Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
"Ke Laila baki isa kiyi wannan shugabancin ba na dai faɗa miki, gabaki ɗaya ya dawo
kamar wani mahaukaci." Da tsiwa nace.
In kana ganin ba zaka iya barina inyi wannan shugabancin ba, ai saika sauwaƙe mun,
kaga ko babu komai na baka filin ɗakin da zaka ƙara wani auren, ka haɗata da Asiya, wala
Allah ai ma naɗin sarautar Katsina baki ɗayanta, a sakamakon rabuwa da mai farar ƙafa daka
yi, mahaifiyar mata maza." Tsawa ya daka mun, na kalleshi na watsar, nan yaita zazzaga ruwan
jaraba, har da mun fatali da kayayyakin aikina, yasa kai ya fice, sai zage_zage yake ta faman yi.
Sha'awace ta shigo ta same ni ina kuka. Dafa ni tayi tace.
"Laila ki dakatar da komai, ga kuɗi bari in ranta miki, ku tafi asibiti, ciwon sai tsananta
yake, yanzu haka jinine ya ɓalle mai. A gigice na fito da mayafi a kaina, banbi takan kowa ba.
Sha'awace ta fito da Ɗahiru, muka ɗauki hanyar Bakori a cikin bodi. Sai yamma lis muka isa
asibiti, Ɗahiru ya jiƙe wandonshi sharkab da jini, hawaye naga yana fitarwa ma. Muna shiga
asibiti aka ba Ɗahiru gado, ɗan kuɗin da yake hannuna dashi na buɗe fayil, likitoci har sun zo
kanshi ana duddubashi, ni dai na haɗe hannayena da kumatuna, na zuba ma sarautar Allah
idanu. Bacci yake yi fuskarshi tayi fayau. Wani likita ne ya dubeni yace.
"Mama ki dena damuwa in sha Allah zamu shawo kan matsalar, amman dole zamu
kwantar dashi muga yanda yanayin jikin zai kaya. Amman akwai kuɗin magani da zaku biya" A
baya na bisu, na biya kuɗin maganin, sannan na nufi gida a ƙagauce nayi musu bayani, sai dai
kash mahaifina na samu a kwance a tsakankanin rayuwa da mutuwa, su Yaya Nazeefa da Yaya
Salamatu duk an aika sun zo.
"Laila Jafaru harya tafi yayo kiranki, ashe kuma kuna asibiti. Muma asibitin zamu je, dan
kwananshi bakwai baya gane ma wanda yake kanshi. Duk muka yi duru_duru, a wajan
mahaifina ya cika, rai yayi halinshi. Zaiyana irin tashin hankali da damuwar da muke shiga ɓata
lokacine. Kan kace me aka shiga yin shelar mutuwar mahaifinmu, Inna Laraba ce ta kwana da
Ɗahiru a asibiti, mu kuma muka kwana munaima mahaifinmu da yayi kwanan keso adda'a.
Washe gari aka kaishi gidanshi na gaskiya, da Shehu akaita zaman makoki, babu laifi wannan
karon su Asiya da matar malam sun zo. Ana cikin zaman makokinne Baba mai riga Allah yai
mata rasuwa itama, sakamakon ciwon ciki na dare ɗaya. Sake ɗunguma can akayi kuma. Ni
kuma na koma asibiti.
"Malama Laila wannan yaron sai anyi mishi aiki dangane da lalurar dake damunshi, in
ba haka ba, zai dinga yin al'ada duk wata kamar yadda ko wacce mace take yi. Sabida yanayin
tsarin halittarshi, a binciken da muka gudanar mun gano ya fi ƙarfi ta ɓangaren maza, Nera
dubu talatinne kuɗin aikin. In kuɗin sun samu sai ku dawo mu rubuta muku takadda zuwa
babban asibitin cikin gari. Mun sallameku, ya dage yasha maganinshi dukka." Na kiɗima sosai
da wannan bayanin da Likita yaimun. Godiya nayi mishi, muka bar asibitin zuwa gida, nan muka
ci gaba da karɓar gaisuwar Baba mai riga. Sha'awa da Iklima su ka ci gaba da gudanar da koya
ma mata saƙa da ɗinki. Ranar arba'in ɗin mahaifinmu akayi mana rabon gado. Mun tashi da
gonakai da shanu, da hatsi cikin rumbu biyu,banda kuɗi tsabarshi. Munyi koke koke sosai da
sosai. Ban baro Bakori ba saida na koma asibiti suka rubuta mun takaddar da in munje asibitin
birni zamu nuna, sai dai sunce mun sai ƙarshen wata,ishirin ga wata zamu je. Gida na dawo,
nan naci gaba da kulawa da matan da ake koyarwa sana'a. Wa'adin da aka ɗibar mana a asibiti
yana cika, na ɗauki Ɗahiru muka wuce. Tare da Shehu muka je, nayi mamaki sosai da tsaiwar
da Shehu yayi dangane da neman lafiyar Ɗahiru. Mun daɗe sosai a asibiti, dan sai da ya warke
tsab ya dawo cikakken namiji, sannan aka sallamemu, muka dawo gida. Haka rayuwa taita
garawa, abubbuwa da dama sukaita faruwa, Su Karima sun dawo ganin gida, bayan shekara
guda. A lokacin nace ma Shehu yarana bazasu koma birni ba. Yanzu ina da arzikin da zan iya
tallafin ƴaƴana. Dan jam'iyyar matan Arewa tayi mun dukkan alkairai, ta dalilin wannan ƙungiyar,
naga gwamnonin jihohi da dama, kuma sunyi mana alkhairai masu tarin yawa. A yanzu na
zama fitilar dake haskaka gidan Shehu, yaran Asiya duk biyun da ciki suka dawo daga gidan
aikinsu. Ni naja gaba aka ƙwato musu hakkinsu, mune har kotu, sun haihu, Asiya taci gaba da
rainon yaran shege a gabanta. Rayuwa kenan, haƙuri shine jigon rayuwa, mai haƙuri shike dafa
dutse yasha romonshi. Iyayenmu duk Allah yayi musu rasuwa, mun zama dattijai a cikin gidan.
Ɗahiru ya zama babban ɗan kasuwar da ake ji dashi, ƙaton shagon atampopine dashi a babbar
kasuwa, ya tamfatsa katon gida a cikin ƙauyan unguwar alƙali. Ya ja Su Sabitu ƴan uku, suke
taimaka mishi a kasuwa, dan shi kullum a cikin tafiye, tafiye yake. Karima da ƙannenta mata
sunyi aurensu, Karima a cikin garin Katsina tayi auren,tana zaune lafiya sumul a gidan
mijinta.ƙannen nata kuma duk a ƙauyukan dake maƙwabtaka damu su kai auren. Suna gidajen
aurensu cikin rufin asiri. Yaran Asiya mazan na roƙi Ɗahiru ya buɗe musu ƙaramin shagon siyar
da takalma a gefen shagonshi. Tunda basu da aikin yi, ga iyalai suna dashi Asiya ranar tayi
kuka bana wasa ba, ni naita rarrashinta. Rayuwa tayi mun kyau tayi haske. Ɗahiru yana daga
cikin masu taimaka ma matan ƙauyanmu, da Azimi layi sosai ake ja a ƙofar gidanmu, dan
Ɗahiru na raba gero da Suger. Ni kuma ina rabon kayan abinci a ƙarƙashin jam'iyyar matan
arewa. Babbar matsalata shine, duk su Sabitu sunyi aure, sun hayayyafa. Amman Ɗahiru fur
yaƙi yarda yayi aure, yace zai mutu yana bauta mana, musamman ni. Ranar wata juma'a muka
tashi da tashin hankali, Kawu Ɗahiru ne ya fito tsakar gida tsirara, yana ihu yana fisgar gashin
kanshi.
"Kayanasu karka kasheni kuskure nayi, nabi Allah na bika, na bika kayanasu" Abunda yaita
maimaitawa kenan. Shehu da Lauwali sunyi cirko cirko, sun rasa me zasu yi ma kawu Ɗahiru.
Haka muna ji muna gani Ɗahiru ya naɗe kamar alkaki, jini ke zuba a bakinshi dalala. Zaratan
yaranane suka Shigo Ɗahiru yana gaba, suna biye dashi a baya. Kamarshi sak da Shehu. "Baba lafiya meke faruwa haka? Cewar Ɗahiru kenan, yana tambayar Lauwali. Bayani yayi
mishi cewar muma gani kawai muka yi yana ihu.' Ihun Ɗahiru ƙaruwa yayi, sai fisge duk wani
gashin jikinshi yake yi, wajan na jini, Hannu Ɗahiru yasa ya ciske jelarsa ta fice daga jikinshi.
Take ya shiga wani gurnani a take ya mutu, mutuwar tozarci da wulaƙanci, tsirara a gaban kowa
da kowa. Su Tani hannu suka ɗaura aka, sukaita xunduma ihu. Ɗahiru ya ja hannuna zuwa cikin
ɗakina, dan baya ƙaunar abunda zai ɓata mun rai. Zaunar dani yayi yace.
"Ummi ki dena kuka, bana son ganinki a cikin ko wacce irin damuwa.Bari inyi miki albishir ko
zaki ji sanyi. Dan Kawu Ɗahiru kowa yasan mushirikine, ni bazan halarci sallar gawarshi ba ma.
Meye bayyiba a gidannan. Babu irin surkullen da baiyi ba a tsakar gidannan. Ajjiyar zuchiya na
sauke, haƙiƙa yau zuchiyata ta tsinke, na sake girmama ƙudurar uban giji. "Ummi bana dani, dake, da Baba da Baba Asiya zamu sauke farali, zakiyi sallah a masallacin
ma'aiki. Tsabar farin ciki, hawayene ya soma zuba a idanuna shatata ina godiya ga mahaliccina.
Na dubeshi nace.
Allah yaima rayuwarka albarka, ubangiji ya kareka, ya tsareka, Allah yaima albarka, Allah ya
sada fuskokinmu a aljannatul firdausi. Amman babban farin cikina shine kayi aure wannan
yaron. Shine farin cikina." Hawayenshi ya share yace.
"Ummi wa kike son in aura?"
Jamila yarinyar Yaya Jamila, ita nake son ka aura." Ajjiyar zuchiya ya sauke.
"An gama zanyi aure, amman ku yarda ke da Baba ku tare a gidana dana gina." Nan take na
amince mishi. Mutane ƙalilinne suka sallaci gawar Ɗahiru, domun gari kowa yasan Ɗahiru
bokanci yake yi. Ya mutu ya bar yaranshi da abun faɗen da baza'a dena faɗeba, sai sanda
duniya ta naɗe. Lokaci nayi muka ziyarci ma'aikin Allah. Muna dawowa Ɗahiru yayi aure. Kafin
mu dawo Ɗahiru yasa ƙannenshi sun gyara mana waje a cikin tabkeken gidanshi, mai yalwar
ɗakuna, anan muka tare, harda Asiya. Amman yaranta maza da iyalansu, suna tsohon
gidanmu, da iyalan nasu, sai dai su shigo su gaishemu.Yara matan dake gaban Asiya suma
sunyi aure, sabida sun tuba sun nutsu, amman sun jima basu auruba, sun garu, duniya tayi
musu atishawa. Rayuwa tayi kyau tayi albarka. Ƴaƴa rahama ne. Kullum Shehu a cikin
rarrashina da tarairayata yake yi. Na zama babbar mace hamshaƙiya. Yaranmu sai jikoki suke
tara mana, zuriya tana ta girma tana burunƙasa.
MRS BUKHARI
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA ASHIRIN DA BIYAR
ƊANBO:
HINDU:
"Fatsima tasa aka sakeki kuma aka biki da mugun duka haka? Sakin har nawa ne, shegiya kike
kuka zaki bada mata" Zainaba ta kalli Hindu tace.
"Saki uku tasa yai mun, wallahi Baba inason mijina nikam" Tsabaragen takaici Hindu rufe
Zainaba da mugun duka tayi, tana dukanta tana kuka, itama kukan take yi. Daƙyar su matan
gida suka ƙwaceta. Suna cikin haka Audu ya shigo jikinshi a mugun mace mus da takadda a
hannunshi. Jagwab ya zauna yana zabgama Hindu wani irin mugun kallon tsana, Zainaba yabi
da kallo, yaga bakinta yana zubar da jini. Hawayene suka soma sakkowa a kumatunshi. Bai yi
magana ba, ya fice a ɗakin zuwa turakarshi. A canma jagwab ya zauna ya shiga zurfin tunani.
Haƙiƙa shi kanshi yasan yayi zalunci ga Shamsiyya da yaranta, ta yaya zai iya kare kanshi
akan abinda yara sukai ƙararshi akai? Shi kanshi ya shiga kogin dana sani, mara madafa, dan
yasan Shamsiyya ba zata taɓa mancewa da irin azabtar da'ita da yayi ba. Tunano baya ya
soma yi, a lokacin da yake zuwa ƙofar gidansu taɗi, da irin musayar kalaman soyayya da suke
yi a tsakaninsu. Abubbuwa iri_iri yaita tunanowa, Hindu da dai taga shirin yayi yawa, sai tabi
Audu ɗakinshi, a kwance ta sameshi idanunshi jawur.
"Malam ince dai lafiya ko? Naga ka shigo jiki a mace baka ce mana komai ba, kuma kana
ganin Zainaba mijin yayi mata makirin duka, ya rangaɗo mata saki har uku. Ni fa wallahi bazan
yarda ba Malam. Dubanta yayi da kyau yace.
"Ai bazan daki ƴar mutane ni ince nawa yaran su sha ba. Gwargwadon yadda zan cutar da
ƴar wasu, gwargwadon yanda za'a cutar da nawa yaran. Ta gode Allah ma, da har ta gane
gidansu ma. Ki fita ki bani waje ina son hutawa, kuma ki shirya zaman kotu, ki sanar da Shazili
ma, su Zaliha sun doka mu a kotu." Wata zabura tayi tasa hannu aka tace. "Ni Hindu naga ta kaina, kishiya tara rana ɗaya, ta goma na ƙofar gida. Kotu fa kace, anya
yarannan yaran sunna ne kuwa? Kai ɗin suka maka a kotu? Nan cikinta ya juya ba shiri ta tsure
sai zawo, Audu dai baya iya cewa komai.
Anyi roƙon duniya akam Shamsiyya ta janye ƙarar amman su Shatu sunce basu amince ba.
Hindu da Shazili suna cikin tashin hankali.
KOTU:
SHAMSIYYA:
Muna zaune a bakin kotun, muna tsumayar a gama shari'ar dake gaban tamu kafin mu shiga.
Hindu da yaranta da ƴan uwanta, suna gefe guda. Nima muna gofe guda, da yara dasu Goggo
Rakiya. Audu yana gefe guda shi da abokinshi, ya zabga tagumi. Yayi matuƙar rama, kamar
bashi da lafiya ne ma, dan ina gani abokinshi ya zaunar dashi zaune. Saida aka ƙare shari'ar da
akeyi sannan alƙalin ya nemi ganawa damu a ofishinshi.
"Barista Zaliha tayi mun bayanin komai, na zaɓi mu tattauna a ofishinane dan kar duniya ta
zagi Audu. Amman Shamsiyya zanso ki bani labarin irin zaluncin da Audu yai miki, karki rage
komai, hakkinku dana yaranki za'a kwato miki. Numfasawa nayi, na dubi Audu wanda yake mun
kallon inji ƙanshi. Hindu da Shazali kuwa sai zazzare idanun tsoro suke yi, Shagari, kuwa yayi
shiru sai faman jijjiga kai yake yi. Nan na soma zayyanema alƙali irin zaman da mukayi da
Audu, da Hindu, da irin zaluncin da sukaimun. Ofishin ya ɗauki shiru, sai hawaye muke sharewa
ni da yarana da ƴan uwana. Alƙalinnan na kalla nace.
Ni na yafe musu, ai musu sassauci, babu komai ai duniya ce. Shatu tace.
"Ina da ja ya mai shari'a. Mu munason a kwato mana hakkinmu a wajan mahaifinmu, na
kasa kula damu da yayi" Zaliha tace.
"Gaskiya ne yallaɓai muna son a ƙwato mana hakkinmu" Idanu na lumshe, Audu kuwa
gabaki ɗaya ya galabaita, sai runtse idanu yake yi. Alƙali ya gama rubuce rubucenshi ya dubi
Audu yace.
"Me zaka ce Audu, kana da ja, ko ƙarin bayani a bisa bayanin da Shamsiyya tayi?" Murya
na rawa yace.
"Bani da ja yallaɓai. Wallahi duk abinda ta faɗa nayi mata, da sa hannun wannan
algungumar matar tawa, wacce take sani a keken ɓera, ta haifamun kangarurrun yaran da suka
gagaremu daga ni, har ita. Tabbas bansan komai nasu Shatu da ƴan uwanta ba. Sai dai tsana
da tsangwamarsu kaɗai na sani. Bani da bakin da zan roƙi gafararku ƴaƴana, amman ku
gafarceni nayi kuskure." Hawaye yake sharewa, harda dafe ƙirji, da dukkan halama ciwo yake ji
a zuchiyarshi. Hindu da Shazili suma sai haƙuri suke bayarwa. Alƙali ya umarci Audu da biyana
duk wahalhalun da nayi akan ci da sha, da ilmantar mishi da yaranshi da nayi. Sai ai mishi
afuwa, ita kuma Hindu tayi alƙawarin ba zata kuma ƙulla wani makircin ba. Shazili kuma akace
zaiyi zaman gidan kaso na wata biyu, tare da cin tararshi na dubu talatin. Audu ya amince zai
bani gonakanshi duk biyun daya gada. Tare da yin alƙawarin bazai kuma cuta mun ba. Haka dai
alƙalinnan mai adalci yai mana sulhu a tsakaninmu. Muka dawo gida. Audu ya ɗebo duk
takaddun kadarorinshi ya danƙama su Zaliha. Suka sa hannu suka amsa, sannan suka ɗaukeni
daga gidan.
Bamu sake waiwayar ƙauyannan ba, har sai da sha'anin bukukuwansu Shatu ya taso, ni kuma
nace dole sai dai ayi bikinnan a gidan mahaifinsu. Shine muka dawo gidan, munzo mun tadda
Audu cikin jinya, wujiga_wujiga, duk ya rame ya ƙanjame, sai an tayar sai an ƙwantar. Ina
hawaye na dubi Hindu nace. "Tun yaushe yake fama da wannan ciwon Hindu?" Cikin kuka Hindu tace.
"Watanshi shida cur a kwance, Usman ya koma wajanki a birni babu jimawa ciwon ya
kwantar dashi, dama a tsaitsaye yake ta fama da ciwon, tun lokacin da wannan abun ya faru
yake fama, kuma barinki gidan ya kuma ɗaga hankalinshi sosai. Wallahi bashi kaɗaiba
Shamsiyya ni kaina gidan da ƙauyan baya mun daɗi. Tunda jama'ar ƙauyannan suka ganoni,
shikenan fita wannan ta gagareni. Ku yafeni Shatu na tuba. Hawaye na share, na dubi Mariya
ƴar gidan Hindu wacce take gidan aure.
Mariya ganin gida kikazo yine, na ganki da yara?" Hindu tace.
"Ummm inji mai ciwon baki. Mijinta ne ya rasu, takaba take yi. Bata gama takabar ba,
dangin mijin suka raba gado, aka tasheta a gidan. Tuminin takabarta kawai suka bata, hakkin
yaranta na hannun wan mahaifin nasu. Duk haka muke zaune, ga Zainaba Hannatu ta samu
tayi aure da ƙyar, wallahi wuya take ci a gidan Auren. Duka kuwa wane Audu. Ga mijii ba lafiya,
yara mazan kuma. Shagari ta ƴaƴanshi kawai yake yi, wallahi hatsin da zamu saka a bakinmu
gagararmu yake yi. Matarshi ta gama asirceshi, sai abinda tace yake yi. Ƙiri_ƙiri take hanashi
kulawa damu. Shazali kuma ba sana'a yake yi ba. Gashi da iyali. Shi kuma Muttaƙa ya jijjiga
wata sata a birni, shi da abokanshi, yanzu haka maganar nan da nake miki yana gidan gyaran
hali a birni. Wai saiya shekara ashirin za'a sakoshi." Kuka suke yi dukkansu, suna roƙon gafarar
ƴan uwan nasu. Ajjiyar zuchiya na sauke.
Allah ya kyauta, yanzu shi Audu an kaishi asibiti ne?" A kunyace Hindu tace.
"Ina wanne asibiti Shamsiyya, ana maganar abincin da za'aci kina maganar asibiti.
Ruwan kokkone a cikinmu dukkanmu. Hankalina ya tashi, lallai Allah, Allah ne. Shatu da ƴan
uwanta suka kinkimi Audu zuwa motar da Shatu ta sai mun. Suka wuce asibiti. Ni da su Hindu
kuma muka hau keken shanu, xuwa Bakura. Gado aka ba Audu, munje mun samu har an ɗaura
mishi ruwa. Kwananshi bakwai ya soma murmurewa, harya kuma roƙon gafararmu. Takaddun
kadarorinshi na maido mishi. Da ƙyar ya karɓa. Sati biyu Audu yayi yana jinya, kafin aka
sallamemu, muka dawo gida, da goma sha tara na arziki. Saida Audu ya nutsu na sanar dashi
zancen biki. Aikuwa gadan_gadan Audu ya shiga shirin biki. Gonarshi ya siyar, ya bani nera
dubu saba'in kuɗin kayan ɗakin su Shatu. Anyi biki amare sun tare a gidajensu. Suna zaune
lafiya, sai ƴan matsalolin rayuwa da ba'a rasasu, in dai da rayuwa. Tsufa yaci gaba