Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
gaban kuliya, suna neman a ƙwato
musu hakkinsu dana mahaifiyarsu. Tun daga lokacin da aka haifesu har zuwa girmansu. Domun
baisan komai nasu ba. Kuma ya cuskuna ma uwarsu ainun. Dan haka suna neman hakkinsu a
wajan Audu." Goggo Rakiya na kaiwa nan, fada ta ɗauki tafi da sowa. Saida mai gari ya dakatar
dasu. Ya dubi Goggo Rakiya yace.
"Rakiya, ni ina ganin da anyi sulhu anan fada ta da zaifi. Duk da nasan dolen Audu da
Shazili su amsa kiran kuliya. Amma ya yara zasu kai ƙarar mahaifinsu? Shifa tuwo ba'a sauya
mishi suna.
Goggo Rakiya tace.
"Amma in ba'a sauyama tuwo suna, ai hannunka yana ruɓewa ka je asibiti a yanke maka ko?
To da kabarshi mana kaga in baici gangar jikinba duka." Fada tayi shiru kowa saida ya kaɗu da
wannan lamari. Aka saka su Zaliha a gaba akaita tattaunawa a kansu, cewar baza suyi albarka
ba." Mai gari ya tashi fadawa biyu yasa suyi mishi kiran Audu."
Audu:
Yana zaune yana shan fura, Hindu kuma tana gefenshi sai sake zuga shi take yi akan lallai, ko
a cikin gidanne tunda da samari, ya tursasa musu su auri su Shatu kowa ya huta."
"Damma baka zuwa sha'ani, da kaji yanda ake zagin Shamsiyya da ƙattin yaranta. Kuma
abun takaicin, zagin har takan nawa yaran yake sakkowa. Yanzu Hannatu, mane minta cewa fa
yayi in da gaske su Shatu yayyenta ne, bazai iya aurenta ba. Cikin dabara yanzu nake son tayi
mun kiran yaron mu zauna mu tattauna" Audu yace. "Shawararki mai kyauce sosai Hindu, ni kam nayi dacen samun mace mai hangen nesa.
Aini ban tuno da samarin gidan ba, da bazan fita har dawa ina shelar masu aurensu ba."
Sallamar Salame suka jiyo a ƙofar ɗakin. Hindu ta amsa mata."
"Baban Shatu, mai gari ne ya aiko ayi kiranka. Manzannin suna waje"
"To gani nan Salame" Miƙewa yayi, yasa babbar riga, ya kifa hularshi.
"E bari inje ɗin Hindu, ƙila an samu wanda ya daki ƙirji zaiyi jahaɗin auren ɗaya daga
cikin yarannan ne" Yana kaiwa nan ya fita. Hindu ta sauke ajjiyar zuchiya na cin galaba akan
raba Audu da yaran Musina data yi." Zainaba ce ta shigo cikin ɗakin hindu da kururuwar ihu,
fuskarta duk a kumbure, da halama duka taci sosai." "Ma'aikin Allah na madina ni Hindu. Haɗarin Bodi kuka yi ne Zainaba?" Cikin kuka tace.
" Fatsima ce tasa Tanimu ya rubuta mun takaddata saki uku. Kuma yace in tawo da
yarana baya ƙaunar mu. Bayan tasa yayi mun mugun duka." Ɗiyar Zainaba ce ƙarama ta shigo
mai sunan Hindu. Ga goyo ɗanye a bayan Zainaba."
MRS BUKHARI[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA ASHIRIN"
INA MIƘA ƊUNBUN GODIYATA S GAREKU MASOYA RUBUTUNA. HAƘIƘA WANNAN
LABARIN YA KAINI WANI MATSAYI DA MATAKIN DA BAN TAƁA TUNANIN ZAI KAINI BA.
HAJIYA TURAI NAGA SAƘO INA GODIYA MAI TARIN YAWA.
YAWALE:
Ƙarema yarana kallo yake yi. Masha Allah ko wanne cikinsu ya ginu da tarbiyya, gasu da
mugun haɗin kai da soyayyar junansu. Gashi kowa yana da abun hannunshi. Yaran mowa
Kumatu kuwa, Saminun ne dama dama a cikinsu, amma du sauran basa sana'a sai yawon
ɓel_ɓel da bin inuwa. Muttaƙa kuwa yayi nisa baya jin kira. Yanzu haka yana can a kulle a
kurkukun bayan gari, mai gari yasa an kamoshi shi da abokan satar tashi, ya garƙamesu a mari.
Babu irin bori da tumamin da Kumatu bata yi ba a tsakar gida."
"Musina nayi mamakin abunda kike shirin sa yarana suyi. Wata kam ba kya ƙaunar kiga
muna zaune lafiya. Shin me Kumatu tayi miki da kika ƙi jinin yaranki su haɗe kansu da yaranta?
Duk abinda yaranki suka kawo miki sai dai kici ke kaɗai. Kin nuna musu banda galihu a wajanki,
kuma baki basu tarbiyyar su kula da Yadikkonsu Kumatu ba. Wai dam ɗiban albarka har Jamilu
ya mallaki garjejen fili a ƙauyannan amman ni ubanshi banda labari Musina, ga gonakai daya
mallaka da sa hannun mai gari amman ni ina nan hoto jibi yanda na dawo dan tsabar wahala
komai nawa ya ƙare, dan baƙin hali yarana dana arziki amman kin hana su taimaka mun.
Wallahi zan kafa dokoki a gidannan kuma dole abi, zaman zai sauya ko dan haɗin kan
yaranmu. Ni dai bance uhm ba, bare um_um jira nake ya gama zazzago duk abinda yake
cikinshi tukunna, su Jamilu sunyi tsuru_tsuru suna kallon mahaifinsu, ba'a taɓa yin zama irin
wannan ba a gidannan sai yau.
"Daga yau duk abinda yaran wajanki suka siyo suka kawo miki, na ci, ko sutura, to dole su
siyo da Yadikkonsu, in basu da halin yi muku duka, sai suyi haƙuri. Nan Alawiyya take wucewa
da babban buhu shaƙe da kayan alatu, bushashahen kifi a miyarki kamar zaiyi magana, amman
baki basu tarbiyyar su kula dani ba. To itama duk wata inya ƙare duk abinda ta siyo a raba da
Kumatu. Jamilu da yake ɗiban hatsin da bai wuce rabin buhu ba ya bamu, shima na soke dole
ya raba duk hatsin daya samu gida biyu, rabin a rumbunki, rabi a rumbun Kumatu bayan ya
ware na siyarwa. Kema Kulu inajin labarin jar biya da kike kawo ma uwarki cike da zabi duk
wata. Daga yau ko ki haɗa da Kumatu ko ki bari.Ita kanta Kattume ƴar gatan uwa da tana wajan
zamannan wallahi saina bigeta ma, dan inajin hidin_dimun da take yi ita da mijinta a gidannan,
amman dai_dai da hatsi baki taɓa bari ta auno bata Kumatu ba. Sannan Alawiyya da Zubaida
duk su fitar da mijin Aure na gaji da ganinsu a gabana anayi mun ɗan kallo a gari. Wani iri
numfashina yake yi, da ba dan yara ne a gabanmu ba, da yau Yawale yaga hau irin namu na
masu haƙuri. Waigowa yayi wajan su Jamilu da suke jere da Saminu.
"Kai Jamilu na haɗaka da Zulai ƴar wajan Yayana Jamilu ka aureta, mun gama maganar
da Yaya Jamilun, tuwona maina. Kai kuma Mustafa sai ka auri marka yarinyar Mudi duk a haɗe
ayi auren dana Ƙasimu. Ke kuma Sauma'iyya mun gama magana da Zaidu zai aureki ya haɗaki
da Harira zaki ci gaba da zama a cikin gidannan. Gida bai ƙoshi ba baza'a kaima dawa ba.
Alawiyya, Zubaida, ku fidda mijin aure nanda mako guda in ba haka ba. Akwai samari fal
gidannan zan tilasta musu su aureku, duk da baza su so auren fitsararru irinku ba. Ƙasimu ka
samu Saminu zai yankar maka fili, kuma Jamilu ku sameshi a yanka muku." Kallon Yawale
kawai nake yi, ko kunya baya ji sai hukunci yake zartarwa akan yarana dana gama wahala
akansu. Har yake tunanin haɗa Jamiluna da Zulai yarinyar data zubar da ciki watan jiya, yawon
bin maza take yi kwararo_kwararo. Ita kuma Marka ba ƙaramar fitsararriya bace, dan ko aiki,ko
aike uwarta bata isa ta sanyata ba, sune za'a aura ma yarana, dan anga Allah ya tallafi
rayuwarsu komai ya wuce rayuwa tayi mana shar. Su Jamilu sai kallona suke yi, kallo irinna kiyi
mana rai. Ni dai Yawale da Kumatu nake kallo kawai, cike da maɗaukakin mamaki.
"Sannan Kumatu zanci gaba da muku rabon kwana ke da Musina, kuma duk nauyinta
dake kaina zan sauke mata, fatana ku zauna lafiya.'
Kutumar bura ubanka, Yawale kaine kake faɗen haka da bakinka?" Bansan sanda
bakina ya subce na narko wannan ashariya a gaban yara ba. Duk suka kalleni, nayi maza na
sauke kaina. Yawake kuwa sai murmusawa yake yi, babu halamar fishi ko tunzura akan
ashariyar dana narko mishi. Kallon su jamilu yayi yace. "Ku tashi ku tafi, na sallameku Allah yayi muku albarka, ayi haƙuri kuma a yafi juna.
Komai ya wuce yaran kirki" sai washe baki Yawale yake yi, nasan dukiyar hannunsu yake kallo
kawai. Ina kallo yaran suka watse, ai fitarsu ke da wuya na miƙe.
Yawale bari kaji in faɗama, aure ni da kai ya ƙare daga yau, yau kaji kana son ka sake
mayar dani matarka, sabida yarana sun samu arziki. Ni kuma ina baƙin ciki kaci dukiyarsu. Har
hake cewa wai duk abinda suka kawo mun su ba Kumatu. Da kai da Kumatu Allah ya tsine
muku albarka, ƴan iska, ƴan kutumar uba. Kuma wallahi babu ɗana guda ɗaya da zaiyi aure a
zuriyarka. Yarona daya salwanta sanadiyyar sharrin da Kumatu tayi mishi. Bazan yafe ba, sai
wutar Allah ta ciku." Da Yawale da Kumatun duk baki suka buɗe suna kallona. Dan na fusata
ainun, shi kuma Yawale sai lallashina yake yi, sabida yana son cin banza. Kumatu tace.
"Musina Yawalen kike zagi haka? Wani mugun kallo na jefa mata nace.
"Dake dashi kun yayimi ƙwanyar bura ubanku, wakilin ɗaurin aurenku yaci uwatai. Haka na
fice a ɗakin kamar kububuwa, ina huci dan jikina har kyarma yake yi mun, na koma nawa ɗakin.
Duk yaran suna tsaitsaye sunyi cirko_cirko. Su kansu basu taɓa ganina a cikin irin wannan
yanayin ba. Hakanne ya tilasta musu yin shiru, gudun karsu faɗi wani abun da zai kuma
tunzurani. Kulu ta kasa tafiya gidanta, da dukkan halamu kwana zata yi, matan duk suka
baibayeni"
Mrs Bukhari
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: GAWURTATTU UKU
Lamba ta Ashirin da ɗaya
BAKORI:
Laila:
Da idanu nabi Shehu ina karantar yanayinshi kawai.
"Laila tunda babu gaisuwa ina wuni" murmushi nayi mishi, na miƙa mishi Ɗahiru, yasa hannu
ya karɓeshi yana kallonshi, take sai fuskarshi ta sauya, daga fara'a zuwa akasin hakan.
Ina Wuni Shehu, kazo lafiya?"
"Lafiya lau Laila. Kuma na fito jeji lafiyar Allah, harma an zaɓeni a matsayin wanda za'a
bama kujerar sarkin mafarauta, har an saka rana. Sai dai ina fargabar abunda kaje kazo,
sabida wannan yaron naki, zai iya kawo mun cikas a mulkina. Hakanne yasa zan ƙara aure
Laila, harma an saka bikin namu, saura kwana goma cib." Banyi mamakin auren da Shehu yace
zauyi ba, maganganunshi sunfi bani mamaki gaya. Auren mace sama da ɗaya haka addininmu
yazo dashi, muddin in miji zai iya adalci a tsakani. Malam bahaushe yana girmama lamarin ƙarin
aure sosai, musamman ga mu ƴan ƙauye, dan ɗan ƙauye iyakar jin daɗinshi ya ƙare a
kwanciyar aure da mace ne, shi yasa suke girmama dare. Balle Shehu da yafi ƙarfina, dan nayi
imani Shehu yafi ƙarfin mace biyu ma. Amma aurennan babu makawa zaiyi ne danya mayar
dani bora, an gama canfani cewar ni mai farar ƙafa ce.
Allah ya sanya alkairi. Na taya ka murnar cin nasarar zama zakin mafarauta. Aure kuma
Allah ya bamu zaman lafiya. Ina neman alfarma Shehu."
Jin ban ɗaga hankalina ba yasa Shehu ya sassauto.
"Ina jinki Laila" Nisawa nayi cikin ɗacin rai da ƙunan zuchiya nace.
Saura kwana goma muyi arba'in ina son ka ƙara mun kwana goma akai, sabida zanyi
ziyare_ziyaren dangi na. Har can Dutsin ma nake son zuwa wajan Baba Kande." Kai ya sosa
yace.
"Babu komai, zaki iya ƙara kwana goma akai ma, baki da matsala. Karɓeshi ki kwantar
dashi, ni zan koma." Hawayen da nake dannewa ya zubo mun, ganin yanda yake nuna halin ko
in kula akan Ɗahiru. Nasan ni da Ɗahiru cikin garari zamu yi rayuwa a hannun Shehu, ga aure
zaiyi sabida ya samu kwanciyar hankali a wajan matar da zai aura. A tunaninshi ma na gama
tashi a aiki, tunda ya gama buɗani, ya nakasa mun ƙafata, tawa ta ƙare ko? Hmm maza
mutanen mu ( Allah ya gafartama Aisha Ɗan kano) Kallona yayi yace.
"Hmm Laila kenan, ashe ba zaki godemun ba dana zaɓi in ƙara aure ba tare dana sakeki
ba? Kinsan irin iftila'in dazai shafeni a sanadiyyar wannan abun da kika haifa kuwa, baki da
labarin yanzu haka a gida, amma daina sayen kayan siyarwan da su Baba suke sayarwa,
sabida baza'a iya aiko yara ba, shine har kina da idanun kuka dan zan ƙara aure, me yasa mata
baku da adalcine ku, baza ku tausaya ma maza ba?" A al'adance laifine babba in ɗago in kalli
Shehu ma a yayin da yake cikin fishi, in kuwa na mayar mishi da martani, tamkar na aikata wani
zunubine mai girma. Dole na haɗiye maganganun da Shehu ya dinga yaɓa mini, a wajen ya fita
ya barni, Ɗahiru na rungume a hannuna. Ina jiyo Shehu na gaisawa da Malam daya shigo
yanzu.
Shehu:
"A Shehu kaine a tafe da rana haka?" Cewar malam. Shehu cikin girma da ladabi ya gaishe
da malam, yake kuma labarta mishi batun zaiyi aure nan da kwana goma. Su Daddo suna
tsakar gidan suna jiyo su. Malam yace.
"Naji labarin a wajan Buba, dan jiya na shiga Dutsin ma ɗin naje cin kasuwa. Kuma ya
labarta mun komai. Fatanmu yarannan Allah ya basu zaman lafiya a tsakaninsu kawai. Ina taya
ka murna Sarkin mafarauta" Dariya da Shehu da malam suka saka, yayi musu sallama ya fita.
Ta Asibi:
"Malam ni na kasa gane wannan zarwancen da kuke yi da Shehu fa" Murmushi Malam yayi,
tare da nufosu. A gefensu ya samu waje yaima kanshi mazauni.
"Auren da Shehu Zaiyi ba kowa zai Aura ba, sai Asiya ƴar Kande ƙanwarki Ta Asibi. Malam
Buba mahaifin Asiyan ya shaida mun, wai sunfi shekara guda suna nema. Shehun ya auri Laila
da kaɗan suka soma nema. Abunda Allah ya nufa, Annabi sai ceto. Daddo tace.
"Asiya dai ɗiyar ƙanwar Yaya uwa ɗaya uba ɗaya, ita Shehu zai aura Malam? Ai ana barin
halas dan kunya, duk matan da suke a gari, baiga wacce tayi mishi ba sai Asiya, yarinyar da
taje birni ta gama buɗe idanunta a gidan aiki da aka kaita. Ta Asibi tama rasa tacewa, ta rasa
dalilin da yasa ƴar uwarta bata ƙaunar farin cikinta, gashi su biyu rak iyayensu suka haifa. Taso
ta Auri malam Zangina dan taso ta ribaceshi ya jiya ma Ta Asibi baya. Amma da yake yafi
sha'awar mace mai alkunya ne yasa yaima Kande tawaye. Da bata samu hakan ba saita ƙulla
zazzafar gaba da ƙiyayya a tsakaninta da ƴar uwar tata. Ta Asibi kasancewar itace babba, sai
taita yin haƙuri da halayyar Kande, taci gaba da janta a jika, taci gaba da ziyartarta tana kuma yi
mata alkairi. Shine daga baya ta saki jikinta, ashe ta ciki na ciki. Baƙin ciki Ta Asibi ta dinga
haɗiya. Malam yace.
"Ta Asibi naga kin ƙume, abinda nake so dake shine. Kuyi haƙuri ku duka, kuma ku taushi
zuchiyar Laila ta daure tayi ma Shehu biyayya akan auren ƴar uwarta da zaiyi. Taci girma ta
kame kanta a matsayinta na babba. Kuma, ku daure karku nuna ma Kande wani abu na
sosuwar rai, gudun lalacewar zumuncinku, da Laila da Asiya duk naki ne. Abinda Shehu yayi ba
laifi bane, tunda ba Allah ya saɓa ma ba. Sai dai yin hakan ya kaucewa al'adar malam
bahaushe mu da aka sani da yakana da alƙunya. Kande zata zo yau haka Malam Buban ya
faɗa mun." Yana kai aya ya kurkure bakinshi da ruwan buta yaja langar abincinshi, ya soma cin
gwaɗon zogale. Bai idasa gama cin zogalennanba saiga sallamar Kande da ɗan buhun kayanta
a ƙunshe, Asiya na biye da'ita. Ta Asibi ta kallesu dukkansu tana jin wani zafi da zugin Kande.
Malam Zangina ne yai mata ido, saita ɗan saki fuskarta.
"Kande kune tafe a kwanɗeɗiyar ranar nan? Maraba lale, sannunku da zuwa Asiya"
Cewar Daddo kenan dan Ta Asibi ta kasa iya sarrafa harshenta balle tayi musu sannu da zuwa.
Kande ta ya da buhun kayanta, tana faɗin.
"Wash Allah makashin kakata Rakiya. Malam Zangina yau baka fita kasuwar bane?"
Cikin girma yace.
"Nafita. Abinci dai nadawo inci, sai in koma Jafaru shima saiya je yaci. Sannunku da
Hanya." Gaggaisawa akayi dukka. Malam Zangina ya wanke hannunshi, yai musu sallama ya
fice."
Laila:
Ina tsaye ina share hawayena, na jiyo shigowar Inna Kande, kasancewar tana da ƙarfin murya.
Da sauri nashare hawayena. Na shinfiɗe Ɗahiru na fita.
Inna kune a tafe? Asiya hmm ai nayi fishi wallahi kuwa" Kusa da Inna Kande naje na
zauna,muka gaggaisa. Baki ɗaya saina kasa gane ma Asiya dan ko fara'a taƙi yi mun. Saɓanin
da, da in muka haɗu tamkar zamu cinye junanmu, hira kuwa sai mun raba dare munayi. Saita
tunomun zance da take rakani wajan Shehu in yazo, muita wasa da dariya. Maganar Inna
Kande ce ta katse mun tunanina.
"Laila ashe mata