, sabo da abin da yayanta yai mata
sosai takejin ciwon abin, tare da tunanin hanyar da zatabi a hukunta poul akan abin da yai

mata, tun da aunty ta hana ta agayawa Abba Nur bata fasa gayawa Allah ba, duk sallalolinta
guda biyar saita ambaci sunan sa, tana mai zubar da hawayen dakaicin.Ajiyan zuciya Nur ta yi
sannan ta tashi zaune zuciyarta cike da kuna, Aunty Saratu ce ta shigo dakin ganin yadda Nur
ke cikin tunani ta ce, "Ke har yanzu bazaki saki rankiba ko, to ki je wani ciwon ya kamaki ke kika
sani."
Ba tunani nake ba kaina ne ke ciwo, kallonta kawai Aunty ta yi ta kauda kai tare da fadin, "Mun
yi magana da Mamy yanzun, bayan bikin Abdallah za'a gayawa Abban ku, don a yiwa tufkar
hanci, sai kici gaba da zuwa makaranta abinki."
Ajiyan zuwa Nur ta yi tare da cewa "Yauwa Aunty, har naji dadi"
Wani irin kallo Aunty ta mata sannan ta ce "Wawiya kawai, wato ke koma menene zai faru a
gayawa Abba."
Dan murmushi Nur ta yi sannan tace "Wallahi yafi Aunty, ko Yaya Bashir nasan bazai yadda
ba"
"Hmmm Nur kenan, Ina gargadin ki karki bari mazan gidan nan suji, ta shi ki gayara gadon,
Abdallah yamin waya gashinan zuwa shida amaryarshi"
"Nan gidan?"
"Eh" Aunty ta bata amsa, mikewa Nur ta yi tare da fadin "Haka ake yi aunty? Ai ba'a daura
auren ba ko?
"Nace ya tambayo labar takalminta ya ce min gasunan zuwa, kedai tashi ki gyara gadon,
zamani ne ai."
Cike da farin ciki Nur ta amsa take taji duk wata damuwarta ta yaye, jin amarya Yaya Abdallah
zatazo yau dinan kuma gashi Za'a gayawa Abba abin da Poul ya mata.
Gadon ta gyara yayin da Aunty take fitowa da dakalma sabbi fil wadda Amarya zatazo ta
duba, Sallama da sukaji bakin kofa yasa suka dago a tare suka kalli kofar, Helen ce tsaye
abakin kofar, dan haka aunty tai saurin sakin ledan dake hannunta sannan ta taho cike da fada
ta tare Helen tare da cewa, "Fice kibamu wuje, me ya kawoki?, Baki da labarin abin da Dan
uwanki yaima Nur ne? Maza ki fice karki kara shigowa gidan nan."
Jikin Helen a sanyaye ta ce "Aunty nazo ganin Nur ne, kwana biyu bataje makaranta ba na
gayawa Mamma ta ce inzo inga jikinta."
Lumshe Ido aunty ta yi domin da Alama Helen basan Abin da

11 / 25