Ciwon Ya Mace Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   19 / 25

54K to 57K   out of 73.1K words

zaizo ya kaini asibiti, ki shirya daga can sai mu biya mu duba Poul din." Zaro Ido
Nur ta yi tare da cewa "Kina son ya Bashir ya karyani kenan bazani ba."
"Shikenan" Bilkisu ta fada tana bin Nur da kallo, itako Nur tun da Bilkusu ta yi mgnr duba Poul
zuciyarta ta fara nutsuwa, dan haka zuwa can tace "Aunty Bilikisu, amma sai dai idan bada
Yaya Bashir zamu ba" Murmushi Bilikisu tayi tana daga kwance sannan tace "To ya kike ganin
zamu yi mu zille mishi, ni kaina bason zuwa asibitin nake ba, Wai su Mamy ne suka matsa mishi
akaini asibiti, wai sunce mishi ciki gareni." Yar dariya Nur ta yi tare da cewa ai gara adubaki
aman yayi yawa kuma tun daga ranar baki kara cin wani abincin kirki ba, da gaskeyarsu kila na
kusa samun yaro"

Yar dariya Bilikisu tayi tare da cewa, "Magani dai zasu bani, amma ni banda ciki, indai ba
ana sha a ruwa ba"
Wannan karon ma dariya Nur ta yi tare da cewa Ni dai ba ruwana, wannan maganar manya
ce,
"Kema babbace Nur, to yanzun ya kike ganin zakuyi mu zilewa Yaya Bashir din?"
Aunty kwanciya zakiyi ida yazo yaga baki shirya ba zai bamu kudin mota yace idan mun
shirya mu wuce."
Cike da murmushina Bilkusu tace to haka za'ayi indai hakan zai Samar miki da kwanciyar
hankali.
CIWON YA MACE
By
Fadila Lamido

ADABI WRITER'S ASSOCIATION


Page 42-43

Murmushi Nur ta yi batare da ta sani ba, duk da cewa ta juyawa Bilkisu baya amma ta gane Nur
murmushi take, dan haka ta shiga tunanin yadda al'amuran zasu kasance domin da alama Nur
tana son Poul Bata kula zuciyarta ne sabo da ganin bazai yuwuba. Zuwa can Bilkisu ta ji
tsayuwan mota, dan haka ta kalli Nur adaidai lokacin da Nur take cewa "Aunty rufe Ido gashi
nan" Batare Da Bilkisu tace komaiba ta rufe idonta, Waigowa Nur ta yi taga idon Bilkisu a rufe,
dan haka tai saurin shigewa bayi, tana turo kofar r Abdallah na buga kofar tare da Sallama a
bakinshi, buguwa yayi tayi har ya gaji ya wuce, sannan Nur ta fito ta nufa kofar afalo, samunshi
ta yi zaune afalon suna gaisawa dasu Mamy, bayan sun gaisa tace "Yaya ina bayine" Cikin
sakin fuska yace "Nayi tunanin ma bakwa dakinne, Ina Aunty tamu ta shirya dai ko?" Karyar da
kai Nur ta yi sannan tace "Bata tashiba in je in tasota?, Cike da mamaki yace "Kar dai Abdallah
be sanar mata da maganar zuwa asibitin ba"
"Ya gaya mata, harma tace zan rakata, in tasota ta yi wanka?" Agogon dake daure a kan
hannunsa ya kalla, sannan yace "Yanzun har saina jirata ta yi wanka? Zanyi latti ai" Mikewa
yayi tare da saka hannu cikin aljihu ya ciro kudi ya mikawa Nur tare da cewa "Ki tasheta, in
kunshirya sai ku wuce, amma kuna isa kimin waya, zan hadaku da likitan dazai dubata." Cike da gamsuwa Nur tace "To" Saida ya fice sannan ta koma daki, inda ta samu Bilkisu ta
gama shiryawa, dole suka dan tsaya suka bata lokaci sannan suka fito suka wuce, kamar yadda
Bashir ya ce haka suka yi, bayan an gama mata gwajegwajen da za'a mata aka sallame su, Har
zasu fita Bilkisu tacewa likitan "Ba wani magani da zaka rubuta mini?" Dagowa yayi ya kalleta
sannan yace "Bashir zai taho dashi" Cike da gamsuwa suka fice, sannan suka wuce asibitin da
Poul ke kwance.
Duk su biyun sanye suke cikin babban hijjabi har kasa, saidai ita Bilkusu tasa jibgigiyar rigar
sanyi ta ciki, dan haka tayi katuwa, number Zainab tasa a wayar Bilkisu ta kira, bayan ta dauka
ta sanar da ita gata a sibitin, nan danan kuwa Zainab ta fito cike da fara'a, Hannun Nur ta rike
yayin da Nur Kuma tai saurin roko hannun Bilkisu duk da cewa bata jin karfin jikinta a haka suka

tafi, Mamma ce kadai a dakin, tana Zaune gefen Poul tana mishi fifita, ganin shigowan su Nur
yasata dago tana musu sannu, Zainab ce tabawa Bilkisu kujerar da ta tashi, ita da Nur Kuma
suka tsaya a tsaye, ciki da fara'a Zainab kecewa "Mamma ki gaya mishi ga Nur" kallon Mamma
Nur ta yi, itama tana sanye da hijjabi ga carbi nade a hannunta, sunkuyar da kai tana mamakin
ganin mamma cikin damuwa, kenan duk da Wulakancin da Poul din yake mata tana sonshi a
haka yanzun, muryan Mamma taji tace "Poul!" Batare da ya bude baki ba ya amsa, dan haka ta
sake cewa "Ga Nur tazo dubaka" Cikin Sauri ya bude idon tare da rarraba su, zuwa can idonshi
ya sauka akanta, tana tsaye ta dafa kujeran da aunty ke Kai, gaidashi Bilikisu ta yi ya dago
mata hannu, Daker Nur ta iya yi mishi ya jiki, sannan ta sunkuyar da kanta kasa, nan Mamma ta
fara basu labarin ciwon sh,i inda ta alakanta abin da rashin cin abinci ne, shiko Poul tun daga
lokacin be sake rufe Ido ba, lokaci bayan lokaci Yana kallon Inda Nur take dan haka ta kasa
sakin jiki a wurin, domin gani take ya hanata sakat da kallonshi da baya karewa, Zainab na
Murmushi tamai ta yin cin abinci yace a'a. Shiru wurin yayi zuwa can Zainab ta nufa kofar fita
tare da Kiran Mamma suka fice tare, ganin haka Bilkisu ma ta mike tare da cewa Nur "In kin
gama ina waje kiyi sauri Amma." Kamar Jira Poul yake Yana ganin fitan Blikisu yayi ajiyan
zuciya tare da waigowa ya kalleta, har yanzun tana rike da saman kujeran da aunty ke kai.
Hannun sa ya miko mata tare da cewa "Rike ni in tashi" Yadda take haka take har yanzu bata
bata motsaba, dan haka ya kara miko hannun tare da cewa "Dan Allah fa!" Wannan karon
dagowa ta yi ta kalleshi sannan ta sake sunkuyar da kanta kasa, ganin haka ya sa ya maida
hannunshi tare da cewa "Washh" sannan ya dubeta yace "Haram ne ko? Babu kyau?" Batare
da ta dagoba ta daga kanta alamar eh, dan haka yayi murmushi sannan yace "Tam idan Helen
ta dawo zata dagani" Wannan karon yi tayi kamar batajiba, zuwa can taji ya sake cewa "Ita ta
gaya miki banda lafiya?" Wannan karon ma dai kai ta daga, dan haka ya sake yin mirmushi
sannan yace "Ta gaya min abin da yayanki yace, amman yanzun ansan kinzo?" Bata saba
karyaba dan haka ta girgiza kai alamar a'a, ajiyan zuciya yayi sannan yace "Na gode" Shiru
suka sake yi zuwa can yace "Anjima in zakiyi waya dani? in kira number gidanku da wayar
Helen? Tunda ke nace ki kirani kin ki" Can kasa makoshi tace "Wacece Helen?" Lumshe Ido
yayi duk da cewa can kasa tayi maganar amman ya ji me tace sabo da Yana kallon bakinta, dan
haka yace "Na manta ta canza suna ko? meye sunan ma?" Wannan karon kawar da kai Nur ta
yi sannan tace "Zainab" jinjina kai yayi sannan yace 'Baki amsa ba min tambayar da nayi
mikiba, idan na Kira zakiyi magana dani?" Tsintan kanta ta yi da daga Kai, Dan haka ya lumshe
Ido tare da cewa "Na gode, kuje tunda kince ba'asan kinzoba, waccen wacece kuke tare?"
Kawar dakai Nur ta yi sannan tace "Matar Yaya na ne0"
"Bashir?" Ya sake jeho mata tambayan, kaita girgiza tare da mamaki ta Yaya aka yi yasan
sunan Bashir, bata rufe bakiba yace "Wadda aka yi baki kwanaki Abdallah ko?" Kai ta daga har
yanzun da mamaki akan fuskarta, ganin wurin ya sake yin shiru ta juya tare da cewa "Allah ya
sauwake" Saidai harta fita bataji ya amasa. Tare dasu Mamma ta samu aunty Bilkisu, sallama suka yi suka wuce, bayan sun dawo gidama
Nur kadai taci abinci, Bilkisu ko kudundunewa tayi sabo da sanyin Dake damunta, Nur ko ta
kasa cire fuskar Poul a zuciyarta, tun da ta dawo tunashi take a lokacin da yake miko mata
hannu. Misalin 08:00pm Bashir yazo gidan, dan haka Nur tanajin sallaman sa ta fice, acikin
dakin Mamy ta aameshi suna gaisawa da Mamy, zama ta yi bayan sun gama gaisawa da Mamy
ya juya ya kalli Nur tare da cewa "Ya mai jikin?"

"Da sauki" Nur ta fada alokacin da Mamy ke cewa "Aikuwa ita za'a tambaya mai jiki, tunda
sunce kwana take amai, ko dai yau zata koma dakin Auntyn ku ne?" Cikin Sauri Nur tace "A'a
gaskiya, idan Kuma hakane saidai mu koma tare." Mamy ce tace "Ai saikuje taren, acan din
zaifi, dan wani lokacin kila bazaki tashiba bare ko taimaketa." Bashir ko tun da Nur tai maganar yabita da kallon mamaki tare da cewa, "Lallai Nur kina
yaudaran kanki, wato bazata tafi ta barkiba, yanzun idan mijinta ya dawo fa?" Jimmm Nur ta yi
zuwa can ta dago tace "Dama Abba yace su zauna anan"
Wannan karon dariya Bashir yayi adaidai lokacin da Aunty ta shigo, ganin Bashir nata
kyalkyata dariya tace "Bashir ya samu mugunta kenan?" Mamy ce tace "Shi da Nur ne, abun da
ya faru ta gaya mata itama dariya ta yi tare da cewa ai Nur babu komai cikin kanta sai kuruciya,
lokaci kadan-kadan take da hankali, ai ranar da ya dawo ko kwana daya bazai karaba zai dauki
matarshi, sai kinga yadda ya fitineni shekaranjiya da daddare, tsakar dare fa wai ya kirata bata
dagaba" Bashir da Nur ne suka yi dariya yayin da Nur ta karashe dariyar da cewa "Allah yasa
ya dade acan, walllahi gidan yanxun yafi Dadi" Itako Mamy kawar da kanta ta yi tare da cewa
Bashir "Ka amso maganin dai ko? Sunce likitan yace Kai zaka taho dashi." Ledan dake
gabanshi ya jawo ya mikawa Aunty, yayin da ta shiga dubawa, tana duba maganin ta dago cike
da murmushi tace "Ina sakamakon to?, Hannun yasa a aljihu ya ciro takardar ya mikawa Aunty,
budewa ta yi tare da cewa "Ma sha Allah, Alhamdulillah, ai ni dama nacewa mijinta cike gareta,
yana min musu" Murmushin Bashir yayi tare da kawar da kai, itama Mamy godiya tawa Allah
afili kuwa cewa ta yi "Allah ya rabasu lafiya, sannan ta mike ta ta fita adakin. Itako Nur sunkuyar
da kanta ta yi fuskarta cike da murmushi, acikin zuciyarta take cewa "Lallai Aunty Bilkisu ta iya
wayau, hiranta da kawarta Madina ne ya dawo mata, zuwa can ta yi dariya tare da mikewa,
tana kokarin fita Bashir yace "Aunty ki bata maganin ta kaimata, ko wanni akwai yadda za'asha
a jiki, laden aunty ta mikawa Nur har ta kusa kofa Aunty ta sake kiran Nur, takardan dake
hannunta ta mika mata tare da cewa "Har takardan ma kai mata, yaran zamani kila har toho
zata yi ta nuna mishi" dariya Nur ta yi sannan ta fice a dakin ko da Nur ta kaiwa Bilkisu tashi ta
yi tasha magungunan sannan ta dauki takardan ta aje gefenta, kafin wani lokacin bacci ya
dauketa, Nur ko tana ganin Bilikisu tayi bacci ta dauki wayarta sabo da yawan kallon Number
Poul da take jikin katinsa tuni ta haddace number, bayan ta saka Number kasa dannawa ta yi
domin wata zuciyar sosai take kwabarta, zuwa can ta tsincikanta da dannawa, saidai ta kasa
sawa a kunnenta, muryansa tajiyo duk da cewa wayar na nesa da kunnenta, Jin yadda yake
Kiran sunanta yasa ta nufa kunnenta da wayar, ji ta yi yana cewa "Nur bakya jina ne?" Can
kasan makoshi tace "Ina ji" Ajiyan zuciya yayi mai karfi sannan yace "Na gode da kika kirani,
tun dazon nake dakon kiranki, domin na kasa bacci sam, ni kadai nasan irin radadin da nake ji
azuciyata, awannan karon ji tayi kalmar Bata mata dadiba, Wai zuciyarshi na mishi radadi,
tsintan kanta ta yi da cewa "Dama zuciyar ce ke ciwo?" Lumshe Ido Poul yayi sannan yace "I ta
tafi komai damuna Nur" juyawa ta yi ta kalli Bilkisu Dake bacci sannan tace "To asibitin baka
gaya musu bane ai da sun baka magani" Ajiyan zuciya yayi sannan yace "Basu da maganin shi
Nur, na riga na gama yankewa kaina hukunci, babu wani magani da zaiyi tasiri ajikina, domin
kunar da zuciyata take min kece kadai maganinta, na tabbatar da hakanne bayan ganin ki da na
yi dazon, tun daga lokacin naji na samu lafiya, yanzun haka Ina gida tun dazon nake kallon
wayar, kiranki kawai nake jira, na gane kece maganin ciwona.
Wannan karon Nur batace komaiba, bayan tsawon lokaci yace "Bakice komaiba?" Can kasan

makoshi tace "Ai Gashi nakira." Cike da murmushi yace "Na gode, amman kinsan menene
nakosa? Burina inga kinzama tawa, kuma jikina na bani hankalina bazai taba kwanciyaba
sainaga na mallakeki, bana yin sekon daya batare da na tunaki ba, Nur kina ganin idan nazo
gidanku za'abani auren ki? Shiru ta yi batace komaiba, domin gabanta faduwa yake sosai, "Nur kinyi shiru bakice
komaiba" Tsawon lokaci suka dauka batare da yaji tace kalaba, dan haka ya canza tambayan
da cewa, "Nur in tambaye ki?" Can kasa-kasa tace "Umm" Ajiyan zuciya yayi sannan yace "Kina
so na?" Shiru yaji tsawon lokaci, zuwa can Kuma yaji kamar tana kuka, dan haka yace "Kuka
kike yi?" Wani abu Nur ta hadiye mai zafi awuyanta tare da share hawayen da ya fara zubo
mata, Bayan shiru na wasu lokaci yace, "Gobe zanzo wurin Babanki kamar yadda kikace
abaya..."
Katseshi Nur ta yi da cewa "Karkazo dan Allah"
Saboda me? Ina ce wancen ranar kece kikace min inje wurin Baban ki?"
"Yanzun nasan bazai yadda, kuma Yaya Bashir yamin gargadi sosai, bazasu yadda ba
nasani."
Shiru yayi tsayon lokaci, zuwa can yace "Inda ace ni musumine kina gannin zasu amince su
bani ke?"
Eh Nur ta fada a hankali, dan haka yace shikenan, ki kwanta kiyi bacci karki damu kinji?"
Ahankali ta amsa da "To" Jin yana Shirin kashe wayar tai saurin cewa "Karka kira wannan
wayar na matan Yaya nane." Murmushi yayi tare da cewa "Bazan kiraba ai, amma dan Allah
gobe ma ki kirani" Amsawa tayi sannan ta kashe wayar. Washegari tun da asuba Bilkisu ta fita
neman abincin sabanin da da bata iya cin komai. Sannin lalurarta yasa aunty fitowa ta dama
mata kunnum tsaniya, nan falon ta zauna tasha tai gyatsa, sannan ta iya yin sallah, da rana
iyayen Aunty Bilkisu sukazo gidan duba jikinta, sosai tai murna da zuwan su, lokacin da zasu
tafi gaba daya su suka fito rakasu har bakin mota, bayan sun zauna a motar ne kishiyar Maman
Bilkisu tacewa Bilikisu "Toh Bilki ki dinga lura da cin abinci, Allah ya raba lafiya" Jimmm, Biliku ta
yi kafin tace To kawai sannan tai saurin juyawa cikin gidan kamar zata yi kuka, Mamy, Aunty
Saratu da Nur kuwa a tare suka dawo cikin gida, afalo Nur tabar su Mamy ta nufu daki, tana
shiga ta samun Bilkisu ta yi zaune a bakin gado, kwalla cike daf da idonta, yayin da takardan da
ta kawo mata jiya yake rike a hannunta, tsaye Nur ta yi tana kallonta, ganin kafufuwan Nur yasa
Bilkisu dagowa ta kallli Nur a daidai lokacin da hawayen da suka cika idonta suka gangaro zuwa
kumatunta, hannu tasa ta share sannan ta mike tsaye tare da cukurkude dakardan tana ya
mutsata cikin hannunta, cikin yanayin dake nuna tana cikin tashin hankali...
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido

ADABI WRITER'S ASSOCIATION


Page 44-45

Kallo Nur ta bita dashi cike da Mamaki, yanzu ta shigo cikin gidan tana murnan zuwan iyayenta,

ko mene ne yasata shiga cikin damuwa Kuma, karasowa Nur ta yi bakin gadon ta zauna,
sannan ta sake kallon Bilkisu da har yanzun take share hawaye, wani tunani ne ya fado amta
arai, dan haka ta kalli Bilkisu tace, "Aunty dan kinga 'yan gida kike kuka?" Dariya tasoyi Amman
idonta na sauka akan takardan take hannun Bilkisu saita hade fuskar acikin zuciyarta tace,
"Kamar Aunty Bilkisu nada damuwa da takardan nan, me yasa take matseta cikin hannunta?"
Ganin babu mai Bata amsa ta mike tare da cewa "Aunty Bilkisu wai mene ne? batakai ga Bata
amsa ba wayarta tai kara, saurin kallon wayar Bilkisu tayi sannan ta amsa kiran, daga yanayin
amsa da take badawa Nur ta gane da Yaya Abdallah take wayar, bayan amsa ya jikin da ya
mata sukaci gaba da hira, murmushi Nur taga ta yi kadan, dan haka ta fice domin ta bata wuri ta
sake da mijinta. Tun daga wannan ranar Nur ta saba da waya da Poul, bayan Bilikisu tagama
wayar da Abdallah ko wanne dare Nur zata Kira Poul susha hira, sosai Nur ke sakewa da
Bilkisu bata boye mata komai, duk da cewa tun da Bilikisu ta samu cikin ta rage walwala, Mamy
da aunty kuwa sai abin da Bilikisu keso ake dafawa a gidan, sosai suke bata kulawa, rashin
walwalan Bilkusu be damu Nur sosai ba, domin tanaji ana cewa masu cikin sai a hankali dan
haka idan taga ta kwanta ta yi shiru saidai ta dauki wayarta ta kira Poul, sosai suka saba, duk
da cewa bata tunanin auren zai iya yuwa tsakanin su.

BAYAN WATA BIYAR

Tuni su Nur suka kammala jarabawa har sakamakon ya fito, dan haka Abba ya fara mata ciko
cikon makarantar koyon aikin jinya kamar yadda take so, a yanzu burin Abba be wuce yaga ta
fara zuwa makarantar ba, sabo da yanzu ya yadda da nutsuwarta, kuma ya

19 / 25