Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN
KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK
MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA
ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA
ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI
WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE
"IYALI kake magana, wannan ƴar marasa tarbiyyar itace iyalin? A zafafe take magana cikin
rufewar idanu. Bilkisa wacce tunda suke abinsu bata ce komai ba, sai yanzu da taji ana neman
taɓa mutuncin iyayenta shine tace
"Kul kalmar aibanta iyayena ya sake fitowa daga bakin ki. Dan ko wanda ya haɗamu ni da ke
bai isa ya aibanta iyayena ba. Dan sun yi mishi riga da wanda bashi ni da su kayi. Ko ba haka
ba Gwanda?" Ta ƙarke maganar cikin rausaya murya. Dariyar mugunta Kaila yayi, yana ganin
anzo gaɓar da zai sa Hajiyayye ta fita da ƙafafuwanta." "Ƙwarai kuwa kuwa ɗanyan gwal, Dady ai yayi mun sutura daya bani cikakkiyar buduwa ba ɓari
ba. Ba irin matan da samarin sawo ke luguiguitawa ba. Ga mamannan a cikkike gwanin
banƙawa. Ni mai zance da Dady sai adda'a ai"
"Allah ya isa tsakanina da kai Kaila macuci ka....." Bata ƙarashe zancan ba taga Kaila ya jefa
Bilkisa gado yana neman danneta, da mugun gudu ta fita har tana tuntuɓe, tana tsoron ganin
tsaraicin Bilkisa. Zuchiyarta sai fat_fat take yi. Kai ta gyaɗa tana jinjinama ƙarfin zuchiyar Tani
ita data gansu tsirara ma, kuma ranar kwananta, amman washe gari kamar ma ba'ai komai ba"
Nadamar ba ma Kaila jikinta ya shigeta, yau ga Kaila da su ka watse tare shi yake mata
shaguɓe kuma abun takaicin shine a gaban kishiya. Ta lura sai ta sassauta kishinta zata kai ga
cimma manufarta akan Bilkisa. Amman in ta ga Bilkisan ne sai taji zuchiyarta na ingizata. Sai
dai muce da Hajiyayye kash ta bar kari tun ran tubani daga ranar da ta fisge waya a hannun
Kaila su kai zage_zage da Bilkisa, daga ranar raini ya shiga tsakaninsu babu sauran ragowar
mutunci ( uwayen gida ƙalubale a gareku) Haka dai daren ya kasancema Hajiyayye ko rintsawa
ta kasa yi, tana kwance tana ƙirgen silin ɗin ɗakinta. Yayin da Kaila yake jikin matarshi suna
aikin samun lada. Haka ta ɓangaren Tani ba ta iya bacci ba a wannan dare.
ALLAH YAYI DARE GARI YA WAYE:
SHANONO:
Tun duku_duku nayi wanka fes. Inno ta kama Dauda ta wankeshi tsab, farin ruwan ciwo sai
fitowa yake daga shakirarshi, shi ke haddasa mishi wari mai shiga har maƙogoro. Zuwa karfe
taran safe har mun fito, Yaya Use ce za tai mun rakiya zuwa Jos ɗin. Su Inno kuma sai wa'adin
da suka yanke ma kansu ya cika zasu dawo gida. Sallama mu kai ma kowa a gidan muka fita.
Mashin ne ya kaimu har zuwa bakin titi. Baffa Janaidu bai barmu ba har saida motarmu ta cika
dam misalin sha ɗayan rana Sannan ya tafi. Tunda na zauna a motar nan gabana ke faɗuwa
domin bansan me zan je gidan in tarar ba ma, bansan ta inda zan yi ma Kaila bayani ya
fahimce ni ba. Dauda yana zaune a cinyata, jaririna yana bayan Yaya Use. Sai mutsu_mutsu
Dauda yake yi, baya iya zama waje guda, sabida tsutsotsin dake fitowa a shakirarshi suna ci
mishi jiki, musamman dana sanya mishi ƙunzugu. Hankalina take ya kuma tashi sai kuka.
"Wai meye hakan Tani? Kin tusa yaro a gaba sai aukin kuka kike yi. Kiyi haƙuri kiyi ta mishi
adda'a Allah zai bashi lafiya da yardar sa, harma ya zama tarihi. Kaila kuma kafin in koma gida
zan same shi mu yi magana, dan zan ɗan miki kwana biyu kafin in koma gida. Baban yara ma
bai san ina hanyar dawowa ba." Allah sarki ɗan uwa rabin jiki, ɗan uwa abun wuya. Muna tafe
Yaya Use tana ta bani kalma, sai tausata take yi. Sai na ɗan ji dama_dama a raina kaɗan.
Fargabata yanzu biyu ce. Na farko Kaila ne, na biyu ciwon Dauda ne. Matsalolina na jingenesu
a gefe ba ta su nake yi ba. Domin na yanke ma kaina wani hukunci da nake ganin shi zai fiye
mun alkhairi, kuma hakan zai taimaka ƙila Kaila ya amince yaci gaba da zama dani. Motarmu
sai gudu take yi. Maza da mata sai hira suke yi. Kowa na kalla sai in ganshi yana dariya, ko in
ganshi cikin walwala. Allah sarki walwala ko sai yaushe zata sake kawo min ziyara cikin
rayuwata oho. Ƙila ni da walwala munyi hannun riga har abada. Amman ina fatan ƴaƴana su
dawo mun da walwala cikin rayuwata. Allah ka bani damar da zan dama har in tsaya akan
karatun yarana su zama wani abun. Allah ka dubeni yaran sune kaɗai sanyin idaniyata. Da
yamma sakaliya muka iso tashar farar gada, daga nan muka hau abun hawa zuwa gida, ni dai
gabana sai faɗuwa yake yi kawai, hankalina duk a tashe yake. Da sallama a bakunanmu muka
shiga cikin gidan.
"Shiga ciki ke Tani, Bani keyn ɗakin naki mu mu shiga, bai dace ki shiga da Dauda ciki ba. Ya
kamata Kaila ya fara sani tukunna." Ɗan mabuɗin na bata ta buɗe, ni kuma na shiga cikin
gidan. Hajiyayye tana zaune tana soya miyar tumatur taci uban kwalliya da atampar da Kaila ya
ƙwace a wajena ya bata. Lamarin da ya matuƙar bani mamaki kenan,dan ni sai yanzu ma naga
kyan atampar.
"Me zan gani Umman Sulaiman haihuwa ki kayi kome, naga babu ciki a jikinki? Yaya Use ce ta
shigo ciki da fara'a ta dubi Hindatu da take tambayata, hannunta riƙe da jariri tace.
"Haihuwa tayi, Shanono na biyu yazo. Sannunku da gida mun same ku lafiya?" Hajiyayye tana
juya miya tace.
"Ikon Allah wai na kwance ya faɗi. Ai kuwa bamu ji ko labarin haihuwarnan ba, kuma mai gidan
shi ya sani?" Yaya Use ta dubi Hajiyayye, sai naga ta kalleni da mamaki, nasan bazai wuce
ganin atampar jikin Hajiyayye ba ne. Daurewa tayi tace.
"Ya sani, shine ma yace ta dawo ai"
"Allah ya raya mace ko Namiji?" Cewar Hajiyayye.
"Namiji aka samu, Hauwa an fita daga kan nono" Ta ƙarashe maganar tana yaƙe. Babu wanda
yayi yunƙurin tasowa ya ga jaririn balle su ɗaukeshi, komawa ɗakina mu ka yi.
"Tani atampar jikin Hajiyayye kamar itace atampar da Inno ta bakinnan cikin bikin Sallah ko?"
Yaƙe nayi nace.
A'a irinta ce dai, me zai kai kayana jikin kishiya" Ƙuramin idanu tayi tace.
"Wallahi itace Tani ɓoye mun zaki yi dai kawai. Amman akan me zaki ɗauka ki bata Inno ce fa
ta baki dan tasan baki da wasu kayan fita, dan neman wajan zama shine kika ɗauka kika ba
Hajiyayye matar da bata da burin daya wuce taga zubar hawayenki?" Nasan babu wata ƙarya
dana isa in yi ma Yaya Use, dan tana da ƙwaƙwa sosai, tun sanda muke yara tana da saurin
ɗago abu. Sai kawai na zaɓi faɗa mata gaskiya.
"Kusun uwa har lalacewar taki a cikin gidan ta kai kaila ya karɓi kaya a hannunki ya ba
matarshi, ke kuma da yake lusarace sai kika bata ko, shi bai siya miki ba, wanda aka baki ya
amsa? Bari kiji wallahi sai na sa Hajiyayye ta cire kayannan ta bani. In ma ke ba zaki yi amfani
dashi ba, to itama bata isa tayi ba. Uwarmu ce ta nemo ta bamu domin tanason ganinmu muma
fes. Wato yafi son yaga matarshi cikin ado, ke kuma ko oho." Shirin fita tayi da sauri na riƙo
hannunta tsorona Allah tsorona kar Kaila ya yi zuchiya ya rabu dani, yarana bazan iya barinsu a
gidannan ba. Sannan ina tsoron kar rikicin ya taɓa zaman Dauda a gidannan." Kafin in yi
magana mu ka jiyo sallama da wata siririyar murya. Amsawa Yaya Use tayi, tare da ba da izinin
shigowa. Bilkisa ce ta shigo, tana saye da wasu ƙananun kaya riga da wando na yadi, amman
basu kamata ba, sun yi mata kyau, sai da ta cika ɗakinnan da ƙamshinta dam.
"Sannunku Anty Tani kun dawo? Maraba" Hannu tasa ta karɓi jaririn dake hannun yaya Use,
amman tana ɗaukarshi tayi maza ta miƙa mata shi.
"Masha Allah, Allah ya raya shi, dama ina kwance ne a ɗakin gwanda na jiyo shigowarku shine
nace bari in zo in yi muku barka, ni zan koma"
Nagode sosai Bilkisa, Allah ya saka da Alkhairi" Fita tayi da sauri, nasan hakan na da nasaba
da zarni, da kuma warin da Dauda yake yi, da ƙarnin nono da jaririn shima yake yi. Yaya Use
nai ma kallon kiyi mun rai. Wucewa tayi fuu zuwa tsakar gida, kai na dafe, na zauna a kusa da
Dauda na shiga sauke numfashi. Banaso yaya Use tayi wani abun da zai sake jefa ni a matsala,
kuma in aurena ya mutu sune na farko_farko wajan ƙyamatata da ɗaure mun fuska, amman
yanzu gashi taje tana son yin rigima da Hajiyayye akan kaya. Kuma nasan rashin kunyar
Hajiyayye bana wasa bane.
Fitowarta daga ɗaki kenan Yaya Use ta fito.
"Hajiyayye mu shiga daga ciki zamu yi magana in babu damuwa" Wani kallon banza Hajiyayye
tayi mata dan ta riga da tasan akan abinda tazo.
"Nan ma ai ya isa, babu bare a cikin gidan, ba irin gidanku na haya bane, gidan mai gidanmu
ne. Yawu Yaya Use ta haɗiye tace.
"Tunda haka kika ce ai shikenan. Kayan dake jikinki nake son ki cire mun bakin ki alaikum ki
miko su." Cikin gatsali Hajiyayye tace.
"In kuma ba haka ba fa?"
"Sai in tuɓe ki in ga uban daya isa ya ji dalili dan kutumar ubanki" Ina cikin ɗaki nake jiyo
wannan gurmi. Ba shiri na miƙe.
Dauda ina zuwa kaji ko? Kar ka fito. Da gudu na fito, na samu Hindatu tazo ta shiga tsakaninsu.
"Hindatu ki matsa, ni ba karamin aikina bane in yima Hajiyayye zigidir a tsakar gidannan. Kaya
dai ba nata bane kaya na Tani ne. Ya zama dole ta cire ta miƙo su"
"Ai Kaila ne ya bani, dan haka in kina son a cire miki kayanku, sai ki jira in yazo sai ya bani
umarni amman ba dai ke ba. Kuma ni bazan haɗa kirji dake ba, ni ba fitsarariya bace wacce
take yawo kwararo kwararo na bara, dama ance ƴan jagora basu da kamun kai." Abinda nake
gudu shi yake shirin faruwa. Bilkisa ce ta fito daga turakar Kaila, ita da wata budurwar farar
yarinya sol. Bilkisa ta shige ɗaki ita kuma yarinyar ta soma shanya. Abinda ya ɗaure mun kai
gajerun wandon kaila da singiletinshi take shanyawa.
To wacece wannan kuma? " Ƙaran marin da naji ne ya dawo dani hayyacina. Hajiyayye na gani
dafe da kunci. Hannu Yaya Use tasa ta fincike Hindatu kefe. Dama Yaya Use irin ƙatuwar
macece, gata da ƙiba sosai. Kamo Hajiyayye tayi, nayi maza na shiga tsakani. Hajiyayye na
ganin haka ta kawo naushi ya sauka a gadon bayana. Wallahi sai da ƴan hangina suka motsa
tsabar zafin naushin. Nasan tana sane sarai ta naushe ni. Ni kuma nasan in na barta da Yaya
Use abun bazai yi kyau ba, ga ciki a jikinta." Zagi Hajiyayye ta soma narko mana, tana haɗawa
da su Inno. Idanun Yaya Use ya rufe, nan kokawa ta kaure a tsakani. Jikake tutur_tutur. Ni da
Hindatu muka kasa raba wannan dambarwa, gashi har Yaya Use ta keta ma Hajiyayye riga har
nonuwanta sun bayyana. Kuma bakinta bai mutu ba.
"Shegiya tsinannu masu baƙin jini. Yaran mabarata ƴan jagora karuwai waɗanda suka saba
tambaɗewa" Wannan kalmar yasa Yaya Use ta raɗa Hajiyayye da ƙasa, mazaunanta suka
zauna daɓas a ƙasa zaman daɓaro take jini ya ɓalle mata" Bako ɗankwali a kaina haka na fita
na kirawo maƙota, a guje suka shigo. Da ƙyar aka ɓanɓare Yaya Use a jikin Hajiyayye, ta cire
mata riga da zanin jikinta. Daga ita sai sikel ɗin ciki, nonuwanta gasu a waje duƙwai. Hajiyayye
da taga jini na malala a jikinta sai ta shiga murƙususu tana cewa
"Nashiga uku ta kashe mun yaro a ciki, shikenan sun kashe mun ɗan cikina, a ciki ta dinga
naushina. Na mutu, ku kira mun Kaila" Sabida tsabaragen makirci ba sai Hajiyayye ta sandare
ba, ta soma kakkafe idanuwanta. Ita kanta yaya Use hankalinta ya tashi ainun. Kuma tsoro ya
kamata. Ni kam dama nasan hukunci saki ya tabbata a kaina. Ba shiri aka kinkimi Hajiyayye sai
asibiti, Hindatu ma ta bisu. Duk wannan abun da akeyi Bilkisa bata ko keƙo ba, balle tace kuyi
haƙuri. Gida ya cika da mata, sai ba Yaya Use rashin gaskiya akeyi. Danme zata daki mai
tsowon ciki, a ciki. Ita kuma sai rantsuwar ai ita sam bata daki cikinta ba take ta afkin yin. Jikina
a sanyaye na shiga ɗaki. Sai lokacin na samu zarafin yin kuka.
Shikenan aurena ya mutu. Sai da na hanaki amman kika ƙi hanuwa, yanzu wa gari ya waya?
Allah kaɗai yasan irin sharrin da Hajiyayye zata yi a wajan Kaila. Ba'ayi abu ba ma ta ƙirƙira
tace anyi, kaila ya ci zarafina akai, balle an yin" Yaya Use nan ta shiga zagina tana hargagi.
"Dalla rufa mun baki, ni banje da zummar dukanta ba. Amman wallahi bata isa ta zagi iyayenmu
in tsaya ina kallonta ba. Kina jin mugayen maganganun da take fesarwa, ni zata nuna ma rashin
kunya ina ƴar gajora?" Gani da tayi hankalina ya tashi da yawa ne yasa ta sassauta murya ta
shiga lallashina.
"Ki fito da maganin Dauda a dafa, zuwa anjima ya soma amfani dashi. Wadannan kayan kuma
ki adana."
A'a Yaya Use, ki tafi dasu dai." Jakata na buɗe na bata ƙullin magangunan. Tare muka fita, kurfo
biyu muka ɗaura, ni na ɗaura sanwar girki ita kuma ta ɗaura ruwan zafi. Sabira ce ta shigo da
sallamarta, da alama daga anguwa take"
"Maraba lale umman Sulaiman an dawo? Yaya Use ke aka bari da ɗaura ruwan jegon?" Yaya
Use tayi yaƙe kawai, dan hankalinta baya tare da'ita.
"Tani abunda naji a anguwa gaskiya ne, wai kun haɗu ke da yaya Use kun zauna a ruwan cikin
Hajiyayye zaku kasheta? Wai ranga_ranga aka kaita asibiti, ance ma sai an yi mata tiyata"
Daga ni har Yaya Use salati muka saka, jikina yana rawa.
Wallahi Sabira ba haka zancan yake ba" Nan yaya Use ta labarta mata yadda akayi"
"Hmmm da kin sani baki neme ta da faɗa ba. Muguwar makirace. Kuma kinga Tani a dofane
take a cikin gidannan, wannan maganar zata iya zama babba sosai ta ɓangaren Baban su
Sulaiman dama dangin ita Hajiyayyen, dan na lura yayyenta suna da fitina sosai" Tare muka
haɗu mu ka shiga jimami a tsakar gidannan. Sai zuwa can bayan isha sai ga su Sani sun shigo.
Sai murnar ganina suke yi, ni kuwa sai dariyar yaƙe nake yi musu. Sallama Sabira tayi mana
akan sai gobe zata shigo. Taliya na ɓararraka musu, na baje musu ita a tire.
Yaya maza kuje ku ci, Dauda Yayanku yana cikin ɗaki a kwance bai da lafiya, kuje ku ci tare"
Shafi'i yace.
"Umma dama ba Yaya Sani bane babban yayanmu ba?" Murmushin dole nayi nace.
Dauda ya girmi Sani sosai ma, ɗan uwanku ne ni na haifeshi, kuje ku ganshi " Sani yace.
"Umma shi Babanshi da ban ko?" Wannan maganar ta daki zuchiyata sosai da sosai, amman
haka na kanne nace.
E Babanku ba ɗaya ba. Amman duka ni na haifeku" Shafi'i zai sake jefo tambaya, Yaya Use ta
koresu. Jikin Yaya Use a sanyaye tace.
"Tani je ki watsa ruwa ki fito ki samu kici abinci. In sha Allah sharrin Hajiyayye kanta zai koma.
Kuma banyi da niyyar in jefa ki a matsala ba. Asalima nayi ne domin ƙwato miki ƴanci ta yanda
gaba ba zasu yi miki milkin mallaka ba, daga ita har Baban Sulaiman ɗin. Amman kiyi haƙuri
ƙanwata" zuchiyarta ce ta sake tsinkewa, bance komai ba na je nayo wanka na fito. Hindatu ce
ta shigo da sallamarta. Da sauri na isa kusa da'ita.
Yaya jikin nata Hindatu dan Allah?" Hindatu ta yi mun wani kallon wulaƙanci tace.
"Na baro su an shiga da'ita ɗakin tiyata, sakamakon hallakata da Use ta kusan yi. Ran danginta
yayi zafi, dan sun yi rantsuwar baza su yarda ba. Kinsan dai Hajiyayye da gatanta. Kaila ma
yana hanyar dawowa gidan yanzu" A nan ta tafi ta barni da wannan. Jikina ya mutu murus,
hantar cikina sai kaɗawa take yi. Yaya Use dake zaune da abinci a gabanta, itama tayi kasaƙe
ta kasa ƙara sa loma a bakinta.
"Tani kiyi haƙuri, da sharri suke neman mu shi yasa, ta Allah ba tasu ba. Mu je ɗaki" Hannuna
taja zuwa ciki, yara sai jan Dauda da surutu suke yi. Shi kuma ya takure a kuryar katifa, sai
mutsi_mutsu yake yi.
"Zauna ki daure kici abinci, jego kike yi kin sani. Dauda tawo muje in maka wanka ko ka samu
ƙarfin jikin, sai a shafa maka maganin, ka sha kuma na shan." Hannunshi