Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book Compelet

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   9 / 24

24K to 27K   out of 70.8K words

yayi yinƙurin taya ni. Tun sassafe na kira Anty Use da Anty Karime a waya na sanar
musu da batun abincin jeren, sun ce zasu zo da safen su taya ni aikin. Kuma na aika ma
Sabira. Zuwa ƙarfe taran safe duk suka hallara, har mun soma tuyan kaji, Sabira kuma tana
zaune tana gyaran kayan lambu. Ganin su Yaya Use ne yasa Hindatu zuwa ta kama mana
aikin. Kayan miya ta gyara yara suka tafi kai niƙa, ni kuma ina gefe ina ɓarar maggi ina cije leɓe
na ciwo.
"Tani ki je ki tambayo Rammai me za'a girka ma baƙin kinga na gama da suyar naman." To
kawai nace, na yi sallama a ɗakin Hindatu Baba Rammai na can. Bayan mun gaisa nake
tambayarta mai za'a girka"
"Wannan ai ya rage naki Tani. Komai na hannunki du abunda kuka san zai burge baƙin sai kuyi.
Dan Allah ayi abinci mai daɗi dai ga kaji nan wadatattu mutanennan masu arziki ne sosai, a
kamanta musu."
To shikenan Baba Rammai"
Fitowa nayi na same su.
To tace mu yi koma meye, ya kuke gani me za'a girka?" Yaya Use tace.
"To ni dai ban san kalolin abincin zamani ba, ban iya ba ko ba gaskiya ba, nafi ƙwarewa a
abincin gargajiya." Yaya Karime tace.
"Nima dai wallahi ko jallof ɗin taliya ban iya girkata ba, in nayi duk sai ta raɓe a cikin romon"
Sabira tace.
"Babu damuwa ni na iya, sai ku taya ni muyi. Party jallof rice za mu yi, da pepper chicken, sai
ayi musu coslow tunda akwai kayan lambu da yawa" To da taimakon Sabira data kasance kan
gama komai muka kammala girke_girken mu. Ni dai bani da manyan kuloli na zamani,
Hajiyayye nayi_nayi da'ita ta ba da nata a zuba abincin taƙi, daga ƙarshe da Baba Rammai tasa
baki sai kawai ta fashe da kuka ta kuma rantse ba zata bayar ba. Sai Sabira ce ta je gidanta ta
ɗakko mana manyan kuloli na Alfarma, tsabar ƙyalli ras nake ganin fuskata a kular nan. Bayan
mun kammala komai Baba Rammai tace a kai ɗakin Hindatu a ajjiye abincin. Yaya Use ce ta
shigar da komai, a tsakar gidan suka zauna suna cin nasu abincin. Ni kuma na shiga wanka, ina
fitowa na shiga ɗaki na saka riga da zani na atampa wanda Habiba Bala ta bani. Babu abinda
na shafa a fuskata. Dirin motoci da ihun yara na jiyo a dai_dai window na suna faɗin
"Kayan amarya ek_ek" Sai naji zuchiyata na son leƙawa in ga waɗanne irine matan da suka
tawo jeren. Ai kuwa da sauri na matsa bakin windon na leƙa. Wasu manyan mata ƙosassun ƴan
boko na gani a tsaye a bakin motar kaya, sai turanci suke yi a tsakaninsu da juna. Kaila na
hango cikin girmamawa ya isa garesu, sai ɗan guntun turanci suke yi mai, shi kuma yana zare
idanu gudun kar su kai shi maƙura, dan ɗan turanci nashi bai wuce cikin cokali ba, shima ya
iyane a sanadiyyar zaman shagon wani inyamuri a bayan banki, shagon takalma da jakunkuna.
Kamar akan gidan suke yi mishi magana dai, dan naga suna kallon gidan suna yamutse fuska,
ajjiyar zuchiya na sauke na bar windon. Su Yaya Use ne da Sabira suka shigo, a tsaye suka
ganni da wannan riga da zani na atampa, rigar tayi mun yawa har wuyan na zamewa.
"Baƙin ku sun iso Tani, ni naji sai turanci suke ta zazzagawa a waje." Kafin in kai da magana
muka jiyo sallamarsu da wasu muryoyi masu daɗi, daga ɓangarena Yaya Use ce ta amsa musu.
Suka ƙarasa zuwa cikin gidan Baba Rammai da Hindatu suka tarbesu. Daga haka muka soma
jiyo muryoyin maza da shige da ficensu. Yaya Use ce ta fita, ni ko waje na samu na zauna ina
fama da marurun zuchiyata. Bata jima ba sai gata ta shigo.

"Tabb lallai Kaila ya ɗebo matar da tafi ƙarfinshi gaba da baya. Yarinyarnan da zai aura daga
gani ƴar masu dashi ne. Kunga kaya irin na gani da faɗe kuwa. Hmmm daga kamfanin da aka
sai kayan ma aka tawo da ma'aikata maza su suke gyara ɗakin. Ji nayi wata Baturiya tana
faɗama Rammai." Baki ni dai na taɓe abina. Baba Rammai ce ta ɗaga labulen ɗakina tace. "Ai ya kamata ace kin zo kin tarbi baƙi ko Tani? Sannan ki basu abincinsu sun shawo hanya"
Da To na bita tare da yunƙurawa na tashi tsaye.
"Muje in taimaka miki ke da ba ishasshiyar lafiya ba" Harara Baba Rammai ta sakar ma Sabira,
taja tsaki ta saki labulen tayi gaba abunta. A ɗakin Hindatu aka sauƙi baƙin, Hajiyayye tace
dangin kishiya basu isa sun zauna a ɗakinta ba. Tun muna aikin abinci tayi ficewarta daga
gidan, amman ba zata wuce maƙota ba gidan ƙawayenta. Da sallama muka shiga cikin abun
mamaki a cikin baƙin babu wacce ta amsa sallamarmu sai Yes kawai suka ce mana. Dauriya na
aro na yafa na zauna aka gaggaisa, Baba Rammai ta nuna ni da cewa.
"Hajiya kinga wannan itace uwar gidan Kaila. Amman bazawarace ya aureta." Naji zafi sosai,
baƙin a wulaƙance suka shiga bina da kallo, ni ko murmushi nake yi, abinci muka gabatar musu
da abun sha, kana muka fice a lokacin idanuna ya cika tab da ruwan hawaye. Sai zuwa yamma
lis suka gama abinda ya kawo su, su kai mana sallama. Sai magriba su Yaya Use suka tafi
bayan sun yi mun girki suma sunci, Sabira kuma ta ɗan jima da tafiya itama zata je ta kula da
nata iyalan. Da su Sulaiman ta sake tafiya. Ina zaune muna cin abinci ni da Hauwa nake jiyo
hayaniyar Kaila da Hajiyayye a tsakar gida, wannan karon hayaniyar tayi tsamari, dan ina jiyo
yanda Kaila ke kutuntumama Hajiyayye ashariya, dama Kaila gwanine wajan rashin daraja,
akwai shi da ruwan ashariya. Da ƙyar dai fitinar ta lafa ni ko ina ɗaki a kwance abuna ban ko
leko ba ƙofata ma rufe take na saka sakata. Haka ranaku su kai ta shuɗewa ana saura kwana
uku biki, gida ya cika da ƴan Wudil dangin mahaifin Kaila, da ƴan Akwanga dangin Baba
Rammai. Ƙannen ƙanin Mahaifin Kaila ne kacal suka sauka a ɗakina, yara kuma suna gidan
Sabira acan suke kwana. Aikin girki kuwa nice gaba_gaba taimakamun kawai jama'ar bikin ke
yi, amman in ban ɗaura sanwa ba babu wanda zai fito ya ɗaura. Ana jibi ɗaurin aure aka tashi
mutum huɗu biyu daga ɓarayin Baba Rammai , biyun kuma ƴan Wudil ne domun kai akwatin
Amarya wanda dama ita yaba kuɗin ta sai komai domin irin yanda take ba gaye hakkinshi.
Sassafe suka kama hanya domun a ranar suke son dawowa, basu suka shigo gida ba sai taran
dare. Washe gari aka shiga hidimar biki gadan_gadan wanda a ranar Kaila da mutanenshi suka
nufi Zaria acan zasu kwana in an ɗaura aure su tawo da Amarya da danginta. Ranar juma'a
gida ya cika da maƙota ƴan uwa da abokan arziki duk sun hallara, Yaya Use da Yaya Karime
tun taran safe. Mu mu kai ruwa mu kai tsaki a girkin ƴan biki. Tuwon shinkafa miyar taushe mu
ka yi, sai jallof ɗin shinkafa da kaji da akai ma masu kawo amarya da abokan ango. Saye nake
cikin wani lashi ɗinkin doguwar riga, yana daga cikin kayan da Habiba Bala ta bani, babu ko
kwalli a idona balle in shafa mai. Yara kuma nasa musu kayan sallansu, abunka da yara sai
murna da ƙiriniya suke ana biki a gidansu. Hajiyayye ma ɗakinta cike dam da ƴan uwanta da
ƙawayenta na anguwa. Taci ado kamar itace Amaryar, ƙawayenta sai koɗata suke faman yi, an
yi saloon, an yi ƙunshi, duk da na sallah da tayi bai gama fita ba amman akai akayi mata, har
me kwalliya ƙawayenta suka ɗakko mata. Misalin ƙarfe shida da rabi na yamma motocin kawo
Amarya suka soma tsayuwa a dai dai bakin windo na. Cikin ƴan mintuna yiriri_yiriri ya shiga
tashi a kofar gidan. A wannan lokacin ina kwance ina hutawa ne, su Yaya Use kuma suna cikin
gida suna rabon tuwon dare. Tuwon masara miyar bushasshiyar kuɓewa su ka yi. Ina jiyo takun

dangin Amarya, a kunnena najiyo wata ƴar tsohuwa tana faɗin ki shiga ɗakin ki da ƙafar dama,
ki yi adda'a kamar yadda muka shigo dake gidannan Allah yasa sai dai a fitar da gawarki.
Murmushi kawai nayi ina dafe da cikina dake mun juyin waina. Bayan hayaniyar mata ta lafa ne
na soma jiyo hayaniyar Kaila da abokanshi. Ina jiyo sallamarshi Amman bakina yayi nauyi na
kasa amsawa sam.
"Shanono ki sa yara su shigar mana da Abincinmu cikin gidan Tanimu acan zamu ci, yanzu dai
sallah zamu je mu yi" Da ido na bishi, sai naga kamar an sake Kaila tsabar yanda yake ƙyalli da
sheƙi, saye yake da farar shadda sol sai maiƙo shaddar take faman yi, ɗinkin malum_malum na
matasan zamani ce a jikinshi, kanshi saye da hula zanna bukar, ƙafarshi saye da takalmi haf
koba baƙi, ga baƙin zobe ga baƙin agogon fata, idanunshi kuma saye da sabon farin tabarau,
sai ƙamshin shi na tun asali yake yi ƙamshin turaren lailatus sahra, duk sanda na shaƙi wannan
ƙamshi sai ƙwaƙwalwata ta shiga tariyomun faifayin bidiyon irin romon soyayyar da muka
dangwala ni da Kaila. Kai kawai na ɗaga mishi halamar naji, shi ko ko a jikinshi bai damu da
yasan meke damuna ba ya saki labulen yayi gaba. Zafafan hawayene suka gangaromun,
sallamar Hajiyayye ne yasa nayi saurin goge fuskata, na amsa mata sallamarta. Sai gata ta
shigo cikin wata jar sabuwar atampa mai kyau ta sake shiga a karo na uku. Hannunta riƙe da
ƙananun bokatan roba har uku. A bakin katifata ta dure mun.
"Umman Sulaiman ga naki ke da jama'arki, dangin Amarya ne suka bamu"
An gode Allah ya ba da zaman lafiya" Baki ta taɓe tace.
"Hmm har wani roƙon zaman lafiya ma kike yi? Ni ko zuchiyata saura ƙiris ta ƙone ma baki
ɗaya. Kaila ya je ya kwaso mana ƴar gidan masu kuɗi." Murmushi kawai nayi mata. Ta ja dogon
tsaki ta fita abunta, tare da Yaya Use su ka ci karo, ita zata fita, ita kuma zata shigo.
Ga kayan cin_cin nan in ji dangin Amarya, ku ɗibi naku" Bubbuɗe robibin tayi. Ɗaya cike da
cin_cin ɗayar cike da alkaki, ɗayar cike da nakiya sai ƙamsin kayan ƙamshi take zabgawa. Leda
Yaya Use ta ɗakko ta zuba nata dana Yaya Use, ta ƙulla na Sabira dana Inno, sauran ta bar
mana ni da yara. Ƴan uwa masu daɗi sai bayan isha suka mun sallama suka tafi, bayan Yaya
Use ta sallami Kaila da abokanshi da abinci. Ni ko ina yin sallar isha na ɗan ci tuwo na ba
Hauwa taci ta ƙoshi, dani da'itan a wajan mu kai bacci ko hannu ban wanke ba, balle in wanke
bakina. Dake na gaji ainun ban farka ba har sai da asuba, kuɗin cizo sun sha jinunmu sosai
hakama sauro. Mayar da Hauwa nayi kan katifa ni kuma na fita dan ɗauro alwala. Mata ƴan biki
duk sun firfito anata alwala, nima alwalar nayi na gabatar da salla, kana na fita na bi ɗaki_ɗaki
ina gaisawa da dangin Kaila. Da gari yayi sha kuma na dafa tea na toya wainar ƙwai na dangin
Amarya. Yaran ƙanwar Baba Rammai ce suka kai musu. Mu kuma ruwan bunu muka sha da
biredi. Ni dai ina gamawa na yi komawata ɗakina. Yara basu suka shigo gidan ba sai wajajen
goman safe Sabira ta tusosu gaba suka tawo. Ina zaune zaman taɓaro a ƙasa Suka shigo.
"Uwar gida sarautar mata, banga kin yi wanka kin fito shar dake ba. Na hango wulgawar
Hajiyayye ta sha kamfala da ɗankwalin ashoke, ke ko ina ƙunshe a ɗaki. Balaraba ce ta zauna
kusa dani.
"Umma ina kwana?"
Lafiya lau ƴan albarka" Nan suka shiga gaisheni ɗaya bayan ɗaya.
Maza ku shiga cikin gida ku gaishe da iyayenku." Da sauri suka fita harda rige_rigensu. Ledar
kayan filawa da Yaya Use ta ƙulla mata nata na jawo na miƙa mata.
Ga naki kayan garar Amaryar kwa tauna ke da yara. Ina so in faɗa miki ma jibi zamu yi tafiya

dasu Inno zuwa Shanono can garinmu, bikin ƴar ƙanwar Inno."
"Dukka wannan garar amarya leda guda haka, ai yayi yawa Tani. Murmushi nayi nace.
Haba Sabira ai ko duka na zuba miki kin cancanci hakan ne. Kuma kinga fa bokatannan cike
aka kawo mun, wannan amarya akwai maiko a hannun iyayenta gaskiya " Dariya tayi mun tace.
"Gaskiya kam ai ko da ganin danginta, da gani basu san meye talauci ba ma sam. Batun
komawar yara makaranta fa? Naji ana sanarwa a gidan rediyo cewar ran monday makarantun
gwamnati zasu koma karatu, to yaran zaki barsu a wajena amman ko? In an Koma makaranta
sai su soma zuwa kafin su dawo, ga islamiyya ma ran monday zasu koma" Ni kam babu abinda
zance da Sabira da mijinta sai dai adda'ar kairiro, domun maƙotane na gari sosai. Shi ya soma
kama hannun su Sulaiman ya jefa su a makarantar gwamnati mai suna islamiyya pilot primary
school makaranta ce ta gwamnati, to bayan yayi hakan ne, Kaila ya sai musu fensir da
takadda...........✍
MRS BUKHARI
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FADO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 8



_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_

_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani
supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_

*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*


*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*

https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S

*ADDRESS*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224

*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN
KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK
MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*

*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA
ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*

*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA
ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI
WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*

*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*

*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*

sannan ina harkar
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*

KAMARSU

*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*

DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE

Hatta inifom mijin Sabira ne ya ɗinga musu, da basa zuwa ko ina sai gararamba a unguwa.
Haka zalika shi ya sanyasu a islamiyya irin ta cikin anguwa, duk sati suna tafiya da nera
hamsin, shima wannan ko da Kaila yaga suna zuwa bai ce dani komai ba, nima ban tanka mishi
ba. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Sabira a karo na barkatai nace. To zan bar miki su, zan haɗo inifom ɗinsu Sani zai kawo miki. Zaki sha bari_bari kenan bakin ki
sai yayi tsini ashe kafin in dawo. Dariya tayi tace.
"Su Mustapha da Umar fa da kike ganinsu wallahi sun fi Shafi'i da Sulaiman rigima, Sani shi bai
da yawan ƙiriniya magana ma bata isheshi ba. Kullum a cikin raba dambe nake."
Hmm suma ko da yaushe aikin Kenan." Mun jima muna tattaunawa kafin muka fita domun ɗora
girkin rana. Ƴan Wudil kam har sun fito tsab zasu koma, ƴan Akwanga suma ina ji suna cewa
da sun yi azahar zasu tafi. Sallama nayi ma ƴan Wudil, muka shiga hidimar abincin rana. Girkin
dangin Amarya daban Sabira tayi shi. Tuwon shinkafa miyar ganye tayi musu da kaji. Ita tayi
komai da komai, kuma ta ɗauka ta kai musu. Bata jima ba ta fito. Ƴan Akwanga suna cin abinci
suma suka kama gabansu, harda Baba Rammai dan an bogo waya an yi musu haihuwa. Sabira
da Hindatu ne suka yi wanke wanke da gyaran gidan. Fes suka wanke tsakar gidan yayi kyau
sosai. Misalin huɗun yamma muna tsakar gidan ina ɗaura sanwar miyar dare. Sai ga dangin
Amarya su biyu, sun sa Amarya a tsakiya. Suna zuwa in da muke suka tsaya.
"Bayin Allah muna neman ɗakin uwar gidan gidanne, zamu kai amarya bisa doron al'ada."
Sabira ce tayi musu jagora zuwa ɗakina ta nuna musu taburma. Ni kuma na kirawo Hajiyayye
da Hindatu, tare muka shiga ɗakin, na shiga na same su sai yamutse fuska suke yi, ba shakka
zarni ne ya ishesu. Bayan an yi ƴan gaishe_gaishe wata farar mata tace. "Wacece uwar gidanne a cikinku?" Hindatu ce ta nuna ni tana dariyar ƙeta, ta nuna Hajiyayye a
matsayin ta tsakiya. Baki suka sake su kansu, ƙila sun yi tunanin mai aikin gidan Kaila ce ni,
dan sun gagganni face_face ina shan uban aiki kamar jakka tun zuwansu."
"To uwar gida kece babba ga Bilkisa mun kawota domun ku gana, ba Domin mun kawo muku
amanarta ba, amanarta na hannun wanda ya rabota da garinta da ahalinta. Bilkisa ki buɗe
fuskarki abokan zamanki su ganki ki gansu" Bilkisa tana saye da wata lafaya mai adon duwatsu
faca_faca hannu tasa tayi baya da mayafin. Wallahi bani ba hatta Hajiyayye da take jin ita
shahararriyace sai da ta ƙware. Bilkisa gaskiya tana cikin sahun kyawawan matan hausa fulani,
uwa uba gata da haske sosai, ga iya kwalliya da zabin kalar daya dace da launin fatarta.
"Ina yininku Anty da Anty?" Wani ƙwallon kishi na haɗiye nace.
Lafiya lau

9 / 24