Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
MATA..
IYAYEN..
GIJI
DAGA ALƘALAMIN
BADI'AT IBRAHIM
(MRS BUKHARI)
(GAWURTATTU UKU)
( WANNAN LITTAFIN BA ƘIRƘIRARREN LABARI BANE. LABARINE DAYA FARU A ZAHIRI.
LABARINE MAI CIKE DA ƊUMBIN DARASI. DUK WATA MACE DA TACI KARO DA
LABARINNAN, TAYI ƘOƘARI TA BIBIYESHI HAR ƘARSHE. ZATA AMFANA DA ABUBBUWA
DA DAMA.)
LAMBA TA ƊAYA
SAMFOTI
SADAUKARWA:
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN KACOKAM ZUWA GA JAM'IYYAR MATAN AREWA.
ALLAH YA ƘARA ƊAUKAKA WANNAN ƘUNGIYA.
GAISUWA: Gaisuwar ban girma a gareki, shugaba uwa jagorar mata. ( Hajiya Rabi Saulawa.
President ta jam'iyyar matan Arewa) Ina miƙa saƙon gaisuwata a gareki da ahalin gidanki baki
ɗaya.
JINJINA:
ina miƙa jinjinata ga dukkan wata uwa ta faɗin duniya baki ɗaya. Mata iyayen giji.
ƘAWAYENA:
Maman Khairat. ( Ke alkhairi ce a rayuwata)
Maman Yaseer ( ƙawar arziki)
Ummu maheer miss Green ( Mai farar zuchiya)
Ummu Affan Fatima Sunusu Rabi'u. ( Ke ta musamman ce)
Hajjon Bakori ( Ƙawar amana)
Anty Laila Ali Othman ( matsayinki da banne)
Ummu Affan
Da sauran ƙawayena da ban kira sunanku ba. Kuna da yawa ne.
GAISUWA ZUWA GAREKI UWAR ƊAKINA:
ANTY HADIZA BARA'U GIDAN IKO. SARAUNIYAR MARUBUTA, INA JINJINA BAIWARKI,
KUMA INA AMFANA DA RUBUTUNKI"
KATSINA
ƘARAMAR HUKUMAR BAKORI:
LAILA:
Wasu shekaru da suka shuɗe a baya can_can:
So! So!! So!!! Itace igiyar da take zarge da ko wanne ruhi. Wannan igiyar ita ta jefani a cikin
gadar da taima rayuwata mugun bugun da saida ta haddasa ma rayuwata karayar da babu
maɗorin da zai iya kawo mun ɗauki. Ashe na shiga ban ɗauka ba baya fidda ɓarawo, tunda so
ba goriba bane balle kace zarenta iyakar haƙori zai zarge ma, in ka gaji kayi fatali da'ita. Dama
ace ina da ƙafafun da zan iya shure so, ko kuma sandar da zanbi so da mugun gudun da saina
halakashi kowa ya ma ya huta. Akace so Zuma ne, ni dana sha sai ya zame mun farar guba
mai ruguza gangar jiki, so ya maisheni nakashashshiyar ƙarfi da yaji. Kallon mai lalura akeyi
mini, har wasu na danganta hakan da shafar junnu, ba su son so bane yabi dare ya durƙusar
dani ba. Na tattare kaya na daga majalisar so, ni da wannan majalisar haihata_haihata.
Ƙunshin kayana dana ƙunso a ɗankwali mai ɗawusu na yar a filin tsakar ɗakin mahaifiyata.
Idanuna caɓe_caɓe da hawayen daya haɗu ya dame da farin kwallin dake idanuna. Hakan ya
saka fuskata ta ƙara yin baƙi. Mahaifiyata ta dubeni tace.
"Karfa kice mun yaji kikayo da yamma sakaliya haka Laila, baki da hankaline, ko so kike ki
zubar mana da mutunci a gari, ince dai surukanki, da facalolinki basu san yaji kika yo ba ko?"
Cikin in_da_in_da nace."
Ba yaji nayo ba Inna, Auren Shehu ne na dena. So yake ya kashe ni Wallahi".
Bub, ta bige mun bakina da bayan hannunta, take bakina ya fashe ya soma zubar jini. Ga
tsohon ciki a jikina haihuwa ko yanzu ko anjima.
"Kul kika ce zaki toni asirin mijinki, babu kyau yin hakan sam, labule ai asirin ɗakine. Ki
ɗauki ƙunshin kayanki, tunda duhu ya soma rufawa, ki yi komawarki ɗakinki tun kafin mahaifinki
yazo ya tadda ki, wallahi bazaki ji da daɗi ba. Ba tsohon ciki gareki ba, wallahi ko haihuwa zaki
yi yanzu, saiya saɓa miki. Kuma kinsan baki da wajan zama a gidannan ai. Shashashar kawai,
yara basu san darajar aure da miji ba, sai shirme, da bankaura kaɗai suka iya a gidan mutane."
Ni dai ina tsaye, sai shirɓine hawaye nake yi da bayan hannuna. Muryar mahaifina muka jiyo
yana kwaɗama Innata kira.
"Ke Ta Asibi, Ta Asibi ke" Mahaifiyata sabida kaɗuwa kasa amsa kiran tayi. Labulen ɗakin
ya yaye, ya doge a baƙin ƙofar, yana kallona.
"Dan ubanki ashe da gaske ne ke aka gani ɗin kenan?" Ƙunshin kaya na dake ƙasa ya
duba, ya ɗago ya zuba ma mahaifiyata idanu. Dani da'ita duk kawunanmu a sauke suke.
"Ta Asibi, yaji Lailan tayo shine kika bata wajan tsaiwa, kin tsaya sauraronta kenan ko,
sabida zaki bata mafita?".
"A'a Malam Haram giya a gidan liman. Ban tsaya naji komai ba, kuma yanzu zata koma
dama. Laila ɗauki ƙunshin kayanki ki koma ɗakin mijinki, aljannarki tana ƙarƙashin tafin ƙafarshi,
kiyi mishi biyayya. Duk macen duniya da kika ga tayi lib a gidan mijinta, haƙuri take yi, kuma
tana duba makomar rayuwar yaranta. Aure wata tara, baki taɓa zuwa ganin gida ba sai yaji?
Wallahi in kika sake yin wannan kuskuren ni da ke ne, tunda ko saɓani baki taɓa ganin mun
samu da mahaifinki ba, ballantana harta kaini ga yin yaji." Cewar mahaifiyata kenan. Da jin
muryarta cike take da tsantsar tausayina.
"Au jawabi ma kike yi mata? Bari kiga."
Shigowa mahaifina yayi, banyi auneba ya rufeni da duka takota ina. Ko tausayin abunda
ke ƙunshe a cikina baya ji. Wai me yasa maza suka ɗauki mace tamkar baiwar da su ka siyo a
kasuwa da silalla danta bauta musu ne?" A guje na fita da ƙunshin kayana, nama mance cikine
a jikina, tsabaragen kaɗuwar da nayi. Da Kishiyar mahaifiyata naci karo a tsakar gida. Ina wuce
ta nayi da mugun gudu. Mahaifina ya biyoni da mugun gudu shima har waje. Gudu nake yi
sosai yana bina, ina kukan fitar rai, sai da mu kai nisa, sai naga mahaifina ya dakata., Yana
nuna ni da karar dake hannunshi"
Tsaiwa nayi nima na dinga sauke numfashi, ga wani irin haki da yake ta taso mun, irinna
masu tsohon ciki. Haka naita dawowa baya cikin jan ƙafa, har zuwa tashar (Bodi) Keken shanu.
Malam zaka ƙarasa Ƙauyan unguwar Alƙali?"
Kauyen Unguwar alkali dake qarqashin karamar hukumar Bakori ta jahar katsina. ya kasance
kauyene daba makarantar boko, babu ta addini, ba su da wutan lantarki, ba asibiti, ƙauyene dai
irin ƙayau ɗinnan zamu iya cewa. tunda ko ilimin addini bai wadacesuba, sannan basuda
wadataccen ruwa haka suke rayuwarsu. A qauyen sau daya ake aurar wa shine lokacin kaka wato hatsi yadawo gida, suna noma sosai
da sosai. In aka tashi biki, Abokan ango suke girka abincin daza aci aranar daurin aure wannan
al adarsu tun iyaye da kakanni in aka kai amarya da yamma, to adaren ranar akwai wasan da
suke yi tsakanin abokan amarya, da abokan ango, Wanda abokan ango zasu zuba kudi, na
amarya ma zasu zuba. Wanda nashi yafi yawa to shi ya ciri tuta, za kuma a yi mishi kyauta ta
kayan noma, ko buhun masara, ko dawa, ko gero. Wannan kenan.
Dubana matuƙin bodinnan yayi, yace.
"Gaskiya bazan ƙarasaba, iyakacina Rimi nan dandali, anan zan tsaya." Bance mishi
komai ba na shiga cikin Bodinnan na zauna. Mata ne su biyu a cikin Bodin, ko wacce da goyo a
bayanta. Gaggaisawa mu ka yi da matannan. Sannan mu ka ci gaba da zaman jira, saida muka
cika mu goma cib matuƙin Bodin ya ja linzamin bakin shanun suka soma tafiya." Tafiyace mara
sauri sam, dan hanyace mai cike da ciyayi, da gonakai, da kauci. Baka jin ƙaran komai a hanya,
sai haushin karnuka, da kukan kwaɗi, da kukan gyare. Da duk wata dabba da dare ne yake
zama rana a wajanta. Tsoro ne fal raina, dan muna fama da mayu sosai. Munyi tafiya mai ɗan
karen nisa kafin muka iso Rimi dandali. Sai lokacin na sauke ajjiyar zuchiya, dan ina jiyo
hayaniyar samari da ƴan mata, ga hasken wutar kara ina hangowa. A hankali na sauka, dan
jikina yayi mugun laushi, ga ƙafata bata da wani ishashshen lafiya guda ɗaya, ta ɓarayin
hannun dama. A bakin dandalin na tsaya, wajan masu sai da ƙwalam da maƙulashe. Dangin
Algaragis, carbin malam, hana kwalla, alawar ɗinya, ɗan ta matsitsi, kwaskwaro, kantun riɗi,
tsami gaye, ƙurmus, hallaka kwabo. Ga ɓangaren kuma masu, ɗan gauda, bagalaji, tako, rama,
dinkim, ɗan malele, wara, da sauransu.
Ke bani Tako na sile biyar."
Hannu nasa a cikin lalitata na kwaso tsaabar dake ciki, na ƙirga tsabobinta sile biyar na
bata, ta zuba mun tako a leda, harda ƙara mun mai da albasa mai lawashi." Tako wani abin
maƙulashe ne na katsinawa, anayin tako ne da kofaton dabba, saniya, rago, akuya. Katsinawa
suna mugun son tako. Duk da gidan da ake sarrafa tako baya ko iya shiguwa ta daɗi tsabar
wari. Ina tafe ina cin tako na, na ɗaura ƙunshin kayana a kaina. Wani ruwane, naji yana bin
ƙafata dalalala, kuma kamar ruwan yana da ɗan yauki. A haka dai naci gaba da jan ƙafata a
hankali. Wata ƙatuwar mage ce tazo ta wuceni. Gabana ya yanke ya faɗi, yaron dake cikin
cikina shi kanshi saida ya zabura.
"Laila Uwar maza" wannan magen naji ta faɗa, da wata dattijuwar murya. Nan na ya da
ƙunshin kayan nawa na ari na kare. Gudu nayi sosai, ta tsakiyar maza masu kwana a ƙofar
gidajensu na ratsa na shige gidan aurena a guje." Tsattsallake mata, da yara, dake kwance a
tsakar gida nayi. Dan tsakiyar lokacin zafi muke yanzu, ɗaki baya shiguwa, garin Katsina
ƙasace mai zafi, kasancewar tana maƙwabtaka da ƙasar dake da sahara." Garam na tura
ƙyauran ɗakina na shiga."
Shehu na gani a kwance a maulidi na, +gado mai rumfa) Babu ko wando a jikinshi, ya shirɓine
jikinshi da man shafawa mai gurguwa, sai wasa da jikinshi yake yi, a ƙoƙarinshi na son gamsar
da kanshi." Kuka na rushe dashi kawai, ga wani irin kaɗuwa da hantar cikina take yi, marata ma
sai tsungulina take yi. Da sauri Shehu ya diro a gadonnan, ya riƙoni yana ɗan jijjigani.
"Manene Laila, ko Babane ya biyo ki da gudu har nan?
Bai bani zarafin yin magana ba, ya shiga laluben hakkinshi. Tsabar takaici, ban iya cewa dashi
komai ba, a halin da nake ciki ya shiga biyan buƙatarshi, wanda hakan ya ɗebemu mintici da
dama, marata ce ta shiga ciwo ganga_ganga, bayana da ƙafata mai lalura sai amsawa suke yi.
Nayi yunƙurin ture Shehu amman na kasa. Ƙara na saki mai amon da sai da kowa ya jiyo. Da
sauri Shehu ya sake ni, ya rarumi wandonshi da ƴar shararshi ya saka.
Wayyo zan mutu, Shehu ka kirawo mun Matar malam, haihuwa zanyi, Shehu zan mutu." A
gaggauce Shehu ya fita tsakar gidan, ya barni a kwance a leda ina juyin azaba."
Mrs Bukhari ce
Ku kasance tare dani, dan karanta wannan littafin mai ɗauke da salo irin na rayuwar iyayenmu
ta shekarun baya. Labarine mai ɗumbun darasi. Duk macen data karanta littafinnan na tabbatar
zata ilmantu da ilimi mai tarin yawa.
Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman
na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas
mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata
saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin
07068606171
08104335144
08179523215
*GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a
wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi
babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi
ce sannan ta musamman._
*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi
alfahari da su._*
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka
bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023
SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
*Mrs Bukhari ce *
MATA...
IYAYEN..
GIJI
BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
( GAWURTATTU UKU)
LAMBA TA BIYU
SAMFOTI
*_GAWURTATTU UKU2023_*
*_TALLAH TALLAH TALLA️️️️️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU
GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI
ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES
DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._* *_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA
TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA
KUDIN KI IYA SHAGALINKI_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN
UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU,
INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU
RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER
DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA
WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR
COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN
ZO _*
MATAR MALAM:
Fitowarta kenan daga sakaki ( Bayan gida) ta jiyo ihun Laila. Sai kuma taga Shehu a ruɗe ya
fito.
"Shehu lafiya, Laila ta dawo ne, ni naji ihu ko?"
"E matar Malam, naƙuda inaga ta soma, sai juyi take yi aƙasa." Butar hannunta ta ajjiye
tace.
"Ka tashi Mai riga, da Iyami maza. Bari ni in soma zuwa." Tana kaiwa nan ta shige ɗakin
Laila, shi kuma ya wuce Shiyyar su Baba Mai riga mahaifiyarshi.
"Baba Mai riga, Baba"
"Kaik waye wannan haka nenene?"
"Shehunki ne Baba mai riga " Da sauri ta miƙe zaune, tana mutstutstsuke idanu.
"Yaya dai Shehu, ko duk a kan tafiyar Lailan ne? Infa iyayenta na gidi ne, to wallahi cikin
darennan zasu dawo da'ita ko ka gansu asubar fari, abun kunya kuma ta riga data jama kanta,
harfa yaran data haifa za'a iya goranta musu in sun girma. Kama kwantar da hankalinka kaji
ko?" Shehu ya sosa kai yace. "Tama dawo, naƙudace ta tasan mata Baba. Yanzu haka matar Malam na kanta." Ba
shiri ta miƙe daga ita sai ɗaurin gaba, mayafi ta jawo a igiya, ta wuce ta Bar Shehu tsaye a
wajan. Iyami, da Laure surukanta, facalolin Laila ta taso, suka shiga ɗakin Lailan a tare."
Laila;
Ina zaune dirshen a kusa da kwallayen dake jere hawan hawa a ɗakina, sai yarfe hannaye
nake yi, idanuwana sunyi ƙwala_ƙwala, jikina kuwa a jiƙe sharkab yake da ruwan jiɓi."
"Ki durƙusa Laila, ba zaki zauna dirshen haka ba, saiki kashe abunda ke cikin naki." Da jin
haka ba shiri na durƙusa, hannayena duka biyun a dafe a ƙasa. Kafin kace me, ɗakinnan ya
cika da mata, duk sun tsaya akaina. Ga wasu a barandar ƙofar ɗakin, duk sun tare mun iska.
"Iyami maza ki samu Shehu, yaje ƙwar gida ya taso Malam yai mata rubutu tasha, sai kiga
yanzu ta samu kai. Sannan yaje gidan Unguwar zoma ya tado ta itama. Da hanzari Iyami ta
fita, ta faɗama Shehu saƙon da aka bata ta bashi. Da sauri ya fice zuwa waje, ita kuma ta dawo
ciki. Kamar minti talatin haka, ina tsaka da cin kwakwa. Shehu ya kawo rubutunnan, Unguwar
zoma itama isowarta kenan. aka ɗirka mun, amma shiru kake ji. Awa ɗaya awa biyu. Na gama
galabaita na fice a duk wani hayyacina. Sai sannu suke yi mun. Ni kuma haushi suke bani ma.