Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
maza kuma muka samu? Kaik abun baiyi daɗi ba. Dan samuwar
yaronnan zai iya taɓa duniyarki, an riga an canfa irin haihuwarsu." Dam gabana ya faɗi har nake
jin hawaye na shirin subce mun. Daddo tace.
"Wannan duk canfinmu ne Kande na malam bahaushe. Ba wani abunda zai samu Laila
sanadin haihuwar yaronnan sai alkhairi. Ke Laila shiga ɗaki jikinki ɗanye ne. Yanzu ma zanzo
muyi wanka. Kici gaba da kwanciya a gadon ƙasannan." Jikina a saɓule na miƙe, kobi ta kan
Asiya ban sake bi ba.
Ta Asibi:
"Sai muka ji biki Malam yana shaida mana, ashe Asiya Shehun Laila zata aura? Shehunma
bai jima da tafiya ba. Allah ya sa gidan zamanta ne" Cewar Ta Asibi kenan. Kande duk rashin
kunyarta sai taji nauyi ya rufeta, nan ta shiga kame_kame dasokiburutsun zance"
"To ya zanyi. Buba ne ya ɗaure mata gindi. Har duka nayi mata, amman ta kafe sai shi. Wai
tun lokacin bikin Lailan suka soma maganar aure. Yaya Abinda Allah ya nufa saiya faru. Masu
iya magana sukance matar mutum. Shine na tawo da'ita zan kaita wajan Laraba ta zauna a can,
ta dinga yi mata ƙunzugun lalle. In yaso in bikin ya rage kwanaki, saiki tawo da'ita Yaya" Da
Daddo da Ta Asibi sun sha ruwan mamaki. Amman haka suka kanne, Kande ta kwana washe
gari ta juya. Ta Asibi ta ɗauki Asiya ta kaita gidan Laraba. Kwananta bakwai a gidan Laraba,
ana takwas ne Ta Asibi dasu Nazeefa suka ɗunguma zuwa Dutsen ma dan gudanar da biki.
Laila tana nan gaho bata san wa Asiya zata aura ba. Har sai bayan da aka kammala biki
Amarya ta tare a ɗakin angonta. Sannan suka zaunar da Laila dan faiyace mata halin da ake
ciki.
Laila
Mrs Bukhari
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: *_GAWURTATTU UKU2023_*
*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don
koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in
akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan
idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya
don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin
07068606171
08104335144
08179523215
*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._
*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA ASHIRIN DA BIYU
LAILA:
"Laila ki buɗe kunnanki da kyau kiji me Daddonki zata faɗa miki. Kuma kiyi haƙuri da
dukkannin abunda zaki ji." Innata tana kaiwa nan saita fice. Ni kuma jikina har rawa yake yi
tsabaragen kaɗuwa, dama a daren jiya da aka ɗaura auren Shehu banko iya runtsawaba.
Yanzu na gane dalilin matan da suka kasa tawakkali dan mijinsu ya ƙara aure, suyi hauka. Zafi
da ciwon kishi, iyayen gida ne kaɗai ka iya ɗanɗana harsu gane abunda nake nufi ( Su maman
Khairat,Deezatu ai baza su gane me nake nufi ba. Maman Yaseer ce kaɗai za tai mun uziri)
"Laila" Daddo ta kirayi sunana da harshe rarrauna."
"Shehu yayi aure har ya wayi gari a ɗakin amaryarshi. Abunda zamu ɗauraki akai shine
haƙuri da juriya. Mai haƙuri shi kan dafa dutse har yasha romanshi. Ni da gyatumarki kina gani
babu abunda yake shiga tsakaninmu na husuma. A tsakanina da'ita girmamawace, dan sanda
aka auroni, shekaruna goma ina cikin na sha ɗaya. Ita da mahaifinku suka taru suka raineni.
Kinsan dama ko mu jima, ko mu daɗe Shehu dole zai ƙaro aure. Ballema da kika haifi Ɗahiru
kinsan yanda ƙabilarmu ta malam bahaushe ta canfa yara irinsu Ɗahiru. Babban abunda zan
daɗa miki dashi shine, ki rungumi yaronki karki hofantar dashi, dan babu mai kula miki dashi,
saike. Ki dage ki ta mishi adda'a ko Allah zaisa rayuwarshi tayi albarka. Ba kowa Shehu ya aura
ba face Asiyan Kande ƴar uwarki. Amman ki daure ki jure zama da'ita Ta Asibi tace in horeki
karki kuskura ki lalata musu zumuncinsu." Hawaye ya gama wanke mun fuskata har ɗiga yake
yi. Sai yanzu nake tuno irin kallon da Shehu ke jifan Asiya dashi, sau tari ina kama Shehu na
jifan Asiya da murmushi. Kasancewar ƴar uwatace ban taɓa kawo komai a raina ba ashe Shehu
aurenta yake son yayi. Naji zafi ainun dan kwanana biyu ina cikin ruɗu da damuwa. Saida
malam yaita mun nasiha sannan na dangana. Yaya Nafi matar wanmu ita taita zagawa dani
yawon arba'in. Munyi ziyare_ziyare sosai. Bayan mun dawo kuma na soma shirin komawa, duk
da a cikin fargaba nake, dan bansan me zan tadda a gidan ba. Na shirya tsab, Goggo Laraba
da Yaya Nazeefa da Anty Nafi sune sukai mun rakiya. Ina sa ƙafa a cikin gidan gabana ya
yanke ya faɗi, su Iyami suka shiga jaye yaransu ƙananu. Su tsaya ma mu gaisa, sai daga
nesa_nesa. A ɗakin Baba mai riga muka yada zango. "Kune a gari Laraba, sannunku da zuwa"
"Yauwa sannunmu Mai riga, ga Laila mun dawo muku da'ita yadda kuka bamu haka muka
dawo muku da'ita. Ya akaji da taro?" Baba mai riga ta yashe baki tace
"Taro ya watse lafiya. Sauran dangin mahaifin Shehun ma suna can ɗakin matar Malam
basu tafi ba. Laila ya Ɗahirun?" Yaya Nazeefa tace.
"Me gidanki lafiya lau, yayi mul_mul dashi. Ni dai kaina a ƙasa har muka miƙe. Ɗaki_ɗaki
na leƙa aka sake gaggaisawa. Sannan muka shigo ɗakina.
"Yanzu Laila ni inaga bari muyi miki kwalima, tunda sai gobe zamu juya, mu sake miki
fasalin ɗakin. Saiki sake labulen da Inna tayi miki. Ni dai ina zaune sai tunani nake faman yi. Su
kuma gadan_gadan suka shiga aiki. Sai bayan Isha suka game komai. Har zuwa lokacin Shehu
bai leƙo ɗakin ba. Kuma ina jiyo muryarshi, yana kaɗa yara. Idanu na lumshe, a yanda naga
rana haka naga dare. Sai jefin asuba na samu nannauyan bacci ya ɗebeni. Da sassafe su Yaya
Nazeefa suka soma shirin tafiya. Goggo Laraba tace.
"Taso muje ɗakin Asiyan mu gani, tunda ita bata da kunya ta kasa yi miki sannu da
zuwa" Idanu na gwalalo nace.
Goggo me yasa zamu je, ita da Shehun duk sun san mun dawo fa, amman ba wanda
yazo ya duba mu." Sai tace.
"Ke dai ƴannan muje, ki daure ki cusa mata aniyarta." Haka suka sani gaba muka shiga,
Asiya kamar babu wata dangantaka a tsakaninmu da'ita haka tayi mana. Goggo Laraba tayi
mana nasiha, ni kuwa sai ƙarema Asiya kallo nake. Ashe banda komai ba. Wasa_wasa na
zama bola a gidan Shehu, sai Shehu ya ishi Asiya yake zuwa ya nemi hakkinshi. Babu zancan
rabon kwana sam. Ni kuwa haka na dinga kannewa inata jure duk wani abu dazai ɓullo. Ɗahiru
kuwa na mayar da hankali kan renonshi. Tani da kishiyoyinta kullum a cikin faɗace_faɗace da
gore_gore suke. Kawu Ɗahiru kuwa ya zama shahararren malamin da ake ji dashi, dan aikinshi
tamkar yankan wuƙa haka yake. Kullum gidan a cikin baƙi mata yake, kullum sai an yanka kaji
an soya anyi sadaka. Rayuwa taita tamaule damu, Asiya taita baza mulki a zuchiyar Shehu, dan
ko fishi tayi dashi, ranar bashi ba sukuni sam. Ranar naɗin sarautar Shehu ta zagayo, amma ko
labari banji da wuri ba, sai ana jibi za'ayi taron. Haka na auni alkama, da farar shinkafa, na
kaima Sha'awa ƙawata, tai mun nakiya da alkaki, ko wanne fanteka ɗaya. Ranar naɗin sarautar
naci ado cikin yadin banbalasta fari sol, nasha ƙunshi da kitso. Da safe bayan isowar su Yaya
Nazeefa, saita raka ni naje har ɗakin Asiya na kaima Shehu tawa gudunmawar. Ganin haka sai
yaji kunya, yana sanye cikin kayan saƙi, jikinshi cike da layu da guraye, Asiya taci ado da yadin
tentalan, tana gefen hannun Shehu.
"Kiyi haƙuri Laila, Asiya zansa a naɗa a matsayin mai sauraron koken matan mafarauta,
a matsayina na sarkin mafarauta, kinga ita ta'iya rubutu da karatu, ke ko ba ki iyaba. Naji ciwo,
idanuna yai rau_rau, amman saina cije. Nace dashi.
Ai babu komai Shehu, duk dai abinda ka yanke yayi, kaine shugaba, Allah ya taya riƙo
shine fatana." Yaya Nazeefa ta kamo hannuna muka fice. A taƙaice ƴar kallo na zama a filin
naɗin sarautar Shehu. Munsha wasan mafarauta sosai ranar, anyi wasannin al'ada masu ban
ƙawa. Da haka taron ya watse, Shehu ya zama sarki, Asiya shugabar mata. Har taro suke
gudanarwa, duk ƙarshen wata. Dani da Asiya haka mu kaita hayayyafa. Yarana Huɗu cib,
Ɗahiru, Karima, Dauda, Izzatu, Sai tulelen cikin nabiyar. Asiya kuma yaranta Uku namiji ɗaya
mata biyu, sai ƙaramin cikin na huɗu. Faɗar wuyar da nasha a wannan shekarun, ba abu bane
wanda zai rubutu, aimun afuwa.Amman kallo ɗaya kaimun kasan ina azabtuwa, na tsofe, na
bushe, sai hidimar yara nake yi. Ɗahiru kuwa kullum yana ƙunshe a ɗaki, bana bari ya fita, daya
fita yara suke tunkuɗeshi ya faɗi har sai yaji rauni, ko suita tuɓe mai wando suna ma halittarshi
dariya. Kullum yana biye dani, ko kuma ya zauna a dokin ƙofarmu yaita kallon yara suna wasan
ƴar gala_gala a tsakar gida, yaita dariya. Tausayinshi ya cika zuchiyata fam. Shi yasa gabaki
ɗaya na maida hankalina zuwa kanshi. Sallar dare kuwa harya zame mun jiki. Babu da irin
sharrin da Asiya bata bini ba, amma ina ganin falalar adda'a. Tunda na samu wannan cikin,
Asiya ta murɗa kanbunta Shehu bai kuma tako ƙafafunshi da sunan shigowa ɗakin ba. Ga cikin
yazo mun da wani irin laulayi, dan harma na gama fidda rai da rayuwar baki ɗaya. In Yara suka
shiga ɗakin Asiya, sha Allahu da kuka suke fitowa, yaranta ƙananu harta koya musu, hantarar
yayyensu suma.
Ina zaune ina wankin yara. Shehu ya shigo cikin shiga irinta sarakan dawa yace.
"Ke Laila, wancan yaron ya fito, ga mota za'a wuce dasu birni almajirci. Asiya, kema ki kawo
naki, Yaya Iyami, yaran duk su fito. Ƙirji na dafe nace.
Sarki shayi ne a jikin yaronnan, a hakan za'a kaishi almajirci? Jijiyar bata warke ba, jiya da
yasa wando wallahi ya fame ta har saida tayi jini. Sarki karka tagayyara mun yaro" Nan su
Matar Malam su kai ca a kaina. Inaji ina gani, aka fita da Ɗahiru, yana ihun kiran sunana. Ai
take na durƙushe na soma naƙudar dole. A kaina aka rufu, nan naita abu guda, wasa gaske har
washe gari ban haihu ba. Saida suka ga na kusan macewa aka sani a keken shanu, zuwa
Asibiti. Amma Shehu yaƙi zuwa fur, Iyami da matar malam ne suka tafi dani. Ban kuma sanin
ina kaina yake ba. Saina farka naga babu ciki a jikina, ashe tiyata akayi mun.yara maza har
huɗu aka ciro mun, amman ɗaya ana ciroshi, ko kuka bayyi ba ya rasu. Da Shehu na soma
haɗa idanu, yayi zuru yana kallon kyautar da Allah ya bani. Maganar wannan magen ta faɗo
mun da tace " Laila uwar maza" har bayan suna muna asibiti, ƴan uwana suna faman hidima
dani. Dan tunda Shehu yasa kai ya fice a asibitin bai kuma zuwa ba. Ranar sunan matar Malam
tazo nan take shaida mun. Yaran sunci suna. Salisu, Tasi'u Sadisu
Allah ya raya su da imani" Shine abunda nace kawai. Kwananmu tara a asibiti aka
sallame mu. Mahaifina shi ya biya komai daya shafi kuɗi, yaimun goma sha tara na arziki, Yaya
Nazeefa kuma ta bani ɗiyarta Mama dan su taimaka mun, ita da Karima ta wajena da renon
Tawayoyina,tare dasu muka koma gida. Cikin tashin hankali da damuwa naita rainon
Tawayoyina, bana samun tallafi da kulawar kowa. Gasu da kuka sosai. Bayan Shekara da
tafiyar su Ɗahiru, sai gasu sun dawo ganin gida, a lokacin Tawayoyina har sun soma gudunsu
ko'ina. Ɗahiru yayi murna da ganin ƙannenshi. Ya sake yaita wasa a cikinsu yana dariya. Nima
raina fari sol da naga Ɗahiru a cikin walwala. Haka rayuwa taita tafiya. Shekaru suka shuɗe
sosai, su Tawaye har sun girma suma an kaisu almajirci. Asiya ta hana gaba ta hana baya, duk
wata kyautatawa ta hana Shehu yayi mana ni da yara. Su tawaye sun sha azaba sosai a wajan
Asiya da yaranta. Kullum a cikin duka da kyara suke.
Ina tsugunne muna dukan shinkafa zamu cireta daga samfurarerta. Sai ga Malam ya shigo.
"Iyami ki kwashi Su Laila ku tafi ƙofar fada. Akwai baƙi da muka samu daga jam'iyyar matan
arewa. Suna buƙatar a taro kan matan ƙauyen. Tun ɗazu ake ta faman yekuwa." Ni dai inata
aikina, dan duk wani abun arziki ba'a sani a cikinshi, nima bana cusa kaina. Ɗahiru ne yazo zai
kama mana aiki, sai naga jini a bayan rigarshi. Gabana ya yanke ras ya faɗi.
Wannan yaron kaje maza ka sake kayanka" Da sauri ya wuce, ni kuma na bishi da idanu
gabana na faɗuwa. Asiya ce ta fito cikin gwalli tace da Iyami.
"Nifa na fito kuzo muje, Yaya Tani kumujenku mana, Laila kema zaki iya tawowa." Ni babu
tunani a jikina sam, amman haka na ɗauraye jikina na yafa mayafi muka tafi, na bar su Karima
da sauran aikin.
MRS BUKHARI
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: *_GAWURTATTU UKU2023_*
*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA