Iyayen Giji Book Compelet Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   6 / 21

15K to 18K   out of 61.8K words

"Amma iyayenki sunyi ƙoƙari sosai Musina. To ga form ɗinki sai ki cike, nan da sati
biyu za'a soma horas daku, shima horarswar zata kai sati biyu ana yinta. Sai kuma a yayeku,a
ɗan baku jari da zaku dinga jujjuyawa." Godiya Inna Lami tayi ma likitannan sosai. Mu kai mata
sallama muka fito. Har saida Inna Lami taga bodin mu ta tashi, sannan ta nufi gida. Zuchiyata cike dake fal da fargaba. Dan nasan ko ina shure shuren mutuwa dafara na fitowa a
bakina Yawale bazai amince da wannan ƙungiya dana karɓi form ba. Ko ya amince nayi imani
Baba Hauwa bazata taɓa amincewa ba. A zahirin gaskiya inason koyan sana'ar haɗa mandula,
dan mandula in zamu saye, sai dai muyi sallahu a tawo mana dashi daga Azare, amma mu
bamu dashi a ƙauyenmu. Zanso im koya ko dan in dogara da kaina, in kula da yarana. Dan
nasan Yawale bazai kula dasu ba. Gashi ina da buri akan yarana mata in Allah ya bani, ina da
burin ganin sunyi ilimin boko mai zurfi. Dan inason karatun boko sosai. Inna tsaya akan sana'a
sai in kula da karatunsu ai. Da waɗannan saƙe saƙen muka iso madakata. Koda na shiga gidan
babu wanda ma ya amsa sallamata, sai tottoshe hanci suke faman yi. Kai kawai na gyaɗa nayi
shigewata ɗaki. A jiƙe na dawo sharab, kayan jikina na cire, na ɗaura zani a ƙirjina na fita tsakar
gidan. Kayan Fitsarin na wanke, sannan na shika sakaki na ɗauraye jikina, na fito tsakar gida
na ɗaura alwala na koma cikin ɗakina.
Rayuwa haka tai ta garawa, har gida ya cika daf da jama'ar biki. Ranar likinin aka soma bikin
bisa ga al'adar ƙauyen Saleri. Ranar litinin: In dare yayi Babannin Amarya zasu tafi gidan uwar
dakinta, a kamo ta dakyar qawaye sun ɓoyeta, a fisgota, a sa mata lalle wanda aka kwaɓa da
turare, sai a shafa mata suyi ta kuka ita da qawayenta." Ranar talata: za a yini a nata qunshi amarya da qawayanta, Haka laraba da yamma, babbar
qawar Amarya, da mabi da babbar ƙawar Amarya, za su sai lalle a taru a dekashi adama da
ruwa , su fito qofar gida kowacce ta daura tsohon zani, ba riga, mamunansu a bayyane, ayita
zubawa juna duk su jiqe, a hakan za'a tafi gun angwaye ayi ciniki su biya, a dawo gidan da
amarya take wato gidan uwar dakina . Da yawan samarin ƙauyan Saleri, a rana irinta yau, suke
zaɓen matan aure, sabida mamansu a buɗe suke zuwa, mai so saiya zaɓi wacce mamanta yayi
dai_dai da ra'ayinshi. Bayan sun koma gidan uwar ɗakin Amarya, sai su yi wanka. To in dare
yayi kuma, gidansu ango zasu zo su kawo kayan sakun lalle, zasu kawo dakakken lalle, turmin
zani biyu, sabulu, man shafa, turare, takalmi, gazal, jambaki, duk kowanne guda bibbiyu, da
bokiti, baho, moda, kofi, se goro da minti za'a bara goro a faranti kowa ya dauki minti goro ɗaya,
minti biyu "
Ranar laraba: Asuba nayi baza ayi salla ba za'a zagaye garin baki ɗaya a nata waqoqin amarya
iri _iri sai a wuce gidan wali nanma a yita waqa shima seya biya kudi tukunna ayi sallah a karya
kumallo. Yamma nayi se kokuwar tsifa ɗaya bayan ɗaya za'a riqa yi amarya tana dokawa,
ƙawayen amarya sai su taru a kadata ɗaya ta zauna tana tsefe mata kai, saura kuma suna
waqa har agama. kowacce za ta duqa amarya ta zage tayi mata dundu abaya sau biyu, sai su
tafi gun angwaye a biya su. Daga nan sai su wuce gidan amarya. Rufar qofa kafin akawo
amarya, za su rufe ɗaki nanma sai angwaye sun biya sannan su bude a saka amarya.
Ingari yawaye za'a sami budurwar da tsawanta yayi dede dana amarya se tasa kayan amarya a

zagaye gidan dangin miji, ana waqa wannan su bada taro wancan su bada sisi da haka har su
gama a dawo. In dare yayi ko wacce zata dafo abincinta, sunan abin alibidi a yi taci a dakin
amarya, samari su cika kowa da budurwarsa yaci abinci ya bata kudi juma'a. kafin hakan da
safe zuwa dare dangi za su yita kawo gudummowarsu atara kaya a fitar da tsaraba kaya Lodi_
Lodi akai gidan su ango"
Asabar: Yinin gidansu ango, za'a yanka tunkiya abawa "yan matan amarya wuya dashi za suyi
abinci suci idan anzo cin abincin, sai asa zobe aqasan abincin aboye ana cikin cin abinci wacce
ta zaro zobe ita za'ayita tsokana"
Lahadi: kashe wuta, za,a kawo ma amarya sauran kayanta a wanke tukunyar da'aka,aro, baqi
kowa ya tafi biki ya qare. Haka al'adar bikin aure a Saleri yake, har gobe, amma bamu san
dame jibi zata zo ba.
Haka ne ya gudana a bikin Yawale. Ni kuma inata faman jinyar kaina, na zama abun ƙyama
babu mai raɓata, aka yi ta mun waƙe_waƙe a tsakar gida. Yawale kuwa bana ma jin ɗuriyarshi
sam tunda ya tare a ɗakin amaryarshi. Sai a bakin matan gida nake jin sunan Amaryar Yawale
wai sunanta Kumatu. Amarci Yawale yake ragargaza shi da Amaryarshi Kumatu, dan ina jiyo
labarin yadda suke gudanar da amarcinsu a bakin matan gida. Ni dai ina ɗaki ina jinyar kaina,
da zuchiyata, dan in nace bana kishi ma, na yaudari duk wanda zai karanta labarina. Ana
washe gari sati biyu da zuwa na asibiti, na fito da zummar zuwa ɗakin amarya dan inyi magana
da Yawale, ganinshi ma ai yafi ƙarfina a yanzu. Gabana sai faɗuwa yake yi, dan bansan yanda
zamu kwashe da Yawale ba. Amma na shirya duk abunda zance mai, dan dai ya barni inje
koyon sana'arnan.
Assalamu alaikum' Assalamu alaikum" daga ciki na jiyo muryar kumatu tana cewa.
"Wata sabuwar alaranmiya muka samu ne a gidan? Koma waye in zai shigo ya shigo.
Yawale yace
"Musina ce, uwar iyayi ake faɗa miki"
Da ba dan ba dan ba da yau anyi badan, dan ji nake kamar in shiga in shaƙo wuyan Yawale
inta jibgar matsiyaci har sai naga ya dena motsawa. Jiki a mace nasa kai na shiga ɗakin.
Yawale yana shingiɗe a ƙasa anyi mishi shinfiɗa irinta sarakai. Yana kan faifan tum_tum,
guiwar hannunshi dafe da tum_tum. Ga gashsshen zabo a gabansu suna ci, harda lemun
lamurje a gabansu, Kumatu sai wani fifita take yi mishi, harda yi mai sannu, kamar wanda jaki
ya ka dashi. Ɗakin nabi da kallo, caɓi lallai duk inda akayi Kumatu Mahaifinta tahirine dan an zuba mata
dukiya a ɗaki. Gado biyu ne a ɗakin, maulidi da bono. Ga kwaba bango guda mai ƙofofin glass,
can saman kwabar ma tangaran aka jera mata, cikin kwabar kuwa harda samira mai kala. Ga
kwalla hawa kusan goma, ga fanteku suma hawa hawa, haka kumbo ma hawa hawa. Bango
guda kuma akai mata jeren tasoshi sama da seti sittin. Ga tum_tum guda uku tare da faifain shi.
Ga ƙore a rataye a ragaya fin goma, ga shinfiɗa mai taushi a ɗaki, sai ƙamshin turaren binta
sudan ke tashi. Ita kuma Kumatu sai ƙamshin turaren jan miski take yi. Ajjiyar zuchiya na sauke,
inajin nunfashina na bazaranar ɗaukewa.
"Musina ya kamata ki faɗi abunda ya kawo ki ko? Sabida kar kiyi ma Kumatu fitsari a ɗaki."
Cewar Yawale kenan. Buɗar bakin Kumatu tace.
"Ga fitsarin manya da mugun zarni" Dauriya na aro na yafa ma kaina. Na cije nace.
"Dama gobe ne ranar komawa asibiti. Kuma ita likitan tace daga gobe kullum zanje asibiti

harna tsawon sati biyu..."
"Bani da ko ficika Musina, ba kina da kayan jere a ɗakikin ba? Ki kaɗar dashi ki samu na
magani, amma ni in ba wajan maganin Hausa za'ajeba. Ficikata Kwarankwatsa ba zatai ciwon
kai ba." Murmushin takaici nayi na dubeshi nace.
"Umarnin zama a gida nake son ka bani kawai, domun bani da ikon fita ƙofar gida ba
tare da izininka ba. Ficikarka bana buƙata."
"Umma ta gai da Asha, Allah raka taki gona, can dasu gada. Dama jarabarki ce tasa
kika dawo gidan ma. Aini cewa nayi sai kin warke kya dawo." Da dai na riga naji abinda nake
son ji. Ban jira ya haɗiye yawu ba nayi ficewata a ɗakin, zuchiyata sai suya take yi.

Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman
na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas
mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata
saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin

07068606171
08104335144
08179523215



*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_

_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_





MRS BUKHARI
MATA IYAYEN GIJI

BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)

( GAWURTATTU UKU)

INA MIƘA SAƘON GODIYATA GA HAƊAKAR MARUBUTAN NAJERIYA BISA SHAIDAR
KARRAMAWA DA SUKA BANI, AKAN LITTAFINA MAI SUNA ( UNGULU DA KAN ZABO)
NAGODE MATUƘA ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI. INA MIƘA GODIYATA GA
SHUWAGABANNIN HAƊAKAR MARUBUTA, DA ALƘALAN DA SU KAI ALƘALANCI.


*_GAWURTATTU UKU2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*

SAMFOTI


LAMBA TA TAKWAS

BAKORI:
Da isar Shehu Bakori bai zarce ko inaba, sai ƴar kasuwa wajan mahaifin Laila malam Zangina.
Inda anan yake kasuwancin sai da musullar ƙarfe, da musullar da ake cirewa a jikin bushiya da
matajin kai na katako, da wuƙaƙe masu ƙota. Wannan itace sana'ar mahaifin Laila, taburin dake
kusa da nashi kuma teburin wan Laila ne Jibirila. Shi kuma yana siyar da, kayan aikin gona.
Garma, ƙota, cebur, da sauransu. Haka Shehu ya ratso kasuwar nan yazo wajan mahaifin Laila
afujajan.
"Shehu kaine tafe afujajan haka? kar dai almurar yarinyar nan ta kuma tawowa ne? Ka haifi
yarone baka haifi halinsa ba, amma zanje gidan in bata kashi yanzu." Shehu da yake duk a
burkice, dan ana tafe a hanya yana tunano mata mazan da Laila ta haifa mishi, wannan wacce
iriyar ƙaddarace haka? Yace. "Ba kuma fitowa tayi ba. Ta samu kaine"
"A masha Allah, tana dai lafiya ita da abunda aka samu ko?"
"A'a gaskiya, ita da jaririn duk ba lafiya, Laila bata san wanda yake ma kanta ba, jini ne ya
ɓalle mata wallahi, saida aka jiƙa mata manda tasha. Jaririn kuma mata maza ta haifa " wani
zumm mahaifin Laila yaji a jikinshi, yayi shiru yana nazari irin nasu na manya, ya tausaya ma
ɗiyar tashi gaya, kafin daga bisani yace " Hmmmm Allah ya bata lafiya, shi kuma yaro Allah ya raya shi da imani. Muje gidan in
sanar ma da mata, in yaso sai a samu mata su bika ko?"
"Toh" kawai Shehu yace, dan hatta mahaifin Laila Shehu haushinshi yake ji.
"Malam tsalha ga kayana kayi mun jira, yanzu zan dawo" malam Tsalha abokin malam
Zangina ne sosai. Zungui_zungui suke tafiya kowanne cikinsu da abinda yake magana akai a
cikin zuchiyarshi, Malam Zangina sai tunani yake yi, gami da taraddadin halin da iyayen Laila
mata zasu shiga, in sunji halin da take ciki, da kuma abunda ta haifa, dan a wannan zamani
mata maza tamkar mayu, ko aljanu aka ɗaukesu, gidan da akwai mata maza ma, ba'a aiken
yara gidan, kuma an camfa cewar iyaye suna shiga halin fatara da shiga iftila'i kala_kala da
zaran sun haifi mata maza. Har suka iso gida, malam Zangina tunani yake yi, hankali, da
nutsuwa, basu da gurbi a jikinshi tsabar kaɗuwa. Tare suka shiga gidan da Shehu. Malam
Zangina shi ya Faɗama su Ta asibi da Daddo halin da Laila take ciki da abinda ta haifa kuma.
Take Ta Asibi ta soma zubarma da ɗiyarta hawaye. Dan tasan mutanenmu na ƙauye zasu
camfa Laila da yaronta, ƙila ma a ɗaura musu karan tsana. Gabaki ɗaya suka tashi hankulansu,
Shehu sai kallonsu yake yi, yana jin wani mugun haushinsu na ɗarsuwa a ranshi Daddo cikin
murya mai cike da karaya tace.
"Malam to yanzu yaya za'ayi maganar tafiyar?"
"Ke da Laraba saiku je, amma ke dubota zaki yi ki dawo, ita Laraba saita zauna da'ita
zuwa kafin su tawo wanka. Shehu ka shiga ka sha ruwa, zanje Fada in tambayi mai gari mijin
ƙanwar tawa izini, sai mu tawo ku wuce." Fitarshi da mintuna talatin, sai gashi shi da Laraba
ƙanwarshi, itama a kiɗimen take sosai. "Daddo fito ku tafi, zan aiki wannan yaron yaje ya sanar da ƙannenshi batun haihuwar,
ranar suna sai su ɗunguma suje." Daddo ta fito da ƙunshin kayanta a ƙunshe a ɗankwali, Ta
Asibiti ta fito da ƙunshin yajin daddawa, da soyayyen man shanu, da yajin gauta, ta miƙama
Laraba.

"Kuje Laraba Allah ya bata lafiya. Laraba tace.
"Amma Yaya itama Daddon ka barmu muyi zaman mu a can, ita saita kula da Laila, ni
kuma inji da aikace_aikace koya kace Yaya, sabida Laila tana buƙatar kulawa kasan haihuwar
fari ce?" Malam Zangina ya gyaɗa kai yace.
"Babu komai Laraba kuje ɗin." Kama hanya suka yi, Shehu na biye dasu a baya sai
wani cin magani yake yi. A haka har suka isa Saleri yana zabga uban fishi da dana sanin auren
Lailan ma baki ɗaya.
"Ahuwanku dai masu gidan" inji Laraba kenan. Matar malam wacce fitowarta kenan
daga ɗakin Laila tace."
"Laraba sannunku da hanya, kun shawo rana, ku shiga ba insa a kawo muku ruwa." Da
sallama su Laraba suka shiga ɗakin. Amman ganin irin halin da Laila ke ciki ya sake ɗaga
hankalinsu sosai. Matar malam ce ta shigo da sallama, Baba mai riga na biye da'ita da kaskon
wuta. A kusa da gadon Laila ta ajjiye kaskon, ta zuba tazargade a cikin kaskon. Jaririn ta ɗakko
ta dinga busa mishi hayaƙin tazardagennan maganin mayo ne wanda ake amfani dashi a
ƙasashen Hausa dan korar maye, kuma ana yima wanda ake zargin Mayu sun shafeshi.

6 / 21