Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
Jamilu na ganinshi da kayan ya tashi a guje ya nufi
Mustapha, sai kace wani ƙaramin yaro.
"Wa ai wallahi baka isa ba. Gyaran ɗakin da kayi bai isheka ba, saika shigar mun aikina?
Aini nake yin wankin duk sati inya taru." Mustapha na dariya yace.
"Amma naga kana taya Inna aikin sabulu, ga masu sari sunzo. Kaga ga wata ma ta shigo"
Fur Jamilu yaƙi yarda saida ya fisge kayannan a hannun Mustapha ƙarfi da yaji.
Haihuwa mai rana. A rayuwar gidan Yawale da nayi sam babu daɗi. Amma gashi yau na
haifi yara, sun share mun duk hawayena, suna bani dukkannin wata kulawar daya dace.
Damuwata ɗaya ce, rashin waiwayarmu da Idi baiyi ba, sama da shekara ashirin da biyar,
wannan itace kaɗai damuwata. In aka cire wannan, bani da wata damuwa da take damuna
sam. Girgiza kai nayi nace.
Kai Mustapha tawo ka ƙirga mata, bar mishi aikinshi kaji. Ƙasimu sannu ɗan albarka"
Kumatu taja wani tsaki mai ƙarfi. Ni bansan ma ta fito ba, dan mu kaɗaine a tsakar gidan.
Muttaƙa ne ya shigo a guje, ya bangaje Kumatu ta faɗi ƙasa warwars shi kuma ya shige
ɗakinta."
"Wayyo hannuna, wayyo ƙafata" Da sauri na miƙe tsaye.
Kai Ƙasimu zo ka ɗaga Yadikkonku maza. Sannu Kumatu."
Da sauri Ƙasimu yaje ya ɗagata. Fadawan mai gari ne, suka shigo gidan da zabga_zabgar
dorunanrsu.
"Muttaƙa muka biyo, kuma munga shigowarshi. Dan haka a fito mana dashi" Tsurewa Kumatu
tayi. Ai su A'i iyayen gulma anajin haka sai gata ta fito tsulum.
"Bayin Allah ko me yayi haka, kuka biyoshi da waɗannan murtuka_murtukan dorunan? Kuma
yana shigowa ya haure danga ya dire bayan layi" Cewar Kumatu kenan wacce take riƙe da
hannunta da nake tsammanin zata iya samun tsagewar ƙashi tsabar buguwar data yi. Ni dai ina
tsaye ina mamakin Kumatu yanda duk ta gurɓata ma yaranta kab rayuwarsu. Haka fadawannan
suka tafi, bayan sun faɗama Kumatu, akuyar mai gari suka sace. Kuma duk inda Muttaƙa ya
shiga a ƙauyan zasu nemo shi. Suka fita suka barta da borin kunya. Sai zage zage take yi,
harda kuka, ga hannunta dake ta faman zugi. "Wallahi ni nasan hannu akasa ma Muttaƙa amma ba yin kanshi bane. Allah ya toni asirin
duk mai sa hannu akan lalacewar yaronnan. Baƙin ciki akeyi mishi, anga ya taso da ƙarfi." Tsaki
naja, nayi zamana naci gaba da aikina. Yarana bayan duk sun gama mun aikina, sai kuma ko
wannensu ya nufi wajan sana'arshi. Da yamma ina zaune ina haɗa sabulu, Yawale ya shigo cikin gidan da leda cike da cefane. Ya
miƙa ma Kumatu.
"Ki gyare kayan miyannan Kumatu, kiyi mana jar miya. Kazar wajan Sauma'iyya ki yanka
mana ita asa a miyar. Zan bata kuɗin. Bakinane sam babu daɗi so nake inci wani ɗan abu mai
galmi, kwana biyunnan bana jin daɗin jikina, kasala da na damuna, gashi mamana na gefen
hannun dama ya soma damuna da ciwo fa." Yawale na kalla nace dashi. Sannu da dawowa Malam "
"Yauwa Musina ya kasuwar Dai"
Alhamdulillah" Ina faɗin haka nayi shigewata cikin ɗaki. Tuwo na zuba, da miyar kuɓewa taji
naman rago, gashi naman yayi laushi. Ina ci ina shima yarana albarka. Jamilu ne yayo Sallama
ya shigo. Hannunshi riƙe da leda cike da lemon taba_taba. Yasan inason taba_taba sosai
musamman manyan da suka yi jawur a bishiya. "Uwo ga lemon taba_taba na sayo miki. Bari in ɓare miki. Zama yayi a gefena ya soma
ɓare mun.
"Uwo waini ya batun maganar Auren Yaya Ƙasimu ne, ni ranar Alawiyya na bani labarin
wai kinje gidansu yarinyar da zai auran. Kuma magana ta faɗa, har Kawu Jamilu yaje ankai
sadaki"
Gaskiya ne. Iyayenta dai sunce a bari sai watan cika ciki, in Allah ya kaimu. To Kawunku
sun shige gaba anyi komai, an biya sadaki, dan Babanku yace bazai sa hannunshi ba. Lokaci
kawai muke jira. Inason in samu Babanku da batun inda shi Ƙasimun zai zauna. Ƙila ya taimaka
ya yanka mishi guri a kusa da Saminu. Sai Zaidu ya gina mishi. Jamilu yace dani. "Uwo Baba Kumatu bazata taɓa barin Baba yayi mana abun arziki ba. Ita fa so take
yaranta ace su kaɗai suka mallaki dukiyar Baba, gado ma dan tasan dole a raba da mune,
kinsan da bazata yadda a raba da ƴan ɗakinnan ba. Amman ga shawara Uwo. Wannan filin
nawa na unguwar madaki, mai zai hana Yaya Ƙasimu ya gina, yayi zamanshi acan kamar zaifi
ko? Kuma filin yana da girma, dani da Mustapha duk zai ishemu muyi gininmu acan. Kinga
shikenan kema saimu maidaki can kiyi zamanki tare damu, kema ki samu farin ciki. Amma mai
kike gani?" Shiru nayi ina nazari. Abunda Jamilu ya faɗa gaskiya ne. Kumatu ba zata taɓa bari
Yawale ya yanka ma Ƙasimu fili ba. Alhamdulillah yarana kansu a haɗe yake, kuma Jamilu yana
samun kuɗi sosai akan amfanin gonarshi da yake siyarwa. Banda hatsin daya cika mana rumbu
dashi, banda wanda yake raba ma matan gida da maƙota. Yanzu haka yana da gonakai biyu
daya siya, ɗaya yana noma shinkafa, ɗaya yana noman riɗi a ciki. Banda gonakai na haya da
yake haya. Dan ƴan uwanshi suna taya shi noman, harda su Alawiyya duk suna taimakon ɗan
uwan nasu.
Maganarka gaskiya ce. Banso suka san da wannan filin ba ma Jamilu. Amman kamawa
tayi. Allah ya saka maka da alkhairi. Bari ya dawo sai in faɗa mishi, a samu a hankali a soma
gini.
Ai kuwa hakan Akayi. Ko da Ƙasimu ya dawo, saina zaunar dashi na labarta mishi abunda
muka tattauna da Jamilu. Duk sunji daɗi kuma sunyi na'am da shawararshi. Ba'a wani ɗauki
lokaci ba Ƙasimu ya soma gininshi. Labari dai ya zagaye harya faɗa kunnen Yawale. Ranar
afujajan ya shigo cikin gidan. Yana kwaɗa mun mugun kira. Saida gabana ya tsinke ya faɗi.
Buzu_buzu ya shigo da uban gemu"
"Da gaske ne, Ƙasimu ne yake gini a unguwar madaki?" Murmusawa nayi nace."
E shine, Jamilu ne ya bashi filin ya gina iya inda zai zauna da iyalinshi" Ƙuta Yawale yayi
yace.
"Duk girman filinnan na Jamilunne, ko iyakar inda yaba Ƙasimunne nashi? Kiyi magana
mana, sai wani murmushin ɗaukar rai kike yi" Ai Kumatu na jin haka zuruf ta miƙe ta baro,
ɓarzar dawar da take yi ta matso kusa da Yawale. Kallonsu nayi dukka nace.
Duka filin nashi ne, ai wannan ƙaramine ma daga cikin filayenshi, banda gonakai daya
mallaka" Ba Kumatu ba ba, har Yawale saida ya kaɗu da abinda yaji nace, take ya soma kumfar
baki.
"To baki isa ki raba mun kan yara ba wallahi. Duk ƙoƙarin da Kumatu ta dinga yi tun
yaran na ƙananu dan ganin ta haɗe kansu, kinƙi yarda. Yanzu sabida kinason duniya ta zageni,
wata na ya kama a ƙauyannan ace na kasa ba yarana fili suyi gini a gidana, saida suka je waje,
shi yasa kika amince musu su fitan ko? Sabida munafukace ke ƴar iska, har yarona ya mallaki
irin waɗannan uban kadarorin ace ni ubanshi bani da labari? Fili tabkeken gaske, wanda mai
gari ne kaɗai yake da irinsu. Hawaye ya soma zubarwa. Kumatu ta cabke da cewa."
"Ka dena kuka Malam, Ai Musina bata ƙaunar zaman lafiya, shi yasa kullum cikin cusa
ma baƙin ciki take. Yawale yace
"Dake da yaran naki duka, ina son ganinku a turakata bayan sallar isha" Wucewa yayi
yana share hawayenshi. Girgiza kai kawai nayi na koma ɗaki abuna. Bayan sallar isha duk
muka hallara a turakar Yawale, da yarana da yaran Kumatu.
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: *_GAWURTATTU UKU2023_*
*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don
koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in
akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan
idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya
don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin
07068606171
08104335144
08179523215
*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._
*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
MRS BUKHARI
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA GOMA SHA TAKWAS:
Hawayene suke surnanowa ta gefen idona, suna sauka a matashin da kaina yake. Yau ni Audu
ya daka a gaban yarana, da girmana yasa hannu yaimun dukan da har saida aka danganani da
asibiti? Lallai na yarda Hindu ta shiga ta fita, ta cusa ƙiyayya mai ƙarfi a tsakanina da Audu. Duk
da shima yana da nashi halin muguntar. Dan tun kafin Hindu tazo yake bani kashi. Shatu ce ta
juyo, sai muka haɗa idanu. Kuka ta fashe dashi, wanda na kasa tantance na menene.
"Mama sannu kin farka? Basira maza kirawo mana likita, kice ta tashi. Jiki a saɓule Basira ta
fita. Da idanu kawai nake binsu, ko ina ciwo da tsami yake yi mun a jikina.
Ina Usman Shatu?"
"Usman, yana gida, Kawu Ɗan lami yana jinyarshi, Shazili ya ƙarya mishi mishi hannu."
Wasu irin hawayene masu ƙarfi suke ta ƙoƙarin makanta ganina. Har harshena yana sarƙewa
nace.
Me ya haɗa Usman da Shazili, har abun yakai yake son durƙusarmun da yaro? Allah kana
gani." Zaliha tace.
"Sabida ya riƙe hannun Baba sunyi kokawa, yana ƙoƙarin ƙwatarki, shine Shazili ya ɓalla
hannun nashi. Kuma suka rufar mishi da duka, shi da su Yaya Shagari, da Auwalu. Yanzu haka
mun shigar da ƙarar Baba Hindu, da shi kanshi Baban, da Shazilin. Kuma ni kotu zamu shiga.
Zamu kwato muku hakkinku, kuma duk wani hakki da Baba ya tauye mana, zamu nemi kotu ta
kwato mana hakkinmu. Lokaci yayi da baza mu iya zura idanu Baba da Hindu suci gaba da
takaki ba. Ɗaukeki daga gidan zamuyi ma." Mari na dallama Zaliha, wanda saida yasa ta miƙe
tsaye a zabure. Take tausayinta ya kamani. Nasan yarana sune gata na, na gode ma Allah daya
bani aron lafiyar da na dinga neman kuɗi, badan komai ba, sai dan in haskama yarana hanya.
Haƙiƙa ni kaina na ƙudurce a raina, ƙarshen zamana da Audu yazo kenan. Sai dai bazan so
yaranshi su jashi a ƙasa ba. Duk lalacewar masa tafi ƙarfin kashin shanu.
Uban naku da matar uban naku, da ƴan uwan naku kuka miƙa sunayensu hannun
hukuma? Ashe boko da sanin ƴancin kai shima hauka ne? Albaka nake fata kuyi a rayuwa,
fatana ku rabu damu lafiya. Wannan jikin ya saba da wahalar Audu tun kafin kuzo duniya. Ku yi
haƙuri ƴaƴana ku janye, in dai harni na tsugunna na haifeku." Basu da yadda zasu yi, dole suka
ce dani sun janye. Kwanana shidda a asibiti aka sallameni. Babu laifi fuskar tawa ta ɗan saɓe.
Kai tsaye su Zaliha suka wuce dani gidan da suke zaune. Suka kaini har gidan wata dattijuwa
data kasance uwar ɗakunsu. Nayi ta binda da godiya. Muna zaune da daddare a falo, muna cin
gashashshiyar kaza. Yarana sai jana da hira suke yi, burinsu suga ina walwala. Amman ina, sai
dai na samar musu ƙirƙirarren farin ciki, badan yaudaraba sai dan in basu nutsuwa. Kwana na
biyu a wajansu, muka dawo gida. Matan gida, da maƙota sai aukin sannu suke yi mini. Masu
gulma nayi, masu zunɗe nayi. Hindu kuwa muna haɗa idanu ta fashe da dariya, ta shige ɗaki
tana wani rausaya sai kace yarinya. Ɗakin da Usman yake jinya muka shiga. Yana zaune ana
shafa mishi kitsen damo a hannun nashi. Ɗan Lami yana gefenshi. Sai aukin sannu muke ma
juna ni da Usman. Saida mai maganin ya fita, Ɗan Lami ya faɗa ni da faɗa.
"Ke wacce iriyar shin me ruwa uku ce ( Sha_sha_sha) Yara suna son kwato miki
darajarki, amma kina gwalesu. Kinfi sha'awar ciwon zuchiya yayi ajalinki kenan? Ya zama dole
a shigar da ƙararnan. Dan wallahi abun ya isa haka tura kuma takai bango. To bari kiji abunda
yake faruwa tun ranar da aka fita dake jina_jina a gidannan. Audu har fada yaje, ya bada
sanarwar duk saurayi, ko tsoho, ko dattijon da ya shirya aure, ga yara a gidanshi kyauta, sadaki
kawai za'a biya. Ba wannan bane abun mamakin ba. Wallahi har aka kwana aka wuni, babu
wanda yace yanason waɗannan yara. Sai gulmace_gulmace aketa faman yi a gari, wai Shatu ta
kawo daduro har gida. Hindu ta dinga bi gida_gida tana sake tabbatar ma da mata cewar kama
Shatu akayi da daduro a ɗakin mahaifiyarta. Jibi abinda suka ma ɗanki, ke kanki jibi fuskarki. A
wannan karon dole Audu ya sakeki." Goggo Rakiya wacce ta jima da tsaiwa a dokin ƙofa, kuma
a kunnenta akayi bayanin komai tace.
"Ya zama dole ki yarda da abunda ƴan albarkar yarannan suka zo mana dashi. Da ba
dan sunyi iliminba, da haka zaku zama ɗaya daga ke harsu, shin me ruwa uku kawai (
Sha_sha_sha) Zaliha kuyi abunda kuka saka a gaba. Allah yayi muku jagora, sai inda ƙarfina ya
ƙare ni kuma" haka suka sani a gaba har saida na amince a maka su Audu a kotu ala tilas.
Cikin kwana biyu, Zaliha ta dawo da takaddar sammaci. Ɗan lami, da Goggo Rakiya su suka
tafi da sammacinnan har fada.
Ni kuwa koda muka dawo gida, jikina sam yaƙi daɗi, ga tunane tunane da suka addabi
zuchiyata. Ga habaice_habaicen Hindu wanda ta matsa mun lamda dasu a kwanakinnan. Audu
kuwa sai sabgogin gabanshi yake yi, shi da Shazili gani suke zasu ci banza. Ƙuta nayi nace.
Mu zuba, inda dane bani da ƙarfin ramawa, bani da muryar da za'a saurari kukana. Yanzu
karana ya kai tseko"
Fada:
"Allah ya taimaki mai gari. Wannan takaddar sammacice daga kotun birni. Ta Audu ce mijin
ƴarmu, da Shazili, da Hindu, Yaranshi ne suka doka shi a