Iyayen Giji Book Compelet Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   9 / 21

24K to 27K   out of 61.8K words

har Hindu bata bari ba saida ta zage. Amma Hindu saida tayi ma Yaya Bebi rashin kunya.
Kuma itace babba a gidan, har iyaye mata basu cika tsallake maganar da Bebi ta zartar ba.
Baba Sahura tace. "Amman Ƴannan baki da mutunci baki data ido. Yayar mijin naki kike sa'in sa da'ita sabida
ɗibar albarka, duk ɗiban albarkar da iyayenki suka zo su kai mana a gidannan bai isheki ba ko?"
Murmushi kawai nayi, dana tuno yanda suka dinga haba_haba da Hindu sanda tazo,
musamman da suka ga ta haifi maza har biyu. Sai gashi rana guda suna Allah tur da ɗabi'un
Hindu, dana iyayenta. Yarana na kaɗa muka shiga ɗaki. Haka Yaya Bebi ta tafi anata bata
haƙuri a bisa fitsarar da Hindu tayi mata. Baba kuma haka ta dinga jinyar naushin da Audu yayi
mata. Ya tare kacokam a ɗakin Hindu, baya raba kwana dani, baya bani kuɗin cefane, daga
ƙarshe ma Hindu ta zuga shi yace kar kin kuma ɗibar mai abinci a rumbu, ina dafawa muna
almubazzarancinshi. Da kuka na isa ɓayarin su Baba Shatu, na same su ita da Baba Sahura
suna taɓa hira.
"A Shamsiyya lafiya ya da kuka haka meke faruwa?"
Baba Shatu, Audu ne yace kar in kuma ɗibar mishi abinci a rumbu in dafa, wai
almusazzaranci muke yi mishi da abincin nashi, kuma wallahi ni ban taɓa dafa abinci na dafa
yayi yawa harna zuba ma tumaki ba, Hindu ce ke dafa abinci da yawa ta barshi ya ɓaci ta zuba
ma awaki. Ni na gaji ya sallameni kawai cin kashin yayi yawa" hawayene suka ci gaba da
zurubtu a kumatuna. Baba Sahura ta sauke ajjiyar zuchiya tace.
"Tashi kije zamu kirawoshi mu mishi magana, ki dena kukan ƴannan, maganar ke kin gaji
kuma fitsarace da rashin mutumci" Da kukan na kuma fitowa. Hindu tana tsakar gida tana daka
ma Audu dawo tana waƙe_waƙen habaici. Ina kuka nazo na wuce matan gidan. Ina jiyo Shewar
da Hindu ta saka. Shirya su Shatu nayi tsab nasa ta kama hannun ƙannenta nace suje
gidanmu, da daddare Ƙanina ya dawo dasu." Hakan kuwa akayi, tafe_tafe har sati guda bata
sauya zane ba. Ina tsaye yinwa na shirin kada ni, su Shatu kuwa suna gidanmu. Kwalla na
buɗe na zaro joji da yadin banbalasta asalin mai maiƙo da nauyi. Mahaifina ne yayi mun a

lokacin aure na, ya siya mun dan in ɗinka in samu na fita taron mata. Goya Tahira nayi, na jefa
kayan a cikin goyon na rufu da mayafi na fita. Kai tsaye gidan Inna dillaliya na shiga na bata
wannan kaya ta siye. Ta kuwa siya da daraja sosai. Gida na dawo na je ƙofar ɗakin Hindu nayi
sallama, Hindu ta amsa ciki_ciki tare da bani izinin shiga." Audu yana kwance babu riga, Hindu
tana dama mishi dawo.
"Lafiya meya kawoki ba dai akan abinci bane ko? Almubazzara sabida baki san daɗin
dukiya ba shine kike dafa abinci jingim ki barshi ya lalace ki bama awaki ko, dan na rufa miki
asiri shine kika je kinaso ki shiga tsakanina da mahaifana. Ta Allah ba taki ba Shamsiyya."
Murmushin takaici nayi, zuchiyata sai gashewa take yi, nace. Inason ka bani izini inje gidan Goggo Rakiya ne dan Allah"
"Kiji daga yau har gaban abada, duk inda kika ji kina son zuwa, na lamunce miki, ai matar
so irin su Hindu su ake yima kulle jar fata ba irinku ba. Fitarmun daga ɗaki" Hindu ta kalleni
taimun gwalo. Miƙewa nayi na wuce can hayi gidan Goggo Rakiya. Ina shiga na ɓalle da kuka
ga yunwa na shirin halakani. Zaunar dani Goggo Rakiya tayi, ta bani ɗunamen tuwo da ruwa
mai sanyi, saida naci na ƙoshi, sai naji na samu sassauci yunwa masifa ce. Goggo Rakiya tace.
"Shamsiyya ni shawarar da zan baki shine ki soma sana'a. Zan ara miki jari, akwai wata
tinkiyata mai ciki, zan siyar in dunƙuli kuɗin in baki, ki ja jari. Kina ganina babu ƙauyen da bana
kutsawa aci kasuwa dani. Kuma kinga irin cinikin ƙuli da man ƙuli da nake yi ai? Ƙauye_ƙauye
nake fita nemo gyaɗa fa ba'a bori da sanyin jiki. Musamman ma da yaranki suka kasance mata,
kinsan dai Audu bazai ma yaranki kayan ɗaki ba ko? Ƙarshenta a ɗebesu zuwa birni a
turbutsasu a gidan aiki. Ni kaina yarana biyu saida suka je su kai aikatau na shekara guda
_guda da rabi, saida suka taro kuɗin kayan ɗaki kafin aka aurad dasu. Na baya_bayannan
kuwa da sana'ata tayi ƙarfi ai kinga ni na aurad da abuna. Saifa kin tashi tsaye, kishiyarki irin
mugayen makiran matannanne, amma da sannu zata girbe koma mai ta shuka. Ajjiyar zuchiya
na sauke nace.
Goggo Rakiya bama sai kin sai da tunkiya ba, na ɗan saida suturuna kinga kuɗin, sana'ar
da zan soma ce ban sani ba. Shine nazo kiyi mun ido, tunda babu ƙauyen da baki sani ba"
"Kinyi kyan kai, kawo kuɗin in adana miki, gobe asubar fari tayi miki a gidannan, dan
gobe kasuwar ƙauyuka da yawa suna ci. Sai muje ki zazzaga ki sari abinda yayi miki. Amman
ina zuwa" fita tayi ta nufi rumbu, ta haɗomun kayan abinci sosai, ta ɗakko muttala biyar ta bani,
harda karar girki saida ta ɗaure mun. Godiya nayi sosai na nufi hanyar gida. Ina dawowa ban
jima ba su Shatu suka shigo, suma da ƙunshin garin dawa da Inna ta ƙunso musu, harda kuka,
daddawa, manda. Uwa mai daɗi kenan, Allah sarki, ni ina tausaya mata, ita tana tausaya mun,
Allah kai mana mafita.
Washe gari asubar fari kuwa, na kama hanya, su Shatu kuma nace musu in haske yayi ta
tattare ƙannenta su tafi gidanmu. Ina isa gidan Goggo Rakiya, a daddafe muka karya kumallo,
nan muka ɗauki hanya. Da yake ban sababa nasha wuya sosai, a ƙauye na uku ne na yanke
shawarar kayan koli zan sara kawai, tunda ko ledar yin ƙunzugun yara wuya take yi mana sosai,
har sai mun dangana da Bakura tukunna.
Goggo Rakiya, na samu sana'a, kayan koli zan sara, musamman ledar ƙunzugun yara, da
tawul ɗin ƙunzugun, sai in ɗan haɗa da ƴan kunnen yara da manya, da turaren tsinke, na
rambo, da 999. Goggo Rakiya tace.
"Kin kuwa yi dabara kab ƙauyen babu wata mace da take siyar da kayan koli, sai tsaffi

masu saida farin kwalli, da kuratandun kwalli. Maza zo muje in haɗaki da Ya gana, kin ganta
can, sai muji yaya abun yake, tunda shi kasuwanci in daka aka shigeshi ana wahala, zo muje.
Wajan Yagana Goggo Rakiya ta kaini, taimun bayanin yadda koli take, kuma na gamsu da sa'ar
koli. Anan na sassari abunda nasan babu a ƙauyenmu. Sai yamma lis muka nufi hanyar gida,
da tarin tulin buhunhunan gyaɗa na Goggo Rakiya cikin bodi tab. Sai dab magriba na shiga
gidan, sai wani gani_gani matan gidan keyi mini. Wucewa nayi ɗaki na ajjiye kayan sari na,
sannan na fito nayo walwala na koma na rama sallolin da ake bina. Sannan na ɗauki ledar na
nufi ɓarayin su Baba Shatu. Na nuna musu, suka sa mun albarka, sannan na koma ɗakina, dan
a ƙoshe nake mun sha dawo a kasuwa. Sai da aka sallaci Isha Mamuda ƙanina ya rako su
Shatu, kwanciya mu kayi dukkanmu. Da yake na gaji baccin nayi shi mai daɗi cike da mafarkai
masu daɗi.


*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*


MRS BUKHARI
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: BADIAT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
(GAWURTATTU UKU)

Lamba ta goma sha biyu


Washe gari tun sassafe na fito, na baje kayan kolina akan tabarma, nace.
"Matan gida ka kayan siyarwa azo a siya fa" Hindu da take cikin madafi tana dafa abinci, ta
fito zuruf. Dan a gidan ko wacce girkinta take yi daban, hatta runbu kowanne Namiji da nashi
rumbun. Sunturi ta soma yi a tsakar gidan sai huci take yi. Ni dai hankalina na kan kaya da
matan gida suke ta siye. Saida suka kammala tsab, na ɗauki kayannan na zuba a fanteka, na
fita. Haka naita zagaye gida gida, har gaba da ƙauyenmu saida naje. Kuma nayi ciniki sosai,
wasu sun biya a take wasu kuma sun ɗauka akan sai nan da kwana biyu zasu biya. Jefin
azahar na shigo gida, da ƴan tsirarin kayan daya rage. Ina dure fantekata, na wuce madafi na
haɗa kara na tsaida ruwan sanwa. Da sauri Hindu ta shige ɗaki wajan Audu.


Hindu:
"Malam tashi kaji abun mamaki, yau baƙin ciki kamar zai kasheni, ashe munafurtata kakeyi,
shine ka zage kaba Shamsiyya jari, ka ɗibar mata hatsi. Kaji gorin data dinga yi mun a tsakar
gida kuwa." Kukan baƙin ciki ta raushe ma da Audu dashi. A zabure ya miƙe yace.
"Ita da bakinta tace miki nina bata jari da hatsi? Wallahi sharri take son tayi mun, gashi ta
haɗamu rikici, haba Hinduwa ta, ai kinsan Audu bazai munafurceki ba, Bari ina zuwa." Furr ya
tashi ya fito. Hindu ta daka tsalle ta shiga rawa."

Shamsiyya:
Ina duƙe ina tuƙa tuwo kawai naji duka takota ina, ihu na soma yi, da ƙyar matan gida suka
kwaceni a hannun Audu tuwona sai ƙauri yake yi.
"Mara mutunci ni zakiyi wa ƙarya." Baba Sahura tace.
"Ba magana akeyi maka ba ka share mutane maras mutunci, me tayi maka kake dukanta
haka? Haba Audu yanzu ba zaka bar Shamsiyya tasha ruwa ba." Yana huci yace.
"Baba Sahura, tsakar gida ta fito tana faɗe wai na bata jari,na bata hatsi. Hatsin da
almubazzarancinshi take yi mun, shi yasa na hanata, gashi yanzu tuwo take tuƙawa, ta satar
mun abinci tana son ganin ta haɗani rikici da Hindu." Baba Shatu tace.
"Kai kaji da kunnenka sanda take faɗe ko labarin aka kai maka?, Audu wallahi kaji tsoron
Allah. Ni na kasa sanin waye mai gaskiya a tsakaninka da Shamsiyya fa. Ni dai wucewa nayi
na koma kitchen ina kuka ina tuƙin tuwon. Daya sulala na kwashe, muka shiga ɗaki da yarana.
Amman fa na kasa sa loma a bakina, wannan auren ni ya'isheni, yarana na saka a gaba, sai
loma suke kaiwa bakinsu, hankalin su a kwance, sai naji nafi jin sha'awar rayuwar yarinta, fiye
da girma. Haka rayuwa taita juyawa tamkar tamaule. Abubbuwa da dama sun faffaru, shekaru
sun tura, har ni da Hindu mun sake haihuwa. Wannan karon duk mata muka haifa. Shekara
ɗaya da wata biyar na kuma haihuwa wannan karon namiji na samu. Na haihu da wata biyar
Hindu ta kuma suntulo ɗiyarta mace. A lokacin komai ya kuma dagulewa, ɗan jarin da nake

taƙama dashi hidimar yara ya cinye. Dena sana'ar koli nayi, na sai da kayan jerena kab, na tada
jari. Goggo Rakiya taimun ido a sana'ar man ƙuli da kulin. Sana'ace mai wuyar gaske, dan curin
tunkuza ta fidda mai akwai wuya. Amma akwai riba. Yarana nake son sawa a makarantar boko,
amma Audu fur yaƙi yarda. Ni kuma a wannan karon na nuna mishi tsurin kai irin namu na
mata, dan har ƙara na kaishi wajan malam Babba, daga wajanshi da abun yaƙi muka ɗunguma
gaban mai gari. Da ƙyar Audu ya yarda na jefa yarana a makaranta, zagi kuwa babu irin wanda
bansha ba a wajan su Baba Sahura, da matan gidan. Damma iyayena Allah yayi musu
rasuwane, da bazan ma soma jayayya da Audu ba sam. Naci alwashi in duk ƙarfin jikina zai
ƙare, zan ƙarar dashi a sana'ata dan in baiwa yarana mata ilimi, burina inga rayuwarsu tayi kyau
ta inganta. Da wasa bana yi musu sha'awar aure a cikin wannan ƙauyan, ko da za su yi, nafi
son su san ilimin zamani, dana addini, na tabbatar komai zaizo musu da sauƙi in sha Allah.
Soma zuwansu makaranta ya sani farin ciki mara musaltuwa. Tun tara suke fita a gida, su hau
bodi zuwa Bakura. Basu suke shigowa ba, sai yamma lis. Kuma Allah ya dafa mun yaran suka
mayar da hankali sosai a karatun. Nima sai naji na sake samun ƙarfin guiwar zage damtse
wajan sana'ata. Yaran Hindu kuwa babu yasu a wajan Audu. Duk mazan an tarkatasu zuwa
almajirci, da sauran yaran gidan. Mata_matan kawai aka bar mata. Suma kuma ta shiga ɗaura
musu abun sana'a suna shiga Bakura. Daga haka suka ɗebo hanyar lalacewa."
Ina zaune a tsakar gida ina murjin tunkuza, sai na jiyo muryar Audu yana raɗa mun kira.
"Shamsiyya nifa bazan yarda da iskanci ba. Yarannan ance ana ganinsu a wajan
makaranta a wani kango. Ba zaki lalata mun yara ba, dole abar makarantar su dawo gida
kawai." Gabana ya yanke ya faɗi tare da fatan Allah yasa ba haka zancan yake ba.
Haba Audu, meya ruwanka da su Shatu yaran bora? Ai wallahi na ɗauka ko zaki ka gani
zai cinyesu, ba zaka iya kawo musu ɗauki ba. Amma ka sani yarana dole suyi karatu, dan da
gumina, da jinin jikina nake neman kuɗin da zan biya musu na littattafai da fensiri. Kuma ina
binsu da adda'ar kariya." "Rufa mun baki bazasu sake zuwa ba na faɗa miki." Hindu ce tayi maza ta iso gabanshi
tace.
"Haba malam, ka barsu suci gaba da zuwa makaranta, kai baka jin ana labarinsu a
ƙauyennan su da yaran gidan malam? Su kaɗaine suke zuwa boko duk ƙauyannan,kuma sune
marasa kunyar ƙauyannan, nifa inna shiga gidan sha'ani, har nuna ni akeyi tamkar watan
ramadana. Barta ai tunda ita bata bin umarninka. Nan da take yawo ƙwararo kwararo da tasa a
kanta tana tallar kayan koli, sau nawa ka hanata? Amma ai bata hanu ba sam. Muje malam
kasha dawo mai sanyi" a gaba ta tusashi suka shige. Wani yawu na haɗiye muƙut, na zauna
naci gaba da aikina. Har su Shatu suka dawo zuciyata ɗaci take yi mun. A ɗaki nake
tambayarsu ance ana ganinsu a wani kango ba a makaranta ba. Shatu tace.
"La Inna wallahi bamu taɓa shiga wani kango ba. Sau ɗaya da zamu wuce na leƙa
kangon dake jikin makarantarmu, saina hango, Siyama ita da wasu maza. Amma kamar abinci
take siyar musu, da muka haɗa idanu, shine ta miƙe da sauri."
Ajjiyar zuchiya na sauke.
"Ku kiyaye Shatu, ki kula da ƙannenki, su kuma Allah ya shiryesu. Kizo ki kai ma matar mai
gari man ƙulinta, tun ɗazu take aike, amma yaran gidan duk manyan sun kama gabansu."

MRS BUKHARI[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU




Lamba ta goma sha huɗu




MUSINA:
Ina sauka a bodi na nufi gida a jiƙe sharab. Da malam naci karo a zaure.
"Musina ince dai lafiya na ganki da kaya niƙi_niƙi a ɗaure, karki sake ki cemun yaji kikayo"
Babu komai malam, a asibiti ne ake buƙatar in dinga zuwa kullum daga yau har nanda mako
biyu. Shine Yawalen yace in dawo gida tunda kusa ne" Nazarina yake tayi, kafin yace.
"Kin tabbatar shi yace ki zauna har sai kin kammala da asibiti, kuma kin tabbatar ba matsa
mishi kikayi ba, hakan kuma bazai zama kin shiga hakkinshi ba?
E Malam " Kawai na iya cewa, tsorona kar malam ya rubto ni.
"Ki shiga ciki, to ki ajjiye kayan ki sake wasu, saiki tafi asibitin. Ajjiyar zuchiya na sauke banyi
zaton abun zai zo mun da sauƙi haka ba. Baba Lami na ɗaka na shigo. Na iske Inna bata nan.
"Musina kece da kaya, kaddai sakinki Yawale yayi?" Harta soma fitar da kwalla.
A'a inna Lami ba sakina yayi ba. Sabida yanayin asibiti ne, kuma Malam ya amince." Baki ta
washe, ta

9 / 21