Iyayen Giji Book Compelet Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   5 / 21

12K to 15K   out of 61.8K words

lafiya?"
Baba ciwon yoyyon fitsari ne ya kamani, kuma na roƙi Yawale ya kawo ni asibiti yace
baida kuɗi, daga baya kuma yace in dawo gida, in ku kai mun magani na warke zai zo ya
ɗaukeni." Inna Lami kishiyar mahaifiyata ta dubi mahaifiyata wacce suke kiranta Tarana tace.
"Tarana yau nake jin ɗan gatan uwa, wato mu nema mata lafiya, sai yazo ya ɗauki
abunshi ko? Haka fa mijin Hanne yai mana sanadin mutuwarta." Inna dai bata ce komai ba sai
haɗiyan ƙududu take. Malam Dauda mahaifina yace.
"Yawale baiyi laifiba ko a musulunci, da lafiya ya aureta, amman ku sani in wata lalura ta
sameta yaji bazai iya zama da'ita, zai iya sauwaƙe mata. Lo kuma yaji bazai iya nema mata
lafiya ba, zai iya turota wajanmu mu saimu nema mata lafiya, inta warke kuma yazo ya tafi da
matarshi. Ku mata kun cika kacancana zancen da bai kai ya kawo ba. Ke Lami ɗauketa kuje
asibiti muji me zasu ce, da kun gama ki wuce ki rakata ɗakinta, bata da wajan zama anan, nina
haifeta bazan ƙi nema mata lafiya ba, amma bazata zauna mun a gida ba, hakkin cinta, shanta,
makwancinta a wuyan Yawale kaɗai ya rataya." Inna Lami tace.
"Amma Malam ayi haka kuwa?
"Amma yi Lami, ga wannan jaka ɗaya ce ku tafi ku ga likita, ke kuma Musina ga muttala
biyu ki riƙe, sai haƙuri. Ina kuka nace.
Baba dan Allah ka barni in zauna anan ɗin inna warke sai in koma" dubana yayi yace.
"Uwata in badan kinci darajar mai sunanki ba, dana baki kashi a gidannan ƴar jakar uba,
ana nuna muku hanya kuna bauɗewa. Banyi zuchiya ba nace.
Baba wannan yaron ya dawo yau daga birni, amma yunwa tana damunshi, kuma idanun
sahunshi du sun fashe sabida sashi a mari da akeyi a makaranta. Dan Allah ko zaka yi ma
Yawalen magana yai haƙuri ya barshi a gida ya ƙara tasawa.
"Ke uwata tashi ki tafi. Yawale shi ke da cikakken iko a kanki da yaranki, ta yaro kyau
take bata ƙarko, ke ashe in da kinsan wuyar da muka sha a almajirci zaki ɗauka baza muyi rai
bane ko kiyi tunanin iyayenmu basa ƙaunarmu ne. Gatan da za'a nuna mishi kenan, ita rayuwa
ƴar gwagwarmaya ce. Mu gashi yanzu mun gama tuni, kuma muna cin gajiyar almajirci. Lami
ɗagata ku tafi. Abincinshi ya karɓa ya fice. Mahaifita ce ta bani kaya na sake, na sake ƙunzugu.
Muna tafe ina kuka har muka isa asibitin, inna Lami sai rarrashina take yi, tana bani magana.
Bamu samu likitan ƴan yoyyon fitsari ba, ranar Laraba kaɗai ake zuwa. Haka Inna Lami ta sani
a gaba har gida. Bamu muka isa ba sai bayan magriba. Ɗakin Baba Huwaila ta kaini sabida
tsabar kara irin ta iyayenmu. Sai Baba Huwaila ce tasa akayi kiran Baba Hauwa tazo.
"Ga Musina na dawo da'ita mahaifinta yace aba Yawale haƙuri ya barta ta zauna, zamu
nema mata lafiya in sha Allah, daga asibitin ma muka wuto nan, sai ran laraba zamu koma dan
bamu samu malaman kiwon lafiyar ba." Baba Huwaila tace.
"Musinan ce ba lafiya Lami? Ai mu bamu da masaniya, kinga Yanzu Yawalen ya bar nan
ɗakin dawowarsu daga tafiya kenan shi da wanshi." Cike da mamaki Inna Lami ta dubeni.

Labarta musu lalurar dake damuna tayi. Nan suka shiga sallallami, buɗar bakin Baba Hauwa
tace.
"Ni ko ina da shawara Lami. Da kun bar Musina a gida tayi jinya, nake ganin kamar zata
fi samun kulawa a can. Yawalen ma bikinshi shingin mako ɗaya zai auri ƴar aminiyata a can
rugar malam harɗo can hayi, yau ɗinnan wanshi ya rakashi aka tsaida ranar, ga can lefen ma.
Wasu sababbin Kumbuna na gani masu hawa uku, da babba da mabi da babba, da ƙaramin na
saman sai walƙiya suke yi. Muƙut na haɗiye kibiyar kishi, idanuna suka cika tab da hawaye, ita
kanta Inna Lami jikinta ya mace, tace.
"Ayya Allah ya sanya alkhairi, wannan amarya tako yi goshi. Baba Hauwa tace.
"Ku buɗa kuga kayan ciki mana."
Inna lami ta buɗa kumbunannan, kayan alfarma Yawale ya zuba ma amaryarshi, su atamfa mai
ɗawisu, goji, banbalasta, leshi, karen miski, ɗankwali mai geza, ɗan duros, fatari, rigar mama,
jan baki, gazal, sarkar murjani, da tsakiya, agogo, da takalma masu tsini, da mayafai. Kaya
rigijibjib dai, dan banma gama kalloba, Inna Lami sai ɗaga kayan take tana mamakin irin uwar
dukiyar da Yawale ya narka, amma ya kasa nema mun lafiyata. Inna Lami tace. "Amma Hauwa
yarinyar nan a barta a ɗakinta ta zauna, zan dinga zuwa dubata, biki kuma da Yawale zai ƙara
Allah ya sanya alkhairi."
"To tunda hakan kika ce ai saita zauna." Har ɗaki Inna Lami ta rakani. Sannan ta dawo
ɗakin Baba Huwaila ta kwana. Ni kuwa ina kwance a ƙasa Yawale ya turo ƙofar ya shigo. Kuka
ya samu inayi.
"Baki ji abinda bace miki bane shine kika wani dawo ko? To ga ɗakinnan ki zauna na bar
miki. Fuu ya fice a ɗakin, kwanan damuwa da baƙin ciki nayi dare yayi mun tsayi sosai. Washe
gari da sassafe Inna Lami tayi mana sallama ta kama hanya. Ni kuwa da wankin kayan fitsari na
tashi. Labarin lalurata ya bazu har maƙobta, sai jaje aketa yi mini, Baba Hauwa tace in dena
zuwa madafi aiki har saina warke. Ina dai zuwa inyi mata gyara, akan po nake zama a koda
yaushe, sai zuwa dare kuma sai inyi ƙunzugu, kafin gari ya waye fitsari har gudu yake.
Yau Laraba, yau zan koma asibiti, amma na ƙudiri niyyar kai tsaye asibitin zani, gidan
ma bazan shiga ba tunda ba ƙaunata suke yi ba. Ina gama aiki na nufi shiyyar su Baba Hauwa,
na gyara mata ɗaki. A tsakar gida naci karo da Idi, murya ƙasa ƙasa nace dashi.
Ka sameni a bayan gonar mai gari yanzu, karka faɗama kowa" Fita nayi a gidan na nufi
bayan gari. Zama nayi a kan wani kututture ina jiran zuwan Idi"


Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman
na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas
mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata
saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin

07068606171
08104335144
08179523215



*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_



MRS BUKHARI
MATA IYAYEN GIJI


BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
( GAWURTATTU UKU)




*_GAWURTATTU UKU2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*

*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*

SAMFOTI

LAMBA TA BAKWAI



Na ɗan jima a zaune a wajan.
"Baba! Baba!!"
Na jiyo muryarshi yana kirana cike da yarinta. Ko dana hangoshi gudu yake yi sosai, yana
isowa ya faɗa jikina. Tsam na tiƙeshi fata nake dama mu dauwama a haka.
"Inna kinyi ma Baba magana bazan sake tafiya in barki ba ko?" Kanshi na shafa, nace.
Haba ɗannan ai wannan karatun da kake yi shine gatanka, kuma kayi haƙuri da duk abinda
malaminku yake yi maka, gyaran tarbiyya yake yi muku. Kul na kuma jin kace bazaka koma ba,
ka zamto mai bin umarnin mahaifinka a koda yaushe." Badan inaso ba na bashi haƙuri, nayi
hakanne dan in kore mishi damuwa, gami da ƙarfafashi, ga ƙafafunshi duk raunin ƙarfen mari,
ga datti da tsagewar fata har wani ɗoyi_ɗoyi yake yi. Ga ɗakin duhu da malaminsu ke rufesu a
ciki, ni tsorona ma kar yarona ya rasa idanunshi, dan Mahaifinmu ya taɓa bamu labarin wani
abokinsu ada lokacin suna wajan almajirci ya kasance mai yawan yin laifin da yasa kusan
kullum sai an sashi a ɗakin duhu, daga ƙarshe wannan ɗakin shi yai sanadiyyar
makancewarshi, sai gida aka mayar ma da iyayenshi shi. Babu wani mataki da aka ɗauka na
shari'a shikenan an cuci iyayenshi. Na jima ina yi ma Idi nasiha, ina kuma kwatanta mishi
rayuwa, mun jima sosai a wajan, daga baya mu kai sallama ni na nufi tashar Bodi, shi kuma ya
nufi dandali.
Kafin in isa Azare na jiƙe sharab da fitsari. Hakanne ya tilasta mun zuwa gida dan in gyara
kaina. Kayana dana bari rannan shi mahaifiyata ta ɗakko mun na saka nayi ƙunzugu, sannan
tace.
"Naji cewar wai Yawale zai ƙara aure ko? Karma ki sake kice zaki ta da hankalinki a karon
banza. Tunda kika taso kika tarad damu mu biyu da Lami a gidannan, kuma mun cakuɗe
yaranmu ta yanda mu kaɗai muke iya banbancewa. Ki sanya salama a zuchiyarki, kici gaba da
bin Yawale sawu da ƙafa. Zaki ci ribar yin haƙuri, Allah ya raya miki yaranku SU KULA DAKE."
Inna Lami ce tayo sallama ta shirya tsab.
"Tarana na fito, Musina tawo mu tafi maza, harma fa nasa tun safe Yayanku yaje ya kama
mana layi." Jiki ba ƙarfi na fito muka wuce."

In baka zuwa asibiti bazaka gane cewar ana ciwo ba. Nayi zaton masu yoyyon fitsari basu da
yawa, amma abun mamaki sai naga a ɓangarenmu munfi mata hamsin. Harda ƙananun yara da
basu wuce shekaru goma ba. Ashe nawa nafila ne, dan naga mata da dama da suke zaune
amma fitsari na gudu a ƙasa daga jikinsu. Gun duk zarni. Ƴar nutsuwa na samu. Muna zaune
ba'a soma ganin likita ba, kamar ma likitan baya nan. Sai muka ga wasu mata manya sun shigo.
Sai nuna musu mu akeyi, sunata mana sannu da jiki. Basu jima da tafiya ba Likita ta iso. Nan
kuma aka shiga bin layin shiga ganin likita. Duk wacce ta shiga sai in ganta ta fito da takadda.
Har layi yazo kaina na tashi jiki ba kwari, Ƙasimu yana hannun Inna Lami. Tare muka shiga
ɗakin ganawa da likita.
"Bismilla zauna" waje ta nuna mana.
"Musina ko zaki iya bani labarin sauyin yanayin da kika samu a jikinki kamun wannan
lalurar ta ɓullo miki?" Hawaye na soma zubarwa, nama kasa bata amsa. Likitannan ta dubi Inna
Lami tace.
"Baba tare kuke da mai gidan nata ne?"
"O'o ƴannan mu kaɗaine, ni uwarta ce, sai yaronta na goye. A Saleri take ba anan ba.
"Amma ina mai gidanta? Ai ya kamata ace shi zai rakota. Wai me yasa maza suke
gudunmu da zaran laruri ya samemu, kuma duk yawancin lalurin sune suke zama sanadiyyar
ɗaura mana, sai su dinga gudunmu in matsala ta samu. Nayi imani da shine wannan lalurar ta
sameshi, ƙarshenta ita zata rakoshi asibiti, kuma taita ƙarfafa mishi guiwa. Baba Lokacin da
tazo haihuwa a gida ta haihu ko asibiti?
"Ƴannan a gida ta haihu, bata taɓa zuwa asibiti ba dai_dai da sunan awo, sanadiyyar
wannan lalurinne yasa muka zo." Ɗan rubuce_rubuce tayi sannan tace.
"Musina kinyi doguwar naƙudane a lokacin da kika haifi jaririnki, sannan watanshi
nawa ne? Ki saki jiki kiyi mun bayani asibiti ana zuwane dan a samu mafita, ba'a ɓoye komai.
Baki ga tarin mata masu yoyyon fitsari a waje ba? Wasu ma aiki za'ayi musu, ga wasu tari da
yawa suna kwance a cikin asibitinnan an basu gado." Daurewa nayi nace. Nayi naƙuda ta kusan kwana biyu, kuma iyayen mijina sun hana a kawoni asibiti, dan
alokacin mai gidan yaso a kawoni. Ko dana haihu har akayi suna ban dawo dai_dai ba. Yanzu
wata huɗu da haihuwar tawa. Kwana takwas yau da faruwar abun."
"Okey jikin naki ma da sauƙi kuma kinyi kyan kai sosai da kika zo asibiti, ba wajan
maganin gargajiya ba. Zan ɗauraki kan wata shawara Musina mu gwada na tsawon sati biyu
mu gani. In kika koma gida kita shan ruwa kawai, ko da ƙishi ko babu, fitsarin da kike yi zai ƙaru
amma karki damu da hakan. In anyi sati biyu saiki dawo asibiti. Sannan in ba dai dare bane ya
rufa ba, ki dena saka ƙunzugu, ki dinga barin wurin yana samun iska dan gudun wari da kuma
gujema ƙwayoyin cuta masu cinye al'aurar mata wato Infection sanyi kenan a hausance.
Sannan akwai wata gidauniya data ajjiye mana forms guda hamsin, kuma ga mata masu lalurar
fitsari kawai suka bada umarnin a raba. Wannan gidauniyar zata ɗebi mata masu lalurar
fitsarine ta horar dasu kan sana'a irinsu ɗinki, haɗa mandula, da sabulun soda, da omo na gari,
da man shafawa. Kuma a kyauta zata horar daku, sannan ta raba jari gareku in zata yaye ku.
Ga Form nera nera biyar zaki bayar a baki form. Za'a gudanar da aikinnan a filin firamare tamu,
ina fatan zaki zama ɗaya daga cikin waɗanda za'a horar ko Musina? Bana fatan mijinki ya
hanaki wannan abun kiyi ƙoƙarin kasancewa ɗaya daga ciki, dan zai taimaka miki ki tsaya da
ƙafafunki." Ajjiyar zuchiya na sauke, jakata na buɗa na ciro nera biyar kamar yadda tace. A

gabanta ta ajjiye Form ɗin tace.
"Bari in cike miki, sannan ɓangaren wacce sana'a kika zaɓa?.
Likita aina iya karatu da rubutu, na ajimi da hausar boko nayi firamare a makarantar
gwamnati ta Azare." Murna naga wannan likitan nayi tace.

5 / 21