Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
matsayin amsa ba. Buhun na ƙulle na
dubi A'i da tai kasaƙe tana kallon ikon Allah nace.
Taimaka ki ɗaura mun a ka A'i" Baki ta buɗe.
"Kaddai a darennan kike shirin tafiya. Baba Hauwa suna da labarin ɗanyan hukuncin da
Yawale ya yanke kuwa? Wallahi karki tafi ki zauna, Kumatu ce ta haɗa komai ni dai nasan baki
ma Yawale komai ba, sai haƙurin zama dashi ma da kike yi, kar ki barma yaranki abun faɗe
Musina. Kallon dana watsa mata ne yasa tayi gum da bakinta, ta taimaka mun na aza buhun a
kaina. Fita nayi daga gidan. Na kaima Uwa mai siyan kaya,ta siya amma tace mun gobe da
safe inzo in amshi kuɗin. Godiya nayi mata na koma gida. Ƙunxugu na sake, ina zaune ina jan
carbi hawaye sai wanke mun fuskata yake yi, roƙona da burina shine, Allah yasa in rayu tare da
yarana har zuwa matakin girma, da mallakar hankalinsu. Ba dan ko da wasa ina sha'awar zama
da Yawale ba sam, sai ɗan ɗorewar farin ciki, gami da walwalar ƴaƴana dana kasance musu
bango majinginarsu"
A'i:
"Jamilu Yawale fa ya saki Musina. Ita kuma ta hau dokin zuchiya harta soma kwashe kaya ta
tafi gidama yanzu maganar da nake yi maka, abun ya bani mamaki gaskiya" Dena cin tuwo
Jamilu yayi, nomar daya yanko ya ajjiye.
"Ya saketa fa kikace? Lallai Yawale bashi da hankali, akan waccen figaggiyar Kumatun ya
saki uwar Ƴaƴanshi daga yin sabon aure? Da safe zan je in yima Baba magana, su Baba
Hauwa ma banyi tunanin in sun sani ba. Duk da dai naga sunfi ƙaunar yarinyar da Yawale ya
auro, kuma Baba Hauwa ba zata ga laifinta ba Ɗiyar aminiyartace. Amma bari inje in samu
Mudi mu tattauna" yana kaiwa ƙarshen maganarshi, ya wanke hannunshi a cikin kwanon da aka
zubo mishi ruwan wanke hannun, ya fice. A'i sai kiranshi take, ita bata so akaji mutuwar sarki a
bakinta ba. Gulma kawai ta kawo ma mijinta, kuma bata zaci zai ɗau abun da mahimmanci
haka ba."
Jamilu:
Har yana tuntuɓe tsabar sauri. Ƙofar ɗakin Mudi yaje ya kwankwasa. Mudi ya fito daga shi sai
godon wanda, yana lashe hannunshi da yayi jaga_jaga da miya."
"Yaya Jamilu lafiya kuwa, naga yanzu muka rabu?"
"Hmm Mudi kai dai bari wani labari A'i ta tare ni dashi. Wai Yawale ya saki Musina, harma
ta tafi gidansu a darennan, kuma da kaya. Banyi tunanin yarinyarnan laifi tayi mishi ba. Tunda
wannan laluri ya sameta, Baba Hauwa da Yawale suka ɗauki karen tsana suka ɗaurama
Musina. Sannan munafukar amaryarshi ita take kuma ingizashi, tunda tasan tana da fada a
wajan Baba. Baba Huwaila dai ita baka gane a ina take kasan ita in dai abu baiyi mata ba tana
faɗe. Baba zamu je mu samu a turakarshi da safe, sai a kirawo Yawalen ya sanar damu dalilin
da yasa ya saketa, mu kuma zamu je mu dawo da'ita. Kaje ka kwanta da safe ma tattauna."
Mudi yace.
"To Yaya sai da safe. Amma abun baiyi daɗi ba gaskiya"
Musina:
A zaune bacci yai awon gaba dani. Sai cikin dare dana farka na gyara kwanciyata, bayan na ba
Ƙasimu ruwa da nono.
Washe gari da sassafe na gama komai, na ƙulle ƴan kayana a ɗan kwali, na fito na kulle ɗakina.
Kai tsaye na nufi ɓangaren su Baba Hauwa. Da Idi na haɗa idanu, ya sakar mun murmushi.
Yana zaune yana cin tuwo.
"Ina kwana Baba?" Baba Hauwa tace.
"Lafiya, ina kuma zaki da sassafennan ina da zuwa gida?" Kai na kuma saukewa ƙasa. Shin
wai me naima rayuwa ne ta juya mun baya? Yawale ya raboni da dangina, ya kawoni cikin nashi
dangin. Ya juya mun baya, iyayenshi da ƴan uwanshi kab bana jin daɗin zama dasu, me nayi
ma Yawale da rayuwa ne?" "Ba magana nake yi miki ba, kin wani zo kin zauna mun ke da kike yoyyon fitsari,
sale_sakin ki mun fitsari a filin ɗaki ko me? Yau ga hauka da naɗe_naɗe wai mutuwa taga
ladani. Idi na kalla shima ni yake kallo. Ƙwalla ce take shirin zubo mun nayi saurin mayar da'ita.
Gida zani sai nan da sati biyu zan dawo. Yau zanga likita, kuma daga yau har zuwa sati
biyun kullum zamu je" Baki ta taɓe tace.
"Da zan baki shawara da kinyi zamanki a gida, in kika warke fes saiki dawo ɗakinki, tunda
yanzun ma ba rabon kwana akeyi dake ba. Jibi fa yanda kike zarni Musina" Kaina na ƙasa harta
gama faɗan abunda yake ranta tas. Sannan na tashi na fita. Ƙunshin kayana na ɗauka a bakin
ƙofar ɗakin, na fice a gidan. Ajjiyar zuchiya na sauke da naji iskar waje ta doki gangar jikina.
Tsabar takura ji nake yi kamar iskar waje data gidan Yawale akwai banbanci. Ina tafe ina
tunanin rayuwa, da irin yanda Yawale ya soni kamar zai halaka kanshi, a lokacin har tausayin
irin son da Yawale yake yi mun nake yi, dan gani nake yi in mutuwa ta ɗaukeni da ƙuruciyata,
Yawale zai iya tagayyara. Hmm ashe shigo_shigo babu zurfi ne kawai, gadar zare ya saƙamun
na faɗa ya barni da wayyo Allah.
Jamilu:
Sallama Jamilu yayi a bakin turakar mahaifinsu shi da Mudi, suna jiran a basu izinin shiga.
"Jamilu shigo mana, ina kishingiɗe jikinnne ba daɗi. Shiga suka yi, suka tadda mahaifin nasu
a kwance, Baba Huwaila na gefenshi. Baba Hauwa ce ta shigo da sallama. Amsa mata su ka yi,
kana ta nemi waje ta zauna. Saida aka gama gaggaisawa, Jamilu yaima mahaifinsu malam Idi
bayanin abunda yaji daga bakin A'i. Zama malam Idi yayi, saida ya jingina kafin yace. "Shi Yawalen ne ya saki Musinar, to akan me, wani abunne ya haɗasu? Jamilu yacr.
"Baba bamu sani ba, amma a daren jiya tabar gidan ta kasa bari gari ya waye." Baba
Hauwa tace.
"Wai wacce Musina ake magana, matar Yawale? Yanzunnan fa muka rabu da'ita akan zata
je gida sai nan da sati biyu zata dawo. Sakinta ashe yayi?" Jamilu yace.
"Ha'a nifa tun daren jiya A'i ta faɗa mun ita da kanta ta taya Musina ɗaukar kaya." Malam
idi Yace.
"Karawo shi Yawalen shi kaɗaine zai faɗa mana gaskiya, amma wallahi in kuwa sakin
yarinyar nan yayi ni dashi ne a gidanan"
Yawale:
Gama cin abincinshi kenan, Mudi yayi sallama cewar Baba na nemanshi. Tsaki yaja.
"Bazai wuce akan Musina bane Baba yasa ayi kirana. Amma wallahi in dai ƙarata takai
wajan Baba zata gane kuskurenta. Rigarshi ya saka.
"Kumatu daga nan zan wuce kasuwa, ya kamata ace na koma kasuwa, ai an gama cin
amarcin. Cikin yamutse fuska Kumata tace.
"In zaka dawo ka tawo mun da ɗata bakina yawu sai gudana kawai yake yi. A dawo lafiya
Allah ya tsare hanya." Sallama yayi mata sannan ya nufi ɗakin mahaifinshi, anan ya taradda da
iyayen nashi da Yayunshi. Malam Idi yace.
"Shin menene gaskiyar jita_jitar da aketa yaɗawa kan cewar ka saki Musina. Wasu ma
suka ce tun jiya ta ɗebi kaya a buhu ta tafi. Babarka kuma tace yau da safe Musina tazo tayi
mata sallama akam zata je gida sai nan da mako biyu zata dawo." Yawale ji yayi inama da
gaske ne ya rabu da Musina da yafi kowa jin daɗi. Dan sai akan Kumatu yasan yayi aure, dan
macace wacce tasan makamar kula da mai gida a gado, kuma tafi Musina ruwan ni'ima, shi
yasa yake jin sonta ya zama na daban a zuchiyarshi. Daurewa yayi yace.
"Ni ban sake ta ba Baba. Jiya da daddare tazo ta sameni a ɗakin Kumatu, take faɗa mun
likita yace daga yau zata dinga zuwa asibiti kullum harna tsawon mako biyu, shine take neman
alfarma in barta ta zauna a gida, har saita gama ganin likita. Kuma na bata dama. Banda labarin
kwashe kaya da Musina tayi gaskiya. Ƙwafa Malam Idi yayi tace. "Zaman lafiyanka dani shine da wasa kar inji ka saki Musina. Dan na lura da
take_takenku kai da mahaifiyarka, tunda ta aura ma ƴar aminiyarta.'
"Ha'a Malam ai ba haka akeyi ba. Mai ɗaki shi yasan inda yake zubar mishi da ruwa. Ya
zaka yanke ɗanyen hukunci haka?"
"Hauwa kul na kuma jin bakin ki, ko bayan raina ban yarje mishi ya saki uwargidanshi ba.
Kai kuma ya kamata ka soma zuwa aiki. Ni yanzu bazan iya aikin jima ba sam, kune zaku ci
gaba da zuwa. "To" kawai Yawale yace ya fice. Ƙofar ɗakin Musina yaje, ya bankaɗe ƙofar ɗakin
ya leƙa. Gadaje biyu sune abunda suka rage sai kwaba da babu komai cikinta. Tabbas Musina
tafiya tayi, a ranshi yaji yana fatan karta dawo, inama iyayenta zasu aiko suce a basu
takaddarta da zuchiyarshi tafi haka fari. A wangale ya fice ya bar ƙofar. Kumatu data fito tsakar
gida taci karo da labari mai daɗi cewar an saki Musina. Murna ta shiga yi, a tunaninta taci
nasarar samun Yawale ita kaɗai.
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: *_GAWURTATTU UKU2023_*
*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don
koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in
akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan
idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya
don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin
07068606171
08104335144
08179523215
*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._
*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
MRS BUKHARIMRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU
Lamba ta goma sha biyar
Unguwar Alƙali:
GIDAN MAI GARI:
Fitowa yayi a ɗakinshi zuwa tsakar gidanshi.
"Uwani, Uwani!! Uwani uwar gidan mai gari ce. Da sauri Uwani ta fito daga ɗaki.
"Kisa Zainabu ta shirya ta sameni a shagon waje, ba'a fada ba, Baban yaronnan nata Zulƙifulu
ya dawo. Jiya da daddare, magatakarda yake sanar dani, yaji labarin shigowarshi a wajan ƴan
doka. Har nasa fadawa suje gidan ayi kiranshi, da ƴan uwanshi. Shima malam Ayuba nasa ayi
kiranshi da ɗiyarshi Binta, da duk dai wanda wannan rikicin ya shafa. Zamu tattauna a shagon
waje, dan tattaunawar tana buƙatar sirri." Tsaki Uwani tayi tace.
"Amma Allah yayi wadaran yaronnan Malam dan ya cutar damu, ya cutar da yarinyar,
shekara sama da goma ta rasa manemin aure. Ƴan uwana da danginka duk a ciki an rasa mai
aurenta. Cutarwar tayi yawa. Ni malam inason kaimun izini in rakota dan a tattauna komai a
gabana." Mai gari yace. "Uwani kenan. Ni kaina a kullum inna kalli Zainabu yanda ta tsofe a gida, wallahi abun yana
yi mun ciwo. Amma ki sani ba Baban Zulƙifulu kaɗai bane mai laifi, yarinyar nan ita da kanta ta
bada kai bori ya hau fa. Ku tawo fadar dai." Yana kaiwa nan ya fice."
Laila:
Matar malam ce ta leƙo ɗakina, suka gaisa dasu Daddo, taji lafiyata dana jaririna. Sannan tace.
"Laila tawo, mu tafi wanka, an juye ruwan karya huce." Miƙewa nayi, ina jan ƙafata harna fice.
Daddo:
"Laraba kinga yanda Laila ta nakasa kuwa, ƙafarta fa ɗaya janta take yi, bata iya ɗagawa. Bari
dai ta fito muji" shigowar Iyami da kaskon wuta ne ya katse musu hirar, Laure ce ta shigo da
baho na wankan jariri. Bayan sun gaggaisa. Iyami tayi ma yaro wanka ta banka tazargade a
cikin wuta taima Jaririn hayaƙi. Laure ta gyare ɗakin, suka fitar da kayan da Laila, da jaririnta
suka tuɓe. A haka Laila ta shigo ta samesu jigum."
Laila:
ina fitowa na sake kaya, na shafe jikina da man kaɗanya, sannan na zauna. Baba mai Riga da
matar Malam ne suka shigo.
"Ga tuwo Laila, kici ki ƙoshi. Gaishe da Baba mai Riga nayi. Sannan na koma na soma cin
tuwon, jaririna yana hannun Daddo."
"Baƙi kukayi ne Mai riga, ni naji jiya anata magana a tsakar gida" cewar Daddo. Baba mai
riga tace."
"Manyan baƙi ma kuwa, ƙanin su Malam ne Ɗahiru ya dawo, takwaran wannan" Ta nuna
jaririna"
"Shekara fin goma da tafiyarshi birni, sai jiya Allah yasa suka dawo" Shehu ya shigo
kuwa?" Goggo Laraba tace.
"Bai shigo ba, na ɗauka tun sassafe zai shigo yaga lafiyarta." Kafin tace wani abun sai
muka jiyo sallamar malam. Yana cewa.
"Matar malam, Mai riga kuzo mai gari ya aiko fa" Da sauri suka fita, buɗe labulen da
sukayi, na hango Shehu a tsaye a kusa da Malam. Hawayen daya tawo mun ne ya gangaro
bansan sanda ya zubo ba."
Malam:
"Mai gari ya aiko yana son ganinmu, Baban Yara nace yayi gaba shi da Lauwali. To Ɗahiru
kuma tun safe Shehu yake nemanshi, babu shi babu dalilinshi, bamu ganshi ba ko'a masallaci.
Amman zanje can fadar, Shehu zai kuma zagayawa ya duboshi. Na faɗa muku ne dan ku sani.
Yaro yana son ya jefa mu a matsala, ai yasan abubbuwan daya tabka babbane" Nan Malam ya
wuce ya barsu. Shehu kuma ya shiga ɗakin Laila."
Laila:
Hawaye nake sharewa na jiyo sallamar Shehu. Durƙusawa yayi ya gaishe da su Daddo babu
ɗigon far'a a fuskarshi. A daƙile ya amsa gaisuwata. Goggo Laraba ta miƙo mai Ɗahiru. Shehu
ya noƙe tare da cewa.
"Sauri nake yi Goggo Laraba, dama gaisheku nazo yi, zuwa anjima zanzo." Yana ficewa na
raushe da kuka. Shehu yana nufin bazai karɓi kyautar da Ubangiji ya bamu ba kenan, butulci
yake son yayi?" Goggo Laraba ce ta matso kusa dani.
"Laila ki dena kuka. Shawarar da zamu baki, wannan yaron naki ne, ki rungumi abunki
kawai. Amma na lura kina cikin