Iyayen Giji Book Compelet Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   4 / 21

9K to 12K   out of 61.8K words

ina jiyota tana zage_zage a tsakar gidan.
Tashi nayi na fita wajan girkin.
Amma kamun mu gama girkin, na shiga sakaki, ( bayan gida) yafi sau ashirin, fitsari nake yi
sosai. Bayan mun gama girkin muka shiga rabo. Surukan gidan muka soma cirema, sai ko
wacce ta ɗakko langar tuwo da miya na mijinta. Bayan mun zuzzuba musu, sai aka zuba ma
yara. Muma muka zuba namu a ƙawuwar ƙwarya wacce ake kira da mazubi. Lauma biyar nayi
ma tuwonnan, na tsame hannuna. A jiƙe na koma ɗakina, ina hawaye. Ƙunzugu nayi da fallen
zani guda. Ina zaune ina ba Ƙasimu daya farka nono, zuchiyata sai harbawa take yi da sauri,
tunanina baya jikina sam. Yawale ne ya shigo sai wani cicciza yake yi, yana ta batsewa. Langar
tuwonshi na jawo mai gabanshi, da kwanon sha dana zuba mishi farau_farau a ciki.
Sannu da dawowa Yawale" A daƙile yace.
"Musina karki kuma bari su Baba suyi ƙararki akan rashin kunya da kike yi musu akan
yara. Dan har yanzu ban mance fitsara da ɗiban albarkar da kika yi ba, lokacin da na tsige Idi a
nono, na ba Baba ba. Kuma shima wannan kina Yayewa zan kyautar dashi, kina kuma haifa
zan kuma kyautarwa. Sannan wallahi in kika sake tado mun da maganar inje Birni in dubo Idi
kuma, zan iya salwantar miki da iyoyin aurenki, danni ɗiban albarkar da kike yi mun a gidannan
takai intaha." Yawu na haɗiye muƙut, take jikina ya shiga kakkarwa. Dan mu matan hausawa
muna tsoron saki, mace duk ƙuncin da take ciki, tana kiyaye abunda zai zamana an kai ga
sakinta. Alhalin a mafi yawan lokuta sakin shine a'ala a garemu, duk da inka fita daga gidan
auren naka, baka san gida wa zaka kuma faɗawa ba, tunda mazan ba tukwane bane balle ka
ƙwanƙwasa ka samu gidi, amma kuma a rashin tayi ake barin arha . Ina mamakin irin wannan
milkin mallakan da iyaye suke yi mana akan yaranmu, yanzu laifine dan na damu da nawa, a
matsayina na Uwa? Nisawa nayi nace.
Yawale kayi haƙuri, in sha Allah ba zaka sake jin bakina akan ko wanne yarona ba. Wannan
yaron kuma tuni na jima da sama zuchiyata dangana. Rayuwar shekara biyu yayi, a ƙirjina da
cinyata, aka rabani dashi, daga baya ma aka kaishi almajirci na dena ganinshi baki ɗaya ma."
"Kuma in maza ɗari zaki haifa haka zasu tafi almajirci, ko kina mutuwa kina tashi ne, nj
yarana bazan miƙa su hannun turawa ba, kamar yanda iyayenki su ka yi kiskuren miƙa ki, gashi
a sakamakon karatun boko zaman aure, da bin miji yana shirin gagararki." kwanon tuwon ya ja
ya soma kantara loma. Ni kuma sai kallonshi nake yi. Ina ina ɗigar hawaye. Yawale." Ɗagowa yayi yace.
"Wooo haba Musina kar inci abincinne koko me kike nufi ne?. Ɗauriya na ara na yafa ma
kaina, nace.
Daman gani nake kamar yoyyon fitsarine ya kamani, shine nake neman izininka, gobe
zan shiga Azare inje asibiti a duba ni." Jim yayi yana kallona.
" In sha Allahu ma ba yoyyon fitsarin daya kamaki, yama akayi kika san yoyyon fitsari?"
"Yayata marigayiya Hanne, ciwon daya kasheta kenan, ita asibin binni ma Babanmu
yasa aka kaita. Kuma tun la'asar nake sunturin shiga sakaki, yanzu haka maganar nan da nake
yi maka, ƙunzugune a jikina" ina kaiwa nan na soma kuka.
"Ke dalla tsayar da kukannan haka, banson shirme irin naku na mata. Maganar asibiti
kuma babu inda zaki wallahi. Ki shirya dai in kaiki waccan ruggar ta fulani wajan malam
Sakaraɗa, ya baki magani kizo ki dafa kiyi ta sha. Ince dai babu wanda yasan halin dai da kike

ciki a cikin gidannan ko?
Kai na girgiza mishi halamar eh. Sannan nace.
"Yawale kayi ma Allah ka yarda inje gida Baba ya kaini asibiti, wallahi yaya Hanne ma da
maganin gargajiyar aka soma, saida ciwon ya cinyeta aka kaita asibiti dana gidan yaƙi." Tsawa
ya daka mun, saida na zabura, tsabar ƙarfin tsawar.
"Tunda gidanku ne ke auranki ai dole kije gida a kai ki asibiti, wata kan kinma raina duk
ƙoƙarin da nake yi a kanki ko? Maganin gargajiyar da zan karɓo miki shi ba magani bane?asibiti
ko shirmen banza. Ke duk maganin gargajiyar mu ka sha, gamu gadagau da lafiyar mu, wallahi
daga nan zan iya zuwa har Azare da bala'in gudu, tsabar lafiya, kuma ba'a taɓa kai zuriyar
gidanmu asibiti ba, a kanki baki isa a soma ba, uwar iya. Dan haka na gargajiya zaki yi. Kice
ciwon ma gado ne." Yana kaiwa nan ya wanke hannunshi, ya haye maulidi. Nafi kwatan dare a
zaune a wajan ina dubka da warwara, maganganun da Yawale ya yaɓa mun sai yawo suke a
kaina. Ƙunzugun jikina ya jiƙe sharab har tsungulata yake yi. Sake ƙunzugun nayi, wanda na
cire kuma nasa a bokitin da nake wanke kayan ƙunzugun Ƙasimu, na tura a ƙarƙashin maulidi,
na jawo matashin kai na yar a ƙasa. Na jima banyi bacci ba. Ina ganin lokacin da Yawale yake
zuwa zance gidanmu a idanuna. Da irin kalamai tausasan da yake jifana dashi. Ko a gida aka
ɓata mun rai, da zaran Yawale yazo zance, zai yaye mun dukkannin damuwa, saiya tabbatar ya
sani farin ciki. Ashe yaudarace kawai. Yau gani a cikin halin da nake buƙatar tsantsar kulawa
daga wajan Yawale, amma yayi kwanciyarshi yayi burus dani, sai munshari yake ja. Tunda na
Auri Yawale muka gama cin amarcinmu salamun_salamun, ban kuma samun farin cikin daya
haura mako ba. Kullum a cikin taraddadi gami da taka tsan_tsan nake, dan ɗan motsi kaɗan
zakayi, saiya zama gagarumin laifi, a wajan miji, ko iyayenshi.



MRS BUKHARI


INA MIƘA GODIYA TA DA DUKKAN MASOYA WANNAN LITTAFI NAWA. HAƘIƘA YAU NAGA
RUWAN SOYAYYA. NA AMSA WAYA TAFI SAU GOMA, ANA TAMBAYATA YAU BANYI
POSTING BA. NAGODE DA SOYAYYA.
AKWAI WATA BAIWAR ALLAH DATA SAKA MUN SAƘO A MOTA DAGA NIGER ZUWA INDA
NAKE RIVERS STATE. DUK AKAN WANNAN LITTAFI. NAGODE SOSAI. DAMA DANA BUƊE
INGA.....


Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman
na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas
mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata
saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin

07068606171
08104335144
08179523215



*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._

_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
MATA IYAYEN GIJI

BADI'AT IBRAHIM (MRS BUKHARI)
( GAWURTATTU UKU)

*_GAWURTATTU UKU2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER

DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*


SAMFOTI


LAMBA TA SHIDA



Da ƙyar ɓarawon bacci wahalalle ya kwashe ni.
Kamar a mafarki naji ana tokarata da ƙafa ana shureni. Da sauri na farka tare da saurin zama.
Yawale na gani a tsaye a kaina, hancinshi a toshe.
"Kinji kunya wallahi Musina, fitsarin kwance da girmanki, jibi yanda fitsarinki ya fita har waje
yana gudana. Da sakel gaskiya." Tsaki yaja ya tsallakeni ya tafi sallar asubahi. Cikin hanzari na
miƙe, kayan fitsarin na haɗa dana jiya du na wawwanke na shanya. Ruwa na samu na wanke
ɗakin tasa na goge, turare ɗan goma na yayyafa a ɗakin. Sannan nayo wanka da ruwa mai ɗari.
Ina idar da Sallah, Ƙasimu ya farka da kuka. Nima hawayen nake ta zubarwa. Nono na zura
mishi a baki. Babu ko sallama Yawale ya shigo. A kaina ya tsaya ƙiƙam kamar ɗan doka, sai
toshe hancinshi yake yi, yana mun muzurai.
Ina kwana Yawale?
Baice dani komai ba, ban daddara ba nace.
Zuwa ƙarfe nawa zamu tafi can ruggan?" Ananne na fusata shi ainun, dama mai neman
kukane aka jefeshi da kashin awakai.
"A haka zamu je rugga muna tafe kina fitsari kamar wata tunkiya kenan? Allah ya tsari
gatarina da saran shuka. Ke bari kiji abunda nake so dake shine. Ki shirya tsab ki tafi gida, ayi
miki magani a can ala bashi in kika warke sumul sai in je in ɗakko ku. Bazan iyaba, kinji zarnin
da ku ke yi daga ke har yaron kuwa?" Yana kaiwa nan ya wuce wajan kwalla inda anan
kayanshi na sawa suke. Kaya ya sake ya fice. Baima kalleni ba balle ya tausaya mun.
Murmushi kawai nayi. Na jima da fahimtar halin maza, lafiyar mace da ƙuruciyarta kawai suka
iya cinyewa. Da zaran ciwo ko girma ya saukar mata, shikenan a wajansu ta zama bola, daga
wannan lokacin zasu iya wanko budurwa tsarar jikarsu ma su aura, tunda su tsufa bai fiye
shafarsu kamar mu mata ba. Barinma mazan ƙauye, wanda ƙashinsu ya ginu da tuwon dawa,
da zogala, da yaɗiya. Ƙasimu na saɓa a bayana, na fita tsakar gidan. Kai tsaye shiyyar su Baba
Hauwa na nufa. Bayan na gaisheta ne, na shiga yi mata aikace_akace kamar yadda yake bisa
al'ada da tarbiyya irinta malam bahaushe. Na gyare mata ɗakinta tass. Na fito da wankin
kayanta kala uku na wanke mata tas. Sannan na koma ɗaki na sake ƙunzugu, na wanke wanda
na cire na shanya. Madafi na nufa wajan facalolina. Bayan mun gaggaisa kuma sai muka shiga
aikin ɗunamen tuwo da dama ruwan kokko. A'i tace.

"Musina sai kika ji tafiya ta kama su Yawale da jamilu ko?" Tsabar takaici E kawai nace
mata naci gaba da abinda zai fishsheni. Damuwar dake gabana ma tafi ƙarfina, dan haka bazan
ɗaura damuwar Yawale a raina ba. Rana fatse_fatse ina shirin kulle ɗakina zan tafi gida. Sai
kawai na jiyo ihun yara a waje, ana cewa. "Ga almajirai sunzo ganin gida, ayi noma a koma makaranta, dan damuna tana dab da
tsaiwa, harma munje munyi sharar gona. A guje suka shigo gidan tuɗuɗu. Ina gani su A'i suka
rungumi yaransu, amma irinsu Laure dani masu na fari ba damar ko kallo ka yawanta yi. Yanzu
sai ace kayi fitsara, kai da ɗanka, sai a iya zazzaginka ma, a gaban yaran. Shi yasa yaranma
suke tasowa basa ganin girman mu, yaro a ƙauye uwarshi zata iya cewa yayi mata abu, ko yaje
mata aika, kakarshi wato uwar miji tace bazashi ba, a gabanshi kuma. Da sun girma kuwa sai
abinda iyayensu maza suka ce dasu, shawara ma yaro bazai naima a wajan uwarshi ba. Banyi
aune ba Idi ya tawo a guje ya ruƙunƙunemun zane yana dariya. Kallonshi nayi da kyau, yaro
ɗan shekara Shida, wanda bai wuci inyi mishi wanka, da wankin kashi ba, shine ɗawainiyar kula
da kanshi ta rataya a wuyanshi, kaico. Hannunshi na jaye na ɗan tureshi gefe badan raina yaso
hakan ba, sai dan gudun matsalar da kaje kazo tai sanadin auren nawa baki ɗaya ma. A guje
yayi cikin gidan yana kwaɗama Baba Hauwa kira, dama a ɗakin yake. Inba dai idanuna basu
suna mun dai_dai ba, sai naga Idi kamar ɗingisa ƙafafunshi yake yi. Kulle ɗakina nayi na wuce
shiyyar su Baba Hauwa.
Sallamu Alaikum, sannu Baba." Da harara ta bini.
"Lafiya da dawowar yaro zaki shiga yi mun sunturi a ɗaki, menene to rasa kunya ɓeran
danga? Wallahi ki kiyayeni Musina, inba haka ba kina dab da barin gidanma baki ɗaya" Kai na
sauke ƙasa kawai, inason kallon Idi ko zanji daɗi amma babu wannan damar.
Gida zani shine nace bara inzo inyi muku sallama "
"To ki gaida magabata" Tuwo ta tura ma Idi a kwanon samira. Tashi nayi na fita. Naje
naima Baba Huwaila sallama, sannan na kama hanyar zuwa tashar bodi. Ina tafe harna kusan
isa tashar, sai kawai naji an riƙe mun mayafina ta baya. Juyowar da zanyi muka haɗa idanu da
Idi. Murmushi muka sakarma juna dukkanmu, hannunshi naja zuwa gefe can. Yaya karatun kana taɓawa ko, kuma kana maida hankali a karatun dai ko?" Hawaye ya
soma sharewa, gefe da gefen bakinshi duk ya fashe, ga wani ƙaton makero a kanshi sai ci
yake. Tsugunnawa nayi nace.
Ya'isa me yasa kake kukan to?"
"Baba kice ma Baba ya cireni a makarantar, kullum da duka da ruwan sanyi ake
tashinmu, kullum bana samun abinci inci da daddare. Malam Zulƙe kuma yaita samu a mari,
ƙafata ciwo take yi, in ranar labara bamu bada kuɗin laraba ba, saiya samu a ɗakin duhu mu
kwana." Hankalina naji ya tashi ainun, da rai na yarona yana kwana da yunwa, ya kwana a
mari, da ɗakin duhu. Inna ci gaba da zura idanu inaga kamar banyi ma shi kanshi Idin adalci ba.
Tuno da zafi da azabar dake cikin naƙuda nayi. A lokacin dana Haifi Idi saida na kwana biyu cir
jiri na ɗibata bana iya gane kowa. Amma yau dubi halin da mahaifinshi ya sashi a ciki. Ƙafarshi
ya nuna mun, ƙarfen mari duk ya fasa mai idanun sawu.
Kayi haƙuri zan roƙeshi ya barka a gida, yanzu ka koma gida kaji, gidanmu zanje. Bari in
baka nera uku ka sai marau_marau nasan kana so." Abunka da yaro sai kuma ya washe baki,
ina bashi ya kwasa a guje yana jujjuya kai irinna murnar yarinta. Murmushi nayi, tare da share
hawayen daya gangaro a kuncina. Munyi tafiya sosai, sai wajajen la'asar na isa Azare. Gida na

wuce, na riga na jiƙe sharab ruwan fitsari sai wanke mun ƙafafu yake yi. Ina shiga na zube a
gaban iyayena mata.
"Lafiya Musina zaki shigo da kuka meke faruwa?" Cewar abokiyar zaman mahaifiyata,
Innata tana zaune a turmi tana yanka kuɓewa zata shanya. Kallona kawai tayi, tana ganina
tasan ina cikin matsala, amma sai cemun tayi.
"Ana miki magana kin tusa mutane a gaba kina kuka, ki sakko da goyon, ɗan baɗo yayi
miki fitsari a baya." Ana cikin haka mahaifina ya shigo, shima ya tambayeni ko

4 / 21