Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
ya aje, sannan ya karasa wurin ya zauna, cike da Murna Nur ta gaidashi
sannan shima ya gaidasu Abba, Aunty ce ta zuba mishi yaci kadan, sannan ya koma falon ya
zauna tare da cewa Nur, "Ki sauri ki gama kizo" Cukalin ta aje tare da mikewa ta dawo kusa
dashi, kallonsu Abba yayi sannan yace "Kaga ka hanata cin abincin" "Ta koshine Abba" Ledojin
dake nesa dashi kadan ya nuna mata tare da cewa, "Ki dauki ledojincan ki ki kaiwa Amarya inji
ango" dariya Nur ta yi sannan ta tsuguna ta deba ladojin, kudi ya ciro ya mikawa Nur ya ce
"Kice injishi fa" Amsawa ta yi da to sannan ta juya, Abba da tunda Nur ta mike yake kallon su ne
ya kira Nur a lokacin da take daf da shiga kofar da zata sadata da dakin, bayan ta dawo ta
tsaya ya kalli Bashir ya ce, "Ita ina nata? Me yasa bazai tuna da kanwarshiba? Bayan ita take
debewa matar tashi kewa?" Yar dariya Bashir yayi sannan ya nuna ledan dake hannunshi tare
da cewa "Abba ga nata nan ai" Dauke fuska Abba yayi tare da cewa "Yauwa ya kyauta" Ita ko
Nur juyawa ta yi takaiwa Bilkisu sannan ta dawo rike da jakar makarantarta tana cewa, Yaya
Bashir mun fara jarabawa fa ka dade bakazo gidan nan ba"
"Da banzo ba ai ko a waya baki kirani ba" Bashir ya fada yana mika mata ledar, karba ta yi ta
daura a jikinta tare da cewa "Dan wannan?" Wani irin kallo ya yi mata sannan ya kalli Abba,
ganin baya kallon su yace, "Kinsan da yaya na saya miki wannan din? Sabulone kawai bani da
kudi" Hannu yasa a aljihu ya ciro kudi ya mika mata tare da cewa "Amasa idan zan tafi kiban
dubu uku ki rike biyu" Abba Nur ta kallah har yanzun abincin shi yake ci dan haka tace "Kai ka
saya min sabulo amman kana son kacewa Abba shine kudin ma so kake suka kamar shi ya
bani?"
"Eh mana, ko kinfi son suyita ganin laifinshi?" Ajikinta ya daura kudin sannan yace "Matso mu
yi hoto tad'i zani, ta matsamin tana son ta ganki" Cike da zumudi Nur ta aje kayan hannunta a
gefe ta matsa kusa dashi, wayar ya mika mata tare da cewa "Amsa ki dauke mu" Kin amsa Nur
ta yi ganin inda yake kallonta tace "Kai ka daukemu mana, katuwa zanyi idan na rike wayar" "Nima bana rike waya idan za'ayi hoto"
Juyawa Nur ta yi ta kalli Aunty Saratu tace "Aunty zoko daukemu, budurwar shi zai nunawa
hotunmu Kuma wai saidai ni na rike wayar dan karyayi muni" Daure fuska Aunty ta yi tare da
cewa "Nice marainiyar wawonku ko? ku ta hoto ma kuke yi" Karake maganar ta yi da Jan tsaki,
batare da Abba yace komaiba ya mike yaje ya amsa wayar tare da cewa "Ni bari na musu" Cike
da fara'a Bashir da Nur suka gyara zamansu, hoto daya Abba ya dauka ya mika wa Nur wayar
tare da zama cikin falon, kallon hoton Nur ta yi ta kwashe da dariya tare da cewa "Be yi kyauba
Abba, baka iya daukan hotoba, shima Abba cike da dariya yace "Kawo ingani" Mika mishi wayar
ta yi ya kalla sannan yace "Maye beyi kyanba anan? hannunshi yasa ya nuna Bashir yace "Ga
Bashir ga Kuma Maryam, to meye abin da beyin ba? Ko baku bane a jiki?"
"Mune Abba, Amma a karkace ka dauka, wurin mamy da Aunty Nur ta tafi da wayar suma
dariya suke, yayin da Nur din ma keta dariya, idonta akan wayar ta nufa Yaya Bashir tare da
cewa "Kallah hoton ya Bashir" Dagowa ta yi da nufin kallon sa, gabanta taji ya fadin dalilin
ganisa yana tattara katin da Poul ke aiko mata dashi gaba daya suna watse a cinyanshi,
tattarawa yake tare da yi mata wani irin kallo dan haka gaba daya ta rude alamu rashin gaskiya
ya bayyana a tattare da ita...
CIWON 'YA MACE 21
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 41-42
Ganin inda Nur ta rude ya tattara duk katin yasa a aljihunshi, sannan ya fara tattara littaffan Nur
ya mayar cikin jakar ya mika mata, jikinta a sanyaye ta amsa sannan ta juya ta shiga dakin tana
satan kallon fuskar Bashir, taso mai maganar saidai tana gudun kar su Abba suji, koda ta shiga
dakin tagumi ta yi tana rike da jakar ta kasa ajewa, Bilkisu Dake waya a gefe ce ta kalleta zuwa
can ta sauke wayar tare da cewa "Lafiya kuwa Nur?" Bude baki ta yi da nufin yin magana
sukaga Yaya Bashir ya shigo, dan haka duk suka maida hankalinsu gare shi, yayin da idon Nur
ya nuna zallar rashin gaskiya. Kokarin fita a dakin Bilkisu ke yi Bashir yace tai zamanta saidai
duk da haka Saida ta fice.
Bashir kuwa kallo ya karewa Nur sannan yace "So nawa kikaje Ofishin Poul?" Dagowa ta yi
ta kalleshi sannan tace "Yaya Bashir ban taba zuwa ba.."
"Karya kike yi? Bakyazuwa me kike da katinshi a jakar makarantarki?" Sunkuyar da kanta ta yi
kasa tare da matso hawaye, ganin haka ya sake cewa "Ba magana nake Dake ba?" Wannan
karon cikin kuka tace "Shine ya bani"
"Ya baki akan wani dalili?" Wannan karon ma Nur kasa cewa komai ta yi zuwa can yace Cikin
fada "Zan mareki kuwa, ba mana nake miki ba?" Fashewa Nur ta yi da kuka tare da cewa "Yaya
shi wai Sona yake" Dakowa Bashir yayi ya zauna dafda Nur tare da cewa "Inyamurin? Kintaba
zuwa wurinshine?" Wannan karon dakai Nur ta bashi amsa dan haka ya kjreta da Ido tare da
cewa "Gaskiya zaki gaya min fa"
"Yaya Bashir wallahi ban taba zuwa ba" Wannan karon ajiyan zuciya yayi sannan ya ce "Mai
yasa baki Gaya min ba?"
"Ni ban dauki abin da mahimciba, so yake in kirashi a waya, ni kuma duk sanda ya bani cewa
nake yabace amman sai ya Kuma vani wani" Ajiyan zuciya Abdallah ya sake yi tare da cewa
zaici ubanshi kuwa, bazai yiyuba arnen banza da wofi kawai, bayan haka ma ai ba mutuncine
dashi ba, dawa yake magana a unguwarna, dan ubanshi ko musulunta yayi yanzun waye zai
bashi yar shi acikin unguwar na? Idan yace zai kawo mana iskanci sai mu rusa gidan yabar
unguwar nan" Mikewa yayi a fusace tare da cewa "Zan kira Abdallah mu yi shawara sai munyi
maganinshi."
Bayan fitanshi Nur kara rudewa ta yi dan haka taita kuka tare da tuna zancen Aunty da take
cewa karta yarda kowa yaji maganarta da Poul, yanzun gahi ita ba ma kulashi ta yi ba amman
abubuwan suna shirin jagulewa.
******
"Bashir naga kiranka dazon ina kan haya" Abdallah ya fada a lokacin da yake kokarin zama
adan karamin falon da ya sauka, shafa kai Bashir yayi sannan yace "Eh yanzun zamu iya yin
magana?"
"Ina jinka mai yake faruwa?"
"Ina wannan guy din Na gidansu wannan yariyar Helen kawar Nur?" Kafa daya Abdallah ya
dauka ya daura akan daya, tare da cewa "Eh, naji, Poul kenan ko?"
"Yauwa, shi, wai shine yake bawa Nur katin Ofishinsa wai yana sonta" Shiru yaji Abdallah yayi
tsayon lokaci dan haka ya sake cewa, "Abdallah kana jina?"
"Ina jinka mana kaci gaba Ina ji"
"Katinsa fa yafi ashirin a hannunta, ita kuma dake wawiyace tanata tarawa, yadda Allah dai ya
taimaka Bata taba zuwa ba." Katsewa shi Abdallah yayi da cewa "To idan ma taje Ina
ruwanka?"
"Ban gane ina ruwana ba?"
"Eh mana, meya dameka aciki? Yanzun dan ka ganta da wadda ba musulimiba shine abin da
zaka tashi hankalinka, to Bari kaji, Ni ko da sarkin inyamurai zata yi mu'amala babu abin da ya
dameni da ita, wani wahalane banyi da itaba abaya, amma saida ta nemi ta karar min da
mutunci..." Katseshi Bashir yayi da cewa "Amma Abdallah idan ya mata wayaufa ya cutar da ita, Ni dakai
ne zamu hadu mu dakatar da abin domin ko musulunta yayi bazamu Bari ya auretaba."
Tsaki Abdallah yaja tare da cewa "Ai saikaje kayi tayi, nikam Ina nan idan sarkin arna zata
aura banda matsala" Wacce irin magana ne kake yi haka Abdallah, ni ina maganar nanne har
zuciyata matsayinta na yar uwata da bazan bari wani abu ya cucetaba, kaima kuma yadda zanji
akanta haka ya kamata kaji sabo da ban fika kusa da ita ba" Jimmm, Abdallah yayi zuwa can yace "Zaka min rashin kunya ne?"
"Ba haka bane, kawai dai inaganin be kamata ka yanke zumunci bane, naji tayi maka ba daidai
ba, amma ai ita yatiyace, idan aka barta wayasan Mai zai faru da ita"
"Ai shi nace maka Bashir idan kaga zaka yi wani abu ka yi kabar jirana, karka sake min
maganarta, ni ba abin da ya dameni da ita" katse wayar Abdallah yayi batare da ya jira cewar
Bashir ba, Bashir ma wayar ya kalla sannan ya shiga cikin gidan cike da bacin rai.
Falo ya zauna tare da kwalawa Nur kira, nan danan ta fito jikinta a sanyaye, gefenshi ya
nuna mata ta zauna sannan yace, "Kinsan mai nake so dake?" Kai Nur ta girgiza alamar a'a,
"Karki kara yadda ya miki magana ki amsa, ke waima a ina kuke haduwa ?" Cikin kwalkwal da
Ido Nur tace "Idan naje gidan biyawa Zainab makaranta..." Tun kan ta rufe baki yace karki kara
biya mata makarantar, idan kuma ya tareki a hanya yayi miki mgn ki gaya mini, zanci ubanshi,
wa yake kulawa duk cikin unguwarnan, zan tara mishi jama'a!" Yadda ya gada murya wannan
lokacin yasa Mamy fitowa tana raba Ido tare da fadin "Lafiya kuwa Bashir?" Mikewa yayi a
fusace yana cewa "Lafiya lau Mamy" Ficewa yayi dan haka Mamy ta maido da kallonta ga Nur
dake hawaye tace "Mene ne ke faruwa" itama mikewa ta yi cike da rashin gaskiya tace
"Bakomai" Daki ta shige dan haka Mamy ta tabe bakinta ta wuce abinta.
Koda Nur ta koma daki rufda ciki tayi tana hawaye sosai take jinta cikin damuwa, haka ta wuni
babu walwala, bayan sun yi Shirin kwanciya Bilkisu ta dubi Nur tace "Wai ke baxaki saki jikinki
bane, kodai kina son mutumin ne? Jin wannan tambayan yasa Nur ta tashi zaune, tare da
cewa, Ni ba sonshi nake ba, yadda naga yaya Bashir ya tafi cikin fushi ne abin ke damuna,
Kuma nasan halinshi komai yana iya yi"
Kallonta Bilikisu ta yi soi sannan tace, "Karki kara bari yaji Koda ace ya miki magana karki
gaya a gida, domin hakan zai iya haifar da rigima, na lura Bashir yafi Abdallah zafi, Wai dan
Allah in tambayeki mana?" Dagowa Nur ta yi ta kalli Bilkisu sannan tace "Ina jinki."
"Wai da Yaya Bashir da Abdallah waye Babba?"
Cikin sauri Nur tace "Yaya Abdallah ne Babba kinga kusan kansu daya ne ko?"
"Eh, kansu daya, Bashir ma yafi Abdallah kiba kadan, amman shi Bashir Baffah ne Babanshi
ko?"
Yar dariya Nur ta yi sannan tace "Eh ai dukkanmu Baffah ne Babanmu."
"Bangane ba Nur, karki kara sani cikin rudu, Bashir ne dai d'an Baffah ko?"
Wannan karon yar dariya Nur ta yi sannan tace "Wai ke baki sani ba da gaske? Yaya Bashir fa
dan Mamy ne, kannin Yaya Abdallah ne duk su biyun Mamy ta haifesu."
Cike da mamiki Bilkisu tace "Ikon Allah, ni na dauka Umma ce maman Yaya Bashir ai"
"A'a umma yarta daya mace ce, da kadan ta girme ni, kuma ta rasu"
"Allah sarki, yanzun shi Baffah bashi da yara kenan shiyasa Bashir yake zaune agidan?"
Daga kai Nur ta yi tare da cewa "Ni daya ce yarshi yanxun." Wanni irin kallo Bilkisu tai wa Nur
tare da cewa "Waike ma ba Mamy bace ta haifeki?"
"Mamatace, Amma ba ita ta haifeni ba, Yaya Abdallah be gaya miki ba?" Ciki da mamaki
Bilkisu tace "A'a, nasha tambayanshi sai yace min Mamy ce ta haifeki ke dashi uwa daya uba
daya."
Jimmm, Nur ta yi, zuwa can tace Ummy ce ta haifini, amman inajin Mamy sosai a zuciyata
domin da ita na saba, na dade ban yadda wai Ummy bace ta haifeni, sabo da nafi samun
kuwalawa da nuna kyauna daga Mamy". Cike da Mamaki Bilisu ta sake cewa "Ummy maman
su Jamil kenan ko?" Da kai Nur tabawa Bilkisu amsa yayin da ta sake cewa "To Jamil da Jamal
ma yaran Baffane kenan?"
"A'a bayan ta rabo da babansu ta auri Baffah da suka rabo Kuma ta sake komawa wurin
babansu Yaya Jamal" Wannan karon ma cike da Mamaki Bilkisu tace "Na gane, kenan ke tunda
ta fita ta barki wurin Mamy"
"Eh Ni dai na taso naganni wurin Mamy, amman dafari wurin Umma ta barni, soyayyar da Mamy
ke min yasa ta daukoni ta rike tun a lokacin, dan haka yanzun na saba da ita fiya da kowa,
domin tana nuna min soyayyar da bata nunawa yaranta na cikinta, tun tasowanta bazan iya
cewa ga banbaci daya da ta nuna min ba, da ita da danginta sun rukeni kamar yadda zasu rike
d'an daMamy ta haifa, sau daya Maman Mamy Kaka ta taba nuna min banbanci, Kuma akan
Yaya Abdallah ne.
Dan Murmushi Bilikisu ta yi sannan tace "Ma dai kula keda yayan Abdallah nan naku bakwa
shiri, wai mai yasa?"
"Bakomai, kinsanshi da son girma, Ni kuma na cika shishshige da yawan magana wannan
yasa bama shiri sam"
Fashewa Bilkisu ta yi da dariya tare da cewa "Yanzun dan wannan yake jin haushinki, dariya ta
cigaba da yi ganin haka Nur ma ta danyi dariya, yadda Bilkisu ke dariya tare da ceawa aiko
saina shirya ku yasata kwarewa, nan ta shiga tari tare da hawaye, sannu Nur ke mata zuwa can
ta tashi ta shiga bayi, amai taita kwarawa ganin tarin yaki tsayawa Nur taje ta Kira su Mamy,
bayan zuwan su Mamy aka samu tarin ya tsaya, Aunty ta wanke mata fuska suka fito, nan Nur
ta basu labarin dariya take ta kware, sannu sukaita mata bayan tarin ya lafa suka fice adakin,
tun daga lokacin Blikisu ta kwanta ta rufa, rawan sanyi taitayi zuwa can Kuma ta mike a guje ta
koma bayin, amai Nur taji na yi dan haka tabi bayanta, kafin gari ya waye Saida ta yi amai sau
biyar, dan haka Basu yi baccin kirkiba, da safe Nur na kwance taji Bilkisu na waya da Abdallah,
tana gaya mishi amanta shidda cikin dare, sun dade suna waya daga baya suka yi sallama, Nur
ko Shirin islamiyya ta yi sannan ta karbo abin Kari, bayan sun karya ta wuce makaranta,
misalin sha daya na safe ta taso, abakin makarantar taga Zainab tsaye sanye da hijjabi,
karasawa wajenta tayi cikin waige-waige, bayan ta tabbatar babu Yaya Bsmashir a kusa ta
karasa tare da cewa "Daga ina, lafiya?"
"Daga asibiti nake Nur" Zainab ta fada cikin yanayin dake nuna tana cikin damuwa" waye babu
lafiya?
"Poul ne, Nur a kwance kawai yake tun jiya baya iya cewa komai, kuma baya cin abinci"
jimmm Nur ta yi sannan ta fara tafiya tare da cewa "Allah ya bashi lafiya" Ahankali Zainab ta
sake cewa "Nur dan Allah kizo muje ki gaidashi nasan zaiji dadi"
"Tabb wallahi bazani ba Zainab, bari kiji a gida ko ke an hanani magana dake bare kuma shi,
gidan kuma an hanani shi shiga, Yaya Bashir din mu yace idan ya sake min maga sai kowa
yajisu, sauri Nur ta Kara tana cewa "Ki tafi karya a gammu tare" A wurin Zainab ta tsaya cikin
sanyin jiki sosai, har Nur tai nisa tana tsaye a wurin. Bayan Nur ta Isa gida wannan karon ma cikin barko ta samu Bilkisu da alama jikin ya matsa
mata har yanzun, da rana koda Nur ta amso abinci cewa ta yi bataci, abincin Nur ta fara ci da
nufi taci ta barwa Bilkisu nata. Yadda Nur ke cakalar abincin yasa Bilkisu binta da kallo, gani ta
yi ta kasa cin abincin ta tsurawa wuri daya Ido, dan haka tace "Nur!" Azabure Nur ta kalli Bilkisu
tare da amsawa, "Tunanin me kike haka?" Bilkisu ta sake tambaya, babu komai Nur ta fada,
sannan tacigaba da cin abincin, saidai Bilkusu ta lura Nur na cikin damuwa har dare haka Nur
take, saita tsurawa wuri daya ido, abincinsu na dare kuwa cikinsu babu wadda ya taba, domin
ita kanta Bilkisu yadda ta kwana amai shekaranjiya yauma hakan ce, washegari da safe Bilkisu
ta kalli Nur tace "Ikon Allah, jiya cikinmu babu wadda yaci abinci, ni dai nasan lalurarace, tun
kwarewan da na yi bandawo daidai ba, ke kuwa wani abu ke damunki Kuma kin kasa Gaya min,
dagowa Nur ta yi ta kalli Aunty sannan tace, Ni fa ba abin da ke damuna, kawai jiya ne Zainab
tace min Poul yana asibiti wai bashi da lafiya, bansan maiyasaba abin ya tsaya min a zuciya ba,
na kasa kawar da tunanin araina hakanan sai naga Ina tuna fuskarshi"
"Tabb, kice kin kamo yariya, ashe kina son shi?" Bilkisu ta fada cike da Mamaki "A'a ba so
bane, ko tausayinshi banayi, amman da gaski daga jiya zuwa yau Ina tuna fuskarshi."
"Hmmm Yariya ki zubar da makamanki ki nema mafita, kin kamo, mun yi waya da Abdallah
yace "Bashir