Iyayen Giji Book Compelet Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   10 / 21

27K to 30K   out of 61.8K words

kunto Ƙasimu a bayana. Sakaki na faɗa nayo wanka da ruwan sanyi naji daɗin jikina.
Kaya na sake nayi ƙunzugu na fito.
Inna Lami zan tafi, Ƙasimu zan barshi a gida, bashi da rigima, in yayi kuka a ɗirka mishi
kokko. Murmushi tayi mun da halama taji daɗin dawowa gida da nayi. Tace.
"Amma fitsarin yana raguwa kuwa?"
"Sosai satin farko nasha wuya ko baccin kirki banayi, inda kika san ruwan jikina zai ƙare, ni
kuma na dinga shan ruwa. A sati na biyu saina samu sassauci, in nayi ƙunzugu yana yin awa
biyu bai jiƙe ba." Baki ta washe tace.
"In sha Allahu ba za'ayi miki aiki ba. Ko Hanne mijinta da malam ne sukai ajalinta, saida
komai ya kwaɓe aka kaita asibiti. Maza jeki abunki." Fita nayi ina jin wani sanyi a raina wanda
bansan ko na meye ba. Babu layi sosai yau a asibitin. Waje na samu cikin ƴan uwana masu irin
lalurata, a haka har layi yazo kaina. Likita tayi murna da ganina, kuma na faɗa mata yanayin
jikin nawa, tace.
"Jiki yayi kyau Musina, kuma babu maganar aiki. Zan ƙara miki sati biyu, daga sati biyu sai in
baki sati ɗaya, kafinnan muna fatan fitsarin ya daidaita, ki dinga jin taruwarshi a ƙasan mararki.
Ya batun koyon sana'ar fa?"

Daga nan can zanje Likita mijina ya amince"
"Naji daɗi, ki dage ki saka himma akan abunda zaki koya, ai zai taimaka miki sosai, kuma
zaki kula da kanki da yaranki ma gaba in sha Allah. Godiya nayi mata na fita. Kai tsaye zuwa
Azare firamare. Mata na hango danƙam, kai na girgiza.
Ashe haka masu lalurar yoyyon fitsari muke da yawa? Allah sarki mata, duk wata wahala a
kanmu take ƙarewa, sufa maza ƴan gata ne. Sai dai su je nema, su kawo, su huta da mace,
shikenan aikinsu. Mu tare ake yin nomar hatsin ma damu. Mata mu ɗauki ciki, muyi aikin gida,
mu haihu, muyi reno, muyi tarbiyya, mu kula da mai gidan. Banda sauran ƙananun
aikace'aikace na yau da kullum MATA IYAYEN GIJI ( YA ALLAH KA SANYA HASKE DA FARIN
CIKI A ƘIRJIN KO WACCE UWA). Form na nuna ma mai tsare da ƙofar shiga makarantar,
sannan ya barni na shiga. Na samesu anata ciki_cikin rarrabe ajujuwa. Ni faɗawa nayi ajin
koyon mandula, da sabulun soda, da omon gari. Koda aka gama ware mu, lokacin harya wuce
dole aka tsaida komai kan sai zuwa gobe, taran safe za'a soma. Tare da ja mana kunnen yin
latti.
Washe gari da sassafe na taya su Inna aikace_aikace. Nayi wanka tsab, naba Ƙasimu mama
yasha yayi gyatsa, na miƙama Inna Lami shi. Dan a ɗakinta na sauka. Ina shirin fita kenan Yaya
Harira babbar ƴar inna Lami tazo ita da yaranta daga jama'are. A gurguje muka gaisa na fice.
Naje na samu dab za'a soma koyar da sabulun soda.
"Mata Assalamu alaikum barkan mu da safiya, yaya jikin naku?" Muka amsa mata da "Da
sauƙi"
"To masha Allah. Ko wacce dan Allah ta nutsu, kuma ta saki jikinta, babu mai hantararta ko
tsangwamarta, banda surutu kuma. Wannan sana'o'e zamu koya muku su kyauta ne, sabida
matanmu na karkara suma su tsaya da ƙafafunsu, wata gidauniyar mata ce ta ɗauki nauyin yin
wannan abun aikhairin, mai suna ( GASKIYA DOKIN ƘARFE, WANDA ANTY ZARATU
FASKARI TAKE JAGORANTA. FARAR MACE ALKYABBAR MATA, UWAR GIDA SARAUTAR
MATA )daga Faskari muke, mai gari shine mai masaukinmu. Da fatan zaku bamu haɗin kai.

Yanda ake haɗa sabulun soda.

Wannan manja ne na miya, wanda ake cireshu daga jikin kwakwar manja.
Wannan kuma costic soda.
Wannan ruwa ne
Waɗannan sune kayan da zamuyi amfani dashi.

Da farko zaki samu ruwa ki jiƙa costic soda ɗinki ya kwana. Saiki samu manki ki zuba a roba
mai faɗi in kika zuba, saiki samo muciya ko bulugari, kina zuba ruwan costic soda kina juyawa
a hankali, in kika gama zubawa sai kita tuƙawa a hankali a hankali har ya haɗe jikinshi. Saiki
juye a mazubi, ki barshi ya kwana, saiki yayyanka dai_dai na siyarwa. Shikenan sabulunki ya
kammala, kuma bugu da ƙari gashi da kumfa. Yanzu zamu yi muku wannan sabulu ido da ido
ku koya." Muna zazzaune a tabarma, matannan su uku suka haɗa sabulunnan abun gwanin
sha'awa. Duk abunda suka ce ni kuwa saina rubuta, danma ajin baya tafiya, muna yawan fita
fitsari. A haka muka gama ajin yau.
Tafe_tafe dai haka rayuwa tai ta tafiya, har muka gama ajinmu na koyon sana'a. Alhamdulillah

na gane komai na rubuta komai. Sun yaye mu, sun rarraba mana kemikal kyauta. Masu kuɗi
sun kuma siye. Nima na siya, kuma sunce da mun shiga kasuwar gari, muka tambaya ɓangaren
ƴan kemikal za'a nuna mana. Jikina yayi sauƙi sosai, fitsari saura kaɗan_kaɗan. Mako ɗaya na
roƙi malam ya ƙaramun akan dana gama ganin likita sai in wuce. Maganin gargajiya malam ya
sa aka dafa mini, na dinga sha shima. Cikin kwana uku da soma shan maganin fitsari ya
dai_daita har inajin taruwarshi a marata, sai naje na tsugunna nayi nishi sannan ya zubo. Bani
kaɗaiba duk wani masoyina nasan ya taya ni farin cikin samuwar lafiyata. ( Musamman maman
khairat, maman Yaseer, ummu Inteesar, Deezatu, da Ɗambatta. )Ina fatan Allah ya bama
waɗanda basu warke ba lafiya. Waɗanda kuma lafiyarsu ƙalau Allah ya ƙara musu lafiya da
imani. Ranar da mako ya zagayo na koma asibiti, likita tayi farin ciki da samuwar lafiyata, ta
ɗaurani bisa wasu shawarwari, har kyautar sutura tayi mun kala uku masu kyau da tsaɗa. Na
dinga mata godiya. Ina fitowa na koma gida na soma tattare komatsaina. Har zuchiyata ta
jagule na soma hawaye. Malam ya bada kuɗi da hatsi a bani. Suma su Inna suka ɗan haɗomun
tsarabar mata. Ina kuka na fita, sai haƙuri suke bani, banza nayi dasu, dan da suna ƙaunata ba
zasu ce in koma ma Yawale ba. Sati na uku a gida, ko sau ɗaya baizo ba. Babu wanda ya biyo
sawuna a gidan, amma ansa in koma babu ko rakiya, ba dole ma Yawale da Kumatu suita mun
wulaƙamci ba. Gani suke yi kamar bani da gata. Har aka isa Saleri ban fasa kuka ba, saida na
iso ƙofar gida na share fuskata. Da sallama na shiga gidan.
Gabaki ɗaya matan gidan suka zuba mun idanu cike da mamakin dawowata. Su buɗe baki su
amsan sallamata, abun ya gagaresu. Kumatu wani turus tayi ta dinga bina da idanu. A'i
shugabar munafukai ce tayi magana.
"Musina kece tafe da yamma sakaliya haka, ashe zaki dawo? Murmushin tura haushi nayi
nace.
Mai zai hana ni da gidan mijina, kuma uban ƴaƴana, ko an faɗa miki sakina Yawalen yayi?
Nan na shige ɗakina dana ganshi a wangale,na bar Kumatu da cizon yatsa. Ganin ɗakina a
buɗe nanma raina ya kuma ɓaci ainun. Kayana na dure na fito, sai kallon ƙafata da hannayena
suke nasha ƙunshin saleteb wanda Inna Lami ta kusan raba dare tana jera mun. Gashi ya turu
kamar jinin kare. Naje gidan aminiyata Ma'u ta yarfa mun kitso, ta kuma bani shawarwari masu
tarin yawa, ta yanda zan kula da mutuncina in kame girmana. Ɗakin Baba Huwaila na soma
shiga muka gaisa. Sannan na shiga ɗakin Baba Hauwa. Itama muka gaisa, anan take faɗa mun
Yawale sunje aiki a gona da yaran gidan. Ina komawa ɓarayinmu, na soma firfito da kayan
ɗakina ina kwalima. Saida na wanke ɗakin tas sannan na mayar da gadajen da kwabata da
babu komai a cikinta. Na kunna turaren wuta, ko ina ya ɗauki ƙamshi. Sannan na fito na wuce
sakaki. Kumatu da su A'i sai aikin kallona kawai suke ta faman yi. Ni dariya ma suka bani. Ina
fitowa daga sakaki, na ɗaura alwala nayi shigewata ciki. Sai da daddare can na haɗa sabulu na,
na juye a mazubi, na barshi a saman kwaba. Sannan nayi bacci. Ko ƙeyar Yawale ban gani ba.
Washe gari da yamma na yayyanka sabulun na fito dashi wajan matan gida. Hmm a daren
ranar kusan raba dare Yawale da Kumatu suka yi suna rikici.
Ni kuwa sabgar Yawale bana fatan kuma shiga. Sana'a kawai naba mahimmanci. Da sannu
matan gidan suka gane na warke, sai kuma muka ci gaba da aikin girki tare kamar yadda akeyi
da.
Rayuwa haka tai ta juyi dani, yau fari gobe ɓaki. In Idi yazo haka zan haɗa mai kayan abinci, in
ɗauki kuɗi in bashi, sabida bana son yana yawon barace_barace. Ashe daya je malaminsu yake

amsar kayan abincin, yasa manyan almajirai su lalubeshi ya karɓe kuɗin, kuma ya sashi a mari.
Ranar da Idi ya faɗamun wannan maganar bacci ma kasa yi nayi. Haka dai rayuwar taita Tafiya.
Mu kaita haife_haife ni da Kumatu, rayuwa kenan.wata rana wacce bazan taɓa mancewa ba.
Ina zaune a tsakar gida, ina yanka Sabulu. Alawiyya tana gefe tana wankin ƙannenta, sauran
mazan gidan kuma duk sun tafi almajirci, iyakar yaranmu mata ne kawai a gabanmu. Kwatsam
sai gasu Idi sunzo ganin gida. Nayi farin ciki sosai dana ganshi, amma ya rame sosai, kuma
idanunshi naga yayi jawur. A guje ƙannenshi suka suka je inda yake suna murna. Sauma'iyya
ƴar gidan Kumatu ma sake wankin da suke yi da kumatu tayi, a zuro a guje. Kumatu ta ɗago
cikin jaraba tace.
"Dan ubanki kina mace, kike gudu kamar wata jaka?" Murmusawa kawai nayi. Idi kuwa cikin
fara'a ya tsugunna a gabana.
"Uwo barka da gidan, mun sameku lafiya?"
Lafiya lau wannan yaron, ya karatun?.
"Alhamdulillah, kafin ma in tawo saida na biya wajan Ƙasimu, da su Jamilu na dubosu,
sunce in gaisheki. Juyawa yayi wajan Kumatu yace.
"Ina wuni Baba Kumatu?" A daƙile ta amsa mishi. Ana cikin haka, Saminu ɗan wajan
Kumatu ya shigo da buhun kayanshi, makarantarsu ɗaya da Idi. Sai lokacin Kumatu ta soma
washe baki. Baba Hauwa ce ta iso wajan.
"Ah mai gida takobin yaƙi kaine a tafe? Ɗan nema shine saida ka soma zuwa wajan
uwarka tukunna ko?" Kai na sauke kawai. Idi yace.
"To ai dole inzo in nemi albarka kafin in je wajan tsohuwar matata ko? Dariya suka yi
dukkansu.
"Meya same ka naga ka rame idanka yayi ja da yawa?" Ajjiyar zuchiya na sauke, dan
tambayar da zanyi mishi kenan, Baba Hauwa ta iso wajan.
"Idanuna ne suke ciwo, har asibiti ma na kwanta, gidan da nake ɗan musu
aikace_aikace su suka kaini asibiti. Amma da sauƙi, sai dai idanun ya samu matsala, in rana ta
take bana gani sosai, amma ina shan magani, sunce wata mai zuwa in koma asibitin, in banji
dama ba, zasu yanka mun tabarau." Hawayene ya subto mun. Babu shiri na miƙe na shige ciki.
Leda Idi yaba Alawiyya ta tabami. Sannan ya miƙama Sauma'iyya nasu. Baba Hauwa kuma ta
jashi suka tafi.
Bani na samu keɓewa dashi ba, sai bayan sallar isa ya shigo.
"Uwo saura shekara guda muyi sauka in sha Allah" murmushin din daɗi nayi nace.
"Amma idanun naka da sauƙi ko? Nayi imani malaminku ne ya kashe ma idanu, amma bani
da yanda zanyi ne"
"Ai ko a asibitin ma likitoci sun faɗa Uwo. Amma babu komai, bayan wuya sai daɗi. Muna ta
tattaunawa, ledar tsarabar daya bamu ya jawo. Atampace, da takalmi, da mayafi. Ya ware a
gefe yace ga nawa. Sai atampa da man shafawa yace na Alawiyya da Kulu. Albarka na sanya
mishi. Yai mun sallama ya fita.

Yawale:
Da sallama ya shiga ɗakin Kumatu, ya tadda Saminu a zaune.
"Au tare kuke ashe da wancan yaron Saminu"

Cikin kulawa Yawale yake magana da Saminu, harda tambayarshi yanayin birni, da kuma
yanayin karatun. Can idanunshi suka sauka a kan Atampa da man shafawan da Idi ya ba
Kumatu tsaraba."
"Wannan kayan fa Kumatu? Dama jira take.
"Hmm malam wai yaronnan Idi ne yayo mana tsaraba. Uwarshi kuwa nata leda guda,
banda nasu Baba. Nifa Saminu yasha faɗa mun ana kama manyan kuɗi a jikinshi a makaranta.
To Ta mai gari ma ta faɗa mun, kasan ɗanta Bala makarantarsu ɗaya. Ya tabbata dai Idi ɓarawo
ne" Yawale ya dubeta da kyau yace "Amma duk kina da wannan labarin kika kasa sanar dani, kina jira har sai ranar da
yaronnan zaije yayo wata gagarumar satar da ƴan doka zasu zo su naɗeni ina zaman zamana
ko?"
"Malam ka faɗa ace sabida ɗan kishiya ne" Ai bata gama magana ba, Yawale ya fice, sai
ɓarayin su Baba. Yana shiga ya cukuma Idi, ya fito dashi tsakar gida, anan yaita tamaule dashi.
Kowa ya fito, Su Jamilu, da Mudi suka tambayi Yawale me Idi yayi. Cikin kumfar Baki ya sanar
musu. "Sata yake yi a birni, har malaminsu na kama kuɗi masu gwaɓi a jikinshi." Suna jin haka
kowa ya shiga salati, Yawale yaci gaba da jibgar Idi.


Musina:.
Kalmar sata da Yawale ya dangantata da ɗana yafi mun dukanshi da yake yi zafi. Zuchiyata
sam taƙi nutsuwa, musamman da naji Yawale yana faɗin Idi yazo ya bar mishi gidanshi. Da
gudu na isa shiyyarsu Baba. Amma ganin yanda Idi ya fita hayyacinshi ya ɗaga mun hankali,
fiye da tashin hankalin da nake ciki kafin in iso. Idi ya dubeni yace. "Uwo ni ba ɓarawo bane. Ki yarda dani.
Na yarda dakai, nasan cikinku babu wanda nayi mishi tarbiyyar da zai ɗauki abun wani."
Marina Jamilu yayi har yana huci. Nan matan gidan suka hayayyaƙo mun, dole nayi shiru.
"Uwo ku dena kukan. Zan tafi, amman zan dawo in ɗaukeki a gidannan a lokacin da babu
wanda ya'isa ya hanani fitar dake a cikin wannan ƙaddararren gidan da kike zaune dan sabida
mu yaranki. Kuma zan kare mutuncin kaina" Inaji ina gani aka tusa ƙeyar Idi a gaba. Tun daga
lokacin hawan jini ya kamani, dan na shiga damuwa mai tarin yawa. Ƙauye kowa ya ɗauka, dan
Kumatu sai yaɗa abun take faman yi"

Bayan wasu shekaru.

MRS BUKHARI


*_GAWURTATTU UKU2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH_

*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI.
GAWURTATTU UKU



Lamba ta goma sha uku.


Saleri:

Musina:
Ina shiga ɗakina na soma sauke jerena kab ina ɗurawa a buhu. Duk wani kayan ƙawa saida na
cire na zuba a buhu, matan gida sai leƙowa suke yi. A'i uwar gulma matar Jamilu wan Yawale
tace.
"Musina kaddai rantsuwar da Kumatu tayi a tsakar gidannan akan sai Yawale ya sakeki,
itace tayi tasiri? Kumatu dama tace saita ɗaukeki akan yaranki" Wani ƙunci da tashin hankali ne
ya shigeni, maganar A'i tasa na kaɗu ainun. Dan bana fatan in tsallake in bar yarana su rayu
babu ni a kusa dasu. Amma na sani Kumatu bata isa tayi mun abunda Allah baiyi mun ba,
kuma duk abinda zai faru a kaina, rubuce yake a littafin ƙaddarata. Murmushi na ƙaƙaro nayi ma
A'i kawai, na kasa ce mata komai dan in nace magana zanyi to kuka zai tawo mun dole A'i taga
rauni da gazawata, banma kuma san me zance ma A'i a

10 / 21