Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
ya faru tsakanin yayanta da
Nur ba, Nur dake bayan Aunty ne ta mike, tahowa ta yi wurin ta riko hannun Helen tana fadin
"Shigo ciki."
"Bayan Nur tabi tana satan kallon Aunty, bakin gadon Aunty suka zauna yayin da Aunty ta juya
ta bisu da kallo tare da mamakin Kaunar da ke tsakanin Nur da Helen wadda a yanzun ta koma
Zainab, ficewa Aunty ta yi ta basu guri saidai acikin zuciyarta Allah Allah take Helen din tazo ta
fice a gidan. Bayan Helen sun gaisa da Nur ta ciro waya a yar kamar jakar dake hannunta tare da cewa
"Mamma ce tace idan nazo in kirata ku gaisa" cike da fara'a Nur tace to "Kirata to."
Dana wayar Helen ta yi sannan tasata a kunnenta tare da fadin "Gata"
Amsan wayar Nur ta yi tasa a kunnenta tare da Sallama, batare da ta jira an amsa sallaman
ba ta shiga cewa, "Mamma kwana biyu bana fita, Kuma ko na fito bazan kara shigowa gidan ku
ba, Poul ya zargeni akan komawar ku addinina, Kuma har yasa an dauko masani yaci mun
mutunci, Mamma fashewa Nur ta yi da kuka tsayon lokaci tana yi Cikin wayar, jin aba'ace komai
ba ta sake cewa, Mamma!
Gabantane yayi mummunan faduwa dalilin jin Muryan Poul da ta yi Cikin wayar....
CIWON YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
PAGE 27-28
Cikin sauri ta dago wayar ta kalla sannan ta sake mayarwa kunnenta batare da tace komai ba.
Muryansa ta sakeji ya ce, "Me yasa bakya zuwa makaranta? ko kina tsorona ne? Kin fada a
gida?"
Duk tambayan babu wadda ta amsa aciki, jin shirun yayi yawa ya sake ya cewa, "Ki fito kije
makaranta abin ki, babu abin da zan miki, na gane cewa babu sa hannun ki, na gano bakin
zaren, kuma komai zai dawo kamar baya, yanzun dai abin da nake so dake ki yafeni, kuma ki
fito dan Allah, ina kofar gidanku, akwai abin da zan gaya miki..." Mikewa Nur ta yi a fusace ta jefawa Zainab wayar tare da cewa, "Idan kin je kice mishi
bazanzoba, bayan wancen karon ya daukeni a titi yanzu zaizo har gida ya daukeni sabo da
yaga ba'a dauki matakiba?" Cikin sanyin murya Zainab tace, "Ba daukarki zai yi ba Nur, ya ce
mini hakuri zai baki, ni abin ya fara daure min kai, kulum na dawo makaranta sai ya tambayeni
mun hadu dake, idan nace bamu haduba ya fice, anjima ya sake tambayata, yanzu Kuma kawai
ya ce mini inzo muje gidanku a baki hakuri."
"Ya gaya miki abin da ya mni?
"A'a Ni yace min ma ko kince zaki gaya min kar in saurareki, amman dai in baki hakuri."
Wanni irin kallo Nur taiwa Zainab sannan tace, "To yanzun in gaya miki ko baza ki saurareni
ba?"
Jimmm Zainab ta yi sannan ta ce, "Karki gaya min tun da ya baki hakuri, yanzun kizo muje
yana jiramu na ga kamar ma bashi da lafiya ne."
"Ai yanzu ya fara ciwo, aduk sanda na saka goshina akasa saina roki Allah ya saka min, idan
kinje ki gaya mishi bazai warke ba ya dinga ciwo kenan daga nan har ranar mutuwanshi, kuma
tunda kin goyi bayanshi karki sake zuwa gidanmu, ki gaya mishi ya shirya zuwa kotu bayan
bikin Yaya Abdallah, sai anbi mini hakkina akan abin da ya yii mini... Zainab bata cire idonta akan Nur ba saida ta ji wayar na ta sake daukan kara, ganin Poul ne
ke kiran ta juya da nufin fitowa a gidan dan tasan ya gaji da jirane. Zainab na fita Aunty ta shigo
dakin fuskarta dauke da murmushi, dakuwa taiwa Nur tare a fadin "Wai ni Nur waye ke koya
miki magana haka? Wani maganar idan kika yi saina tsaya na kirga shekarun ki, me yasa zaki
yi fada da kawarki tun ta kuruciya akan wani.?"
"Aunty ba wani bane yayan tane ai."
"Eh, be dace kiyi fada da ita ba..."
"Aunty cewa fa yayi wai yana kofar gida inzo kinga har a gidan ma zuwa zai ya daukeni sabo
da yaga ba a kamashi ba ranar..."
"A'a Nur bana tunanin haka, ai da kinje ba abin da zai miki."
"Aunty Poul din? Ni ko ganin shi banson na kara yi, itama Zainab din ba ruwana da ita har
mamma"
Dariya Aunty ta sake yi tana kallon yadda Nur ke share hawaye. Bayan ta gama karewa Nur
kallo ta tashi ta isa bakin window, labulen ta daga sannan ta leka har yanzun Motar poul na
tsaye a kofar gidan, yayin da helen ke tsaye abakin motae tana magana. Dariya Aunty ta yi tare
da sakin labulen sannan ta dawo daf da Nur ta zauna tana kokarin boye murmushinta. ****
"Kisan duk yadda za ki yi ki fito min da ita, ina son in gantane kawai."
"Bazata fito ba fa, maganganu take marasa dadi ta ke ta fada, kuma tace na fada maka"
"Karki gaya mini, amman ki koma ki bata hakuri tazo."
"Ta ce fa bayan bikin yayansu Abbanta zaikai ka kotu akan abin da kai mata." Shiru Poul ya yi
tsayon lokaci, zuwa can ya shafa kanshi tare da fadin, "Ban mata komai ba, idan sun kaini kotu
zan iya kwatan kaina, ni yanzun damuwata kawai kizo min da ita."
Juyawa Zainab ta yi domin ta rasa yadda zata yi ya hakura, dan ita bawani saba magana
dashi ta yi ba, ko da ta koma nacin duniya taiwa Nur ta ki zuwa dan haka ko da ta koma kasa
magana ta yi tai tsaye kawai tana wasa da yatsunta. Shima Poul kallo ya kare mata sannan ya
figi motar sa ya wuce, ganin ba gida ya nufa ba Zainab tai a jiya zuwa sannan ta koma gida
mamaki cike da zuciyarta.
Itako Nur shigowan Abdallah ne ya dauke mata damuwar maganar Poul, bayansa kawai take
kallo domin ta masifar kosawa ta ga matar tashi, sai dai har wannan lokacin bata hango kowa
ba domin Abdallah dogo ne sosai, mikewa ta yi da sauri ta nufi tahowa tare da leken bayanshi
wata zarkadediyar budurwa ta hanga kanta sunkuye dan haka tai saurin zuwa ta rungumeta
tare da fadin "Oyoyo." Cike da fara'a suka rungumi juna sannan suka taho zuwa cikin, tuni
Abdallah ya zauna binsu da kallo kawai yake, sosai Nur ta bashi mamakin ganin in da take ta
farin ciki da ganin yariyar da zai aura. Itama Nur bakin gadon ta koma tana kallon yariyar, Aunty
taita bata takalmi tana gwadawa har ta debi wadda take so, tare da Yaya Abdallah suka zaba,
da kanshi yake saita mata takalmin har ta gama, ga dukkan alamu yana son yariyar sosai, dan
baya miti daya batare da ya kalleta ba, yayin da yake yawan kai bakinsa saitin kunnenta yai
mata magana kasa kasa, idan zata bashi amsa kuwa kunnensa ya ke kaiwa gurin bakinta,
bayan ya gama saurara yayi murmushi sannan ya koma gurin zaman shi. Har suka bar gidan
Nur murmushi take domin sun matukar bata sha'awa, kuma sun dace da juna sosai, har mota ta
raka su bayan sun tafi ta dawo gida cike da fara'a. Afalo ta samu aunty na bawa Mamy labarin
Bilkisu, yayin da mama keta fara'a "Wlh bakiga yariyar ba kyakyawa da ita, kuma wallahi d'aya
sharaf da ita, dan bata wuce Nur ba"
Cike da fara Mamy tace "Eh lallai karama ce tun da kika kwatanta ta da Nur"
"Wlh Mamy har dan jikin nasu ma, mama kawai Nur zata fita, sai Kuma dan haske kadan,
gaskiya na yaba da yariyar ga tarbiya."
"Wannan karon ma Murmushi Mamy ta yi tare da cewa "Toh ai shikenan, Allah dai ya zaunar
dasu lafiya."
"Amin" Aunty ta amsa, ita ko Nur tunda taji aunty ta ce wai tafita nono maganar da Abdallah
yayi kwanaki ya shiga dawo mata, in da ya ke cewa ita da ga han hangota hanci ake fara gani
da wasu abubuwa, kawar da zanjen ta yi tare da fadin "I dan ma haka yake nufi Allah ya Isa."
Mamy da Aunty wuni ranar kayan akwatin sukaita hadawa dan gobe za'akai, kafin yamma
sun gama zuba duk abin da ya dace. Misalin 10:37pm Abba da Abdallah ne tsaye a tsakar
gidan, yayin da Abba kecewa, "Bana son in sakejin maganar daga biki, ai kaika nemo yariyar
nan ba wani bane ya nemo maka, dan haka banga dalilin dagawaba, idan baka da wajen da
zaka ajeta acan kana iya zuwa ka gano garin in yaso daga baya kazo ka sauki matarka."
Cike da gamsu Abdallah yace "Shikenan Abba, dama..." Kasa karawa yayi dalilin hango
budurwar yariya tana shigowa gidan, ganin In da Abdallah ke kallo ya sa Abba kallon waje tare
da fadin "Waye nan?"
Cak ta tsaya tare da cewa "Ni ce."
"Kece wa?!" Abba ya fada cikin tsawa tare da har gowa "Zainab ce Abba"
"Wacce Zainab din?!" Abba ya sake tambaya tambaya cikin kosawa, karasowa ta tayi tare da
fadin, "Kawar Nur ce."
Kawar Nur? Cikin rashin fahimta Abba ke matsawa gabanta Yana mai jafa mata tambaya, ganin
haka Abdallah ya ce, "Yariyar nan ce kawarta kanwar Poul" Dakatawa Abba yayi tare da cewa
"To to na ji, lafiya dai ko?"
"Lafiya lau Abba."
"To me ya fito dake da dare haka" Abba ya fada yana duba agogo dake daure a hannunsa.
"Abba nazo wurin Nur ne zan amsa litrafina....
Batare da Abdallah ya bari ta rufe bakiba ya ce ta yi bacci ai yanzu, haba agogon hannun sa ya
kalla sannan yaci gaba da cewa, "Shadaya ne take shirin yi fa.?"
Kawar da kai Abba yayi sannan ya ce "Ki daina fitowa da daddare haka, kai Abdallah rakata
ciki, idan Nur din ta yi bacci ka bata jakar Nur din ta dauki abin da take so....
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 29-30
Gaba Abdallah yayi badan ransa ya so ba, saidai suna zuwa afalo ya nufi hanyar dakinsa
batare da ya ce da ita komaiba.
Aunty dake zaune ce ta kalli Zainab tace "Ke Kuma lafiya?"
Yadda ta gayawa Abba haka ta gayawa Aunty saidai ita Aunty bata yaddaba, dan haka ta ce
"Kin ga Zainab Nur ta dade dayin bacci, ku yi hakuri sai da safe." Bayan tafiyar Helen Mamy ta
kalli Aunty ta ce, "Yariyar nan fa inaga sai an rabasu da Nur Kinga dan uwanta ba kirkine dashi
ba." Kin kula zancen Aunty ta yi da cewa "Ita ko tsoron daren ma bata ji kareke maganar ta yi
tana kokarin mikewa tare da yiwa Mamy sallama ta shige daki.
Itako Mamy da abin ta kwana a kasan ranta, burinta kawai a gama bikin Abdallah a dauki
matakin raba su da Zainab domin kada hakan ya jawo wata matsalar. Nur ma bata da burin da
ya wuce asanarwa Abba, domin zuwa gidan da yayi yasa ta sake tsorata, domin gani take tana
fita za'a sake dauketa. Washegari da misalin karfe bakwai Zainab ta sake shigowa gidan, da
Sallama abakinta, Aunty bataji mamakin ganinta ba, amman Mamy har Saida taji cikinta ya
murda domin dai Zainab Bata saba musu irin wannan zuwan ba, bayan ta gaida su Mamy Aunty
ta nuna mata dakinta da Nur din ke ciki dan haka ta nufi dakin, har ta shige bakin Mamy na
bude sabo da mamakin da ta shiga, ajiyan zuciya ta yi sannan ta ce da Aunty "Ni fa Ina jin
tsoron shigowan yariyar nan gidan nan."
"Karki wani ji tsoro, jiya da tazo na tsinci maganar su, Ina tunanin Poul din ke turota ta bawa
Nur hakuri." Cike da mamaki Mamy ta ce, "A yaushe kikaji hakan? Bayan jiya sanda tazo Nur ta
yi bacci" "Ai tazo da rana" aunty ta fada tana kallon fuskar Mamy. Shiru Mamy ta yi tsawon
lokaci sannan tace "To me kika fahimta game da hakan?" "Nifa Ina ganin kila yayi tunani ne ya ga be kyautaba tunda har ya sako kanwarsa acikin
maganar." Har yanzun fuskar Mamy da mamaki tace, "To me Nur din tace?
"Ai yar taki ba baya bace Mamy, domin har kawar tata Bata bari ba jiyan, tatas ta mata..."
Katse Aunty Saratu Mamy ta yi da cewa,"Ta min daidai, wannan shine sanin ciwon kai, shiyasa
a kullum Nur Kara shiga raina take, duk da karamar yariya ce ita, amman tasan abin da ya ke
daidai da Wanda ba daidai ba, ko yayansu bazai nuna mata sanin ya kamataba, wautanta daya
da nake ganin daukar da take yi zata iya canza komai." "Hmmm Mamy kenan, dan dai tana kawo miki tsegumin ya sa zakice tafi Abdallah sanin ya
kamata, a dai dinga tunawa da baya, dan mutun ya yi kuskure sau daya be kamata a manta da
alherinsa na baya ba, dan ko ita Nur din ma dan ana mata uzurine amman itama itama ai da sai
asa zargin kanta, Mamy batabi da kan zance aunty ba domin dama tasan bata cika son ana
fadan laifin Abdallah ba.
****
"Jiya nazo da dare kina bacci"
Cikin kawar da kai Nur ta ce "Lafiya?"
"Lafiya lau." Juyowa Nur ta yi suka fuskanci juna sannan tace "Na ji kince jiya kinzo na yi
bacci?"
"Eh na ga Abba da Yaya Abdallah a tsakar gida sukace kin yi bacci."
"Amman me kikazo yi a daren nasan dai baki taba zuwa gidan nan da daddare ba." Ajiyan
zuciya Zainab ta yi sannan ta ce "Ai nima baki taba cewa babu ruwanki dani ba sai jiya, kasa
bacci na yi shiyasa nazo in baki hakuri."
"Hmmm haushi kika bani, kinki tsayawa kiji abin da zan gaya miki akan dan uwanki, ni abin da
yabani mamaki ma har yaushe kuka shirya da har zaki goyi bayan shi, alhalin kinfi kowa sanin
bashi da kirki, na fita fa zani makaranta ya turo aka daukeni a mota, wasu dirka dirkan maza
wallahi duk daukata garkuwa zasuyi dani, amman muna zuwa gidan abin da ya yi mtatukar
bani mamaki sai na ga Poul ne, yasa a dauko ni akan zargina da yake akan caza addinin ku."
Zaro Ido Zainab ta yi cike da mamaki ta ce, "Amman agida be nuna zai yi hakanba sam, ki yi
hakuri Nur..."
Katseta Nur ta yi Cikin fashewa da kuka tana me cewa "Allah ne kawai ya kubutar dani don so
yayi amin fyade... "
Zaro Ido Zainab ta yi a karo na biyu sannan ta tafi dogon tunani yayin da Nur ta cikaba da
sanar mata duk abin da ya faru cikin kuka bayan ta gama raira Kukanta ta dago ta kalli Zainab
da idon ke cike da kwalla ta ce, "Kuma wallahi bazan yadda ba, bazan taba yafe mishi abin da
ya min ba, in Allah ya yadda sai yaga sakamakon, hakkina bazai taba barinshi ya zauna lafiya
ba"
Cikin yana yin irin na wadda yai nisa a tunani Zainab ta ce "Amma kinsan mene ne?, duk da
cewa ni dai be gaya min abin da ya faru tsakanin ku ba amman kwana biyun nan cikin damuwa
ya ke sosai Nur, kafin jiya yata zama a gida baya zuwa ko ina, yana gefen su, wallahi Nur irin
masifar da ya ke mana saidai mu jiyo yana yima matar shi, itama cikin damuwa take tunda ta
fita jiya har yanzun Bata dawoba, yau kuma sai gashi ya shigo gefenmu yana tambayana ke"
"Sabo da yata nemana ya kamani be ganni ba? Ai tun da ga ranar Ina cikin gida babu Inda nake
zuwa, Allah bazai bashi nasara akainaba"
"Ba haka bane Nur, zuwan da na yi jiya da daddare wallahi har na yi bacci ya tasheni, wai in kai
miki wayan, na ce ai darene yanzun amman ya ce muje ya rakani, tare mukazo har nan kofar
gidan." Wannan karon Nur ji ta yi kamar an buga mata wani abu akai, dan haka ta tsaya tai
shiru tsayon lokaci zuwa can ta ce "To me zai ce min? Idan ma hakuri ne karya bata bakinshi
dan bazan hakuraba"
Cikin sanyin jiki zainab tace "Hakuri zai baki mana Nur"
"Wallahi Bazan hakura ba, tsirara fa ya mini, ya yayyaga kayan makarantar dake jikina duk suka
fatantake, fyade kawai yaso yimin"
"Ai nace be yi daidai ba Nur, amman Koda ace bazaki hakura ba ki tsaya kiji mai yake son
yace miki a cikin wayar nan, idan ya fada abin da ya ke son fada ba shikenan ba, ai ba lallai dan
kinji ki yadda ba, kuma abin da kikace na fada mishi