Iyayen Giji Book Compelet Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   12 / 21

33K to 36K   out of 61.8K words

matsala a zamantakewarki da, Shehu, da iyayen mijinki, dama
facalolinki, ko? Kuma Innarki ta faɗa mun ashe kinyi yaji ma, malam ya koroki ko? Meke
damunki Laila, ki faɗa ko zaki samu sauƙin nauyi a ƙirjinki, sannan a iya saninmu munsan
ƙafafunki suna da lafiya ras aka aura ma Shehu ke. Lalurace ta sameki kika kasa sanar ma
kowa? Cikin ƙunci da ɗacin zuchiya nace.
Goggo Laraba, tunda na auri Shehu, mu kayi mako guda tare, na fahimci Shehu yafi
ƙarfina ta ɓangaren mu'amular aure. Sabida baya gajiya sam. Tun abun bai dameni ba, har
naga abun ya wuce gona da iri, saina soma yima Shehu ƙorafi. Dan kullum ina wayar gari cikin
gajiya, da kasala sosai, ya kasance bana ko sha'awar shiga cikin mutane. Hakanne ya ja mun
tsana a idanun facalolina da iyayen mijina. Wata na biyar a gidan Shehu, ƙafafuna suka riƙe
cikin dare. Tun daga wannan lokacin na rasa gane ma jikina, kullum a cikin rama da ciwo nake.
Shehu tun yana bani haƙuri har ya dena. In yazo da ƙarfin tuwo yake karɓar hakkinshi, har ta

kai har razana nake yi in naji motsi kaɗan, tsabar rashin hayyaci. Shine na gudo gida dana lura
so yake ya kasheni, ko tausayin cikin dake jikina bayayi. Kuma na bashi shawarar ya nemi
magani dan abun bana lafiya bane. Sai ya balbaleni da faɗa. A cikin halin da nake kenan, na
rasa wa zan faɗama danya bani shawarar yanda zan tafiyar da Shehu. Kuka na fasa mai ciwo
ina jin kunyar su Goggo Laraba sosai. Ba dan a cikin tashin hankali nake da son samun mafita
ba, da wasa bazanyi irin maganar nan dasu ba. Shi kanshi Shehun kullum a cikin roƙona yake,
kar in tuni asirinshi, amma ni kuma cutuwa nake yi. Wata tara da yin aure, amma na buɗe sosai,
har tusa ce take fitowa ta gabana, tsabaragen buɗewa." Hawayene suka ci gaba da suntiri a
kumatuna. Ɗahiru ne ya soma kuka.
"Inya_inya_inya" Goggo Laraba ta miƙa mun shi, nasa hannu na karɓeshi. Na ciro Mama
na saka mishi a baki, cikin kunya da nauyin su Goggo Laraba. Goggo Laraba tace.
"Kin tabka babban kuskure da kika zauna a cikin irin wannan halin ba tare da kin sanar
ma magabatanki ba. Daddo kin tuno da Hadiza ƙawata wacce ta haukace a shekarun baya ai?"
Daddo tace.
"Na gane Hadiza, wacce akayi bikinku rana guda ko?" Goggo Laraba tace.
"Itafa. Mijinta wani irin mutum ne mai wata iriyar halitta, gabanshi yana da girman daya
wuce misali. Wallahi ba'a sani ba. Ya dinga kwanciya da Hadiza har sai da ta haukace. Aka
soma binciken dalilin haukar. Shine maƙotanta suke sanar ma iyayenta. Kullum cikin dare suna
jiyo ihunta, tana naiman ɗauki. Daga baya saita soma firgita ita kaɗai. Daga ƙarshe bayan ta
haukace, Allah yayi mata rasuwa a cikin haukar nan. Da mijin ya ƙara aure, wacce ya aura
mutuwa itama tayi, sabida yafi ƙarfinta. Ni ina ganin maslaha anan shine, a kira Shehu a zauna
ayi magana gemu _da_ gemu, yaje ya nemi magani, ai ana samu. In bazai nema ba kuma, a
raba aurennan tun wuri." Da sauri na ɗago na kalleta. Daddo ta dubeni ta maida dubanta ga
Goggo Laraba tace
"Ba'ayi hakan ba Laraba, yin hakan ba maslaha bane. Kinsan wanki bazai yadda da
wannan abun ba. Ni ina ganin abunda ya dace a matsayinmu na dattijai shine. Mu gyara ƴarmu
kawai. Sauƙin da zata samu shine ya kasance kullum tana cikin tarin ni'ima, hakan zai taimaka.
Nasan ta riga ta gama wangalewa, saimu gyarata tsab. Ki kuma ɗaurata akan yanda zata kula
da kanta a koda yaushe. Akan yawan buƙata ba'a kashe aure ba. Mata da yawa suna cikin halin
da ya fi na Laila. Amma sunyi haƙuri sun jajirce. Shehu gani zaiyi kamar Laila ta tozartashi ne.
Ba lallai bane ya yarda cutar da'ita yake yi ba. In da ci, da sha, da sutura. To ta rungumi dukkan
ƙaddarar da zata fuskanta a zamantakewar aurenta. Sabida mu kanmu bamu san wanne hannu
zata sake faɗawa ba." Goggo Laraba tace.
"Dole ta buɗe ai, kullum yana surfarta kamar hatsi. Da yaji tayi dameji, saiya ɓare wata a
leda dal, ita ya zubata a kwandon shara. Mu mata kullum a cikin danne rayuwarmu ake. Maza
kawai ake duba, kuma ake girmama damuwarsu. Mu ko oho, Allah ka zama gatanmu. Laila zan
gyara ki tsab. Zan baki surruka irin namu na tsaffin hannu, ki dinga amfani dasu a koda yaushe.
Magani a gonar yaro." Hawaye na share, nayi shiru ina tunanin maganar Goggo Laraba da
tace. Daya gama cinye moriyata zai kada ni a kwandon shara, ya auro dal a leda. Lumshe
idanu nayi, to ya zanyi da ƙaddarata? In nabar gidan Shehu ya zanyi da Ɗana wanda a wajena
kaɗai zai iya samun kulawa? Dole in zauna ko dan kula da yarona."

Fada

MRS BUKHARI


[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: *_GAWURTATTU UKU2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don
koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in
akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan
idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya
don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin

07068606171
08104335144
08179523215



*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU



LAMBA TA GOMA SHA SHIDA




"Malam. Gani gaku ku dangin Ɗahiru. Ga Zainabu ta wajena. Ga Binta, ga mahaifinta malam
Ayuba. Ita waccan bazawara ta fita a cikin zancan tunda tayi aurenta. Amma ga malam Rabo
mahaifinta yace yana son abi mishi hakkin ƴarshi. To duba da mutuncinku da nake gani, Malam
da Baban Yara. Wallahi da tuni wani labarin akeyi ba wannan ba. Matasanmu ma zasu iya yin
komai. Amma anyi zama na amana tare daku, kuma baku goyi bayan Ɗahiru kan taɓargazar
daya aikata ba. Zainabu ta wajena, tunda wannan iftila'in ya dira a kanta. Du maneman ta suka
tarwatse. Shekara sama da goma yarinya tana gabanmu, ƙannenta sai hayayyafa suke a gidan
mazajensu. Binta tayi Auren harta haihu a gidan Aure, amma surukai suka sata a gaba har sai
da a ka sakota, taci gaba da ɗanɗanar baƙin ciki a ƙauyannan. Yarinyar malam Rabo, ta samu
tayi wani auren ita Allah ya rufa mata asiri. To sai ga labarin dawowar Ɗahiru cikin wannan gari
nawa. Ina fatan zaku bi umarnina, shima zai ɗauki duk hukuncin da zan zartar akanshi? Domin
a samu sulhu. Tunda yarannan suma da nasu laifin, ai ba fyaɗe yayi musu ba. Duk da muna jin
jita_jita a gari cewar. Yana amfani da kwallin ƙiful danya cinma mummunar manufarshi akan duk
yarinyar da tayi mishi. Fada tana son ganin Ɗahiru." Malam yayi gyaran murya yace.
"Allah ya gafarta mai gari. Ina ganin ko babu Ɗahiru ni tamkar uba nake a wajanshi. Kuma
Allah yana gani dai_dai da sakan ban taɓa mance ɓata sunan gidanmu da Ɗahiru yayi ba.
Yanzu haka Shehu yana can yana nemoshi." Shehu ne ya ƙaraso cikin shagon, Ɗahiru na biye
dashi. Suna zama yaron Iyami ya iso. Tsugunnawa yayi ya kwashi gaisuwa sannan yace. "Kawu Ɗahiru ana nemanka a gida. Umma Tani tana naƙuda." Zumbur Ɗahiru ya miƙe. Sai
yayi kwarjini sosai a idanun jama'ar wajan. Aikin Tsubbu ya soma tasiri a jikinshi.
"Aimun afuwa mai gari. Amma ga Malam zaiyi komai. Kuma ina mai ba kowa haƙuri nayi
kuskure nai laifi. Na kuma yi nadama. Kaina bisa ƙasa ina neman aimun sassauci. Yana kaiwa
nan ya fita a shagon. Da mugun gudu ya falfala." Malam yace.

"Ni a shawarce mai gari. Mai zai hana a haɗu a rufa ma juna asiri. Yarannan tunda ga
iyayensu. Muna nemama Ɗahiru aurensu. Ko ba komai wannan sirrin zai iya birne kanshi, duk
da masu iya zance na cewa kunne ya girmi kaka. Amma yarannan da aka samesu bata hanyar
aure ba. Kasancewar iyayensu a ƙarƙashin auren zaiyi musu rumfa, tunda Ɗahiru mahaifinsu
ne. Malam Rabo muna roƙonka kayi haƙuri ka yafe hakkin ɗiyarka tunda tayi aure abunta."
Fada ta ɗauki shiru na wasu lokuta. Dukkansu sun gamsu da shawarar Malam, duk da yaran
babu wanda suka tsana duk duniya sama da Ɗahiru. Amma da yake su mata ne, sai suke ganin
zama ƙarƙashin inuwar auren wanda ya salwantar musu da budurcinsu, kamar ya fiye musu.
Badan komai ba ko dan su fita daga halin tsangwama da kyarar da akeyi ma ƴaƴan da suka
haifa a gaban iyayensu. ( Ita mace a kullum tunaninta ta yaya zata samama yaranta
kyakykyawar rayuwa mai inganci? Ita mace duk sanda ta zama uwa. Duk wani hange, da
hasashenta akan, yaranta yake ƙarewa. Koda ita bazata samu ingantacciyar rayuwa ba. In dai
yaranta zasu yi farin ciki da hakan, ta gammaci ranta ya zame ma yaranta fansa) ( Allah ka
shiga lamarin iyaye mata ka taɓa, ya Allah ka kawo sassauci da rangwame a rayuwar iyaye
mata. Ka dasa ƙauna, da soyayya mara yankewa a tsakanin yara da iyayensu Ameen.") Mai
gari yace
"Na gamsu da bayaninka malam. Kuma na amince da shawararka. Amma a yanzu ku fidda
sadaki, a ɗaura auren a yanzu anan, kowa ya huta. Ku mata matan na sallameku." Tashi suka
yi, suka fice. ( Iyaye mazan kuma suka yadda yaransu su auri wanda ya lalata musu rayuwarsu.
Badan komai ba, dan gudun bakin duniya. Basu yi duba da wacce irin rayuwa yaran zasu
fuskanta a wajan miji, da dangin mijin ba. Basu yi tunani akan tsawon shekarun da Ɗahiru ya
ɗauka bayanan ba, wanne hali yaje ya kwafo, ya ɗaura akan halin akuyancin da suka sanshi
dashi? Oho ba wannan bane abun dubaba a wajansu. Abun duban a wajansu. Sun ya da
kwallon mangoro sun huta da ƙuda) A wajan malam ya ciro abunda ke ajjihunshi, Baban Yara
ma ya ciro nashi, Lauwali ma ya saka nashi. Shehu ya zura hannu a ajjihu sai yaji wayam. Shi
dai yasan da kuɗi a jikinshi. Murmushi yayi daya tuna ashe a ɗaki ɗaya suka kwana da Ɗahiru,
yasan tabbas shi ya yasheshi. Mai hali baya fasa halinshi. A wajan lauwali ya ari kuɗin ya saka.
Take aka ɗaura Auren Ɗahiru da zainab, da Binta. A bisa sadaki jaka huɗu. Kuma aka ƙare
zaman akan da daddare za'a kawo mishi matanshi, da yaranshi biyu. Mace da namiji. A haka
taron ya watse.

Tani:
Mahaifiyarta da ƙannenta ne a kanta. Dan tun safe suka zo gidan, dansu gane ma idanunsu
gaskiyane su Tani sun dawo? Dan tuni aka cire rai dasu. Sai kuma suka zo suka sameta a
halin naƙuda. Jini sai zuba yake yi a jikinta." Ɗahiru daya shigo gidan a guje, sai yayi ɓarayin su
matar Malam. A ƙofar ɗakin matar Malam ya ga dafifin mata, ko wacce hannunta riƙe da
kumatu. Turesu ya dinga yi yana kutsa kai. Ganin iyayen Tani ne a kanta, hakan ya matuƙar
kashe mishi jiki. Amma a hakan ya daure yace.
"Baba ku ɗan bani minti biyu, akwai wani taimako da zanyi mata ne. Yanzu zata sauka. Ba
tare da sunyi tunanin komai a zuchiyarsu ba. Suka bashi waje. Kallon idanun Tani yayi, a runtse
idanunta suke, bata ma cikin hayyacinta. Ƙoƙonnan ya ciro a aljihun ƴar shararshi, yasa hannu
ya dinga kwarfatar jinin daya zuba a ƙasa, yana katse hannun nashi a bakin ƙoƙon. Ta cikin riga
ya saka hannunshi riƙe da ƙoƙon. Wuf ya fice a ɗakin yana waige.

"Inna ku shiga, yanzu zata sauka" Ya wuce har yana shirin faɗuwa. Matar malam sai
rangaɗa mishi kira take yi. Amma banza yayi da'ita, har saida yaje ya nemi waje ya adana
ƙoƙonnan, sannan ya dawo. Ya samu Tani ta suntulo ɗiyarta mace, gyarasu ma akeyi. Matar
malam ta yafatoshi suka koma gefe. "Ɗahiru zabin da naga kaba Iyami ta gyare ta soye, na meye wai? Baki ya washe yace.
"Sadaka ce za'ayi mun Matar Malam. Kinsan dana je binni na koyo ilimin malumta irinna
Malam, zan ɗan dinga taimakon jama'a masu ɗauke da ciwo ayi musu rubutun ayoyin Alkur'ani,
da yardarshi da amincewarshi su samu lafiya. Masu ɗauke damuwa kuma a tayasu roƙon Allah.
Wannan sadakar ta neman yardar Allah ce." Dariya Matar Malam tayi tace. "Ai hakan yafi, da ƴan tsalle_tsallen da kayi. Ƴan satar kajin maƙota duk an daina" Ɗariya
yayi yace
"Matar malam baki da mantuwa gaskiya. Miƙon mahaifar in burne, sai in koma fada na
baro su malam anata fafata sharia." Mahaifar Matar Malam tasa Baba mai riga ta miƙo, aka ba
Ɗahiru. Itama yaje ya adanata a inda Aljani kayanasu zai gani ya ɗauka. Ya nufi hanyar fada
yana tafe yana surukai. "Ai nayi kuɗi na gama, zan kai Tani ta sauke farali, nima inje inyi adda'a,
inga masallacin ma'aikin Allah" Kaciɓus yayi dasu malam a hanya.
"Kai dai baka da hankali kana tafe kana shashanci. Ya jikin Tani ince ta sauka?" Cewar
Malam. Ɗahiru yace
"Ta sauka Malam an samu mai sunan Goggo. Kun gama da fadar ne?" Baban Yara yace
"Mun gama, kuma an samu fahimtar juna. Malam zaiyi ma bayanin komai. Allah ya raya
Goggo" Shehu daya lula duniya tunanin ɗan da Laila ta haifa mishi. Yanzu da Ɗahiru yake faɗar
haihuwar matarshi, sai yake jin inama shine aka haifama lafiyayyar jaririya. Ko mai ya tuno
kuma oho, sai yayi murmushi harda girgiza kai." Suna isa ƙofar gida, Malam ya zaunar da Ɗahiru yayi mishi bayanin komai. Take Ɗahiru ya
shiga lashe baki, yana tunano irin romon daya sharɓa a wajan su Zainabu. Yayi farin ciki sosai
da wannan aure, dan murna ma, har tashi tsaye yayi ya dinga yi ma kanshi kirari. Baban yara
yace "Sai kasa matan ƴaƴanka su share ɗakunan da suke can cikin gida, ta bayan sakaki can
nesa, ɗakuna huɗu ne a jere falle_falle. Kaga kowa saita ɗauki ɗaya, kaima saika ɗauki ɗaya.
Kayi haƙurin zama dasu, yara da suka haifa maka kuma. Ka tausaya musu Ɗahiru." Ɗahiru
kamar na Allah haka yaita godiya. Kuma yayi musu bayanin irin wanda yayi ma Matar Malam
kan malunta da zai soma. Sunyi murna dajin hakan sosai. Da yamma lis aka kawo amare.

Laila:
Ina kwance, muka soma jiyo yiriri_yiriri. Nayi mamaki sosai. Zuwa can sai muka

12 / 21