Iyayen Giji Book Compelet Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   3 / 21

6K to 9K   out of 61.8K words


_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_

MATA IYAYEN GIJI

BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
( GAWURTATTU UKU)

*_GAWURTATTU UKU2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*



NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN KACOKAM GA JAM'IYYAR MATAN AREWA, KUMA
INA MIƘA GODIYATA A GAREKU SHUGABANNIN JAM'IYYAR MATAN AREWA.

KUMA INA ƘARA MIƘA SAƘON TA'AZIYYAR HAJIYA LAILA DOGON YARO UWA MA DA DA
MAMA GA JAM'IYYAR MATAN AREWA. MUTUWACE WACCE BAZA'A MANCE DA'ITA BA,
DUK DA TSOWON LOKACIN DA RASUWAR TA ƊAUKA, AMMA DA ZARAN ZA'A TAƁO
JAM'IYYAR MATAN AREWA, DOLE MUTUWAR HAJIYA LAILA DOGON YARO TA DAWO
ƊANYA SHARAB DA DUBBAN JAMA'A"

JAM'IYYAR MATAN AREWA BA ZATA SHAFE SUNAYENKU BA, HAR ABADA, DOMUN KUN
TAKA MIHIMMIYAR RAWA WAJAN GANIN JAM'IYYAR TACI GABA.

HAJIYA MURJA WAMBAI ( FARA MAI FARAR ANIYA)
HAJIYA RABI SAULAWA
(SHUGABAR ƘASAR JAM'IYYAR MATAN AREWA MAI CI A YANZU, BAYA GOYA MARAYU)
HAJIYA GAJE ( YA GA SUNUSU LAMIƊO)
ANTY RABI MUHAMMAD ( BAN MANCE DAKE BA)
ANTY AISHA MUHAMMAD ( NA JINJINA MIKI)
HAJIYA HALIMA ADAMU
BARISTER AISHA USMAN ( DOLE IN SANYA DAKE)
HAJIYA ZULAIHAT MUHAMMAD ( KIN TAKA MUHIMMIYAR RAWA)


ANTY NURATU ADAMU FASKARI ( KIN BANI GUDUNMAWA TA MUSAMMAN, NA KUMA
YABA DA KULAWARKI GARENI)





LAMBA TA HUƊU
"Shamsiyya kece kika fige kika dawo haka, uwa wacce ake gutsuran namanki?" Baba Shatu
tace.
"Haba Rakiya, mai makon ki tausheta kuma, sai kike ƙoƙarin ingizata inda bai dace ba." A
zafafe tace.
"Amman Shatu kina gani Audu ya ɗakko shirin nakasa mana yarinya? Dubi yanda jini ya taru
a idanunta fa, ga tsohon ciki a jikinta, ina ganin rashin tausayin ai kamar yayi yawa ko?. Ya
kamata a tsawata mishi, kawar da kai da muke yi, baya nufin bamu damu da Shamsiyya ba,
muna yin hakanne dan siya mata mutunci da kima a idanun surukanta, da facalolinta." Buɗar
bakin Baba Sahura kishiyar Baba Shatu tace.
"To kema kinsan ba zamu kasa tsawatar mishi ba, albasace ba tai halin ruwa ba, kinsan
yaranmu na yau, ganinmu suke yi mu iyayensu mata kamar ba abakin komai ba, to yaro tun
yana cinyarka za'aita zaginka, ana wulaƙantaka a gabanshi, sai kiga sun taso basa bamu
daraja. Amma ai kamar yadda mahaifiyarta tayi haƙuri da dukan mahaifinta, itama ya kamata
tayi koyi da mahaifiyarta ko?" Naji ciwon maganar Baba Sahura sosai, haka hawaye yaita sintiri
a kuncina. Hannun Goggo Rakiya naja muka wuce ɗaki, dan ta kasa haƙuri sai zazzagama
Baba Sahura jaraba take yi, ni kuma ina gudun abunda zai jawo mun abun faɗe a wannan
ƙauye namu. Muna shiga na fashe da kuka, nan Goggo Rakiya ta shiga lallashina.
"Goggo Rakiya dama ashe haka auren yake, ashe haka maza suke, shine ake tururuwar

yin aure, ashe babu komai a cikin aure, sai ƙunci da tashin hankali? Tun muna yara muke ganin
mahaifiyarmu na kuka, wata rana muna jiyo yanda mahaifinmu ke zaneta tamkar jakar daya
ɗauro ma kaya, taƙi tafiya. Yau gashi nima na faɗa irin taskun da mahaifiyata take ciki. Kuma
nasan a haka zanta zaman haƙuri, har ranar da Allah zai kawo mun ɗauki." Goggo Rakiya tace. "Da zan fasa miki irin haƙurin da Ta Annabi tayi a zaman aurenta ko da zaki kwashi
abubbuwa da dama Shamsiyya. Mahaifiyarki bata taɓa gudowa gida da sunan yaji ba, kuma
bata taɓa kawo ƙarar Babanku ba. Sai ranar da muka gani da idanuwanmu, a lokacin ta haifeki
da ɗanyen jego a jikinta, ranar sunanki da safe. A jikin ƙarfen gado mahaifinki ya ɗaure Ta
Annabi, ya riƙa tabka mata dorina tana ihu. Suna cikin wannan halin muka shigo muka same su,
maƙwanta sun shigo kawo mata ɗauki. A ranar maƙwabtanta suka labarta mana irin ayar da
mahaifinki yake gasa mata a hannu. Karki manta a lokacin akwai yayyenki maza biyu a
gabansu. Yau gashi ankai wani matsayi da matakin da Ta Annabi itace hasken cikin gidan
mahaifinki, tayi haƙurine ba dan komai ba, sai dan ku data haifa dan bata ko sha'awar
tsallakewa ta barku." Tsabar tashin hankali da kaɗuwa take naƙuda ta kamani. Kafin Magriba ta
rufa, na santalo yarinyata mace. Babu irin zagi da ɗiban albarkan da Audu baiyi mun ba, akan
haifar mace dana kuma yi.
Ranar suna yarinya taci suna Tahira. Ashe a ranar aka ɗaura auren Audu, ni ina ɗaki
bansan wainar da ake toyawa ba.
Zaman doya da manja muke yi tsakanina da Amaryar Audu Hindu. Audu ya tare a ɗakin
amarya, anata ɗonan romon Amarci, ni kuma ina daga gefe ina kula da yarana.
Gorantama Audu aka soma yi a gidan dambe, har anayi mishi kirari da ragon namiji. Ranar
kuwa nasha zagi a wajan Audu. Hindu tace.
"Ka sha kuruminka goga na Hindu, ga cikin magaji nan a jikina. Nice zan haifa maka
magaji da yardar Allah. Tun daga wannan rana, Audu ya ƙara ƙaimi wajan kulawa da Hindu, har
zuwa lokacin data sintilo ɗanta kyakkyawa namiji. Ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Audu.
Muttaƙa, ana kiranshi da Baban gida. Sai da Hindu ta Haifi yaronta na biyu, Audu ya dawo
ɗakina kafin Hindu ta gama biki, dan rabon kwanan da yake yi mana na rashin tsoron Allah ne.
Zai iya kwana bakwai a ɗakin Hindu kafin ya dawo ɗakina, wani lokaci daya kwana ɗaya zai
koma ɗakin Hindu, a hakan na kuma haifan Basira, harda ƙaramin ciki a jikina yanzu haka..
Ashe dawowa ɗakina da Audu yayi hakan ya ƙona ran Hindu ainun. Har ɗakina ta shigo ta
dinga tsiwa akan Audu, tana yi mishi ɗiban albarka. Daya fusata ya shiga jibgarta kamar anyi
mishi wahayi. Baki na taɓe, ai miji madoki baya dena duka, har sai ranar da tsufa ya rufan
mishi.
"Allah ya isana, shege mara mutunci, tsinanne azzalumi. Inji Hindu wacce bakinta yaƙi
rufuwa. Duka har tsakar gida. Baba Shatu, da Baba Sahura suka tawo a guje, suka riƙe Hindu
wacce take ta kutuntumawa Audu zagi, bakinta duk ya fashe yana zubar jini.
"Shege ɗan gidan taƙi zama."
Wani irin naushi Audu ya kai mata, Baba Shatu ta tare Hindu, ai kuwa Audu ya sauke mata
naushi a bakinta. Ji kake gib. Take bakin Baba Shatu ya fashe, yawu da jini, da haƙora biyu
suka zubo. A take ta hangure ( suma).


Mrs Bukhari ce.

Ai mun dai afuwa, yau lahadi oga na gida. Masu ƙorafin sun rikice kuma. Ya kamata ku gane
wani ɓangaren labarin na taɓa. Dan labarin mata iyayen giji, bai ta'anlaƙa a kan tauraruwa ɗaya
ba. Muna da taurari da yawa, kuma zamu shiga gidajensu da garinsu, mu taɓo rayuwarsu. Allah
yasa kun fahimta?

Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman
na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas
mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata
saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin

07068606171
08104335144
08179523215



*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_

1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
(GAWURTATTU UKU)

*_GAWURTATTU UKU2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*

SAMFOTI





LAMBA TA BIYAR

Saleri:
Ƙarƙashin ƙaramar hukumar Azare, jihar Bauchin Najeriya.

Saleri ƙauyene ƙayayau, daga Azare sai an wuce rugage biyar kafin a iso Saleri. Kab garin
Saleri, basu da katangar ƙasa, sai dangar kara. Gidajen ƙauyen a jere suke babu fasali, dan in
ka shiga gida ɗaya, a cikinshi zaka iya ɓullawa gidaje sama da goma. Suna da makarantar
boko, da malamai biyu, malamin lissafi, da malamin turanci. Wannan makarantar ada ana
karatu a ciki, shima daga lokacin rani kawai, da zaran damina tayi, yara suna gona. Amma
yanzu ba'a karatu a wannan makarantar, wani mahaukaci ne yake kwana a ciki. Babu asibiti,
har sai sun hau Bodi ya fita dasu zuwa Azare tukunna. Babu wutar lantarki, rijiya ɗaya ce a
garin jol, duk jama,ar Saleri a wannan rijiya suke ɗiban ruwa, sai rafi da suke zuwa wanki,
dabbobinsu ma a rafin suke shan ruwa. basu da injina, Mata ke surfe hatsi su dake ya zama
gari, sai su sarrafashi, in buski zasu yi kuma, a dutsin niƙa na hannu suke zuba hatsin su ɓarje
shi. Suna noma ka'in da na in. Mata da yara in damina tayi, tare duk ake zuwa ayi noma. Mace
zata iya hayan gona, ita da yaranta maza da mata su nome gonar. Mai garin Saleri wanda ya
rasu yana da kambun baka. Da yaga saurayi ya taso da gaye, da jarumta, zaiyi tofin Allah ya
tsine akan yaron. Da sannu sannu yaron zai kwanta jinyar da saita zama silar ajalinsa. Amma
yanzu Allah yayi ma Mai garinnan rasuwa, har an naɗa wani.

Musina:
Alwala nake ɗaurawa, ina zaune akan wani dutsi. Kukan Yarona Ƙasimu na jiyo, a zabure na
miƙe, dan inje in ɗaukoshi, shekaran jiya_jiyannan ya faɗo akan maulidi (gado mai rumfa) ya
dauje hanci. Salati na jiyo Baba Hauwa na rabtaɓawa harda tafa hannaye.
"Kai amma Musina baki da kunya wallahi. A gabana ina uwar mijinki kike zabura dan ɗanki
kin jiyo yana kuka? Lallai Yawale ya auro mana fitsararriya, ko dama ance kinyi makarantar
firamare. Amman in banda rashin neman albarka yaushe zaki yi haka a gaban Yar miji ma,
ballantana har kiyi a gabana ni uwar mijinki. Kishiyarta Baba Huwaila ta amshe da cewa. "Ke kin mance sanda Yawale ya karɓi Idi ya baki ne, wanne irin kuka da rama ne bata yi ba.
Har yanzu ƙulafacin Idin take yi. Mu da sai mun haifi yara uku ana kwacewa, saika haifi na
huɗune za'a barma. Haka zamu kawar da kanmu akan yarannan, har sai sun girma zasu san
iyayensu na ainihi, raɓarmu ba bama bari yarannan suyu sabida kawaici irin namu na
hausawa." Jin faɗowar Ƙasimu da shiɗewarshi, yasa na bar wajan a jijice, ni nama mance da su
Baba Huwaila sam. A ƙasa na taddashi, hancinshi ya kuma daujewa, bakinshi sai jini yake
zubarwa. Hannuna yana rawa na ɗagoshi, kujerar tsugunna na jawo na zauna a gaban
kwabata, kusa da kumbunan dake ƙasa a jere hawan hawa. Nono na zura mishi, na soma shafa
kanshi, sai ajjiyar zuchiya yake saukewa. Ni kuma sai hawaye nake fitarwa. Wannan wacce irin
rayuwace mara ƴanci, rana zafi inuwa ƙuna. Zafi a wajan surukai, zafi a wajan miji, zafi a wajan
facaloli, a hannun uban mijina kawai nake samun dama dama, sai Yayan Yawale, da ƙannen sa
maza.
"Yayi tabbatacciyar maras kunya. Ni ina magana shine kika tawo kika barni a wajan ko?. Mu
ada, in uwar miji na magana ma, wallahi tari wannan baki isa kiyi ba, balle ki ki tafi ki barta a
tsaye tana magana, da shike iyayenki sun damƙa ragamar tarbiyyarki a hannun yahudawa
marasa addini shi yasa. Amma a al'adance ke fitsararriyace ta ƙarshen zance" Da sauri na
ɗago, Baba Huwaila ce riƙe da labulen ɗakina. Kasa cewa komai nayi, dana bata haƙuri zata ce
na kuma yin wani babban laifin, koma tace zaginta nayi. Hawaye kawai nake zubarwa.
"Yayi kyau, sabida anyi miki faɗa, shine kika tusa yaro a gaba, kina zubar hawaye ko? To
bari kiji shi kanshi Ƙasimun kina yayeshi zan karɓeshi, kiyi maza ki tashi ki koma bakin aikin
girki, su A'i ai ba bayinki bane da zasu gwafe suna daka, ke kina ɗaki, kuma a gama tuwon kifi
kowa bakin ci.. ." Labulen ɗakin ta saki. Wani irin kuka ne ya turniƙeni, da ƙyar na rarrashi
zuchiyata nayi shiru. Ƙasimu na shinfiɗe a gadon bono. Sai naji danshin ruwa a jikina. Dana
duba jikin Ƙasimu sai naga baiyi fitsari ba. Zanin na sake, na fita tsakar gida na sako alwala,
amma ina cikin Sallah na kuma jin danshin ruwannan, sallamewa nayi jikina ya shiga rawa
To meye wannan, daga ina wannan ruwa? Kai bari dai in sake alwala."
Fita na kuma yi na sako alwala, a taƙaice a daddafe nayi sallah a ranar, daga jikina ruwannan
yake fitowa gashi harna kuma jiƙe zanina. Kuka na rushe dani dana gane na kamu da lalurar
yoyyon fitsarine, hankalina ba ƙaramin mugun tashi yayi ba.
Kuka nake rerawa mai sauti, a haka Baba Hauwa ta buɗe labule ta sameni."
"Au har yanzu kukan kike yi tabbatacciya? Zaki tashi kije ki kama musu aiki ne ko yaya,
maras kunya fitararriya."
Kiyi haƙuri Baba, ganinan.

"Moin rufa mini baki, wacce bata iya shiru in babba nayi mata magana ba."
Labulen ta saki,

3 / 21