Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
aljanna ba'a
ƙarƙashin matata take ba. A wajanki nake neman albarka" munyi kuka sosai dani da yaran
duka. Haƙiƙa Idi ya haifu ya cika ɗa." Fita suka yi da Ƙasimu suka gyara shagon waje tsab,
Ƙasimu ya shigo gida. Shi kuma yace a sanar mun yaje karɓo ɗan mabuɗin madafi."
Idi:
Kai tsaye gidan surukan nashi ya shiga, sabida shi É—ane a gidan. Iyaye kaÉ—ai ya tarar a gidan. A
gaban mahaifiyar Hadiza ya tsugunna, aka gaggsisa, yai musu Allah ya sanya alkhairi tare da
jaddada musu uzirin daya hanashi halartar É—aurin aure."
"Yanzu haka ma, ita mahaifiyar tamu, na tawo da'ita da ƙannena zamu zauna tare."
Mahaifiyar Hadiza tace.
"Ka kuwa kyauta, Allah yayi albarka. In suka huta, muka gama sallamar baƙi muma, zamu
zo a ga juna"
"Zamu zo ma Mama, tanason tazo tayi godiya bisa karamcin da akai mata. Hadizan basa
nan ko?"
"Sun tafi gidan Amarya jere, shi yasa kaga gidan ya yashe ba kowa."
"Ta bar É—an mabuÉ—i a nan, ko dashi ta tafi?" Mahaifiyar Hadiza tace.
"Bari in É—akko maka jakarta ka duba ko zaka samu" ÆŠakko mai jakar tayi ya duba, ya
ɗauƙa, yaima iyayen Hadiza alkhairi, tare dayi musu sallama."
Musina
Wajajen magriba Idi ya shigo da kayan shayi niƙi niƙi, ga gashashshiyar kaza, ga figaggiya
gyararriyar kaza cikin leda mai zane. Kayan shayi da gashashshiyar kazar ya dure a gabanmu
Cikin ladabi ya gaisheni. Ƙannenshi suka gaisheshi.
"Uwo ga kaza na siyo muku. Farfesu kikeso ko a miya kike son a saka miki?" Sai kallon Idi
kawai nake yi. Na rasa me zance mishi tsabar daÉ—i.
Allah yaima albarka, kaima Allah yasa yaran daka haifa su ma haka. Nagode_nagode.
Kaimun duk yanda kake so. Alawiyya karɓi ki gyara."
"A'a Uwo wannan ladan nawa ne, ni kaɗai zanyi. Ƙasimu, zo muje madafi. Tawo da ledar
kayan shayinnan, in haɗa muku. Zubaida ke kuma zoki karɓi faranti ki baje muku gashasshiyar
kasar" Miƙewa suka yi dukkansu suka bi bayanshi. Kwallar data taru a idanuna na sharce. Tare
sukaita hidima dani. Idi bai huta ba, har saida yaga halamar bacci nake ji. Washe gari da farfesun kaza da biredi mai laushi, muka karya. Nan ya samu a mota ya dinga
zagaye damu. Atampopi ya siya mana masu tsadar gaske. Ya kaimu wajan tela mace ta
gwadamu dukkanmu. Ni dai sai hawaye kawai nake zubarwa. Mun dawo mun samu Hadiza da
yara sun dawo, harda Yayar Hadizan. Nayi farin cikin ganin jikokina ainun. Suma da dukkan
halamu sunyi murna. Abunda ya kashe mun jiki shine irin rashin tarbar dana samu a wajan
Hadiza.
"Hadiza zo mana" Idi ya jata gefe, na ga dai yana nuna mata É—akunan da ya mayar mata da
kayanta. Hannun jikokina naja muka shige ciki.
Hadiza:
"Me kake nufi, kana son kace nan É—akunan a ciki zan zauna, ita mahaifiyarka ka bata wancan
? Amman Idris kamar bakai mun adalci ba" Ranshi ya kai ƙololuwar ɓaci sosai, dannewa yayi
yace.
"Tafi ki cancanta da É—akinne, nan gidan É—anta ne, ke kuma nan gidan mijinkine, zan iya
sallamarki, ita kuma sai dai ta sallameni. Ki nutsu Hadiza ina girmamaki sabida alkhairin
iyayenki gareni." Yawu ta haÉ—iye, idanunta fal hawaye, tace.
"Yaya Halima aurenta ya mutu, zata zauna damu anan"
"Bazan hanata zama ba, ga É—akin su Mamana saita dinga kwana dasu"
"A cikin yara zata kwanta fa kace?"
"Bata son kwantawa a cikin yaran ta kaso auren nata? Ki shiga ciki ku kuma gaisawa da
Uwo, ita kuma kin barta tsaye, ta shiga É—akin su Mamana mana. A wajan ya barta, ya wuce ciki.
Halima ta iso da sauri.
"Wai waɗannan bataliyar ƙauyawan daga wacce shiyya suka zone? Meye naga kina shirin
kuka?" Hannunta Hadiza taja zuwa É—akinta. A bakin gado suka zauna.
"Wai mahaifiyarshi da ƙannenshi ya kwaso suka dawo gidannan da zama kab ɗinsu.
Sannan dan wulaƙanci ya fito mun da kayana daga ɗakina ya dawo dani wannan ɗakin. Halima
tace.
"Ki rufama kanki asiri ki rungumi aurenki, kinga dai wuyar da nake sha. Nabi Baban Fatima,
na bishi ba wani canji, yaƙi ya dawo dani. Daga ƙarshe har yayi aurenshi, yana morewa da
matarshi. Ni bazanma zauna ba ace ni na zigaki. Kinga tafiyata" Kayanta ta É—auka ta fita.
Hadiza ta raushe da kukan takaici, ko abinci ta kasa ci. Idi bai shiga daƙinta ba sai wajajen sha
É—ayan dare. Tana zaune dirshen ya shigo. Baiko kalletaba, ya rage kayan dake jikinshi, ya hayo
gadon, yana kallonta ƙur, yanayinta yake karanta.
"Me yasa kika ƙi zuwa ɗakin Uwo, kinzo kin ƙunshe kanki a ɗaki?" Baki ta taɓe tace.
"Wai kar in takura muku ne" murmushin cusa haushi yayi mata yace.
"Kuma hakane, dan muna tattauna abinda zai amfanemu a gaba ne." Juya baya yayi
abunshi, dan zuchiyarshi ma tafasa take:.
Musina:
Fitowa nayi tsakar gida da buta zan É—auro alwala, danni ban saba da makewayi a É—aki ba, gani
nake yi ma ƙazantace zallah. Abunda kunnuwana suka jiyo sun girgiza duniyata baki ɗaya. Take
hawaye suka soma shatata a kumatuna. Hadiza ce ke magana da kuka"
"Allah yana gani, ni bazan iya zama da suruka ba, sannan bazan iya zama da danginka ba.
Idris kar in rufeka, gara kaji gaskiya. Bazan iya zama dasu ba." Kuka ta kuma raushewa dashi.
Muryarshi a daƙile kamar kuka yake haɗiyewa yace.
"Sune rayuwata, duk fafutukar rayuwa da kika ga inayi, dan su samu farin ciki nayi shi. Uwata
ta fiye mun kowa da komai, tayi wahala damu, ta kasance tamkar kendir, ta ƙona kanta, danta
haska mu. Babu wata mace da zan iya zama da'ita alhalin tana gudun mahaifiyata. Dan haka
na sakeki saki ɗaya" Idanu na runtse, inajin kalmar sakin na kaɗa ƙararrarawa a kunnuwana. Ihun Hadiza ne ya
dawo dani kan doka da oda.
"Ni ka saka Idris, ka mance da duk alkhairin da iyayena sukai ma a rayuwa?"
"Baya nufin zasu fi iyayena daraja a wajena. Iyaye dabanne Hadiza, zan zauna in kula da
uwata da dangina, dan nine gatansu." Da ƙyar naja ƙafata zuwa ƙofar ɗakinsu. Kai nasa na
shiga. A tsaye dukkansu na same su"
MRS BUKHARI
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: GAWURTATTU UKU
MRS BUKHARI
LAMBA TA TALATIN
ƘARSHE.
"Likita mahaifimu ne malam Yawale, wanda aka kwantar a babban É—akin maza. To yaune
labarin rashin lafiyar tashi ta riskemu. Kuma na tambayi ƙanina kan ko akwai wani bayani da
kayi musu. Yace A'a.
Likitannan ya É—ago yace.
"E hakane banyi musu bayanin komai ba, domun sai yau bincikenmu ya kammala. Mahaifinku
yana É—auke da cutar sankarar mama ne, na maza. Duk da dai ba'a cika samun maza da cutar
sankarar mama ba. Mutane da dama basu san maza na kamuwa da cutar sankarar mama ba.
Ba a san takaimaiman abin da ke sa maza ke kamuwa da sankarar mama ba, amma dai
haɗarin kamuwa da ita yana ƙaruwa ne sabida.
1 ƙwayoyin halitta da tarihin iyali, ko dangi, ciki har da gadon gurɓatattun ƙwayoyin halitta,
rukunin BRCA1 KO BRCA2
2 Yanayin da zai sa a samu ƙaruwar sinadarin oestrogen a cikin jiki, ciki har da teɓa da lalurar
hanta.
3 Idan an taɓa yin amfani da makamashi wajan ɗaukar hoton ɓangaren ƙirjin mut ( radiothephy)
Babu tabbas kan ko za'a iya É—aukar wasu matakai na rage kasadar kamuwa da cutar, sai dai
wata ƙila ɗaukar waɗannan matakin zai iya taimakawa:
1 Cin abinci mai gina jiki.
2 motsa jiki idan mutum yana da teɓa
3 kauracewa shan barasa da yawa.
Babbar hanyar magance sankarar mama shine gashi, ko ƙona ta da na'ura, ko yin tiyata, ko
kuma cire ƙwayoyin halittar da ke haddasa ta. Mahaifinku yana kan matakin da sai an yanke
mishi mamanshi." Iyaye_iyayene ba'a fishi dasu. Take su Idi hankalinsu ya tashi. Kuma suka
bama likita umarnin aima mahaifin nasu tiyata. Cikin kwana biyu akayi ma Yawale tiyata aka
yanke mishi mamanshi É—aya. Ya jima ainun yana jinya.
Musina:
Ko da Yawale ya samu kanshi yaga kafatanin yaranshi, kewaye dashi, sai ya samu sassauci,
daga raÉ—aÉ—in da yake ji. Gafararmu ya kuma nema, kuma duk muka yafe mishi. Harma Kumatu
taci albarkacina nasa Yawale ya maidata É—akinta. A jakata na bama Kumatu sadaki. Yawale ya
warke, har mun mayar dashi gida. Bamu dawo ba, saida aka mayar da auren Kumatu da
Yawale. Su A'i sai nan nan suke ta faman yi damu. Na zame musu wata abun sha'awa. Kullum
cikin kaya mai tsada nake, É—an kunne kuwa, zinare nake sawa a kunnena. Yaran gidan maza da
mata kab sunyi Aure. Sauma'iyya muka É—auka, mukaima kowa sallama, muka nufi Jos. Na jefa
Sauma'iyya a UMMAHAT ni kuma na tafi jami'atul madina na haÉ—a digirina, na dawo a matsayin
malama. Duk da tsufa ya kamani, amman da ƙarfina sosai. Yara kuwa sai hayayyafa suke ta
faman yi, gida ya cika fam. Yawale suna ƙauye shi da Kumatu, Sauma'iyya tayi Aure abunta. Su
Yawale sai dai su kawo mana ziyara. Yawale yayi_yayi in koma ɗakina, ni kuma naƙi fur, dan a
yanzu nafi ƙarfinshi. Dangina kuwa ba ƙaramin taimaka musu yara ke yi ba. Gidanmu baya rabo
da baƙin ƙauye. Su Kawu Jamilu da Mudi da anji dugu_dugu sai su shigo birni su huta, haka su
A'i ma. Kulu, da Kattume kuma, sun kama sana'a sunayi, Yayunsu ko da yaushe a cikin ƙara
musu jari suke, sun zama masu kuɗin ƙauye sosai. Dan kattume shanu ta ɗaure sama da
goma, gata da ƙatuwar gonar shinkafa. Ita kuma Kulu ɗan ƙaramin kamfani sabulu ta buɗe, take
horar da mata, sana'a, kuma tana yin na siyarwa, tana samun alkhairi sosai. Allah ya ƙarama
rayuwa albarka. Anan labarina ni Musina yazo ƙarshe. Ina godiya ga masoyan wannan labari."
Alhamdulillah anan wannan littafin yazo ƙarshe. Ki bayyana mun ra'ayinki game da wannan
littafin
Sannan wanne gidane yafi burgeki. A cikin mazan wannene dama_dama? Matan fa wacce tafi
shan wahala? Wanne maki zaki ba littafin í ¾í´£í ¾í´£
Ina godiya da ƙaunarku gareni ina alfahari da masoyana. Naga saƙwannin ku, naga kiranku.
Naji daÉ—in addu'o'inku, Allah ya bani nafiya. Sai kun kuma jina tafe da wani jijjigegen labarin mai
tarin darasi, da ilimin zaman rayuwa. NAGODE