Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
"Mai riga ni ina ganin bai dace ace an bar yarinyar nan a gida ba, kamata yayi a tafi
da'ita asibiti." Inji Laraba kenan. Matar malam tace.
"Ana ƙoƙari akan lafiyar tata, kinga kofin rubutu yanzu malam ya aiko, aka shafe mata
jikinta dashi. Baban yara kuwa ya shiga jeji zai tsinko mata magani, ya farauto mata naman
gashi, kar a raina ƙoƙarin Laraba ayi haƙuri" Baba mai riga tace.
"Kinsan ƴan birni duk inda suka kai suka kawo sai sun raina baƙauye. In banda raini
Fulani Laraba, ina ke ina maganar asibiti a nan gidan na mafarauta, ƴan na gada ba ƴan haye
ba. Daga nan cikin gida Shehu zai iya kiran zomo ko gada, kuma dolenta tazo, harmu za'aima
zancan banza?" Laraba ta buɗe baki zata mayar ma da Baba mai riga martani. Daddo ta haneta
ta hanyar girgiza mata kai, sannan tace.
"Mai riga ayi haƙuri kinsan sha'anin yara. Fatanmu Allah ya bata lafiya." Shehu ne yai
sallama ya shigo.
"Matar malam, malam yace a bada jaririn, wanzami yazo zai dubashi ko da maganin da
zai bayar." Laraba tasa hannu ta ɗakko jaririn taba Shehu. A mugun wulaƙance ya karɓi yaron,
yana wani huhhura hancinshi, ala dole waishi an cuceshi."
Shehu:
Fita yayi da Jaririn zuwa ƙofar gida. Akan taburmar kaba ya samu Malam da wanzan.
"Miƙa mishi yaron Shehu, meye haka ka riƙo yaro sheƙeƙe? Wallahi ka kiyayeni shin me
ruwa ukun banza (shashashan banza) Inji Malam.
Shehu baice komai ba, ya miƙa ma wanzan jaririn. A hankali ya sunce ƙunzugun jikin yaron.
Halittarshi ta bayyana ta mace da namiji, na mazan a sama, na matan a ƙasa. Allah sarkin
girma, mai yin yanda yaso da bawanshi, a lokacin da yaso. Sarkin da babu irinshi, sarkin daya
haɗa ma wannan jariri al'aura biyu a jikinshi. Tsarki ya tabbata ga wannan ubangiji. Wanzan ya juya yaron, ya juya, yace da malam.
"Babu wani magani da za'a bama yaronnan da sunan maganin kashe halitta ɗaya ta
jikinshi. Ni abunda nake gani kawai malam, kayi mai rubutun tsari yasha, ƙila mayu ne suka
shafeshi ko aljanu. Riƙeshi Shehu a mayar ma da mata shi sabida sanyi. Ranar suna zanzo inyi
mai aski a cire mishi beli. Shehu jikinshi a mugun mace mus ya mayar da yaron ya dawo ya
zauna a gaban malam.
"Nayi ma jaririn huɗuba da Ɗahiru domun tunawa da ɗan uwanmu. Kai kuma kayi haƙuri,
ka ga uwar yaronnan? Nayi imani saita fika shiga damuwa, dan duk wata tsangwama da
za'aima yaronnan inya girma, ita zaifi taɓawa. Kuma ba'ita taba kanta wannan yaro ba, Allah
shiya bamu. Kai dai kaci gaba da shirinka na shiga jeji dan zaɓen fidda gwani. Akwai rubutu
gora biyu da zaka ƙarashe sha. Fatanmu ace kai ka zama sarkin mafarautan Unguwar Alƙali.
Nasan kai jarumine, sai dai fa jejin da zaku shiga yana da haɗari sosai, ko a mutu ko ayi rai ne.
Shi yasa ma in har mutum ya kwana bakwai a cikin jejin ya fito sumul ake naɗashi sarkin
mafarauta. Kuma Lauwali ya shirya tsab shima dan baka wasu layi da guru na layar zana ba
wanda muka saba amfani dashi ba. Yanzu haka Baban yara akwai wani gashi da zaima shima
laƙanine. Ka mayar da kanka akan sarautar dake tunkaroka karka watsar da darajar gidannan,
mu da muka gaji farauta tun kakanninmu." Godiya Shehu yayi ma Malam. Amma gani yake yi,
kamar ya faɗi akan zaɓen fidda gwani da za'ayi, dan fidda sarkin mafarauta. A tunaninshi
sabida Laila ta haifa mishi mata maza.
Mrs Bukhari ce
Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman
na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas
mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata
saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin
07068606171
08104335144
08179523215
*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._
*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
MATA IYAYEN GIJI
BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
(GAWURTATTU UKU)
*_GAWURTATTU UKU2023_*
*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*
SAMFOTI
LAMBA TA TARA
KADUNA. KURMIN MASHI:
anguwace ta talakawa futuk, duk wanda ka gani a cikin unguwar mai fafutukar neman na sawa
a bakin salatine, hakan yasa gidajen wajan yawancinsu na haya ne. Wani gida na hango da
wata mata a tsakar gidan da tsohon cikinta. Yarane a gabanta mace da namiji. Ƙuɗi ta sunce a
hannun zanenta, nera biyar ta miƙa ma babban, da gani shine babba. "Maza Zulƙifulu ka kama hannun Hadiza kuje makaranta, ga kuɗin laraba nan." Baban
yarannanne ya dirƙo ta katanga, sai gashi tik a tsakar gidan yana haki."
"Subuhanallahi Ɗahiru meye haka kuma, ko dai tsiyar ka kuma yowa ne?" Cikin masifa
yace.
"Dallah rabu dani, wace tsiya zan kuma yowa. Bashi ya cika mun hanjina yana shirin
halakani. Labari naji fa Rabe yaje kira mun ƴan doka akan kuɗinshi." Tani tace.
"Ni kaina duk tsukukunnan bashi suke bina Ɗahiru, fita wannan ta gagareni, yanzu
meye abunyi to?"
"Garin zamu bari Tani, bazan yi sake ƴan doka su kamani ba"
"Me kace Ɗahiru, to in mun bar garin ina muka nufa?" Ɗahiru yace.
"Saleri zamu koma Tani na riga na samu sana'a. Ɗan Audu ya koya mun duba, da
yanda ake dukan ƙasa tayi magana, malumta zan soma da mun isa ƙauyen Saleri. Dama kuma
kinsan nasan wasu laƙanin abubbuwa da dama, yawon almajirci da farauta wanne irine bamu yi
ba, baduniye ne ni cikakke. Sako mayafinki mu wuce, dan tsaiwa ɗiban tsumma zai iya tona
mana asiri." Tani ta riƙe ƙugu tace.
"Ɗahiru ka mance tsiyar daka tabka a Saleri, ko ka manta da yanda muka fito daga
ƙyauyen? Munfa tafi mun bar baya da ƙura, muna jiyo ihun matasa suna shirin ƙone gidanku,
shine yanzu zamu kwashi jiki mu koma ƙauye?"
"Ai Tani duk abinda ya koro ɓera daga rami kika ga ya faɗa wuta. To abunda yake cikin
ramin yafi wutar bala'i."
"Bikinka daya rage saura sati biyu fa, za'a ɗaura mu tafi da matar ƙauyene?
"Kinci ubanki ƴar gatan uwa kai" Dariya Tani tayi. Mayafi ta ɗakko ta fito.
"Ku same ni a titin baya, dan tafiyata daku bazai yiwu ba." Yana kaiwa ƙarshen
maganarshi ya zuba da gudu." Tani taja hannun yara suka nufi titi. A tsaye suka samu Ɗahiru,
suna isowa suka tari abun hawa zuwa tasha. Tafiyar awa biyar ce ta kaisu Bauchi. Daga Bauchi
suka hau motar Azare, daga nan suka shiga bodi. Tani ta galaiba iyakar galabaita.
Saleri:
Laila.
A hankali na buɗe idanuna da Goggo Laraba na soma haɗa idanu, idanuna sai ruwa_ruwa suke
yi.
"Alhamdulillah Daddo Laila ta farka. Sannu Laila kinji, yaya kike ji a jikin naki" Cikin ƙarfin hali
da tawakkali nace.
Bana jin komai sai rashin ƙarfi" Daddo tace.
"Sannu ƴannan Allah ya ƙara sauƙi."
Yunwa nake ji Goggo."
Da sauri Goggo Laraba ta fita, bata jima ba ta dawo da tuwo mai zafi yana ta turiri. Yaji ta baɗa
mun da man shanu. Jikina har yana rawa, duk yawan tuwon sai da na cinye shi tas. Saina soma
jin sanyi_sanyi na shigata. Jaririna nake ta kallo a hannun Daddo tana bashi ruwa. Matar malam
ce ta shigo. "A abun yayi kyau. Sannu Laila, yaya jikin kuma, ta farka kenan?"
Da sauƙi matar Malam.
Zuchiyata sai tunano mun wannan magen dana gani take yi. Amma nasan jaririn dana haifa
mayu basu shafe shi ba. Dan ɗan gidan mafarauta ne, a zauren shigowa zauren gidannan
akwai kafin Mayu a sagale a jikin azara, kusa da inda tsetsewalu suke guje_gujensu. ( Irin ƴan
ƙananun tsuntsayennan da suke karakaina a zaurukan ƙasar Hausa ada) Adda'a nayi akan
Allah yai mun tsari da dukkan abunda zai zama sharri a gareni.
"Ungo Laila ɗan sa mishi nonon ya ɗan dinga zuƙa. A haka har ruwan zai kawo. Hanuna har
rawa yake yi dana karɓeshi. Tausayi da ƙaunar jaririn sai ƙara burunƙasa yake a zuchiyata.
Lumshe idanu nayi, hawaye suka surnano mun. Nonon na zura mishi a baki, carab ya soma
tsotsa, a fakaice na dubeshi, kamanninshi ya fito sak da Shehu. Matar malam tace "Ki shirya ayi wanka, duk da magriba ta kunno, amman baza kiji daɗin jikin naki ba." Fita
tayi, bata jima ba ta dawo.
"Laila maza fito muje kar ruwan ya huce." Kwantar da yaron nayi, na yafa fallen zane na
fita. Muna shiga sakaki matar malam ta tura mun wani kwaɓaɓɓen magani a gabana tace.
"Mayar da ɗan durus ɗinki" mayarwa nayi. Ruwannan da mugun zafi haka matar malam
ta dinga yaɓamun tana zaneni da ganyen darbejiya. Ta dinga zuba mun ganyen darbejiyannan
a tudun cikina. Jini kuwa ya dinga fita, ina jin daɗi, jikina sai warwarewa yake yi. Hannu matar
malam ta saka ta kwakwule maganin data cusamun. Ta bani ƙatuwar butar ƙarfe cike da itatuwa
tace in wanke gabana. Na dinga wankewa a hankali, ina gamawa matar Malam ta rufeni da
zani. Gudu gudu na koma ɗaki. Gaushi ya gama ɗumame ɗakin sai naji ni sawai iska mai daɗi
na busani. Tsakin magani matar Malam ta zuba a wuta tace.
"Maza tsugunna Laila yanzu ƙarin da akayi miki zai haɗe." Tsugunnawa nayi
maganinnan yana shigata ina mugun jin zafi da raɗaɗi,jini sai ɗiga yake yi a cikin garwashin,
saida na haɗa zufa sharab sannan matar Malam ta ɗagani, na samu na sake kaya nayi
ƙunzugu. Bacci nannauya ne ya kwasheni.
Daddo:
"Laraba yarinyar nan fa da ganinta tana cikin damuwa mai yawa. Jiya da daddare uban ya
korota tayo yaji. Wallahi haka muka rasa sukuni ni da Ta Asibi a cikin gidannan. Tunda akayi
auren Laila bata taɓa zuwa ganin gida ba. Jiyan da zata fita sai naga tana ɗingishi, amman na
ɗauka nauyin cikine. Sai naga abun kamar fa ba hakan bane Laraba. Kuma tunda muka zo
gidannan babu wata facala data shigo ɗakinnan da sunan dubiya. Sai Iyami da matar Malam
kawai suke suntiri. Shehun ma sai ciccika yake yi. Ni jikina bai bani ba Laraba." Goggo Laraba
tace.
"Nima naga hakan Daddo, amma ni zan rutsata ta faɗi abunda ke damunta ko zata samu
sassauci a zuchiyarta. Ni tausayi take bani. Wannan yaro data haifa nina tabbatar sanadinshi
matsalolin gidan aure zasu matsa ma Laila lamba. Kinsan maza basu cika tawakkali ba."
Ɗahiru:
A tashar bodi aka sauke su, sai jan yaran yake, Tani kuwa ahankali take jan ƙafafunta, dan ji
take uwa zata haife abunda ke cikintane yanzu tsabar wahala. A haka har suka iso gida, Ɗahiru
sai zazzare idanu yake yi.
"Tani mu shiga can shiyyar su Yaya, ki daure sai rakin tsiya moi dalla." Ɗaga ƙafa ta shiga yi
har zuwa shiyyar su Baba mai riga. Matar Malam ce ta soma ganinsu, fitowarta daga turakar
malam kenan zata ɗebo mishi ruwa.
"Wa nake gani kamar Ɗahiru da Tani? Mai riga, mai riga, malam,Baban Yara ku fito ga
Ɗahiru." Ba iyakar waɗanda Matar Malam ta ambaci sunansu bane kaɗai suka fito ba. Kusan
rabin matan gidan sun fito, cikin al'ajabi da almara. Malam yace.
"Ɗahiru, Tani. Kune kuka dawo a cikin darennan?" Ɗahiru yayi dariya yace.
"Yaya ka manta sanda zamu bar garinnanma da daddare muka barshi, ta katanga ma
bata ƙofa ba?" Ajjiyar zuchiya Malam ya sauke. Baban Yara yace"
"A tafiyarku baya haihuwa tayi ta tara tulin yara masu ƙiriniya sosai. Ɗahiru sai nake
ganin kamar ka tabka babban kuskure da kayi tunanin waiwayar gida. Mai riga ki shiga da Tani
da yara ɗaki. Tani wannan du yaranku ne? Ku da kuka tafi ku biyu, amma gashi kun dawo ku
huɗu, da guxirin na biyar a ciki" Tani wacce take a galabaice tace. "Ke dai Yaya Mai riga bari. Mun wahala a bariki sosai, duk da nasan dawowarmu
tamkar wasa da rayukanmu ne." Matar malam da Baba mai riga suka shiga ciki da Tani da
yaransu. Baban yara ya dubi Shehu yace.
"Kuje da Ɗahiru ɗakin zaure ku kwana tare Shehu." Ɗahiru yace.
"Au Shehu bai aure ba har yanzu? Naga ya zama babban mutun. Ina Lauwali ne?"
Malam yayi dariya yace.
"Lauwali yana wajan tukuba yana gashi. Ga Iyami matarshi ita kaɗai nake tunanin ka
sani a cikin surukan gidan. Lauwali yanzu ai da babban ɗanshi Jafaru suke shiga dawa farauta,
kuma da gani zaifi ubanshi zamani. Shehu matarshi ce ta haihu, ƴan uwanta suna tare da'ita shi
yasa ya koma ɗakin zaure." Ɗahiru yayi dariya. Nan surukan gidan suka shiga