Iyayen Giji Book Compelet Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 21

21K to 24K   out of 61.8K words

gaisheshi tare da
wucewa ɗakin Mai riga dan gaishe da Tani. Shehu kuma suka wuce ciki da Ɗahiru.
"Zauna kawu bari insa Iyami ta kawo maka abinci da ruwa." Dariya Ɗahiru yayi yace.
"Shehu jarumin dawa, ka gagari kowa a dawa." Dariya Shehu yayi kawai ya fita.


Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman
na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas
mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata
saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin

07068606171
08104335144
08179523215



*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*

_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_



MRS BUKHARI
MALLAKIN BADI'AT IBRAHIM
( MRS BUKHARI)
(GAWURTATTU UKU)2023


INA TAYAKI MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWARKI. KIYI HAƘURI NAYI LATTI.
ALLAH YA SAKE MA RAYUWA ALBARKA. KI DAƊE KIYI ƘARKO ( LAILA ALI OTHMAN)
FARAR MACE ALKYABBAR MATA, SUKARI BAKIYI FARIN BANZA BA.


*_GAWURTATTU UKU2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA

WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*


SAMFOTI

LAMBA TA GOMA


Lauwali ne ya shiga ɗakin da Ɗahiru yake ciki da sallama. Yana ganin Ɗahiru ya shiga washe
baki.
"Kawu ashe dai da gasken kune a tafe? Sannunku da zuwa."
"Lauwali sarkin gashi, a gasa zomo, a gasa maciji, a gasa, akuya, a gasa tunkiya da ƴaƴan
cikinta. Ya farauta kuma, naji labarin Jafaru na wajanka yana nema ya gajeka." Dariya Lauwali
yayi.
"Kawu ga gashashshen naman maciji na ƙunso maka." Ɗahiru yace
"Kamar kasan kuwa ina kewa. Kai kowa yabar gida, gida ya barshi. Meye a bariki in ba
hawala ba. Komai nasu tsada, abun ba'a magana. Bani labarin dawa." Naman macijin ya soma
ci. Iyami ce tayi sallama ta shigo, hannunta riƙe da langar tuwo da miya, Shehu na biye da'ita da
sassanyar ruwan tulu a kwanon sha. A gabanshi ta dire, suka kuma gaisawa sannan ta fice.
Lauwali yace.
"Ai Kawu Shehu za'a tambaya labarin dawa, dan yana daga cikin samarin da aka ware za'a
gwada jarumtarsu dan a naɗasu sarautar sarkin mafarauta na ƙauyannan. Jibi ma zasu tafi
gwajin ƙarshe a cikin dajin kankia, daji mai haɗari da ƙwanƙwamai. Amma anata dai girka shi,
malam yana ta taimakawa da rubutu shima, duk wani kauci da sassaƙen daya dace yasha, ya
gama Kawu." Dariya Ɗahiru ya saka har yana buga ƙafafu dan Ɗahiru baduniye ne sosai.
"Kai kace gara da Allah yasa na dawo, ina gida za'ayi naɗinnan naka Shehu. Abun yayi
mun daɗi, kaji shaƙiyyyin yaro mu ba'ai mana tayin sarauta ba sai kai. Wato sarkin mafarauta ya
mutu?" Shehu yace.
"Yayi doguwar jinya sosai kafin ya mutu. Aljanune suka shafeshi suka sabauta mishi
lafiyarsu. Wai wani mai sarauta ya taɓa a cikinsu." Ɗahiru yace.
"Hmmm mahaifinshi ma daya mutu, aljanune suka taɓashi, hauka yayi tuburan yana yawo
da kamfai. Yawancin sarakan mafarauta ƙarshe da aljanu suke fafatawa wanda yaci nasara ya
hallaka abokin gabanshi. Shehu me aka samu ne mace ko namiji ance matarka ta haihu?" Wani
baƙin cikine ya turniƙe Shehu dan baya ƙaunar a dangantashi da Laila ma balle yaronta. Kasa
magana yayi, Lauwali yace.
"Namiji ne, Kawu sunanka ma yaron yaci. Amma mai lalurace ta mata maza. Tunda akayi
haihuwarnan Shehu yake cikin tashin hankali, sai saƙe saƙe yake yi".
"Mata maza, kuma dai nasan mayu basa iya raɓar zuriyar gidanmu, ko dai abokan
hamayya ne suka sabautaka Shehu, dan kar yayi nasara? Kasan dai bazai haifi mata maza yayi
tunanin cin nasara ba. Inma fa zaici nasarar saiya tashi tsaye yayi da gasken gaske tukunna.
Wannan mata anya alkhairi ce a gareka kuwa, daga haihuwar ɗan fari? Wa yasan wanne

jarabar zata haifo nan gaba. Ni ina ganin ka saketa kawai ta ɗauki ɗanta ta kama gabanta. Dan
wulaƙanci a rasa wanda za'aimun magaji dashi sai mata maza? Yarinyarnan karfa ka bari ta
taɓama mihibbarka, ina ganin haɗin naku babu alkairi duk yanda akayi mai farar ƙafa ce."
Hannu yasa ya soma cin tuwon da Iyami ta kawo mishi. Lauwali yace. "Kawu bari in koma tukuba na bar Jafaru a wajan shi kaɗai." Tuwo cike da bakinshi yace.
"To gobe zamu haɗu, dana gama zan kwanta."
Shehu dai yana zaune yana ta jujjuya zancan Ɗahiru a ranshi, duk da shima yana tunanin ko
ya rabu da Laila ne kawai? Amma kuma akwai wani buri da yake son cinmmawa, kuma yana
tunanin in Laila tana ƙarƙashin inuwar aurenshi, burin nashi zaifi saurin cimmuwa, in yaso daga
baya saiya cika ma rigarta iska. "Shehu, ince dai da daddare babu wanda yake fitowa tsakar gida ko? Dan akwai sunan wani
aljani da zan kira biyun dare, zaimun aiki ne, kuma ance ba'ason kowa ya ganni a lokacin da
zan kirawo shi." Shehu ya dubi Ɗahiru yace.
"Babu mai fitowa, inma sun fito sai in zasu sakaki, kuma kaga a bayan gida can nesa yake."
"To sai ka kula duk abinda zaka ji inayi, karka kuskura ka juyo dan zaka iya halaka."
Shehu ya haɗe hannayenshi biyu suka daki idanun hannunwanshi duka biyu irinna ƙauraye
yace.
"Caw badai mutum ba, ba dai aljanba sai dai Allah. Nasha tabara, nasha yasin babu
wani aljani da zai iya ja dani. Kawu wuya a jeji, wuya a kasuwa fa " Dariya suka saka dukkansu.

Ta ɓangaren Malam, da Baban yara kuwa, bacci ya gagara ɗaukarsu suna tsoron mai gobe
zata haifar. Dan sun tabbatar yanzu haka shigowar su Ɗahiru an samu mai gari an sanar mishi.
Gashi bayan tafiyarshi abubbuwa da yawa nashi sun ɓullo, ƙila ma a ƙone musu gidan nasu a
wannan karon."
Tani:
"Ai Yaya mai riga, faɗar wahalar dake cikin bariki ba'a magana wallahi."
"Tani kun tafi kunbar baya da ƙura, dan wallahi guguwace ta tashi mai mugun ƙarfi, wanda
mu kanmu saida ta kusan halaka mana rayuwa. Rikici anyi shi, dan Malam ma aka so a kama,
wai kotun birni suke son a shiga. Ke Malam fa saida ya dena bacci, kullum sallah da sadakar
zazzafan ƙosai. To sai maganar ta mutu. Mahaifanki ma, suka zo suka tada zaune tsaye a
gidannan, akan ada tilas sai mun fito musu da ƴarsu. Sanadiyyar hakan ɗan zumuncin dake
tsakani ya rushe. Wancan yaron ma yaso ya Auri ƴar gidan Iyatu, amma mahaifinki daya daka
tsalle ya duro, dole muka janye. Ke abu dai babu daɗi." Inji Baba mai riga kenan. Matar malam
tace.
"Ai nasan gobe fada zata cika, ke mai garinma da kanshi zai taso babu mamaki." Haka
sukaita tattaunawa dai, daga baya suka kwanta bacci. Dama yaran sun jima dayin nasu baccin.


Ɗahiru.
Ƙarfe biyun dare ya fito tsakar gida tsirara haihuwar uwarshi da ubanshi, da wani turare na kiran
aljanin da aka bashi sunanshi.
"Kayanasu, kayanasu, kayanasu"

Taku Ɗahiru ya soma ji dib dib a bayanshi. Take tsoro ya rufeshi, wani irin hayaƙine ya ya
makanta ganin Ɗahiru. Magana ya soma ji kamar raɗa a kunnenshi.
"Labari ya iso mun. Ka samu duniya, zaka zama daga cikin shahararrun bokayen duniya.
Gari, gari za'a dinga zancanka. Amma aikin da zamu baka da wuya. Muna buƙatar mahaifar da
ƴarka take kwance a ciki. Dan haka gobe za'a haife yarinyar, sannan zamu ajjiye maka ƙoƙo da
zaka taran mana jinin haihuwar matarka. Sannan muna buƙatar zabi guda ashirin, ka kalli
yamma ka murɗe musu wuya ɗaya bayan ɗaya, ka tsotse jininsu tas ka shanye. Ayi sadaka da
naman bayan an soya. Sannan ka samo jaki ka yanka a dokar daji a darennan, ka tona rami
jinin ya tsiyaye a rami, saika ciro harshenshi da idanunshi ka ajjiye mana. Kana yin wannan
aikin ka hau mataki na farko, kuma babu mai ja da kai, musu wannan babu mai yi da kai.
Wannan shine mataki na farko, kuma karka sake a ganka yayin da zaka aikata komai." Ɗib ya
daina jin maganar, a hankali Ɗahiru ya soma ganin gabanshi. Juyawa yayi ya koma ɗakin
zaure. Wando da rigarshi ya mayar. Ya shiga tashin Shehu.
"Kai Shehu, ana kiwon jakai a gidannan ne?" Cikin jin bacci Shehu yace.
"A'a Kawu bamu da jaki ko ɗaya. Kasan ai gidan ɗan fulani maƙocinmu shine mai jakai"
Shiru Ɗahiru yayi. Wuƙa ya zara, ya ɗauki layar zanan Shehu ya fice a gidan."


Tafe yake yana jan jaki har zuwa dokar daji, garin shiru kowa na bacci. Rami Ɗahiru ya shiga
tonawa, sai zufa yake ta faman yi. Yana gama tona raminnan ya yanka jakinnan, bayan sun sha
turka_turka. Ya ciri abunda aljani yace ya cira. Ya bar gawar jakinnan a yashe a wajan. Ya nufo
hanyar dawowa. Yana fitowa daga dajin ana kiran sallar asuba. Hanyar kasuwar ƙauyen dake
maƙwabtaka dasu ya nufa, dan yau ake cin kasuwa a ƙauyen. Ya shiga ƙauyen kasuwa bata
ma soma ci ba. Sallar asuba yayi a ƙauyan, yana zaune aka soma cin kasuwar. Ɓangaren masu
kaji ya duba. Yako samo zabin cikin rahusa jaka ɗaɗɗiyq ya sane su. Buhu ya siya, ya kama
hanya. A wani lungu ya tsaya, ya dinga murɗe wuyan zabinnan yana zuƙe musu jini, a
haka_haka har ya gama ya ɗuresu a buhu. Yana tafe yana murmushi, burinshi ya zama
shahararren gaske ta yanda labarin bokancinshi zai kewaye ƙasarshi Najeria kab. Yaga irin
nasara da tarin dukiyar da abokinshi Ɗan Audu ya tara, duk ta sanadiyyar bokanci. Da kiɗan
gambara yake yi a bakin kasuwa. Amma a halin yanzu ya tamfatsa gida a kurmin mashi, yana
hawa mota, ga malum_malum na shadda, taji aikin aska tara, ya samu sukuni har kumatu da
tumbi ya ajjiye. Ɗan Audu abokin Ɗahiru ne, Ɗahiru yaji sha'awar ya zama mai sukuni kamar
Ɗan Audu. Sabida tun tasowarshi ya taso da mugun son abun duniya. Tun yana yawon bara
yake ƴan sace_sace ƙananu. A hannun Malam ya girma dan tun bayan rasuwar mahaifiyarsu,
riƙon Ɗahiru ya dawo hannun malam a lokacin Ɗahiru na da shekara goma da haihuwa. Ya taso
da rashin ji da muguwar ƙeta, dan ko kaza inta bashi haushi, yana iya kasheta ya huta. Ya taɓa
farke ma wata akuyarsu mai ciki, cikin nata da aska."


Gidan mai Gari:

MRS BUKHARI.

Anan na kawo ƙarshen free page. Wato samfoti. Mai son kasancewa da wannan littafin mai
ɗumbun darasi, mai cike da abun mamaki saiya tuntuɓi gawurtattu uku. Karku mance wannan
labarin ya faru a gaske, ba ƙirƙira akayi ba. Ku nuna mana soyayya masoyanmu na faɗin duniya
baki ɗaya.


Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman
na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas
mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata
saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin

07068606171
08104335144
08179523215



*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_

_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: BADI'AT IBRAHIM ( MRS
BUKHARI)
(GAWURTATTU UKU)





Lamba ta goma sha ɗaya

ƊANBO:
"Ka kashe uwar taka Audu, sakamakon baƙar zuchiyarka. Bala da kai dashi ku kamata a kaita
ɗakinta. A kirawo mai magani kuma". Audu sai Huci kawai yake yi, suna shiga da Baba Shatu

ya fito, bai bari an yayyafa mata ruwa ta farfaɗoba ma. Gadan_gadan ya nufo Hindu wacce take
zaune a inda aka barta. Ya shiga gibgarta kamar Allah ya aikoshi. Ni kuwa wucewa ta nayi
ɗakin Baba Shatu.
Gabaki ɗaya halittarta ta sauya, fuskarta ta kumbura. Da ƙyar mai magani ya buɗe bakin Baba,
tana buɗewa wasu haƙora biyu suka sake zubowa. Kurkura mata magani akayi, nan ma haƙora
biyu suka kuma biyo ruwan maganin, ya bata wasu saiwu yace a dafa mata."
"Shamsiyya karɓi kije ki dafo mata." Karɓa nayi na fice. Dai_dai da fitowar Hindu da goyon
jaririnta, tana jaye da Shagari ta fice tana kutuntumawa Audu ashariya manya_manya irinna
cikakkun sokotawa. Baki na kwaɓe danni Hindu tayi mun dai_dai data nuna ma Audu iyakarshi,
kuma bakinta yaƙi mutuwa dole shine ya haƙura ya barta. Na kuma ji daɗi daya dakata ta gane
duk irin son da Audu yake yi mata, zai iya mata hukunci irin wanda yake yi mini, ko babu komai
na tabbatar, dole rawar kanta ta sauka, wasu abubbuwan zata sauke su.
Amma kash a daren aka dawo da Hindu, iyayenta kuma sukaita cin mutunci kafin su tafi, suna
goyon bayanta, ashariya buhu _buhu haka su kaita zazzagarwa a tsakar gidannan, ashe ko
wanne tsuntsu kukan gidansu yake yi. A daren a ɗakin Hindu Audu ya kwana, ni kuma suka
barni da cizon yatsa. Washe gari, Yaya Bebi tazo ta dinga zagin Audu, babbar yarsu ce ita, taji labarin duk abinda ya
afku,

8 / 21