Ciwon Ya Mace Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   14 / 25

39K to 42K   out of 73.1K words

cire hannu sa ta wuce, jinsa ta yi ya
kuma cewa "Kin ji."
Daga kai ta yi alamar eh, sannan ya cire hannun cikin sauri Nur ta wuce, bayanta ya biyo, ita
ko Nur sauri take har Saida taga tabi hanyar da zata sadata da cikin gida sannan ta juyo ta
kalleshi a daidai lokacin da ya fice daga cikin gidan. Kai tsaye dakinta da shiga, rabon da ta
kwana dakin ta jima, yau daya ta ji tana son kebewa, Sam bata son magana ko hayaniya, ko da
ta shiga dakin gado ta fada sannan ta shiga tunani akan zuwa Poul gidan su, tashi ta sake yi
acikin zuciyarta take cewa, "Yanxu shikena na yafe mishi?, Haka zamuci gaba da kallon juna
alhalin ya kalleni tsirara" Innalilahi wa Inna ilaihir raju'un ta fadi a fili sannan ta sake komawa
gadon ta kwanta, wani sabon yanayi taji a jikinta dan haka ta saurara domin tantace wanni irin
Yana yi ne take ciki a yanzun, tunata kwance jikin Poul ya sa ta runtse Ido tare da sauke ajiyan
zuciya kamar yanzun ne abin ke faruwa, gaba daya ta nemi nutsuwarta ta rasa duk da cewa
bata ga fuskarsa ba ayau amman fuskarsa ta baya ke ta dawo mata, fari ne tass, dan gayen
gaske maiji da nera, ajiyan zuciya ta sake ja sannan tace a fili "Su Yaya Bashir suna Ina Poul
yayi kudi ya barsu alhalin zasu iya girman shi, duk da cewa suma suna da sana'a sai dai ko
rabin-rabin shi Basu kai ba a kudi, dan ko Jamal da Jamil da suke takama da narai bzaasu nuna
mishi komai ba" afili ta sake cewa "Watakila dan ya fisu kudi yasa ya fisu gaye" jin turo kofar da
aka yi ya sata yin shiru tare da kallon Kofar, Aunty ta gani tana shigowa Dan haka ta fara
kokarin sake fuskarta domin kada Aunty ta fahimci wani abu. "Nur ya kike dawo nan?" Aunty ta
yi tambayan tana kokarin zama kusa da Nur"
"Na ga baki sun yi yawa acan ne." Nur ta fada tana kallon fuskar Aunty, kallonta Aunty ta yi
sosai sannan tace "Ki ce min dai kin rage tsoron Paul toh ai shikenan" Mikewa ta yi tana kokarin
fifita har ta kai kofa ta juyo ta sake kallon Nur tace "Kin yi sabon turere ne?" Gaban Nur ne ya
fadi domun kamshin turaren Poul ne ya cika dakin a tunaninta ita kadai ke ji dan haka yanzun
da Aunty ta yi maganar ta daburce, Daker ta iya cewa, "Eh" Ficewa Aunty ta yi, Nur ko na ganin
fitan Aunty ta mike ta nufi bayinta dake cikin daki, kayan dake jikinta ta cire ta wanke su sannan
tai wanka ta dawo ta kwanta, saidai Tunanin Poul ya hana mata runtsawa, tare da mamaki har
lokacin da take wanke kayanta tanajin Kamshin turaren Poul na tashi a jikin su, daker bacci ya
iya daukanta, washagari da safe jinta take cikin farin ciki da annashuwa musamman idan ta
tuna yaune daura auren Abdallah duk da cewa har yanzun ba magana ya ke da ita ba. Alwala
ta yi ta tada sallah saidai ta gaza natsuwa domin sosai Poul ke fado mata, duk da kukarin ganin
ta kawar da tunanin shi dake yawan zuwa mata arai, bayan ta idar ta mike tana ninke dadumar
acikin ranta take cewa Anya ma sallata ta yi kuwa ace ina sallah ina tunanin katon arne, tsaki
taja tare da sake shinfida dardunar ta sake yin wata sallah, sannan ta mike ta shiga cikin gida.
Ayau da ga kalli fukar Mamy zaka gane tana cikin farin ciki, hakama aunty da duk sauran

mutanen gidan, Shi kanshi Abdallah yana ta shiga da fice a cikin gidan fuskarshi babu yabo
babu fallasa, misalin karfe daya gidan ya cika duk dangi sun hallara na kusa Dana nesa.
Nur zaune gaban Mamy sai danna wayar aunty da ke hannunta take, Umma dake zaune can
gefe ne ta kalli Nur ta ce, "Gaskiya Hajiya Halima kin sangarta Nur da yawa, ji inda ta zauna tun
tuni tana faman wasa da waya saikace wata karamar yariya."
Gefen da Nur take Mamy ta kalla sannan tace "Aiko duk wadda ya kalli Nur yasan babu
alamar sangarta a tattare da ita."
"Idan ba lalacewa ba ko kamar Nur yanzun ai kamata yayi ace ta na can tsakar gida ta kama
wani aikin Itama." Wannan karon Mamy fuskartar Umma tayi tare da cewa, "Ba aikin da zatayi
yau, wannan aiki ai na manya ne" Wurin Nur ta juyar da kallonta tare da cewa tashi kije ki
shirya" Mikewa Nur ta yi batare da ta ce komai ba ta nufi dakinta tura kofar, cike da mamake
take kallon gadonta kaya maza ne farare kalla aje akan gadon, a gefe guda Kuma ga takalmi da
agogo tare da turaroka, ajiyan zuciya ta yi domin ta tabbatar da babu wadda zai ajiye kayan nan
sai Bashir, zama ta yi abakin gadon domin gudun karta shiga wanka Bashir ya shigo ya dauki
kayansa batare da ya bata kudin da yace zai bataba, sai dai ga mamakin ta tazama taji motsin
watsa ruwa a bayinta, dan haka ta saurara jin tabass wanka ake yasata mikewa ta nufi kofar
tare da tambayan waye? Tsawon lokaci tana sauraro ba'ace komai ba, dan haka ta sake cewa
waye aciki? Wannan karon ma abace komai ba, duk da haka Nur Bata hakura ba murya ta daga
ta sake cewa Wai waye aciki ne? Awannan karon batare data rufe baki Bata ji ance Ubanki ne!"
Da baya ta koma bakin gadon ta zauna tare da mamakin me ya kawo Abdallah wanka dakinta,
bata gama mamaki ba ta mike da nufin fita dakin domin karma ya fito ya sameta aciki, saidai
harta taba kofar ta tuna da sabulonta dan haka tai saurin komawa wurin kofar bayin tace "Yaya
Abdallah karka taba min sabulona!" Saurarawa ta yi ko zaiyi magana, jin bece komai ba ta sake
ce "Dan Allah karka taba min sabulo kaji" Wannan karon ma dai bece mata komai ba dan haka
ta tsaya a wurin bayan tsayon wani lokaci ya bude kofar ya fito yana daure da towel daga
kugunsa zuwa guiwa, kallo daya yai mata sannan yace, "Au dan Ubanki tsayawa kika yi anan?
Sabolun naki na gwal ne da baza'ayi amfani dashi ba?" Kokarin kutsawa take ta gefen sa cikin
turo baki gaba tace "Yaya Bashir ne ya saya min sau daya na yi amfani dashi"
"Toh ya kare dashi na yi amfani sai ki gaya mishi ya sake sawo miki wani" Kutsawa ta yi ta
gefensa bata damu da gogan jikinshi da ta yi ba har sai da yai saurin rike towel dinsa tare da
bin bayanta da kallo,
guntun sabolun ne rike a hannunta yayin da ta fara kuka tana fadin yau fa na bude, shine har ya
kare haka? ta kare maganar tana kallon fuskar Abdallah, cike da mamaki yace "Zo ki fita kibani
wuri na lura ma ba hankali ne da ke ba." Tsuganawa ta yi ta dauki soson wankanta ta kalla
sannan ta fashe da kuka tare da kokarin ficewa a bayin adaidai lokacin da Abdallah ke cewa
yau na gama masifa soson naki ma laifine dan na yi amfani dashi?
Cikin kuka ta ce "Ai babu wadda ke dauka soson wani agidan nan sai ni za'a dauki nawa?"
Bata rufe bakiba ya dauketa da Marin tare da cewa "Fita kibani wuri." Fashewa ta yi da kuka
sannan ta nufa kofar fita a dakin, bata dire ko Ina ba sai adakin Mamy, tun kafin ta shiga take
cewa "Mamy Kinga Yaya Abdallah ko!" Duk mutanen dakin hankalin su dawowa yayi gareta,
Mamy kuwa cike da fusata tace "Me ya faru?"
"Mari na yayi Mamy" Cikin kuka sosai Nur ke maganar har yanzun tana dafe da kumatunta"
"Kin mishi wani abun ne?" Daga yadda Mamy ke maganar zaka gane ranta a bace ya ke.

"Saboluna ya karar min Kuma jiya Yaya Bashir ya saya mim"
"Wato shi dai Abdallah matsala gareshi banda abinshi Ina ruwanshi da sabolon ki? Yana ina? Ni
fa bana son mugunta, menene nashi da duka kuma? shi baya yin laifin ne me yasa ba a dukan
shi? Mu je" Cike da fada Mamy ta fice a dakin, Aunty ce ta kalli Ummy Dake gefe tace "Kingani
ko? in da kike ma Nur bata kalla ba, ita ta sabulon ta take, ita Kuma Mamy in dai kaji tana fada
a gidan nan to akan Nur ne, dan ayanzun kam ita da Abdallah basa shiri sam, abin da ba'ayi da
kuriciya ba shi ake yi yanzun." Murmushi Ummy ta yi tare da fadin "Allah ya shiryeta dai, banda
abinta da yau daya har ta yi magana" Mikewa Aunty ta yi tare da cewa "Barin je, dan shima fa
ba kanwan lasa bane, Mamy Kuma akan Nur Bata da dama" karake maganar ta yi tare da
ficewa a dakin.
*****
Abdallah na daura agogo su Mamy suka shigo, be yi mamaki ba dan yasan dole Nur takai
karanshi, kallo yabi Mamy dashi yayin da take fadin "Ya zaka daketa ka hanata kuka?" Cikin
San yin murya sosai ya ce "Mamy kiyi hakuri, idan mutanen dake dakina sun fita taje ta kwashe
duk sabolo dake dakina na bata." "Ba ason sabolun naka, Kai kasan kana dashi me ya kawo ka nan wanka?" Wannan karon
lebensa ya lasa alamar Yana cikin damuwa sannan yace, "Mutane sunyi yawa ne Mamy, kuma
kowa wanka yake son yi"
"Idan hakane sai ka dauka sabulonka kazo dashi, Kai baka siya mata sabuloba baka da damar
zuwa ka yi amfani da nata"
"Toh a yi hakuri Mamy baxan karaba" yana fada idonshi cike da farin ruwa.
"Dama neman magana kawai kake, da gangan ka yi, in ba hakaba wanka daya a karar sa
sabolu haka?" Mamy ta fada tana nuna mishi sabulon da Nur tazo mata dashi. Satan kallon Nur
ya yi ya gallara mata harara sannan ya kalli Mamy yace "Nawa ne sabulon in bata ta saya
wani? "Dukan Kuma da kamata fa? Nace idan ka biyata sabulu barin daka mata fa? Zaka hada duka
ka biya ne?"
Shigowan Aunty ya sa duk duka juya suka kalleta Abdallah ko takalmi sa da kularsa ya dauka
ahannu yana kokarin fita acikin dakin, cikkn sauri Aunty tace "Ina Kuma zaka? Ka tsaya ka
gama shiryawa mana." Toh aunty bakya ganin abin da Mamy ke min ne" Ya fada cikin nuna
bacin rai, da alama ya fara fusata, "Kibarahi gara ya fita din,idan ba neman rigima ba shida yazo
cin arziki har ya daketa.?"
"A'a wallahi, ita dai kecin arziki" Aunty ta fada tare da amsan takalman Abdallah ta aje kasa
tana fadin "Karasa shiryawa sannan ka fita."
"Au waton goya mishi baya kike har zakice haka? Ai ba'a canzawa tuwo suna, yadda zaiyi
takama gidan ubanshine itama haka gidan ubantane, ba'a fimu tsumma ba bare ace za'a bada
mana kwarkwata, kuma yazo ya fita tunda ba dakinshi bane"
Aunty kan Nur ta maida kallonta tana fadin "Wallahi Nur baki da kirki, yau daya kin kasa hakuri
da dan'uwanki, yanzun ke wannan abin da ke faruwa dadi ya ke miki? Gida cike da mutane kika
iya ratsasu kikai kara?
Batare da Abdallah yaji me Nur zatace ba ya fice a dakin, da alama yaji haushi sosai Dan ko
kallon Inda Nur ta ke biyi ba, Aunty ma ficewa ta yi yayin da Mamy ta Kara rarrashin Nur sannan
ta fita.

Har wannan lokacin Nur haushi take ji domin ita ta tsana a taba mata sabulo, daker tayo
wankan sabo da haushi tana fitowa ta sake kwanciya a godo batare da shirya ba, wayar Aunty
dake gefenta ta ji ta fara kara, dan haka ta mike tasa hijjabi domin ta mika mata, katsewa ta yi
bayan ta saka hijjabin aka sake kira, wannan lokacin ne ta kalli wayar ganin Yaya Bashir ne tai
saurin dagawa tare da cewa "Yaya!" Daga can cikin wayar yace "Na'am kanwata, Amman kin
gama fushin dai ko?
"Yaya Abdallah ne ya karar min da sabulon daka kawo min."
"Yanzu Mamy ta gaya min, zan kawo miki wani amman ki saki ranki, Kuma kiyi maza ki shirya
ganinan zuwa in dauke ki muje wurin dinner.
Cikin ranta taji farin ciki sai a yanzun ta tuna biki fa ake agidan cike da murna tace "An daura
auren ne?"
"Eh yanzun dai za'a daura."
"Toh Yaya Bashir da an daura ka kirani ka Gaya min in ruga in yiwa Mamy albishir."
"Karki damu kanwata, idan ma kinason kiji kamar kina wurin sai in kira ki da zaran zara'a
daura auren."
"Ina son Yaya Bashir dan Allah ka kirani."
"An gama kanwata, amman wai ni in tambayeki mana."
"Inajin ka."
"Ba yanzun kika gama fada da Abdallah ba amman Kuma kina murna da auren shi.?"
"Ai dan uwana ne Yaya, daman shine yake tsokana ta yanzun dai karka manta ka kirani, Kuma
yanzun zan shirya karfa ka manta ka wuce dinner bakazo ka daukeni ba."
"Yaya za'ayi in manta? kiyi maza ki shirya dai."
Nur na sauke wayar ta mike, kayan da zata saka ta dauko, duk abin da zata bukata ta aje
bakin gado, bayin ta nufa da nufin yin waka taji wayar na kara, dawowa ta yi ta zauna ganin
Yaya Bashir ne ta zauna domin sauraron daurin auren...
CIWON YA MACE
By
Fadila Lamido

ADABI WRITER'S ASSOCIATION


Page 33-34

Tana kara wayar a kunnenta ta ji muryan marokin cikin sifika ya ke maimaita abin da waliyan
Amarya da ango ke fada, sosai Nur ta cika da farin ciki, dan haka ta mike a guje ta nufi dakin
Mamy, tana cewa Mamy an fara daura auren Yaya Abdallah, ta na shiga dakin ta kara wayar a
kunnen Mamy, yayin da mutanen da ke falon suka bita da kallo, itako Mamy cike da fara take
kokarin zame wayar tare da fadin, "Naji Nur, jeki shirya" Nur kuwa kara dannawa Mamy wayar
take, domin da alamu Mamy kunya ya kamata, dariya Nur ke yi da duk mutanen dake dakin,
bata cire wayar a kunnen Mamy ba har Saida taji muryan Yaya Bashir yace, "Toh kindai ji da
Kunnen ki sai ki yi maza ki gayawa Mamy" Mayar da wayar ta yi kunnenta tana cewa "Ai itama
ma a kunnenta aka daura wallahi." Cike da fara'a Bashir yace, "Da gaske ko wasa? Amman kin

kyauta kanwata, Allah ya kaimu ranar namu ko?" Cikin sauri Nur ta fice a dakin, tare da cewa
"Amin Yaya Bashir amman naka ni bandani"
"Me yasa banda ke? Bakya son mu yi aure rana daya?
"Ni bana so Yaya Bashir, karatu zanyi in zama likita, can gidan su Rahma yayarta ba tayi
karatuba mijinta nayin kudi ya auro yar boko, yanzu tana nan agida ta girma tana kunyan
komawa makaranta, sannan kigidan su Hajiya Tani..."
"Tsaya Nur, dakata mana, wannan shine hujarki?"
"Eh, tsaya kaji sauran"
"Bazan tsaya ba, indan wannan ne bari in koya miki yadda zaki dinga cewa, idan an yi miki
maganar aure cewa zakiyi saina gama karatu amman kibar cewa bazakiyi aure ba" Nisawa Nur
ta yi sannan tace, "Bari Kuma kaji ya Bashir, ni ko ban yi aure ba har na mutu babu komai
wallahi, a gidan hajiya tani akawai wata mata, itama batai karatu ba mijinta har hira yake da yan
mata agabanta da turanci tunda yasan baji take ba, da daddare ma yayi ta chart dinshi gabanta
in tayi magana yace abokin kasuwancin shine daga chaina, har saida ya auro yariyar ta gane,
yanzun duk tafiyan da zaiyi da amaryan yake zuwa, itiko uwar gidan duk ta zama abin tausayi
ko kaya mai tsada tasa bata kyau."
"Oh Nur, wato da nace karki bani labarin shine saida kika san yadda kikayi kika gaya min, su
wannan kaddaran su ce ahaka, ke ko Kinga ko yanzun kikayi auren duk matsalar nan da kika
zaiyyano bazaki fuskanceshi ba in sha Allah, barema zaki kara karatu nan da shekara biyu
zuwa uku sai kiyi aure, kinga lokacin kina da shekara 18 ko 19" "Ya Bashir tsaya kaji..." Goshi Bashir ya dafe tare da kallon yadda Abdallah dake gefensa ya
daure fuska tamau, dan haka yai saurin cewa, "Nur tashi ki shirya idan mun hadu ma karasa
maganar yanzun Ina kan hanya ne, kuma ni ke tuka motar" Yana gama fadin haka ya sauke
wayar, sannan ya saci kallon Abdallah tare da fadin, "Nur ce fa" Cike da fada Abdallah yace, "Tunda muka taso Wurin daura auren nan kake waya da ita, Ni
bansan me yasa kake bawa yariyar nan fahimcinba, naga har wani lallabata kake, baka son
bacin ranta."
"Ba haka bane, idan bamu yi hira da itaba waye ne zaiyi da ita Abdallah, sannin kankane a
family mu muna da karancin mata, babu wata mace wadda take sa'arta Kai ko wacce ta girmeta
ma babu, ita kadai ce shiyasa gata nan kullum a firgice..."
"Wannan kuma ita taso, wanni kulawane a baya ban bata ba? Amman tarasa wadda zata
zubarwa mutunci saini, ni daga yau babu ruwana da ita, bani acikin duk wani abu da ya shafeta"
Shiru Abdallah yayi tunawa da yayi basu kadai bane a motar ya hanashi

14 / 25