Iyayen Giji Book Compelet Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   2 / 21

3K to 6K   out of 61.8K words

"Mai riga a samo barkono, sai anyi mata hayaƙi ina ganin." Cewar unguwar zoma kenan."
Baba mai riga tace.
"Laure a duba kaskon nan baya rabo da gaushi, a ɗebo, saiki kawo barkono guda
bakwai."
Azaba kan azaba kenan. Dan mugunta haka anguwar zomannan ta rufeni da zane, ta
zuba barkono a ciki ƙaramin kasko, ta ajjiyeshi gabana. Nan take yajin barkono ya turniƙeni.
Kowa ya dare a ɗakin, daga ni sai ita. Tari nake yi ina zubar da hawaye da majina, sai atishawa
nake yi, kamar wacce ta hau na kada. Ƙashin kwankwasonane naji ya buɗa, wani irin nishi ne
naji yana tunƙudo ƙanshi da kanshi. Wani abune naji ya tokareni. Wannan anguwar zoman na
haskawa, sai naji ket, tasa aska ta ƙarani. Hannu tasa ta jawo jaririn.
"Ayririri yiriririhhhh ta samu kai"
Ɗakin nan ya kuma ɗinkewa. Mabiya kuma akayi akayi ta fito abu yaci tura. Muciya unguwar
zomannan muguwa tasa aka ɗakko mata. Ai kuwa haka taita turbuɗamun a baki, ina kakarin
amai.
Mabiyar ce ta faɗo, take aka yanke cibi.
"Subuhanallahi mai riga me zan gani, kinga aljanin da surukarki ta haifa kuwa." Ras naji
gabana ya tsinke ya zube. Aljani kuma? Na nanata a zuchiyata. Ina durƙushe jaririna sai
canyara kuka yake yi. In wannan ta leƙo saita matsa, sai waccan ta leƙo itama saita matsa. Ni
dai tsabar kunya kaina yana ƙasa, amma zuchiyata sai daka take faman yi. Baba mai riga ce ta tsugunna, tasa hannu tana duba jaririn. Ɗaga kai tayi ta dubi Matar Malam

tayi shiru, tama rasa ta cewa. Jaririna kuwa sai canyara kuka yake yi. Ƙauna da tausayinshi sai
buga mun tambari yake yi. Ina ji ina gani aka rasa wanda zai ɗaukeshi, ko ya bani umarnin
rungume kayana, inna ɗago kuma ace nayi rashin kunya a gaban surukai, da matan Yayun
miji."

Shehu:
Yana zaune a kututturen itacen dake ƙofar gida. Shi da abokanshi biyu. Haruna, da Hamza.
Kukan jariri suka soma jiyowa, yanata canyara kuka.
"Inya_inya_inya_inya"
"Anya kukannan da baƙon duniya yake yi na lafiyane kuwa? Naji kukan yai yawa. Inji abokin
Shehu.
"Nima haka nake ji dai. Amma bana shiga ciki ba, su Laure su sani a waƙa in suna dakan
dawo a tsakar gida.
Malam ne ya tawo shida Baba Kabiru mahaifin Shehu, wanda akafi kira da Baban Yara. Malam
yace.
" Kai Shehu ka leƙa masu haihuwarna kukan kamar bana lafiya ba. Kafin Malam ya rufe baki,
zuruf Shehu ya shige cikin gidan.

Laila:
Hawaye nake ta fitarwa na tausayin jaririna. Muryar Shehu muka jiyo yana tambayar Iyami
matar wanshi ko lafiya?" Iyami tace.
"Wani babban al'amarine mai cike da almara jaririn yake tattare dashi Shehu, danni tunda
uwata ta haifeni ban taɓa cin karo da jariri irin na Laila ba. Amma duk yanda akayi ɗan ruwa
ne, ko kuma mayu sun shafeshi, ko kuma aljanu sunyi mata canje.Tana kaiwa nan tasa hannu
ta ɗauki jaririn tasa akan tsumman zani. Shehu kuwa dajin haka ya fita guiwa ba ƙarfi. Ajjiyar
zuchiya na sauke. Baba mai riga tace.
"Allah ya baki lafiyar shayarwa Laila. Tana kaiwa nan ta juya tayi hanyar fita. Surukan gidan
suka mara mata baya. Ɗakin ya rage dani ni sai matar Malam, Sai Iyami.
"Tashi zauna Laila, bari insa a hura wuta a ɗaura ruwan wanka. Iyami a nemi tsumma a naɗe
mahaifarnan da safe sai aba Shehu ya birne. Iyami tace.
"To matar Malam, amma ruwan wanka kam inaga bojuwar ta juya yanzu, sai dai a kwashe a
kwatanniya kawai. Tun sanda take kan guiwa nasa Laure ta hura wutar.
Ina miƙewa jini kamar jira yake yi saiya ɓalle, take na nemi ganina na rasa, yarab na faɗi
idanuna na shirin kakkafewa. A guje Iyami ta kirawo Baba mai riga da Shehu. A lokacin aka
kwanɗa kiran assatu.
Dishi_dishi nake ganin Shehu da jaririna wanda ko fuskarshi ban kalla ba. Da sauri Laure ta
shigo hannunta riƙe da kofi.
"Ga mandan Baba na jiƙa"
Manda aka ɗagani aka ɗuramun. Kamar ɗaukewar ruwan sama jini ya tsaya cak. Daga nan ban
sake sanin ina nake ba. A duniya ko a lahira.

Shehu:

"Laila, Laila, Matar Malam kinga bata motsi fa." Baba mai riga tace.
"Shehu kayi maza kaje ka sanar da iyayen Laila halin da take ciki kamun ta Allah ta kasance,
zaiyi wuya yarinyarnan ta tashi. Ka shiga jarawaba, gana rashin mata, gana samun ɗa mata
maza.
Shehu ji yayi kamar an kwaɗa mar guduma a maɗigarshi.
"Mata maza Laila ta haifa mun Baba?" Matar malam ce ta katseshi.
"Ta farfaɗo kayi maza Shehu ka sanar da iyayen yarinyarnan halin da ake ciki.
A gigice Shehu ya fita, ya nufi hanyar Bakori. Laila kuwa wani nannauyan baccine yai awon
gaba da'ita na baƙar wahala.





Mrs Bukhari ce



Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman
na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas
mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata
saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin

07068606171
08104335144
08179523215



*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_

*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_

*Mrs Bukhari ce *
MATA IYAYEN GIJI

DAGA ALƘAMIN
BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
GAWURTATTU UKU


LAMBA TA UKU

SAMFOTI


*_GAWURTATTU UKU2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*


Ɗambawa garin marasa kyau, duk kaga ɗan ƙwarai baƙone.

Ɗambo

Ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bakura, Zamfara Gusau.

Ƙauye ne mai cike da ƙauyanci, da gidadanci sosai, ƙauyene da babu wutar lantarki, babu
asibiti, babu makarantar boko, babu ta mahamdayiiya. Duk wannan abun dana lissafo sai
ɗambawa sun shigo garin Bakura suke gudanar dashi. Manoma ne, kuma makiyaya.


GIDAN UWAYEN AMARYA:
Uwar biki, taci kwalliya da jojinta sai sheƙi take yi. Mata maƙwabtane naga suna ta shigewa da
fantekoki manya, cike da tuwon dawa, tuwon, masara, tuwon gero, tuwon ruwa, ( tuwon ɓula)
Ko wacce da nata. Da sun shiga sai su dire wannan fantekar akan gadon kara da aka ajjiye a
tsakar gidan. Wannan kawo abinci daga maƙota zuwa gidan uwar biki, wata al'adar auren
ƙauyen Ɗanbo ne, daɗaɗɗiyar al'adar da aka ƙi yar da'ita, al'adace da take taimakon marasa
ƙarfi sosai. Uwar amarya sai washe baki take yi, tana faman gaggaisawa da jama'a. Mata da
yara sai cin tuwo kala kala suke yi.
"Rakiya kuyi da jiki mana, dan Allah a samu aje gidan maza ayi daɓennan mana." Rakiya
ƙanwar Uwar amarya ce.
Isowa tayi wajan yar Tata, ga dangin uwar amarya daga gefe, mata biyu suna riƙe da ƙyauren
langa_langa sabo fil sai kashe idanu yake yi. Wasu na riƙe da kayan aikin daɓen ɗakin amarya.
"Yaya mu kam mun tafi, gara muje da wuri kam"
"Allah ya tsare hanya."
A jere matannan suka fito kusan rai goma sha biyu. Suna tafe a ƙafa suna waƙar da akeyi
in mata zasu je yin daɓen ɗakin amarya. Ga waƙar kamar haka.

Ayye lalle, ayye lalle waya kawoki, Baba daya kawoki mi aka baki? Tuwo aka bani da fura, inda
naji kiran nan da gudu nika sheƙawa, inbanso neran nan wazobiya ta ɗori, Allah bani mijina
koda ƙadangarene, mu shige ɗan ɗakunmu, sunɗunɗun, maɗunɗun.
Aka suke ta waƙarnan suna tafe.
Ɗabe itama wata al'adar aure ce a Ɗanbo. Dangin amarya suke yin daɓen ɗakin amarya, su
shafa makuba a bango, da Ƙyaure. Amma in aure ya mutu, ana cire ƙyauren, in rabuwar rashin
daɗi sosai akayi, har daɓen ake farfasawa. Washe gari kuma sai a kawo jere, da yamma masu
kai amarya su kawota. Gagarumin biki akeyi sosai a ranar daɓennan. Da sallama su Rakiya suka shiga gidan maza.
"Ahuwanku dai masu gida, ga baƙin arziki, baƙin daɗi, munzo yin daɓen ɗakin Amarya ne."
Ƙanwar mahaifiyar Audu Ango tace.
"Maraba lale da zuwan baƙin arzki. Ku muje a nuna muku shiyyar surukan gidan." A baya
suka bita, suna tafe suna waƙa, tsofaffin cikinsu nayi musu amshi da tafi. Gidan a batse yake da
jama'a fam. Kuma yau da Yamma abokan ango sun shirya wasan Dambe, a gidan wasan Ɗan
kande, kasancewar Damben gargajiya shine aikin Audu, duk da ma dai suna taɓa sana'ar fawa.
Yawanci mahauta sune masu yin damben gargajiya kamar yanda yazo a tarihi. Mahauta sukan
yima saurari dariya, in baya shiga fili, harma su kirashi da matsoraci, wani sa'ilin har mata yake
rasawa. Dan ko wacce mace tafi son jarumin maza, ba rakkon maza ba. Hakanne ya sa
mahauta suke damben gargajiya sosai.

"Ga ɗakinnan" Tana nuna musu ta wuce tana guɗa.
Ɗakin falle ɗaya ne babba. Nan dangin uwar amarya suka zage, sukaita aikin kwaɓar
bigaggiyar ƙasa. Suka shiga daɓen ƙasan ɗakin amarya, suna yi suna waƙar al'ada mata sai tafi
suke yi. Ga waƙar da akeyi in anga daɓen kamar haka.
Ke kika ce kina so, da baki ce kina soba da ba'a baki shiba. Ta zama _ta zama ɗakko hula. Ta
zama _ta zama ɗakko buta. Ta zama _ ta zama ɗakko riga. Haka har zuwa ƙarshe. Mata kuma
suna shewa, ana tafi da amshi.
Suna gama daɓe, suka saka ƙyaure, sannan suka shafa makuba a bangon ɗakin, ya fito shar
dashi, sai ƙamshin ƙasa yake yi.
Dangin ango ne, suka dire musu fanteku. Ɗaya cike da dawo, ɗaya cike da nakiya, ɗaya cike da
diɓila. Bisa ga al'ada. Haka suka ɗauki wannan fanteku aka suna tafe suna waƙa da tafi, har
zuwa gidan Uwar amarya.
Da yamma su Audu suka gabatar da wasan dambe.
Washe gari, bayan sakkowa a masallaci, aka ɗaura Auren Audu da Shamsiyya. Da rana ƙwal
aka soma fito da kayan jeren ɗakin amaya, gado da kwaba tuni mata suka soma gaba da'ita,
kwabar nan aka mata suka azata. A ƙarƙashin kwabarnan mata sunfi rai ashirin. Haka masu
ɗauke da gado ma. Suna gaba, mata masu ɗauke da jere aka suma suna biye. Kwalla, kumbo, fanteku, samiru,
ɗan china, kwanon sulba, gidauniyar cin tuwon mai gida, languna. Da adakar kayan lefe. Ga
kuma fanteku manya da aka cikosu da wara. Dan tuyan wara shine sana'ar Shamsiyya, kuma
al'adace ranar auren yarinya, a samu fanteku a tsaƙe da abinda take siyarwa, naci a kai gidan
surukanta, suci su ture, tare da kayan gara, irinsu. nakiya, ga diɓila, ga ajaye, ga nakiya. Ga su
buhun shinkafa, buhun gero, buhun dawa, buhun masara, ƙwarya bokatan ƙarfe. Da kayan
noma dangin su, haiwa, garma, guraye. komai aka kuma da ƙafa ake kaiwa."
Sun samu tarbar kirki, tare da dangin Audu, da maƙota aka haɗu aka jere ɗakin Shamsiyya.
Tas.
Da yamma kuma, ƙanwar mahaifin Shamsiyya ita ta goyo Shamsiyya a baya. Ana tafe a ƙafa
da mata da ƙawayen amarya ƴan rakiya, suna tafe ana waƙa. Amarya ƴar gata tana baya tana
shurɓune majina. A haka aka kaita ɗakin mijinta. Kwanan ƙawayen amarya biyu a ɗakin
Amarya. Ana Ukunne abokan Audu suka rakoshi ɗaki shima.

Shamsiyya


Na ɗauka rayuwar soyayya haka za taci gaba da ɗorewa. Harma a kwanakin amarcina nayi
magana da gogan nawa kan cewa.
Ni naji sai cewa akeyi aure haƙuri ne. Kuma tausayi da haƙuri ke riƙe ma'aurata ba soyayya
ba. Ni kuma sai naga saɓanin hakan Audu. Shi kanshi a lokacin giyar soyayya ashe ta buga shi,
baya gane komai, cemun yayi
"Romun soyayyarmu dai ba mai ƙarewa bane, haka za muita sharɓarshi in sha Allah.
Haka rayuwa taita garawa damu, kwanaki, watanni, shekaru sai Shuɗewa suke yi. A haihuwa
ta biyu, anan na soma ɗanɗana baƙin ciki da takaicin ɗa namiji. Audu madokine sosai, ko yaya

nayi mishi kuskure sai duka, dukan da zaima sa'anshi a filin daga, irinshi yake yi mun, du ya
farfashemun baki. Dana zari mayafi na tafi gida. Mahaifina ya rakoni da duka har ɗakin mijina.
Na rasa wanda zai tausaya mun ya dubeni. Ƴa mace rayuwa take mara ƴanci, ko a gidan
iyayenta. Iyaye su suka soma banbance mu. Dan da zaran sun haifi ɗa namiji, zasu saka
rayuwarmu a kwandon shara. Da wannan tunanin mazan suke buɗe idanu. Suna buɗe idanune
suga iyayensu mata ai basu da wata daraja a idanun iyayensu maza. Amfaninmu shine, girki,
haihuwa, kashe musu ƙishi. Iyakar darajarmu kenan. Ɗiyata ta farko macece mai sunan
Mahaifiyar Audu wato Aishatu, muna kiranta Shatu, ban cireta a nono ba na kuma haihuwar
Zaliha, ina tsige Shatu, Zaliha ta cabka. Lokaci ɗaya nabi na susuce, haihuwar konika nake yi, a
cikin shekara bakwai da aure, yarana uku, ga wani cikin a maƙale a jikina. Tsohon cikine a
jikina, amma haka jiya da daddare Audu yai mun duka, dan kawai nace ya bani kuɗi in ɗan
tsitstsinto kayan jarirai, dan na Shatu duk ya mutu, Zaliha ce take sawa, Shatun ko suturar arziki
bata da'ita. Nan ya shiga farfaɗamun magana, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Shine
harta kaimu ga duka, haka na wayi gari cikin nauyin jiki da tsami. A zaune nake a dokin ƙofata
ina kaɗa ma Baba Shatu lagwani, na jiyo Sallamar Goggo Rakiya, ƙanwar mahaifiyata.
MRS BUKHARI


Ayi haƙuri babu yawa. Yau asabar mai gidan ya kafa ya tsare


Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman
na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas
mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata
saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin

07068606171
08104335144
08179523215



*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*

2 / 21