Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don
koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in
akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan
idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya
don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin
07068606171
08104335144
08179523215
*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._
*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA ASHIRIN DA UKU
LAILA:
Ƙafafuwa kawai nake jefawa, babu kuzari a jikina. Tunanin daya addabeni, meya kawo jini rigar
Ɗahiru? Tani ce ta katsemun tunanina da cewa.
"Ke Laila, kinga Sha'awa ƙawarki sai magana take yi miki fa" Da sauri na juyo na dubi
Sha'awa, wani sanyi naji sosai sabida dama sona inje in sameta mu tattauna.
"Lafiya Uwar Tawayoyi?" Haka Sha'awa take kirana. Nace mata.
Sha'awa wannan yaron ne naga jini a bayan rigarshi, shine duk kika ganni a ruɗe haka,
naji tsoro sosai. Sha'awa tace.
"Zanje in same shi muji ko lafiya, da mun fito fada zan sa Halima tayo mun kiranshi in
tambayeshi duk yanda mu kayi dashi zan tawo in sanar miki." Ajjiyar zuchiya na sauke
nannauya, sai na ɗanji sukuni a raina. Danfa danfan mata muka riske a zazzaune a fadar mai
gari, an shinshinfiɗa karauni, mata da yaran ƙauyan ni bansan sun kai yawan haka ba. Matan
mai gari, suna daga gefe, sa'ilin da baƙin da mu kayi suma suke gefe a zaune. Ga kayayyaki
buhu_buhu a gabansu a jibge. Wata mata daga cikin baƙinmu, mai gari yaba damar yin
magana. Cikin girma da karamci ta soma bayanin abinda ya kawosu cikin ƙauyannan, da
manufar jam'iyyar matan Arewa. Ta ɗaura da bamu asalin cikakken tarihin kafuwar jam'iyyar
matan Arewa kamar haka.
"A ranar 27 ga watan mayu na shekarar 1963, wasu tarin mata suka haɗu a gidan mai ɗakin
tsohon gwamnan jihar Arewa. Hajiya Asiya Hassan Katsina, da nufin yin ƙwarya_ƙwaryar bikin
shan shayi, dan jin daɗinsu. Wanda hakan ya haifar da tattaunawa, gami da shawarwarin da
suka samar da JAM'IYYAR MATAN AREWA. Babban maƙasudin wannan ƙungiya shine,
rungumar dukkannin wata mace da ke arewacin Najeriya, ba tare da yin la'akari addininta ko
ƙabilarta ba. A cokacin da aka kammala tattaunawar da ta haifar da JAM'IYYAR MATAN
AREWA, an samar da kwamiti acikin matan da suke gurun, dan sanar ma firimiyan jihar Arewa
AHMADU BELLO SARDAUNAN SOKOTO , domun sanar dashi yunƙurin da akayi na samar da
JAM'IYYAR MATAN AREWA wacce ta kasance bata siyasa bace. Dan neman shawarwari, da
tallafi, gami da sa mata albarka, a matsayinshi na shugaba, kuma babban mutum.
Matan da su ka kasance a wajan taron bikin shan shayin sun haɗa da.
1 Laila dogon yaro.
wacce itace
ta fara kawo wannan shawara dan taimakon matan Arewa.
2 Comfot G Dikko
3 Inna Talib
4Helen Akilu
5 Aishatu Joɗs
6Tuha Shehu
7Mardiyya Liman Chiroma
8Ladi Yusuf Gobir
9Bilewu Yusuf Gobir
10Ambashai Shu'ab
11Asiya Hassan Katsina
12Laraba Tata Askira
13Mary Hamman Maiduguri
14Jummal Baba Jimeta
15Margaret Durlong
A ƙarshe kwamitin da aka kafa sun samu ganin firimiyan jihar Arewa SA AHMADU BELLO a
ranar 18 ga watan Yulin shekarar 1968 a gidansa.
Bayan an gabatarma da Sardaunan manufofin Ƙungiya, da kuma irin muradan data ƙunsa ta
sanya a gaba, Sardauna ya yi na'am da irin manufofinsu tare da bayyana jin daɗinsa akan
wannan ƙungiya. Inda yayi musu fatan alkhairi tare kuma da basu gudunmawar Fam ɗari a
matsayin gudunmawa, da kuma yi musu alƙawarin basu filin da za su gina ofishin wannan
ƙungiya ta JAM'IYYAR MATAN AREWA. Daga wannan ganawa da aka yi da SA AHMADU
BELLO SARDAUNAN SOKOTO, sai kwamitin ya gana da matan gwamnan jihar Arewa SA
KASHIM IBRAHIM. Waɗanda su ka kasance a gurin wannan ganawa sun haɗa da.
1Khadija Kashim Ibrahim
2 Ya Halima Kashim Ibrahim
3 Zainab Kashim Ibrahim
4Inna Talib
5Helen Akilu
6 Aishatu joɗa
7Comfort Dikko
8Kydia F Zakari
9 Laila dogon yaro
Bayan kammala dukkan wata tattaunawa da akayi da matan gwamna. Sai ɗaya daga cikin
matanshi, uwar gida Khadija Kashim Ibrahim, ta samu gwamna akan wannan lamari. Nan take
kuwa gwamna ya amince da wannan ƙoƙarin na matan Arewa. Khadija uwar gidan Gwamna ta
kirawo taron ganawa a karon farko, wanda ya gudana a gidan Gwamnati, a ranar 21 ga watan
Yuli na shekarar 1963 da misalin ƙarfe huɗun yamma. Jawabin uwargidan Gwamnan ta
bayyana matuƙar buƙatar samar da ƙungiyar matan arewacin Najeriya tare kuma da yin farin
cikin ganin zaratan mata daga yankin Arewacin ƙasar nan da su ka ɗauki zabarin aikin ciyar da
ƙasar nan gaba. A ƙarshen jawabin nata ta yi godiya ga matan da suka samar da wannan
Ƙungiya tare da yi musu addu'ar Allah ya dafa musu akan wannan kyakykyawar niya tasu.
Bayan kammala taron ne aka tafi domun gudanar da zaɓen shugabannin da za su ɗauki nauyin
shugabantar wannan ƙungiya ta JAM'IYYAR MATAN AREWA . An zaɓi shuwagabannin da
mataimakansu. Sai justis Muhammad Bello a matsayin lauyan ƙungiya.
Jim da kammala zaɓen shuwagabannin wannan ƙungiya ta matan Arewa, shuwagabannin sun
kai ziyarar farko zuwa babban asibitin Kaduna a ranar 1 ga watan Disambar shekarar 1964
daga wannan ziyara aka samar da tunanin samar da gidan Marayu.
An sanar da Firimiyan jihar Arewa wannan tunani, inda ya bayar da filin da za'a samar da gidan
marayun, a titin Dendk da ke cikin garin Kaduna. Daga wannan gidan Marayu jam'iyyar matan
Arewa ta samar da makarantun kwana na sakandare, tare da motocin jigilar maido ɗabibai
jihohinsu. Wannan ƙungiyar bata gaza ba wajan samar da asibiti dake garin kaduna, wanda a
lokacin kyauta ake duba marasa lafiya, kuma har gobe wannan asibitin yana rayuwa, duk da
al'amuran rayuwa sun sauya, yanzu ana ɗan karɓar ƴan kuɗaɗen da basu taka kara sun karya
ba. A shugancin Laila dogon yaro ne wannan ci gaba ya samu, danta kasance jarumar mace,
mai kishin ganin farin cikin matan Arewa, da ci gabansu.Asibitin Laila dogonyaro ake kiran
asibitin. Bayan haka, sai Hajiya Laila dogon yaro ta tara abokan shawararta akayi meeting, a
wannan zama ne aka samar da tunanin faɗaɗa wannan ƙungiya zuwa jihohin Arewa,tare da
buɗe ofishoshi, da naɗa shuwagabanni bayan hakan ya samu kuma, aka sake yin zama dan
ganin ƙungiyar ta yaɗu har zuwa ƙananun hukumomi, tare da fidda shuwagabanni, daga
ƙananun hukumomi, sai suma aka basu aikin yaɗa ƙungiyar Jam'iyyan matan Arewa, zuwa
ƙauyukan dake kewaye da ƙananun hukumomin
Taƙaitaccen tarihin Hajiya Laila dogon yaro.
An haife ta ne a birnin Kano a 1944 aka yi mata aure tana da shekaru 13. Hajiya Laila dogon
yaro tana gaba wajan fafutukar kare hakkin mata, musamman ganin an ilmantar da su. Ta
shugabanci majalisar ƙasa ta ƙungiyoyin mata a najeriya wato national conucil of women's
societies ( NCWS) daga 1995. Ta rasu tana da shekara 66 a shekarar 2011. Ina sake jaddada
ta'aziyyata ga iyalan wannan baiwar Allah, baya goya marayu. A yanzu kuma ( Hajiya Rabi Saulawa ke riƙe da muƙamin presedent a cikin jam'iyyar matan
Arewa. Kuma ita kanta a tsaye take, dan macace jajirtacciya, tana iya ƙoƙarinta dan ganin farin
ciki, da walwalar mata)
Gamu a wannan ƙauye na unguwar alƙali munzo dan mu tallafi mata, kuma a buɗe jam'iyyar
matan Arewa, ƙarƙashin gwamitin da muke son mu buɗe. Amman zanba uwar gidan mai garin
unguwar alƙali dama ta fitar mana da nagartacciyar mace da take ganin zata jagoranci wannan
tafiyar, amman wacce ta zama ta iya karatu da rubutu, sai kuma mataimaka biyu da zasu
taimaketa.
Sunana Hajiya Turai shugabar Jam'iyyar matan Arewa ta ƙaramar hukumar Bakori, tare dani
akwai Hajiya Tabawa shugabar jam'iyar matan Arewa ta ƙaramar hukumar Faskari.
Waje yayi tsit, ni dai sai kallon matannan nake, ina jin inama zan iya zama ɗaya daga cikinsu,
jibesu tsab_tsab dasu, kuma duk mata ne cikakku da suka san ƴancin kansu. Uwar gidan mai
gari ta miƙe tace.
"Ina godiya da wannan karramawar da akayi mun. Sannan ina godiya sosai, kuma ina farin
cikin shigowar wannan jam'iyyar matan Arewa cikin wannan gari namu, wani babban alkhairi ne
ya shigo mana, Allah ya jiƙan Laila dogon yaro. Allah ya saka ma da (MARYAM ABACHA DA
ALKHAIRI) ni a tunanina da nazari na, ina ganin babu wacce ta dace da wannan matsayin
kamar Laila Uwar gidan sarkin Mafarauta, dan ta kasance jajirtacciya, mai haƙuri da rashin raki.
A garinnan babu iriyar tsangwamar da bata shiga ba, amma sau ɗaya bata taɓa zuwa gaban
mai gari ta durƙusa da sunan ƙorafi ba, haka muma da muke sauraron ƙararrakin talakawa,
bamu taɓa cin karo da Laila ta kawo ƙarar kowa ba. Kuma matar Malam ta tabbatar mun da
haƙuri da juriyar Laila. Sai dai bani da masaniya akan iya rubutu, da karatunta." Gabana ne ya
yanke ya faɗi, wani tsoro yayi tsalle ya dira a ƙirjina, nan take sai nake jin kamar numfashina
yana kakkatsewa tsabar farin cikine, ko tsabar kaɗuwa, na kasa banbancewa. Wannan baiwar
Allahn ta bani damar miƙewa dan jama'a su ganni da kyau. Jikina har wani kakkarwa yake yi,
idanu muka haɗa da Shehu wanda ya ɗaga hannu halamar yana da magana.
Mrs Bukhari ce
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: GAWURTATTU UKU
MRS BUKHARI
LAMBA TA ASHIRIN DA HUƊU.
Laila:
Mai gari yaba Shehu damar yin magana.
"Mai gari, wannan matsayi da ake tunanin ba Laila ta kaishi ina? Sannan ba wannan ba, Laila
bata iya karatu da rubutu ba sam. Ina ganin ga Asiya a bata, dama ta saba karɓar kuke." Matar
mai gari tace.
"Shehu kaba baƙi damar gudanar da abinda ya kawo su, dan sauri suke yi, sannan Laila ai
tana da bakin magana ko, kana tunanin ja da hukuncinane?" Gum Shehu yayi, Asiya sai mugun
kallo take danƙara mun. A sannaye nace.
Na iya rubutu da karatu ranki shi daɗe" Ɗaya daga cikin matan jam'iyyar matan Arewa ta
miƙo mun form tace in cike ta gani." Hannuna yana kakkarwa na cike form tsab babu kuskure,
na miƙa mata. Kallona tayi ta girgiza kai da taga shekaruna. Juyowa tayi tace.
"Daga yau Laila ta zama shugabar matan Jam'iyyar matan Arewa na cikin wannan ƙauyen.
Dukkannin wani tallafi da zai shigo ƙauyannan zai shigone ta hannunta. Zamu naɗa wacce zata
taimaka mata, dama mataimakiyar mataimakiyarta. Dukkan wani abun inya taso, kona taro kona
tallafi, zan turo aimun kiran Laila. Zan ajjiye foms a wajanta, duk mai sha'awar shiga wannan
jam'iyyar matan Arewan, sai ya amshi fom a wajan Laila ya cike, akan kuɗi naira biyar. Sannan
tunda mun buɗe jam'iyyar matan Arewa a cikin ƙauyannan, ku kuma ku dage ku burunƙasa
wannan jam'iyyar, sannan ku ƙirƙiri abubbuwa da dama dan taimakon kanku da kanku. Ga
kayan abinci nan, zamu raba ga mata. Bayan uwar gidan mai gari ta kuma zaɓa mana waɗanda
zasu taimaki Laila." Ni dai ina tsaye sai hawayen murna nake shatatarwa ba ƙaƙƙautawa. Da
Asiya da Shehu kuwa, sun cika fashewa kawai suke jira. Sha'awa aka ciro a matsayin
mataimakiyata, sai Iklima amaryar mai gari a matsayin mataimakiyarta. Daga nan suka shiga yi
mana rabo. Harda keken ɗinki guda biyu sababbi, da keken saƙa shima biyu. Suka wakiltani
akan, in kula a koyama mata sana'a da kekunannan, kuma in sha Allah zasu kawo mana tallafin
kekuna masu yawa. Suka bani foms, tare da atampar jam'iyya mai tambarin Arewa a jiki,
atampar bulu, Hajiya Turai shigabar jam'iyyar matan Arewa ta Bakori ta rubuta mun adireshin
gidanta, sannan ta bani izinin duk wani abun daya taso, zan iya nemanta kai tsaye" A haka taro
ya watse, masu taya ni murna nayi, ƴan baƙin ciki ma sunfi yawa. Sha'awace ta taimaka mun,
muka shigar da kekunan gidan mai gari, da sauran mata ƴan uwana. Dan nace a gidan zamu
gabatar da koya ma mata ɗinkin. Jiki a saɓule na shiga gidan. Sha'awa kuma ta tsaya a ɗakin
Zaure inda Ɗahiru yake ciki. A tsakar gida na samu Shehu ya kai mari ya kai gwauro. Ina
shigowa ya tare ni.
"Ashe munafukace ke Laila, yaushe kika iya rubutu da karatu, ni mijinki ban sani ba?" Wani
ƙudidune ya cakeni a ƙahon zuchiyata. Yaci albarkacin Karima data fito da ƙunshin kayanta a
zane. Kallona ya koma wajanta, sai naga yaran su Iyami ma duk sun fito da ƙunshin kayansu,
duk yanda akayi aikatau za'a tafi dasu birni. Yaran Asiya ma suna can, wata biyu kenan har sun
soma yo ma Asiya aike, waccen cin kasuwar data wuce ma harta soma yi musu tarin kayan
aure. Mazajen ƙauye da damansu zuchiyarsu ta mace mus, sam basa iya rungumar ɗawainiyar
ƴaƴansu, maza a turasu almajirci mata a turasu aikatau, su zasu yi ma kansu kayan ɗaki.
Karima tana kuka Shehu ya tusa ƙeyarta, ni kuwa tsabaragen baƙin ciki da takaici na kasa cewa
komai, yana fita ya dawo yace ƙanwar Karima ma ta fito ai shingin kaɗan ta isa aure. Ni dai
waje na samu na zauna, ina kukan zuchi. Ina zaune sai ga Tani da Zainabu sun fito. Sunai ma
matan gida sallama, zasu birni daga can jirginsu zai ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki. Nan gidan ya
kacame da murna, Amaryar Ɗahiru kuwa tana ɗaki ta kasa fitowa, sabida ba da ita za'aje ba, ya
bata haƙuri kam sai wata shekarar. Ɗahiru yana shigowa suka fita, su Baba Mai riga da matar
Malam sai binsu da adda'a akeyi, kamar basu san bokanci Ɗahiru yake yi ba. Shehu ne ya
shigo gidan da sauri.
"Laila ba zaki yi wannan shugabancin ba, na faɗa miki kenan. Ji mata marasa kunya masu
yaƙi da maza, baki isa ki haɗa tafiyarki dasu ba.
Shewar dila kake yi Shehu, in kaga banyi wannan tafiyar ba, bana numfashine a doron
ƙasa. Au cigaban nawa ne baka so, sai ci gaban Asiya ƴar gwal ɗinka ko? To kasani nima
uwace tai silar zuwana duniya" Kasaƙe Shehu yayi yana kallona, Asiya kuwa ta taso tana huci
tace. "Ki fita idanuna in rufe, dan kinsan nafi ƙarfinki tunda har na sace zuchiyar Shehu a
hannunki, kuma na shigo gidan na maisheki bora." Wani irin zabura da nayi saida yasa Asiya
taja baya, mari na kawo mata, ta hankaɗo Shehu gaba, ban sani ba na zabga mishi mari. Nan
su Baba mai riga suka shiga sallallami, kafin kace me, ita da matar malam, da Iyami, da Laure
suka rufu a kaina da duka. Da ƙyar Sha'awa da sauran mata gida suka ƙwaceni, Asiya kuma sai
riƙeta Shehu yake yi, wai saita rama mishi marin da nayi mishi. Sha'awace ta jani zuwa cikin
ɗakina, ganin yaran du babu yasa na fashe da sabon kuka.
"Haba Laila sai kace wata ƙaramar yarinya. Kiyi haƙuri ai in sha Allah wahalarki ta kusan
zuwa ƙarshe, wannan ba komai bane face baƙin ciki, ki tura musu aniyarsu. Yara ki bisu da
adda'a a duk inda suke adda'arki zata isa gareki, nima da nawa yara matan aka tafi birnin, to ya
zamu yi, a dake mu a hana mu kuka. Ɗahiru kuma mun tattauna dashi, Laila al'adafa yaronnan
yake yi, wata uku da farawarshi yace mun. Yanzu haka na baroshi yana murƙususun ciwon
mara. Ni a shawarce ki miƙe ku tafi asibitin Bakori a duba shi, shi zaifi. Amman ki jiƙa manda ki
bani in kai mishi." Hannu nasa a dai dai saitin ƙirjina na dafe. Dan ji nake kamar zai tarwatse,
hawaye kuwa sai wanke mun fuskata yake yi. Namiji da ƙunzugu? Tsarki Allah ya tabbata ga
Allah, ɗan Adam ba a bakin komai yake ba. Jikina sai rawa yake yi, manda na jiƙa na bata ta
tafi kai mishi. Tana fita Shehu ya shigo wuf.